Showing 192001 words to 195000 words out of 321579 words

Chapter 65 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

bainar jama'a, suna jin fargaban abun da zai biyo baya, da kuma halin da uban nasu zai shiga, kuma basu son a gurfanar da shi gaban kotu, sun ?wammace su bashi poison ya sha ya mutu, saboda basu son ma su ga tashin hankalin da zai fuskanta, ?wara ya mutu su san babu shi a duniyar, duk da mutuwar ba hutu bace a gare shi, amma su a wurinsu ?wara tun da ba a gabansu zai fuskanci abun da ya shuka cikin kabarinsa ba, amma in yana a raye sun san ba ?yale shi za'a yi ba, dole ya fuskanci mummunan hukunci mai tsanani, ba zasu iya jure ganin halin da zai shiga ba, kuma ba zasu iya kashe shi da kan su ba, sannan basu son ya kashe kan shi, sun rasa ya za su yi da shi?


Duk da fushin da suke yi da shi hakan baisa sun daina jin ?aunar shi ba, kwata kwata ba su son ya wulakanta a idon duniya, duk da sun san ko sun rufa mashi asiri hakan ba zai hana asirin shi ya tonu ba, sannan Allah yana sane da komai, ko sun rufa masa asiri wallahi ba zai tsira ba tun a gidan duniya sai ya ga sakayyar abun da ya aikata, sai Allah ya kamasa, tayaya ma zasu goyi bayan rufawa azzalumi asiri? Bayan sun san Allah baya a tare da azzalumai, sun kuma san hakan ba daidai bane zama su ja ma kansu ne, bayan haka idan har suka nuna son kai, suka nemi su rufa masa asiri ko su 6oye shi, Allah ba zai bar su ba su kansu.




Hajiya Saratu ta yi kuka tamkar ranta zai fita, ta dinga magiya tana ro?on yayyan nata akan kar su tona asirin Baba, kada su mi?a shi ga hukuma, su taimaketa su taimaki rayuwarta, idan ta rasa baba ina zata saka ranta? Su bar shi in har ba so suke zuciyarta ta buga ta mutu ba, lallashinta suka dinga yi suna bata hakuri tare da tunasar da ita akan kuskuren rufa masa asiri, aya da hadisi suka dinga janyo mata inda Allah da manzonSa suka yi magana akan azzalumai amma Hajiya Saratu ta burkice masu, kwata kwata bata ganewa ita kawai mahaifinta take so, ta kasa ganin laifinsa, tama ?i yarda cewa ya aikata, idanunta sun rufe akan son baban nata, tausayin shi ta ke ji, bata son ya tozarta kuma batason a ta6a lafiyar shi, har faWi take ita ta yafe mashi abun da ya yi mata suma su taimaka su yafe mashi, sannan kada su bari a raba ta da shi, tun da yana da sihiri ya 6ace kawai ya nisanta kanshi da duniyar mutane ya je can ya yi rayuwarshi, lokacin da take faWin maganganun nan tana kuka mai tsuma zuciya, ba ?aramin karya masu zuciya ta yi ba, tsananin tausayinta da kaunarta ne ya kama su.


Sun ga juriyarta da ha?urinta, ta basu mamaki baiwar Allah, duk irin zaluncin da baban ya yi mata ita bata gani ba, tama riga su furta ta yafe mashi duniya da lahiri, babu wanda bai zubar mata da ?walla ba a cikin su.

Ta fama masu raunin dake a zuciyoyinsu, in har zasu biyewa son zuciyarsu da halin da Hajiya Saratu take a ciki to kuwa ba zasu bari baban nasu ya fuskanci hukuncin da ya dace ba.


A ?arshe dai gaba Waya basu da wata mafita da ya wuce su mi?a shi ga hukuma, ba yadda suka iya. Sheikh Imam da ya kawo mazu ziyara ya ji komai da ya faru shi ya gargaWesu ya ja masu kunne akan kar su kuskura su biyewa son zuciyarsu, su yi hakuri su rungumi ?addara, su manta cewa shi mahaifinsu ne, su dinga tuna zaluncin da ya yi masu da al'umma ta hakane zasu samu kwarin gwiwar fallasa shi, amma idan suka yi kokarin rufa masa asiri don gudun kada duniya ta ji toh su sani Allah yana a sama yana kallon su, bazai taba barin azzalumi da wanda ya taimaki azzalumai ba, har da nasiha sheikh Imam ya yi masu. A ?arshe ba yadda suka iya, don dole suka mi?a wuya, a halin yanzu basu da burin da ya wuce babansu ya mutu kafin lokacin da za'a gurfanar da su a gaban kotu =?-?




Chief Owais ne ya fara sakin videos din da suka Wauka na Prisoners a shafukan hukumarsu na Instagram, Facebook da Youtube channel dinsu, wanWanda ke da mabiya miliyan dubu Waruruwa daga kowani sassa na duniya.


Yayin da Director Ziyad ya tutturawa manajojin Obie News Network labarin kurkukun ?addara da ya rubuta shi a wayar shi tun daga farko har ?arshe, komai da ya faru a gidan kurkukun kaddara daki daki ya rubuta, ya basu umarnin su fara buga labarin a jaridarsu, sannan su kuma yaWa shi ya shiga ko'ina na duniya.



Yana a gidan radion nasu kiran Chief Owais ya shigo wayarshi, bayan ya Waga ya ce yana gayyatar gaba daya Press corps na ONN, da ?arfe Waya su halarta a Isod Headquarter zasu tattauna da su..



Lokaci na cika motocin shahararrun ?an jarida suka fara tururuwar shigowa isod headquarter.


Wasu ru?e da Camrecorders, wasu sun ru?e Michrophones..
A katafaren Comference Room na headquarter din suka gudanar da taron..


Gaba daya senior agent suka hallara, tun daga DG, CI, Coo, Senior Agents, U.s armies, General Noah, kusan duk mai ruwa da tsaki a binciken Kurkukun ?addara sai da ya hallara a comference room din Taj ne kadai bai samu zuwa ba.


A saman kujeru kowan nan su ya zauna yayin da manema labarai suka kewaye su.


Bayan sun gabatar da junansu, U.s Armies ne na farko da suka fara bada labarin farkon haWuwar su da Prisoners din da suka ku6uta daga kurkukun kaddara har suka haWu da su a dajin evil forest.


Bayan sun gama, Chief Owais ya daura da nashi tun daga farkon ta yadda U.s Armies suka tuntu6e shi da case din yaran, ya bayyana masu yadda ya ji farkon da abun ya riske shi, bayan ya Wan dakata team members din shi suka Waura da nasu bayanin game da Kurkukun kaddara..


Daga bisani Chief Owais ya bayyana masu ta yadda suka fara gano su wanene Elders, Ya ilahi! Ilahirin press corps din dake agurin saida suka razana matu?a, jin abun da basu ta6a zata ba, hankalinsu ya fi karkata akan Chief Owais, saboda kansu ya Waure sosai, mamakin su ta yadda har ya iya tonawa kakansa asiri da kan shi!!!

Gaskiyarshi ta yi matu?ar razana su.

Lokacin da yake lissafa sunayen Elders, tsantsar rudani ne da razana suka bayyana ?arara a cikin idanun manema labaran dake a kewaye da su, zan iya cewa tun da suke daukar rahoto basu ta6a daukar labari mai girma da razanarwa da kuma karya zuciya irin wannan ba! Abun ya ta6a su matu?a.


Duk wani abu da suke tattaunawa kaitsaye mutanan duniya suke kallon shi, wasu ta tv dinsu, wasu ta radio, wasu ta facebook live, wasu a instagram live, kai ko'ina fa labari ya bazama.


Bayan da suka gama fallasa komai da ya kamata mutane su sani, manema labaran suka fara yi masu tambayoyi suna amsa masu ba tare da jin shakka ba.


"Yallabai, ya kuka ji kaida ahlinku lokacin da asirin kakan ka ya tonu?"

"Yallabai, wani hali kuka shiga da kuka ji kakan ku shine Shugaban kurkukun kaddara?"



"Yallabai zamu iya sanin ina Elders suke a halin yanzu?



"Yalla6ai, ba ku tunanin fallasa asirin kakanka da ka yi zai shafi ahlinku da mu?aman su?"


"Yalla6ai gaba Wayan mu mun kasa yarda da bun da kunnuwanmu suka jiyo mana, saboda rudanin da muka shiga, shin da gaske kakanka dattijon arzi?i yana da sa hannu? Mutum mai ?ima da daraja a duniya, wanda kowa ke girmamawa?


"Yallabai ko zamu iya sanin ina fursinonin kurkukun ?addara suke? Mun dai ga video dinsu amma bamu san a wani hali suke ba, da bu?atar a bamu damar tattaunawa da su."


"Sir, ina Zaheer Tajuddeen da Uzair? Zamu iya ganawa da su? Saboda ?an jaridar mune ta jihar Joss da muka nema muka rasa tsawon shekaru, muna ta neman su ruwa ajallo!"


Tambayoyi iri iri ?an jarida ke yi mashi.


A lokacin Owais ya yi rauni, idanunshi sun kaWa jawur, yana mai jin ba?in cikin fallasa asirin Grandpa dinsa da ya yi, amma ya zai yi? Baya da mafita da ya wuce wannan! Ya zama dole mutane su ji miyagun laifukan da ake aikatawa a doron ?asa ko dan su Wauki darasi, su kuma ?ara imani da tsoron Allah su kuma kiyaye kan su.


Gaba Waya kowa dake a gurin saida ya fahimci halin da yake a ciki, da ido abokansa suka dinga kwantar masa da hankali tare da dafa kafaWunsa suna Wan ?arfafa mashi gwiwa don ya jure.


Ji yake kamar an Waura masa nauyin duniya akansa, dauriya kawai ya ke yi.


Cikin sanyi murya mai rauni ya soma magana cikin harshen turanci,



_"Bazan iya misalta halin da family din mu suka shiga ba a lokacin da muka gano dasa hannun jagoran family dinmu, ko ban fada maku ba, kun sani, kowan nan ku zai iya ?iyastawa a ranshi ya radadin abun yake idan wanda ka yarda da shi ya karya maka zuciyarka? Mun shiga mawuyacin halin da ba zai musaltuba! Ina fata mutane zasu yi mana adalci, kada su tuhume mu ko su zarge mu akan laifi da kakanmu ya aikata, kuma kada a juya mana baya ko a tsangwami ahlinmu saboda bamu da laifi, bamu san komai ba saida asirinsa ya tonu, in har aka daura mana laifin kakanmu zamu shiga mawuyacin hali fiye da wanda muka shiga. Ina ro?on mutane da su agaza mana, su tausaya ma rayuwar ahlinmu, kada wannan abun ya zama silar da za'a dinga cin zarafin mu! Komai da ya faru da mu, mu?addari ne daga Allah, dama can rubutacce ne, kamar yadda bamusan komai ba, toh haka kowa ma zai iya faruwa da shi. Dalilin da yasa na fito bainar jama'a tare da abokan aikina na fallasa komai saboda hakkinku ne ku sani, bamu 6oye maku komai ba, saboda muna so ku ji kuma, don ku ?ara imani ku kuma Wauki darussa daga labarin kurkukun ?addara, duk kuma wani mai aikata wani laifi a 6oye ya ji tsoron Allah ya daina tun kafin asirin shi ya tonu"_



"Akwai wanda ya tambaye ni, ba mu tsoron fallasa asirin kakanmu da muka yi ya shafi ahlinmu da mu?aman su?"

Ya faWa da murmushi akan fuskarshi, girgiza kai ya yi ya ce, "babu tsoro ko fargaba a tare da mu, kafin mu fallasa asirin saida muka yi wannan tunanin, amma bashi ne damuwar mu ba, saboda ba duniya muka zo nema ba, komai da muka mallaka a gidan duniya zamu bar shi, in har za'a yi mana adalci, bai kamata a tuhume mu ko a Waura mana laifin da bamu muka aikata ba, laifin wani baya shafar wani, bayan haka koda wasu sun zarge mu akan abun da ya aikata ina so su sani koda zai shafi mu?amanmu ba zamu damu ba, saboda idan muka mutu daga mu sai halin mu za a binne mu, mu?aman mu baza su cece mu ba, halinmu shi zai cece mu. Mun yi imani da Allah, kuma mun yi imani da ?addara mai kyau da mara kyau, kuma mun san abun da ya faru da mu jarabawa ce daga gare shi, Allah shine shaidar mu, koda wannan abu zai shafe mu ba zamu damu ba, mun san dole akwai waWanda ba zasu fahimce mu ba, akwai waWanda kuma jiran rauninmu suke yi don su muzguna mana, to ina so su sani babu gudu babu ja da baya, ba zamu ta6a karaya ba, saboda Allah shi zai yi mana hisabi ba su ba, duk wanda yayi yun?urin yin amfani da wannan damar don ya 6ata mana suna ko dan ya 6ata mana rai toh ya sani Allah yana kallonsa zai yi mana sakayya, akwai kuma ranar ?in dillanci. Bayan haka, duk abun da kasan in akai maka ba zaka ji daWi ba toh kada ka yi ma wani, kuma ka guji 6ata ran wanda baida abun dogaro da ya wuce Allah, ko don saboda fursinonin kurkukun ?addara yakamata mutane su san irin kalaman da zasu furta idan ba haka ba wani hali kuke tunanin zasu shiga? Idan ana fama masu raunin dake a zuciyar su? Da yawa waWanda suka sadaukar da su iyayensu ne, wasu kawunnansu, wasu danginsu, na sani a cikin masu kallo na da sauraro na, akwai iyaye, akwai kawunnai, akwai yayye da ?anne, kunsan ?uncin da ake ji idan aka ta6a naka ko aka ci zarafinsa, da wannan nake ro?on kowan nan mu da mu kiyaye harshen mu, gaba Wayanmu bamu ke da iko da kawunanmu ba, abun da ya faru da wani mara daWi ka ji dadi ko ka yi dariya kaima baka wuce ya faru da kai ba, don haka idan har ba zamu faWi alkhairi ba, ya fi mu ja baki mu yi shiru..."


Kalaman Chief Owais ya ta6a zuciyoyin miliyoyin jama'a dake kallon su, ta ko'ina comments Win mutane ne ke ta yawo a social media..


"A halin yanzu, gaba Waya fursinonin da muka ku6utar suna a ?ar?ashin kulawar mu, in sha Allah zamu duba yiyuwar baku damar tattaunawa da su kaitsaye, bayan mun gama shari'ar Elders, bayan haka zamu buWe shafukan da zamu dinga kawo maku duk wani abu da ya shafe su" CI ne ya amsa ma Wan jaridar da ya yi tambayar..

"Elders suna a tsare hannun hukumar mu, ba zaku samu damar ganawa da su ba, har sai zuwa lokacin da za'a yi shari'ar su, zamu ci gaba da kawo maku bayanai game da su, ku ci gaba da bibiyar shafukan hukumar mu ta ISOD" Coo ne ya faWa yana mai tabbatar masu da maganar shi.



A ?alla saida suka shafe awa suna tattaunawa da manema labarai tun suna amsa masu tambayoyi da marmari har saida suka fara galabaita.



In a short time, labarin Kurkukun ?addara ya bazu kamar wutar daji, ?an jarida, gidajen talabijin, gidajen yaWa labarai na duniya, da kuma shafukan sada zumunta sun cika da labarin kurkukun ?addara, BBC ne, Fox news channel, Cnn, msnbc, Newsmax, ko'ina zancen Kurkukun kaddara ake yi, labarin ya zama ruwan dare, Elders suna ta shan tsinuwar jama'a, DG da hukumarsu tana ta shan yabo daga bakunan al'ummar duniya, kowa ya jinjinawa kokarinsu musamman Dg da ya iya fallasa asirin kakansa, ya burge jama'a ya kuma siye zuciyoyin mutane, ta ko'ina yabonsa ake yi, mutane suna ta nuna tausayawarsu ga Prisoners, ba a ta6a samun labarin da cikin rana Waya ya samu billions of audience daga sassan duniya ba irin shi=?%?

Ta ko'ina shafukan sada zumunta sun cika da hashtag

# JusticeForTheVictims#justicefortheprisonersoftheprison ofdestiny #RemoveThemFromPower#punishthem#justicemustbeserved#


Hada masu zanga-zanga ta online, wasu ma fitowa suka yi daga gidajen su, suka bazama kan tituna, inda suka bu?aci a yiwa fursinonin kurkukun ?addara adalci, a ?wace wa Elders mu?amansu, a kuma gurfanar da su gaban kotu don su kar6i sakamakon laifukan da suka aikata.


Hukumomin Human Right na ?asashe daban daban kama daga Uk, America, Saudi arab da sauran ?asashe sun buWe wuta akan a hukunta Elders daidai da abun da suka aikatawa yaran da ba su ji ba basu gani ba.

Haka zalika shuwagabannin ?asashen ?etare da aka samu ?an ?asar su cikin Elders da Prisoners suma sun buWe wuta akan ba zasu lamunta ba, sun yi gargaWi akan a gaggauta yankewa Elders tsattsauran hukunci a kuma mayar masu da yaran ?asarsu da aka fitar, bayan haka zasu bibiyi shari'ar har sai sun tabbatar da anyi adalci, idan ba haka ba zasu Wauki tsattsauran mataki.


Gaba Waya hankalin duniya ya dawo kan Elders da Prisoners, abun ba iya Nigeria ya shafa ba, saboda Elders Win da fursinonin akwai jinsin wasu nahiyoyin..


WaWanda suka fi shiga tashin hankali dangin Elders, Mutane sun fusata hakan ya sa jinin su akan akaifa ya ke, neman su suke ruwa a jallo don su fanshe abin da aka yiwa fursinonin kurkukun ?addara, ba dan sojojin dake kewaye da gidajansu ba, da tuni mutane sun sanya musu fetur sun ?one su, ko su saka masu bomb saboda yadda suka zuciya, burinsu su yi arba da Waya daga cikin su don su ?one shi.



Lokacin da labarin abun da ke faruwa ya riski jam'iyar su Alhaji Musa, a lokacin ma suna tsaka da yin party meeting a conference room na headquarter dinsu, kwatsam sai ga kira ya shigo layin party leader Winsu Alhaji Bukar mai Guduma, bayan da ya Waga kawunsa ya ce su duba abun da ke faruwa a labarai.

Nan fa suka kunna news, hankalinsu ya tashi matu?a sun razana da jin labarin kurkukun kaddara, babban tashin hankalinsu hada Wan jam'iyarsu Alhaji Musa, shine abun da ya fi razanar da su ya kuma jefa su a ruWani sosai, sun yi ba?in cikin kasantuwarshi Wan jam'iyar su, ya ja masu tozarci da tsana daga al'umma dama basu da farin jini, wannan abun kunya da firgici har ina, gaba Waya sun yi Allah wadai da Elders, duk da ba?in cikin da Musa ya ?unsa masu hakan bai hana sunyi farin cikin jin cewa hada Baba Obie a ciki ba, dama da haushin shi a cikin zuciyarsu, tun lokacin da ya bar jam'iyarsu ya kafa tashi jam'iyar suke ta neman hanyar da zasu 6ata mashi suna su kuma lalata jam'iyar tashi, sai gashi cikin sau?i yanzu sun samu damar da zasu 6ata ahlin Obie da jam'iyar su.


Haka zalika ?an jam'iyar APP ta su baba Obie, sun tashi da mummunan labarin da ya karya zuciyoyinsu, ya haifar masu da matsanancin tashin hankali da damuwa..



Ha?i?a baba Obie ya karya zukatan mutanan da suka yarda da shi, kowa idan ya ji labarin da farko sai ya sanya kokwanto akan ba zai iya aikatawa ba, amma daga sun ga videos Win Chi??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ef Owais da yake kora jawabi sai jikinsu ya yi sanyi lakwas, saboda sun san jikanshi ba zai yi mashi ?arya ba.



Bangaren masu ruwa da tsaki a mulkin ?asar sun razana da jin labarin kurkukun kaddara, sun kuma Wimauce da jin cewa dattijon arziki uban maza, mutun mai daraja da ?ima a idon duniya shine shugaban kurkukun kaddara, kan wannan al'amarin har zaman tattaunawa suka yi a majalissa kowa ya tofa albarkacin bakinsa kan al'amarin, wasu suna


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login