Showing 198001 words to 201000 words out of 321579 words

Chapter 67 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

hankali Chief Owais ke duban fuskar Praveen da ya sadda kanshi ?asa cikin tsananin tashin hankali da fargaba, gaba Waya babu nutsuwa a tare da shi ga rashin koshin lafiya, la66ansa sun kumbura suntum, gefen idonshi na dama ya kumbura harda kwantsa a cikin su, gaba Waya jikinshi a kumbure yake ga tarin raunukan da ya ji sakamakon bugun da su Sir mubarak suka yi ma shi, har yau bai dawo daidai ba.

Bakomai chief yake kallo a cikin idanun shi ba face tsantsar tsoro, firgici, da damuwa mai haWe da ?unci da ba?in ciki, saboda nauyin Chief Owais da ya ji ya sa shi kasa jure kallon shi.

Girgiza kai Chief Owais ya yi, "Praveen, Allah ba azzalumin bawanSa bane sai dai bawa ya zalunci kan shi. Me ya ja maka Praveen? Ma ya kai ka aikata miyagun laifukan nan? Meyasa ka biyewa son zuciyarka da son abun duniya wanda zamu mutu mu barshi duk min daren daWewa?" Girgiza kai ya yi cike da danasani ya ce, "Bada son raina ba, ba halina bane, sharrin shaiWan ne da sharrin zuciya, nasan ina da son kuWi sosai, zan iya komai don in samu kuWin da zan rufa mana asiri ni da ?ar uwata, amma wallahi ban ta6a kisan kai ba, sai da na haWu da Obinna..."

Bai ?are maganar ba ya dakatar da shi, "Ka iya kuma cin zarafin mata ko? Ko ka yi tunanin bamu ji abun da kake ma ?an aikin gidanmu ba? Ka dinga masu barazanar za ka sa a kore su daga aiki duk don ka samu su baka haWin kai, bayan haka kaine ka yi silar ciwon marwa..." Cike da tsana ya ke kallon shi.



"Dama can babu imani a zuciyarka Praveen, baka da tausayi kuma kai Win mugu ne, ?ar uwarka kaWai kake tausayi, grandpa ya faWa min duk wanda suka saka a kungiyar kurkukun ?addara da son ran shi...."

Sunnar da kan shi ?asa ya yi.


"Ka faWa min tayaya akai ka haWu da Saratu? Da kuma yadda akai baba ya sanyaka a ?ungiyar kurkukun ?addara? Karka ce zaka yi min ?arya ko ka 6oye min wani abu, ?ar uwarka tana a hannunmu, idan ka yi laifi ba kai zamu hukunta ba, ita zamu hukunta.." FaWuwar gaba ya ji, a ruWe yake duban Owais da jajayen idanunsa..

"Na ro?e ka, kada ku ta6a Hajjaty, bata da laifi, batasan komai ba, na ji zan amsa maka tambayoyin ka.." Murmushin gefen fuska Owais ya saki, ya fahimci Hajjaty ce lagwon shi.


dakyar ya ke magana yana sakin nishi.

"Farkon haWuwa na da hajiya Saratu a restaurant Winmu ta zo cin abinci, ni na je kai mata abincin, kawai saboda na goge cokali da rigata ta falla min mari, ta sanya hannu ta 6arar da kayan abincin ?asa, ta soma zazzaga min masifa tana faWin shiyasa bata cika son cin abincin indiya ba ?azamai ne mu, ?as?antattu marasa hankali.."


A lokacin na ji zafin marin da ta yi min, raina ya 6aci da kalamanta amma ban nuna ba, saboda na hango agogon hannunta ta zinari ce, bayan haka ni ina girmama masu kuWi koda zasu wula?anta ni ne indai zan samu abun da nake so.


Har zata tafi na ce mata ta 6arar da abinci bata biya kuWin ba, cikin fushi ta tura hannu cikin handbag Winta, ta zaro dala Wari Wari bama na kuWinmu rupee ba ta watsa mini kan ?irjina ta juya ta fuce, na shiga washe baki ina tattara kudin da suka zube a ?asa, wanda a ?alla a kudinmu na indiya sun kai dubu Wari biyar, nan fa na fara tunanin ta wace hanya zan ?ulla ala?a da ita? Tun da na fahimci tana da arzi?i kuma ?ar masu kudi ce.



Daga nan saina fara bin diddiginta, tun a ranar da ta shige motarta na bi bayanta da mai abun hawa, na ga ta shiga Medical University, a nan na fahimci Waliba ce ta zo karatu daga wata ?asa, saboda na lura ba jinsinmu ba ce.


Da na ci gaba da yin bincike akanta saina na gano ?ar Nigeria ce, kuma ta fito daga babban gida na masu arzi?i, a jami'ar babu wanda ya isa ya taka ta ya zauna lafiya, tun daga Walibai har malaman shakkar 6ata mata rai suke, ita kuma bata da mutunci, ta ?ware gurin bullying Win mutane. Na Wauki lokaci ina shawarar ta yadda zan shiga jikinta, a ?arshe dubara ta faWo mini a rai, na haWa baki da abokaina na sa su farmaketa akan hanyarta ta dawowa daga makaranta zuwa gidanta da take zama don na gano ba a hostel take ba, katafaren gida gare ta harda masu aiki da masu tsaron gidan amma bata da driver ita ke driving da kanta saboda bata son ana sanya mata ido idan zata fita, a yadda na ji.."

Ya Wan dakata yana mayar da numfashi.



Dg ya nutsu yana sauraron shi.


"A ranar da ta fito daga school cikin motarta, batasan muna a biye da bayanta ba saman baburan mu, idan ba zan manta ba wuraren ?arfe biyar na yamma ne, akan idon mu ta shiga gym, har lokacin da ta fito ta shige motarta, ta kuma nufi mall ta shiga, duk muna biye da ita, har sai wuraren ?arfe takwas na dare sannan ta nufi hanyar komawa gidanta, kasantuwar ba jama'a layin da ta shigo, nan muka samu damar farmakarta, abokaina suka fara tarar motarta, suka tsoratar da ita da addunan hannayen su, dama plan ne muka shirya mata, suka yi mata barazanar zasu yi mata fyaWe sannan su kashe ta, cikin ruWu da tashin hankali ta ce su kyaleta ta tafi kar su kuskura su ta6a ta, idan ba so suke su rasa rayukan su ba, idan ma kuWi ne suke so tana da su zata basu ko nawa suke so, amma kar su ta6a lafiyar jikin ta, saida na bari sun fara ?o?arin raba ta da kayan jikinta tukunna ni kuma na fito daga inda na la6e na nufe su da tsawa na ce, 'Kar ku kuskura ku ta6a ta, idan ba so kuke ku rasa rayukanku ba!' Ina ?arasawa muka cuWanya da su faWa ya kaure a tsakanin mu, ta yi ta mamakin yadda na dinga bugun su, ni Waya na bubbuge su, har sai da suka arta a guje suka bar arean wurin.


Kwata kwata bata gane fuskata ba, dama ranar da muka haWu a restaurant bata yi min kallon arziki ba, a lokacin ban wani nuna za?ewa ba, ina haki ina gyara hannun riga ta na dube ta na ce, 'Ki kiyaye fita a irin wannan lokacin, idan ba haka ba, 6ata gari zasu lalata maki rayuwa' Kamar dai yadda jaruman film Win indiya suke yin acting, na juya zan tafi ta yi saurin shan gabana, duk da girman kanta saida na burgeta still wani kallon ?as?anci ta ke bina da shi ganin suturar jikina irin ta marasa galihu ce, cikin sanyin murya ta ce min ta gode da taimakon da na yi mata, ba don ni ba da tuni sun yi nasarar cutar da ita. Na yi murmushin gefen fuska ganin plan Win mu na aiki, na ce mata kar ta damu na saba taimakon mutane, kawai ta bi shawarata.


Ta ce min meye sunana? Kuma a ina nake da zama..
Na ce mata Praveen, ina a layin dake a gaban nasu.
Ta ce ta yi mamakin ?arfina, ta yi zaton abun da take gani a indian movies ?arya ne, amma yau ta ga zahiri.." Na yi dariya, daga nan ta ce min in ba damuwa mu yi musayar number, idan tana bu?atar taimako zata dinga kira na, jikina na 6ari na bata number wayata, bayan mun yi rabu na je muka haWu da abokaina mu kai ta murna kowa ya fara hasasho kuWin da zai samu.


Sai da na jera kwanaki ukku ina tura mata abokaina su farmake ta, kuma a duk lokacin da suke zuwa ni ke taimakonta, bata ta6a gane cewa nike turo mata su ba, idan ta tambaye ni ya akai a duk lokacin da miyagu suka farmaketa nake zuwa kamar aljani? Na ce mata saboda na damu da ita shiyasa nake bin diddiginta. Daga haka sha?uwa ta fara shiga tsakanina da hajiya Saratu, ko da ta nemi sanin dangina na ce mata bani da kowa sai ?ar uwata Waya mu marayu ne, asalin danginmu masu arzi?i ne, silar hatsarin jirgin ?asa muka rasa kowa namu, wanda kuma ma?iya ne suka farmake mu a cikin jirgin ?asan suka kashe kowa sai ni da ?ar uwata kaWai muka rayu, tun daga nan rayuwa ta sauya mana muka koma marasa galihu.

A lokacin ta tausaya min sosai, har ta ce min zata taimaka mana.



Sannu a hankali soyayya ta fara shiga tsakanin mu, muka sha?u da juna, bata ta6a tambaya ta game da ?ar uwata ba, kuma bata ta6a zuwa inda nake ba, sai dai ni in je gidanta, sai da ta kaiga nine drivern dake tu?ata duk inda zata je saboda in dinga bata kariya.


Lokacin da ta kammala karatu, makaranta ta shirya masu graduation celebration, mahaifinta ya zo delhi, a gidanta ya sauka, ta kira ni a waya tana murna ta faWamin daddynta ya zo daga Nigeria tana so in zo mu haWu, amma bata so in sanya kayan yan jagaliya, in nemi kaya masu kyau cikin waWanda take siya mun in saka saboda mahaifinta babban mutunne mai arzi?i da duniya tasan da zaman shi, idan har ya gano wanene ni zai raba mu ne, na ce mata toh.



A ranar da zan je, na Wauki wanka na mutunci na je gidanta, a falo na zauna, masu aiki suka kawo min lafiyayyan abinci, daga bisani ta fito tare da daddynta, kallo Waya da na yi masa saida gabana ya faWi saboda kwarjinin da ke gare sa, da kallo Wayan na fahimci hamsha?in mutunne.



Jiki na a sanyaye na mi?e muka gaisa da shi cikin harshen turanci.

Mun yi fira da shi kaWan, bayan Saratu ta gabatar mashi da ni, ta kuma faWa masa abun da ya faru da danginmu da kuma taimakon da na ke yi mata, ya nuna jin daWinsa sosai, da zan tafi har kyautar agogo ya bani mai tsada.


Bayan dana dawo ni da abokaina muka je kasuwa muka siyar da agogon, mun samu kudi sosai, muka raba kuWin ni da su, nawa kason na je kasuwa nayi ma Divya siyayyar kayan sawa.


Lokacin da Hajiya Saratu zata koma Nigeria, ta ce min in har ina so mu auri juna dole in biyota mu tafi Nigeria in ga danginta, sannan koda zata aure ni, sai dai ni in zauna a ?asarta amma ita bazata iya zama a india ba.


Abu Waya ne damuwata, ?anwata da zan tafi in barta, kuma ina son in tafi saboda nasan idan na bi Saratu zan yi arzi?i sosai, hakan yasa na yanke shawarar bin ta.


Bayan da mu ka zo Nigeria, kawunnanka sun nuna ?in amincewarsu da auren mu, ?iri ?iri suka nuna min tsana da tsangwama saboda ni ba jinsinsu bane kuma bani da asali, bayan haka basu yarda da ni ba, duk na bi na tsargu amma saboda mahaifinku ya tarbe ni da hannu bibbiyu ya nuna min ?auna yasa na saki jikina na ba banza a jiyar su, bayan kwanaki da zuwa na gidan ku, baba Obie ya kira ni a part Winsa mu biyu muka zauna muna fuskantar juna.

Ya ce min yasan komai game da ni da kuma rayuwata..

A ruWe na kallesa na ce bangane me yake nufi ba,
ya yi murmushi ya soma zayyana min tarihin rayuwata tiryan tiryan, gabana ya faWi na bi na ruWe jin ya gano komai game da ni.

Ya kuma cewa yasan ni nake saka abokai na su farmaki Saratu don in kawo mata taimako, meyasa na ke yin haka?

Da mamaki na ce masa tayaya akai yasan duk wannan?

Ya ce min Saratu autar shi ce, yana sonta fiye da komai, kuma duk wanda ya ra6e ta yana bibiyar rayuwarsa saboda baya son abun da zai cutar da ita, ta yadda akai yasan komai game da ni da kuma manufata, abokaina yasa yaransa suka kama, ya basu za6i kodai su faWa masa komai game da ni ya biya su kuWi, ko kuma ya basu kashi kuma su faWa ta tsiya, sai suka za6i su faWa masa komai don ya basu kudi.

Bayan da ya kai min ?arshen maganar tashi ya tambaye ni meyasa na yi haka?
Ganin ya gano komai yasa na bayyana masa manufa ta, na ce saboda ina son in yi arzikin da zan kula da rayuwar ?ar uwata, saboda ita na ke yin komai.


Anan ne yake faWa mun zai yi min hanyar arzi?i mara yankewa, kuma zai bani auran Saratu harma da gurin da zamu zauna ni da ?ar uwata, zai Wauki Wawainiyar cin mu da suturar mu, sannan zai sama min aiki a kamfaninsa amma bisa sharaWin zan yi komai ya ke so!

Na yi murna mara misaltuwa na ce masa na amince koma menene zan yi ya faWamin kawai, ya ce min na tabbata zan yi? baya son na yi danasani daga baya, ko in nuna bazan iya ba, na ce masa aini in dai akan kuWi ne zan iya komai amma banda kisa, ya saki shu'umin murmushinsa. Bayan da ya faWamin komai game da kurkukun ?addara, na razana, hankalina ya tashi, na bi na ruWe na ce bazan iya ba rashin imanina bai kai nan ba, ina jin tsoron in jefa rayuwata da ta ?ar uwata cikin haWari, ni dai ya yi hakuri ya barni in koma India zai fi min kwanciyar hankali.



Dariya ya yi ya ce ai nama riga dana shiga ?ungiyar kurkukun ?addara tun da har na matsa ya faWa min, kuma nasan sirrin su, kodai in amince ta lalama ko kuma ya kashe ni sannan ya kashe ?ar uwata Divya, za6i ya rage nawa.


Ba yadda na iya, da na zauna na yi tunani, zuciyata ta raya min in amince masa ko don saboda al?awarukan da ya ce zai yi min.

Hakan yasa na amince, nima na zama member na kurkukun ?addara, daga bisani da likafa ta ci gaba, ya mayar da ni cikin Elders saboda yana so na, kuma yana nema na.


Runtse ido Chief Owais ya yi wata kibiyar ba?in ciki ce ta soke shi, cikin rawar murya ya furta, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..."

Praveen duk ya sha jinin jikin shi ganin irin fusatar da Owais ya yi.


"Daga baya, shine ya bani iznin in kawo ?ar uwata gidan bayan da na faWa masa na aureta hada yaron mu Waya, ya ce min idan ta zo baya son kowa yasan komai tsakanin mu, zata kasance yar aiki saboda baya son Saratu tasan tana da kishiya, kuma baya son asan ala?ar dake a tsakanin mu, shi kuma yaron mu baison kowa yasan da shi, saboda sadaukar da shi zan yi..."

Kasa ?arasa maganar ya yi idanunsa na tsiyayar da ?walla.


"Ka zalunci kanka Praveen, meyasa lokacin da ya nemi ya jefa ka a gur6atacciyar harkarsa baka ?i amincewa ba? Meyasa baka faWa ma wani ba ko ka kaishi ?ara gurin hukuma? Kai wlh da dai irin wannan musibar ?wara ka bari ya kashe ka kai da ?ar uwar taka sai ya fi maku kwanciyar hankali!" Cikin fushi ya ?are maganar.

"Kaima ka sani Owais, kakanka ya fi ?arfina, wlh babu wanda zai yarda da ni koda na faWa, kuma ban isa in gudu ba, bayan haka hada son abun duniya ne ya rufe min idona, amma ko a cikin Elders ni kaWai ne mai rauni, ban ta6a kisan kai da son raina ba..."


cikin ?unci ya ?are maganar tasa.


"Owais ku taimaka mini, ku rufa min asiri, wlh na tuba, na yi danasanin hali irin nawa, na kuma yi danasanin sanin hajiya Saratu a rayuwata, saboda mahaifinta ne silar komai, Hajjaty bata da kowa in ba ni ba, ina jin kunyar tasan abun da na aikata.." Ya ?arashe maganar yana kuka kamar ?aramin yaro..

Ko kaWan Owais bai ji tausayin shi ba, amma ta wani wurin ya Wan tausaya mashi saboda kakansa ne ummul aba'isin komai amma shima mai laifi ne.

"Bayan kasan kai mai laifi ne, maimakon ka mi?a wuya cikin lalama, sai ka zagaya ta bayan fage, kaje ka Wauki yar uwarka don ku gudu, da hajiya Saratu ta ritsa ku shine ka huce haushinka akanta, ka yi mata bugun kawo wu?a, in ban da kai Win mugu ne, mara hankali, ba kai tunanin ?a'?anka ba? Ita wadda ka cutar ba uwar ?a'?anka ba ce? Koda ba don Allah ka aureta ba, baka tunanin wani hali ya'yanku zasu shiga? Wani irin uba ne kai mai son kai da zon zuciya?" Du?ar da kansa ?asa ya yi, hawaye nata sintiri kan kuncinsa.



"Ko kakanmu da ya kasance azzulami bai gudu ya bar ahlinsa ba, saboda soyayyar mu yasa shi mi?a wuya, kai fa?" Ya faWa cikin 6acin rai.


"Ka so ka kashe ta Allah bai nufa ba ta rayu.. " Gabansa ne ya faWi a razane ya ke duban Owais..

"Bayan da ta ji sau?i, mun faWa mata mun kama ka zamu kawo ta gurinka don ta Wauki fansar abun da ka yi mata, kasan me ta ce?" Jikinsa a sanyaye yake duban Owais..

Ipad Win hannunsa ya daddana, kafin ya juyo masa da screen Win ta, wata irin kunya ce ta lullu6esa ganin Hajiya Saratu a zaune kan gadonta, fuskarta duk tabo, video call ne Owais ya kira ta, tana kallon Pravin da ya muzanta ya kasa haWa idanun shi da nata.



Murmushi ta sakar ma shi,


"Ka aure ni saboda dukiyata, da kuma sura ta ko? Dama masu iya magana sunce kwaWayi mabuWin wahala ne, yanzu wa gari ya waya Pravin? Kana tunanin makomarka kuwa? Mutum mai tarin zunubi irin ka, wlh ka mutu Praveen, ka kashe kanka da kanka, kana cikin musiba. Zafin cin amanar da ka yi mini, ya fi b???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ugun da ka yi min raWaWi a gurina, na yi danasanin auranka, na kuma yi danasanin haifa maka ya'ya da har ka samu damar sadaukar da wasu azzalumi, kaima ka sani, nima ban ta6a sonka ba, na aureka ne, saboda makircin da ka ?ulla min don ka ci arzi?i, kuma ba zan rama ba, na yafe maka, ka ji da hukuncin da kotu zata yanke maka, da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login