Showing 276001 words to 279000 words out of 321579 words

Chapter 93 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

ke yi saboda tsantsar bacin rai, har wani gurnani yake fitarwa..

wani irin faduwar gaba taji, Hankalinta ya tashi matu?a.

kallon kallon su ke jefawa junansu sam ya kasa magana, tun da taga ya kawar da idanunsa daga kallonta ya mayar da su akan akwatinan karfen da ke a kasa da buhunbuhunan makaman da tabari, nan fa tasha jinin jikinta, zufar tashin hankali ta fara wanko mata fuska, adabarbarce ta furta"E..el..elder...."

bata karasa maganar ba, Ya daka mata tsawa tamkar zai fasa dodon kunnanta, Yana huci cike da bakin Ciki Yace"kin bani mamaki! Dake za'a haWa baki a ci amanata? nayi kuskure dana barki araye tun farko.."

duk da tsoron shi da take ji hakan bai hanata yin karfin halin cewa"kamar yadda nima ka bani mamaki Obinna, kaine ka fara cin amanata tun farko.."!


bata ?arasa amayar da abunda ke aranta ba, taga ya nufota gadan gadan Jiki na bari ta soma ja da baya, zagaye dakin suka dinga yi, ta soma yin tsalle tana hayewa kan tukwanan kasan dake adakin cike da tsoron karya kamata, cikin tashin hankali ta dinga daddafe bangon bayanta da tafin hannunta wanda ya 6aci da jinin data goga a jikin Gabriella, wanda silar hakan Yasa sahun yatsunta suka fito radau a jikin bangon kamar an zana shi, gaba Waya saida ta faffashe tukwanan da kafafunta, da ta ga zai cimmata ta 6ace ta koma kan gadonta, ransa ne ya 6aci nan take yayi tsafi gaba daya gadon da take akai ya jirkice wanda silar hakan ta kundumo ?asa har kanta Ya da ku ta suma.


Bata kara sanin inda kanta yake ba, sai dai ta farka ta tsinci kanta a dakin da yake hukunta wadanda suka ci amanarsa nan take ta fahimci shine ya kawota nan..


(Kunji yadda akai Elder Ya rutsa da Khala=?%?)



Wata irin jijjiga Jeremiah ya yi, A lokacin ya gama daidaita jikin shi, dama abunda ya tsayar da shi kenan, babban kuskuren da zasu yi shine su bari Jeremiah ya baro bakin rijiyar, domin kuwa in har ya dira ?afarsa duk wani mai sauran rai da babu sihiri a jikin shi sai ya mutu in ba wani iko na Allah ba, aikuwa yana Waga ?afarsa kafin Ya dire ta ?asa, Danish ya watsa da gudun gaske ya durfafe shi, yana ?arasawa gaban shi ya daka uban tsalle ya haye kanshi ya cakumeshi da hannuwan shi biyu, da iya ?arfin shi na ?arshe ya ingizasu gaba Waya suka rubza cikin rijiyar, nan take murfinta ya maida kan shi ya rufe makullinta ma ya datse kan shi...

(Evil wall rijiya ce mai faWi da tsawo, tsohuwar rijiya ce da tayi shekaru aru aru tun zamanin kakannin Elder tun kan Elder ya gurfanar da kurkukun ?addara rijiyar ta ke anan, gaba Waya rijiyar ginin dutse ne tana da hatsarin gaske mutun bazai iya rayuwa acikin ta ba idan har babu sihiri a jikin shi, saboda giggan shaidanun dake rayuwa a cikin ta, ko ma?iyi na banayiwa fatan ya tsinci kanshi a cikin rijiyar koda a mafarkinsa ne saboda izayar da zai taras, daga jikin kowace kusurwa ta rijiyar yanace dadda6e da Evil spiders da manyan kunamu jibga jibga, ga giant snakes din dake bin jikin bangwayen rijiyar, gaba dayansu evils ne suka rikida ba ainihin kwarin ba ne.

ga wasu zanunnuka masu ban tsoro jikin bangwayen rijiyar, ga wasu halittu bakake munana, masu idanuwa barkatai a jikin su, wasu gashi gashine buzu buzu a jikin su, wasu halittun kuwa har kananun macijjai suke fitarwa ta bakin su, bala'i iri iri, daga kasan rijiyar wani irin fadi gare shi, hada koramar ruwan jini na sihiri da manyan duwatsu, ga wata gajeruwar bishiya mai rassa tare da manyan ganyayyin da sukayiwa kasanta inuwa, daga kasan ta akwai wata shimfiWa ta alfarma da akayita da jan carpet mai fadi anan giant din da suke horaswa ya ke zama kamar gunki bazai taba motsawa ba, in ba evils sun tashi bashi horo ba, koda yaushe da bakar izayar da zasuyi mashi, kamar yadda na fada abaya, tun suna bashi wahala su tsoratar da shi har sai sun kaiga bugun shi da bulalai su dinga azabtar da shi da masifu iri iri tun yana kuka ya suma su farfado da shi, har sai ya koma yana yin komai daga kwance tun daga kan amai, fitsari, kashi, saboda azabar da su ke yi masu takansa su fita hayyacin su, da zarar Elders sun tura ka rijiyar kayi bankwana da farin ciki da duk wani jin dadi, kunnuwanka ba zasu ?ara jin sauti mai dadi ba, sai na tashin hankali, baka da abinci daya wuce ?wari da kwan halittun dake a ciki, ruwan sha kuwa sai dai kasha jinin dake a cikin tulunan da suka aje maka, ko wanka baka isa kayi ba, cikin kazanta zaka zauna shiyasa dayawa matasan da suke diba idan zasu basu horon zama giant da wuya suke tsalle rijiyar shaida nu, mafi rinjayen su anan suke rasa rayukan su.

Rijiyoyin suna da yawa kowani giant a rijiya daya zasu kulle shi, kamar kabari, babu shige babu fuce, rayuwar kunci da azabtarwar, daga lokacin da tsoro yabar idanunsu, suka jure wahalar har suka fara rama bugun da evils keyi masu idan suna gabza fada atsakaninsu to daga nan evils din zasu gane zai iya jurewa, anan ne zasu zana mashi tattoo abayanshi yana kuka da ihu kamar ana zare ranshi saboda azabar raWaWi, irin tattoo din da su ke yi masu, ba irin wanda muka saba gani anayi bane, da akaifu evils suke zana masu shi abayansu, a faWan da suke gabzawa da giant, idan yayi nasarar jure azabtarwar su ya rayu bai mutu ba, daga nan ne zasu samu matsugunni a jikin shi, su gauraya da shi ta yadda zasu ba shi ?arfin su.


A Lokacin da Danish Ya dam?i jeremiah ya ingiza su cikin rijiyar, Tun kan su dira kasan rijiyar a saman iska, suka fara gabza faWa a tsakanin su baka iya jin sautin komai saina buge buge da naushe naushe da nishinsu hadi da gurnanin su kamar zakuna, bugun mutuwa sukewa junan su, babu imani babu tausayi, kowa jininsa akan akaifa ya ke, zuciyar su a wuya take, musamman jeremiah daya kasance mugun mutun, Ya tsani Danish tuntuni, ba dan komai ba sai don saboda lokacin da suke ?anana yafi Danish yiwa elders biyayya idan suka bashi Umarnin ya aikata rashin imani jiki na bari zaiyi, danish kuwa kafiya da taurin kai ya ke yi masu, gashi Allah ya jarabce su da son shi, sai da takaiga sai sun haWa da yi mashi sihiri suke samun abunda suke so, saboda yadda suke gatanta shi yasa Jeremiah ya ke yi mashi hassada, ya kullaci abun aran shi, yasha kulla makirci don ya sanya tsanar danish a zuciyar elders sai dai bai ta6a nasara ba, shiyasa a yanzu dayaga sun fada rijiya su biyu ya ke ta kokarin kawar da shi don ya fanshe bakin cikin daya kunsa mashi.


wani jahilin naushi ya kaiwa Danish a tsakar mararsa, har saida Ya firgice saboda azabar daya ji, bai kaiga dawowa dai dai ba, jeremiah ya tallabe kansa da faffaWan tafukayensa Ya buga jikin bangon rijiyar, tuni kuzarin jikin shi Ya ragu dama ya fara galabaita sosai saboda yakushin da Evil giants sukayi mashi a filin daga, duk da haka bai sare ba, jini na fita ta bakinsa da hancinsa, da bayan kansa, a haka Ya dam?i kan jeremiah Ya daddage da dukkan karfinsa ya maka shi jikin bango, amma kamar ya hada dutse da dutse kwata kwata babu alamun jeremiah Yaji jiki kamar ana kara masa karfinsa abunka ga sabon garkuwa, don bala'e kusan sau uku suna rikida su canza halittar su, kamar zasu kashe junansu babu tausayi ko kadan burin kowan nan su yayi nasara, kafin kace me tuni Wata irin kura mai hade da hayaki tamkar guguwa ta bude su baka iya ganin su kwata kwata, cakumar Danish yayi ya nutsa da su cikin rijiyar burinshi ya kaishi ?asanta don ya azabtar da shi kafin Ya karasa kashe shi, shi kuma baya son yakai kasan rijiyar saboda yana jin tsoron Evils din cikinta su fusata zasu iya tarar mashi yasan cikin dakika zasu iya shafe babin shi.

Duk yadda yaso ya turje saida Ya kasa saboda raunin da yayi, ta karfi ta tsiya Jeremiah Ya ingizasu suka kundumo kasan rijiyar gaba dayansu saida kawunansu suka daku.

Duk da mawuyacin halin da yake a ciki hakan bai hana zuciyar shi tunanin Angel dinsa ba, har lokacin idanunsa basu daina tariyo masa irin haukan da tayi na za'a rabata da shi ba, kalamanta sun tsaya mashi a kahon zuciya, Shagalar da yayi da tunaninta yaja har Jeremiah Ya yi nasarar azabtar da shi, saboda rashin imani da sihiri yayi amfani gurin zane shi da bulalai yayi mashi jina jina, har saida Ya suma kusan sau uku jeremiah Yana farfado da shi.

A lokacin Gaba Waya ya fidda rai da rayuwa, kamar jaki haka Jeremiah ya mayar da shi jini da majina ya hada mashi akan fuskar shi, saida Ya raba shi da kakin jikin shi, Yayi mashi zir haihuwar uwarsa dayaga Ya kusa kashe shi gaba daya baya iya ta6uka komai sai ya fara kokarin yin homo da shi saboda ta hakane kadai zai iya ?wace sihirin jikin shi ya dawo nashi jikin saboda ya ?ara ?arfi na fitar shari'a, bai kaiga cimma manufar shi ba, kwatsam rijiyar ta fara jijjiga, Lokaci daya sautin dariyar Evils mai matukar tsoratarwa da razanarwa Ya cika rijiyar, alamar Evils sun fusata, A lokacin Danish baisan inda kanshi ya ke ba yana akwance cikin jini rai hannun Allah, soft skin dinshi duk ta 6aci da munanan raunuka ko yatsansa bai iya motsawa..

Jeremiah Yana akansa Yana kokarin cimma manufarsa, Kwatsam ba zato ba tsammani evils suka fara ?ewayesu da suffar halittun da suka sauya masu tsotarwa, kamar kyankyasai saboda yawansu, manyansu da kananan su, koda Jeremiah yaga haka sai ya fara sakin shu'umar dariya yayi zaton zasu goya masa bayane akan abunda yake kokarin yi saboda yanzu shine garkuwar kurkuku.

bai yi aune ba, kwatsam Yaga bakin hayaki ya soma kurdadowa yana fita ta bakinsa da hancin shi, kaitsaye hayakin ya ke shiga ta kofofin hancin Danish da bakinsa da duk wata kofa da iska zata iya ratsa jikin shi.

lokaci daya yabi ya ruWe ya zazzare jajayen idanunsa kamar na kwartan mazuru, jikinshi ya kama 6ari kamar mazari, yayin da tsoro da fargaba hadi da tsantsar rudanin al'ajabi?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? suka mamaye zuciyarshi, abin da bai ta6a zata ba, ya rasa gane tayaya akai evils suka bar jikinshi tare da sihirinshi suka koma jikin Danish, da alama reshe ne ya juye da mujiya.


cikin rawar murya ya furta bazai yiwu ba, meyasa zakuyi min haka? Ni ne sabon garkuwarku, Danish maci amanane, baya atare da mu! Ku dawo min da sihirina, Ku dawo jikina, ni ne nafi cancanta in samu karfin sihirinsa ba shi ba, ko kun makance ne? Baku da hankali ne"?


Kamar mahaukaci ya dinga sambatu tare da mikewa ya bi halittun dake kewaye da shi Ya dinga yi masu tsawa yana zaginsu kamar zai doke su.


sai masifa ya ke zazzaga masu ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, wata irin kururuwa ya fasa kamar zaiyi hauka ya tallabe kansa da tafukansa, Ya dinga sakin kara mai tattare da bakin ciki, Har tsalle yakeyi kamar kwaWo dama ba sutura a jikin shi.

Girgizawar da rijiyar tayi ne yasa shi dawowa hayyacin shi, tunkan ya juya idanunsa suka safka akan Inuwar Evil din dake abayan shi, yawu ya haWiya mai daci, gabanshi ya shiga faWuwa.

juyawar da zaiyi keda wuya idanunsa suka sauka akan Danish Dake atsaye kan kafafunsa, gaba daya idanunsa sun juye sun koma fari fat babu launin su, wani abun Waure kai ko ?warzane babu akan fatarsa gaba daya raunukan da yaji sun 6ace 6att ko tabo babu in ka cire tattoo dinsa, bakin cikine Ya turnuke zuciyar Jeremiah, kamar ya hadiyi zuciya ya mutu.

Cikin fushi yace"burinka Ya cika Danish, Ka yi nasarar rabani da sihiri na, ba zaka ta6a bari in fi ka ba, ko da na sakanni ne ko da yaushe kaine agaba, na tsane ka danish, bana son ganinka, mutuwarka nake kwaWayin in gani, bazan kyale ka ba, sai na kwace sihirina sannan In kashe ka.

tun daya fara maganar Danish bai motsa ba, saboda a ba Wini ba shi bane, Evils ne suka tada shi shiyasa harya iya mikewa tsaye, tsautsayi ne Yaja jeremiah Ya durfafesa da gudu Ya daka tsalle Ya dura akanshi kafin yayi wani yunkuri Danish Ya dam?i wuyan shi duk girman jikinshi Ya daga shi sama, nan take ido Ya raina fata, Ya dinga gurnani yana kokarin kwace kansa sai dai Ya kasa, idanunsa suka zazzago waje, Da azaba ta ishe shi Ya fara yi masa magiya akan yayi hakuri Ya kyale shi, kada ya kashe shi, koya manta abokantakar da ke tsakanin su.


Wata shu'umar dariya Danish Ya fasa hahahahaha da wata irin budaddiyar Murya ya furta"baka cancanta ka rayu ba, saboda baka da tausayi, mugunta da zalunci kadai kasa a gaba, burinka kaga bayana, saboda nafika a komai, yanzu zan saukaka maka kishin da kake akaina, Idan na kashe ka ba zaka ?ara ganina ba, balle har ka ?ulla ce ni aranka"

ya karashe maganar tare da matse wuyansa, ta yadda ko numfashi bazai iya fitarwa ba gurnani ya dinga yi yana ta kokarin kwatar kansa, azaba tasa ya saki fitsari, majina ta dinga zalalowa ta hancinsa..

saida ya tabbatar bazai kara amfanuwa ba, tukunna Ya jefar da gangar jikin shi kasa.

Kunaman dake a cikin rijiyar da macijjai suka daddabe shi, suka dinga kai mashi sara da Walli..

ya dinga sakin Ihun azaba, Danish yana atsaye yana kallonshi har saida ransa yabar gangar jikin shi tukunna Ya daka tsalle Yayi sama Ya nufi murfin rijiyar yana karasawa Ya sakar mashi naushi Waya nan take murfin Ya balle biyu ya duro akan kafafunsa kuma nan take ya dawo cikin hayyacinsa..

yanayin fuskarsa ne ya sauya zuwa tsantsar tashin hankali da damuwa ganin gawarwakin sojoji barbaje a kasa, wasu gawarwakin ma ginin daya ruguje Ya rufe su ba'a iya ganin su, babu wani mai rai, kuma kwatata babu gawar giants a gurin sun 6ace 6att..

bawan Allah, aruWe ya shiga neman gawar Chief da ta daddyn Unaisah, da Salsabeel, ya dinga bin gawarwakin yana dudduba fuskokinsu, tuni ya hada gumi, zuciyar shi ta karaya ganin babu corpses din su kwata kwata, da karfi ya dinga kwala masu kira tamkar makoshinsa zai balle shiru babu mai amsa mashi, bakin cikine ya turnuke zuciyar shi, yaji takaici, ganin duk kokarin da yayi don su rayu ya tashi abanza, wata irin ?ara ya fasa mai kuwar gaske har saida ginin Ya girgiza.

Bakomai ne Ya faWo masa aransa ba face tsohuwa khala, cikin sauri Ya zu?unna a gaban gawar wani soja, Ya tu6e kakin sa Ya zura a jikin shi..

Daga inda Ya ke yayi tsafi Ya 6ace 6att bai dira a ko'ina ba, sai a tsakiyar dakin tsohuwa khala ya bayyana..

~__________=?%?__________

Nan ma ya ?ara shiga tashin hankali ganin daskararren jinin daya malale kasan dakin ta ga gadonta daya jirgice nan ta ke ranshi ya bashi sun kashe ta, shikenan ya rasa damar da ya ke da ita, babu wanda zai faWa masa su wanene iyayen sa in ba ita ba, gashi kuma ya rasa ta yanzu!

baima san tayaya zai iya komawa gurin yan uwansa ba, zu6ewa yayi kan gwiwowinsa tsabar bacin rai, idanunsa suka kaWa jawur kamar garwashin wuta, tuni jikinsa ya dau zafi rau, yana a cikin wannan halin kamar ance ya wurga idanun shi jikin bangon dakin ta unexpected ya hango kamar zanan wani abu ja

zumbur ya mike ya nufi zanan Ya ?ura idanun shi Yana kokarin gano menene! dakyar ya iya gane sahun yatsun mutunne da jini.

rufe idanunsa yayi tare da zurfafa tunaninsa nan take cikin ikon Allah kwakwalwarsa ta tuna masa da inda keda zanunnukan yatsun hannayen mutane, wato dakin da Elder ya ke hukunta wanda yaci amanar shi, ka'ida ne idan ya gama azabtar da wanda yaci amanarshi saiya fasa tafin hannunsa Ya manna jikin bangon Wakin, har sai sahun yatsun hannayen shi sun fito raWau tukunna ya ke cire shi, nan take Danish Ya fahimci Khala ta bar sahunne don wani ya kai mata Wauki tun da tasan zasu dawo dakin nata idan suka gama faWan.

lokaci Waya ya waro idanun shi waje tare da ja da baya, batare da bata lokaci ba, Ya 6ace daga dakin Khala..

Lokacin da Elder ya juya Giants suka take mashi baya basu kai ga isa kofar dakin ba suka 6ace ma ganin ta.

Ta kasance ita kadaice a cikin dakin, ga wutar sai kokarin kama jikinta ta ke yi, bata da wani sauran sihiri ajikinta balle ta iya kwance kanta, saboda elder ya riga daya karya garkuwar sihirin dake a jikin ta.

sambatu tadinga yi cikin fitar hayyaci take ambaton duk wata addu'a da tazo bakinta ahaka har numfashinta Ya fara kokawar Waukewa zufar jikinta ta dinga tsastsafowa kamar yayyafin ruwan sama kafin wani lokaci bugun zuciyarta Ya tsaya cak, numfashinta Ya dauke, wutar Tana gab da zata rufe jikinta, Danish Ya duro dakin, cike da tashin hankali ya yi sahirinsa nan take wutar ta mutu kurmus, ramin Ya hade kanshi tamkar ba'a ta6a tsaga ?asan gurin ba, kafafuwanta da suke daure da igiyar kaca nan take igiyoyin suka warware kan su sakamakon tsafin da yayi, kafin ta fado ?asa ya rigata karasawa kasan fankar, igiyar na karasa kwancewa ta fado kan hannayensa, tsananin tausayinta ne ya kama shi ganin yadda hancinta ke fitar da jini, fatar goshinta har ta fara konewa ta tattare tayi duhu alamar wuta ta daki gurin sosai.

ga wani irin ?auri da jikinta ke fitarta, gumi ya wanke ko'ina na jikin ta, rungumeta yayi sosai a jikin shi, kamar zai mayar da ita cikin cikin shi, idanunshi suka cucciko tab da kwalla, duk da baisan meya faru ba, amma yaji aran shi Elders sun gano taci amanarsu shiyasa suka hukuntata, da ba dan Allah yasa tayi dabarar yin alamar da zai gani ba, da yanzu ta kone kurmus ta yadda ko


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login