Showing 75001 words to 78000 words out of 321579 words

Chapter 26 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

hannunsa ya toshe bakin nata.

Saitin kunnnanta ya kai bakinsa da wata irin murya mai cike da shu'umanci ya furta, "Matsoraciya..." Ajiyar zuciya ta sauke tana faman haWiyar yawu...

"FaWa min a ina kika samu kwarin gwiwar nan ne?" Ya faWa yana le?en fuskarta..



"Ka 6ata min rai ne, ni kawai bana jin dadin abun da ka ke yi min ne, basai na fito fili na faWa maka ba ka riga da ka sani .."

"Am sorry my queen, mother of my princess, na kar6i laifina, bazan ?ara ba, nima bada son raina hakan ke faruwa ba, ayyukane su ke yi min yawa amma zan gyara in sha Allah." ta Wan yi mamakin yadda yayi mata magana cikin tausasa harshe.



"Muje ki taimaka min in yi wanka, mun kwana biyu bamu yi wanka atare ba.." Bai jira amsarta ba, cikin sigar yaudara da jan hankali ya Wauketa kamar jinjira ya nufi bathroom da ita.


_______________________________


Lokacin da Taj ya je ma Ummi da zancen neman ta da Chief ya ke yi, hankalinta ba ?aramin tashi yayi ba, zullumi da fargaba suka cika zuciyarta, ta yi ta tunanin meyasa ya ke nemanta?



Kasa fita tayi daga dakinta, har saida Taj ya kirata a waya ya ?ara tunasar da ita game da kiran da Chief ya ke yi mata yace ta same shi yanzun nan a sitting room dinsa tukunna, ta zumbula dogon hijabi ta fito cike da War-War ta nufi sitting room dinsa, saida ta tsaya bakin door din ta daidaita nutsuwarta, kafin tayi sallama cikin nutsastsiyar muryarta.

Daga ciki ya amsa mata sallamar, ya na daga zaune kan sofa ya Waura kafarsa Waya kan Waya yayin da idanunsa ke akan Apple ipad dinsa da ya ke daddanawa, shiga ciki ta yi, tunkan ta ?araso ya nuna mata kujerar dake fuskantar sa, table ne ya raba tsakanin su.


Bayan ta zauna ta sunnar da kanta ?asa cike da jin nauyin sa gaba Waya ya yi mata kwarjini.



"Ina fata kin wuni lafiya."



Da ?yar ta furta, "lafiyalou, ya kake, ya aiki, ya family Win ku"


"Alhamdulillah ina lafiya, suma family Wina suna cikin ?oshin lafiya,"

Shiru suka Wan yi na wani lokaci, daga bisani ta tsinkayi muryarsa a cikin kunnanta,



"Na kwaWaitu da son jin tarihin rayuwarki.."

Zare idanu ta yi, har ta fara tunanin ko dai ya ji komai agurin su Benazir ne.



Bai damu da yanayin ta ba ya ci gaba da maganarsa, still bai Wago ya kalle ta ba, idanunsa na akan apple ipad dinsa da yake cigaba da dannawa,



"A ranar da ?awayenki suka zo gidan nan, Taj ya faWa min halin da kuka shiga lokacin da kuka ga juna, kuma ya ji a bakin Ex-wife din sa cewa ke aminiyarsu ce..."

Har ya ?arashe maganar bai Wago ba, yanayin fuskarta ne ya canza zuwa tsantsar 6acin rai da damuwa, kwata-kwata bata son kowa yasan labarinta, saboda tana jin kunyar a sani, bayan haka bata son ta fama tsohon raunin dake a cikin zuciyarta, abun da ya Waure mata kai meyasa Chief ya ke son jin labarin ta? Ko Taj da suka fi sha?uwa da shi bai nemi ya sani ba sai shi da bai ta6a shiga shirgin ta ba hakan yasa ta dan ji shakkun ta faWa masa..



"Kin yi shiru ba ki ce komai ba,"



Kamar mara gaskiya ta kama yi mashi yan kame kame, muryarta kamar ta mai in'ina ta ce, "Sir, I'm sorry to say why do you want to hear about my life?"



"Saboda ina son in sasanta tsakaninki da ?awayenki, cos a fahimtana kun samu sa6ani ne, kuma akwai wani abu da ya faru wanda yayi silar raba ku. "

Yamusa fuska tayi kwata kwata babu walwala ta furta, "Ina ganin girmanka yallabai, bana fata Allah ya nuna min ranar da zaka nemi wani abu agurina in kasa yi maka shi, amma ina mai baka ha?uri, ni bazan iya baka labarina ba..."

Gently ya Wago da reddish eyes dinsa ya Waurasu akan fuskarta, tuni ta ji wata nutsuwa ta shige ta, wani irin kwarjini yayi mata wanda hakan yasa ta kasa ?arasa maganar tata.



"Pls ki faWamin, In har kin yarda da ni, amma idan kina ganin da takura ki bar shi..."

Yanayin yadda yake yi mata magana cikin kwantar da murya yasa ta dinga jin kamar yaya Shureim ne ke yi mata magana, hatta fuskarsa sai ta dinga koma mata irin ta Shureim, batasan sa'adda ta fara bashi labarin rayuwarta ba, tiryan tiryan ta labarta masa komai daya faru da ita har izuwa lokacin data bar gidan mahaifin ta.

Idanunta cike tab da ?walla ta ?are maganar, lallashin ta ya yi cikin nuna tausayawarshi gareta har ya samu ya shawo kanta.



"Tayaya akai kika bar ?asar nan? Ki ka koma America da zama, bayan kin canza rayuwarki?"

Sunnar da kanta ?asa tayi cike da jin nauyin ta fada.



"Zan fahimce ki Ummi, tun kafin ki fara yi mana aiki mun riga da mun san komai game da rayuwarki a America, don haka kada ki ji komai, abun da ya faru da ke jarabta ce daga Allah..."

Kalamai masu dadi ya faWa mata har sai da ta ji zata iya fada masa komai saboda ta yaba da hankalinsa ta kuma aminta da shi, a tsanake ta fayyace masa komai da ya faru bayan rabuwarta da mahaifin ta.



Da?yar ta ?arasa labarin ganin yadda hankalinsa ya tashi matu?ar sosai, jikinshi har kerma ya ke yi saboda tsabar bacin rai da fusata, bai ta6a jin tsanar mutun kamar yadda ya ji ya tsane sa ba, zaluncin sa yayi yawa, bayan ya rabata da kowa nata, ya kuma maida ta karuwa, cikin fushi ya daki gaban table dinsa da hannunsa.



Hankalinta a tashe ta ce, "Sir meke damunka? Ko labarin dana baka ne baiyi maka dadi ba..!"



"Har yanzu kina atare da Uncle din nata?"

girgiza kai ta yi, "Mun rabu da daWewa,"

Wani kallo yayi mata da ya sa tasha jinin jikin ta, batasan ya san komai ba.

"Ki ji tsoron Allah, Ki faWa min gaskiya!"

Tamkar zata fashe da kuka ta ce, "Pls kada ka tilasta mini, bazan iya faWa maka amsar tambayarka ba, ka yi ha?uri kawai.."

Murmushin takaici ya yi tare da cewa, "Okay, Kin taba haihuwa da shi?"

AruWe take kallonsa jin wata tambaya mara ma'ana, ba dan tana ganin girmansa ba da ba abun da zai sa ta zauna yana mata tambayoyi kamar Wan jarida,

"A'a, amma na ta6a samun cikin shi, wanda silar zubar da cikin da na yi yasa muka samu sa6ani da shi, har ya Wauke ?afa da kawo min ziyara, abun da yasa nayi hakan saboda bana so in 6ata shape din jikina sannan bani bukatar in ?ara haihuwa, ?ata dana bari ta ishe ni in ?arasa rayuwata, ashe ma ?ar da nake ta hauka akanta ta mutu batare da na sani ba...."

Fashewa tayi da kuka ya dinga lallashinta har ya samu ta yi shiru..



"Amma meyasa baki taba kar6ar tayinsa na aure ba?"

Tana cikin share ?walla ta ce, "Saboda ban ta6a son shi da aure ba, bayan haka a duk lokacin da yayi mini magiya akan in amince in auresa, da zarar na amince muka fara shirye shiryen auranmu toh bazai ?ara lafiya ba, har sai ya fasa zancen auren, wannan dalilinne yasa har ila yau bai aure ni ba."


Du?ar da kanta kasa ta yi jikinta yayi sanyi da ganin yanayinsa, duk sai taji ta ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????muzanta, saboda tayi zaton haushin rayuwarta ya ke ji, tuni idanunta sun cicciko da ?walla,



"Kayi hakuri, idan labarin dana baka ya 6ata maka rai, shiyasa tun farko banso ka matsa min akan in fada maka ba.."

A hankali ya buWe idanunsa da suka kaWa jawur ya girgiza mata kai, "Ba abunda kike tunani bane Ummi, labarin ki ya karya min zuciyana, na ji tausayin rayuwar ki..." hankalinta ne ya kwanta jin ba abun da ta zata ba ne.

"Nagode da kika aminta da ni har kika faWa min sirrinki" ?an murmushi ta yi.

"Amma kai ma kamar kana da damuwa, kada ka ce na sanya maka ido, wlh ka rame, babu karsashi a jikin ka"


Murmushin ya?e ya ?a?aro akan fuskarsa, "Kada ki damu da ni, zazzabine ke damuna amma na ji sau?i..." Girgiza kai ta yi, "Yallabai, halin da ka shiga yafi ?arfin zazzabi, kada ka boye min pls, tun da har na aminta da kai na baka labarina dayake sirrina kaima ya kamata ka sanar dani taka damuwar, ko da bazan iya sama maka mafita ba, zan tayaka da addu'a." marairaice masa fuska ta yi.



Shiru yayi jim yana tunanin ya zata Wauki abun in ya fada mata,

Cikin sanyin murya ya ce, "Ummi mun fara gano su wanene Elders na gidan Kurkukun ?addara! Kuma muna zargin uncle din ?awarki Benazir yana Waya daga cikin su..."

Bai ?are maganar ba ganin yadda ta zare idanunta, walwalar fuskarta ta Wauke tamkar bata ta6a yin dariya ba.

A dabarbarce ta ce, "Sir ka san me ka ke faWa kuwa? Wallahi ba dan ina ganin girmanka ba da ba abun da zai hana..." Kasa ?arasawa ta yi, can kuma ta ce, "Bazai yiwu ba, big boss baya Waya daga cikin su, saboda shi ba matsafi bane kuma ba mugu bane, ni nasan wanene big boss! Nasan halinsa ciki da bai, pls ku sake bincike akan shi zaka tabbatar da abun da nake faWa maka!" Rai a Wan 6ace ta faWa, ta ha?i?ance akan gaskiyarta.



"Ke baki tunanin mutumin nan da wata mummunar manufa yake atare dake Ummi? Ke fa malama ce, kina da tarin ilimi akan ki, kinsan mai kyau da mara kyau, taya zaki yi tarayya da fasi?i kuma har kina kare sa daga laifin da ake tuhumarsa...?"


"Baki tunanin saboda kin nuna baki son shi dr. Shureim kikeso shiyasa ya ?ulla makircin da ya shiga tsakanin ki da shureim ya kuma raba ki da mahaifinki saboda yasan bazai bari ki aure shi ba tunda baki son shi, sannan bayan kin gudu da tsakar dare tayaya akai har kika haWu da shi a wannan lokacin? Shi Aljanine baya bacci ne? Ba yadda za'ayi ya fito in the midst of the night batare da wani ?wa??waran dalili ba, gaba Waya plan dinsa ne Ummi..."

Shiru tayi jim ba tare data furta kalma ba, bata san tayaya zata fahimtar da Chief ba, gani take kamar ya fara zarewa.


"Kiyi amfani da hankalinki Ummi, meyasa ya Wauki nauyin karatunku a ?asar germany? ya kuma kama maku hayar gida, bayan haka duk weekend sai ya kawo maku ziyara har ya kwana agidan ku," ya faWa yana kallon cikin idanunta.

Gaba Waya tabi ta ruWe, sai dai kwata kwata bata gasgata maganarsa ba, saboda ta yarda da Uncle Musa fiye da kowa tun da ita ya yi mata hallacci, ya so ta a lokacin da kowa ke gudunta, ya zama danginta a lokacin data rasa dangin da zata jingina da su.




Murmushin takaici ya dan saki, saboda ya fahimci ta cikin sau?i bazata yarda da shi ba,

Zura hannunshi ya yi cikin front pocket na jallabiyarsa ya zaro hotuna,

Kamar daga sama ta ji ya ce, "Nasan har yanzu kuna a tare Ummi, saboda akwai ranar da ya kira ki a waya kin shiga toilet, Batool ta gani ta Wauka batare da sanin ki ba, a yanzu haka ina da hujjojin da za ki gasgata magana ta.."

She was utterly perplexed, but she didn't believe his words at all.

Ya ?arashe maganar tare da Waura mata hotunan akan table dinsa, lokacin da ta daura idanunta akan hotunan wata irin firgita ta yi, gaba daya tabi ta rude, muryarta da mamaki ta ce, "Sas.. Sir ina ka samu waWannan hotunan?"

Ta tambaya a?agare da son jin amsar shi, bai tanka mata ba, har saida ya zaro Wayan hoton ya jera shi da sauran hotunan..



Lokaci Waya ta ?ara ruWewa, labbanta na kerma ta furta, "Baby preety, Sir Ina ka samu hotunan su um??"



Numfasawa yayi kafin ya ce, "zan faWa maki inda na samu hotunan amma ki fara faWa mini miye ala?ar dake atsakanin mutanan dake a cikin hotunan nan?" Jinjina mashi kai tayi kafin ta fara kora masa bayani,



"A tare na san shi da Natasha, sun daWe a tare, karuwarsa ce kuma baturiyar england ce, ita kuma baby preety rainon ta ya kawo mata tun tana jaririya, amma lokacin da ta kai shekara sha shidda ta ce min ya kar6e ta, ya mayar da ita gurin mamanta da ke anan Nigeria.."



Runtse ido chief Owais yayi saboda takaicin da ya turnuke zuciyarsa, aransa ya ayyana hakan na nufin ?an biyu ne ita da ?ar wurinsa! Kamar yadda su ka yi tsammani, Ya sadaukar da Waya, ita kuma Wayar tana agurin mamanta.




"Sir meya faru um? Dan Allah tun da na amsa maka tambayarka, nima ka fadamin a ina ka samu hotunan su! Na ?osa na ji."

Mi?a hannu yayi cikin table drawer din gabansa ya curo diary Win Unaizah ya Waura mata akan table din, "kinga inda na samu hotunan, Kuma diary din nan mallakin Waya daga cikin fursinonin kurkukun kaddara ne, nasan ba zaki manta yarinyar da Unaisah ta bada labarin mahaifinta da ya yaudareta ya sadaukar ita gidan kurkukun kaddara a matsayin Korean School...?"





Wani irin faduwar gaba taji daram dararam kamar ana buga gangunan ya?i a ?irjin ta.

Yatsun hannunta na kerma ta buWe diary din ta soma karanta shi,

Wa'iyazubilla! tana karantawa yayin da brain dinta ke tariyo mata fuskar yarinyar, tabbas ta yarda diary din mallakin baby preety ne babu tantama saboda yawanci duk abunda ta rubuta a cikinsa ta ta6a jin labarin a bakin Natasha.




Bata ?arasa karantawa ba, ta rufe diary din tare da kifa kanta saman shi, wlh bazan iya misalta tashin hankalin da ta shiga ba, She was completely bewildered and shocked, unable to believe it, Aranta tana jin ba zai yiwu uncle Musa ya iya aikata rashin imanin nan ba, mutun mai tsoron Allah da tausayi irin sa would never do such terrible thing, amma kuma ta fara kokwanto saboda in har ba a diary din baby preety ba, to kuwa babu inda za'a samu hotunan Big boss da Natasha da kuma na baby preetyn, sai dai bata so ma zargin su akanshi ya zamana gaskiya.

"Yanzu kin yarda da maganata ko kuwa kina akan bakanki"

Jinjina mashi kai ta yi, "Bani da matsaya, amma na yarda da big boss, kuma na yarda da kai, sai dai bazan iya yarda da abun da ka fada akansa ba, wadannan hotunan na yarda a cikin diary din baby preety aka same su amma bana tunanin itace yarinyar da Unaisah ta bamu labarin ta, please na ro?e ka ku sake bincike akan shi.."


Duk yadda Chief ya so ya kwatanta mata cewa ba mutumin kirki bane ta?i yarda, tana akan bakanta saboda ta aminta da mutuminta, yadda kasan wadda aka asirce, kwata kwata bai ji haushinta ba saima tausayinta da ya mamaye zuciyar shi saboda ya lura ta ruWe ne sosai kuma bata son zargin da suke yi ya tabbata akan shi saboda halin da zata shiga, shiyasa tun farko baima yi tunanin faWa mata komai game da babynta ba saboda gudun halin da zata shiga.




"Ummi, Zan baki lokaci kije ki yi tunani akan abun da na faWa maki, sannan ko da baki yarda ba, Inaso ki bamu hadin kai please..."

Girgiza kai ta yi, "Ka yi ha?uri ba zan iya ba, nayi masa alkawarin bazan ta6a bari wani ya san muna a tare ba, in har ya ji na karya masa alkawari bazai ji dadi ba, zaiga kamar na ci amanarsa ne, ni ko maganarsa bana son yi da wani." Zuciyarsa ta sosu ransa yaso ya 6aci, sai dai bai nuna mata a fuska ba..




"Zaki iya tafiya..." Har zata mi?e ya tsayar da ita, "Zan gargaWe ki, Kada ki kuskura ki bari mutumin nan ya gane abunda muke zargi akansa! bama shi ba, ko da ?awar nan taki ce, idan har na ji maganar nan agurin wani, hmm, ba abun da zai hana in gar?ame ki a cell kuma kema zaki shiga cikin zargin da muke akan sa, sannan kada ki canza masa ku cigaba kamar yadda kuka sa6a."

Maganarsa ta Waga hankalinta, dama da biyu ya yi mata barazana, fuskarta ta ji?e sharkaf da gumi, kwata kwata babu walwala atare da ita, Ya rudar da ita ba kaWan ba, Ya kuma tsoratar da ita.


Hanky ya mi?a mata, "Share zufar dake akan fuskarki, don bana so wani ya gane halin da kike a ciki."

Cikin rawar hannu ta kar6i hanky din ta soma share gumin fuskarta, har ce mata yake yi, "Ki share da kyau fa.." tace toh, bayan ta gama ta juya zata tafi da hanky Win ya dakatar da ita, "Bani abuna.." mi?a masa hanky din ta yi, ko waiwayensa bata yi ba saboda a ?agare take da ta bar sitting room din nasa..

Lumshe idanunshi yayi tare da jingina bayan shi jikin kujarar, bawan Allah abun duniya ya ishe shi, saboda gujewa tunanin da zai haifar masa damuwa yasa baya barin zuciyarsa hakanan batare da yayi tasbihi ba =ؔ?



Bayan fitar Ummi daga dakin, jikin bango ta jingina bayanta, yayin da zuciyarta ke tariyo mata wasu abubuwa da suka haifar mata da kokwanto akan mutuminta! bakomai ta fi tunawa ba face ranar data fara ganin Danish babu shirt a jikinsa! zanen tattoo dinsa ya tsaya mata a rai, har yau bata manta ba, saboda sak irin na big boss ne, kamar anyi photo copy dinsa an Waura masa abayansa, kuma tun da take mu'amala da americans bata ta6a ganin mai irin tattoo dinshi ba, sai akan Danish shiyasa ranar data ganshi al'ajabi ya kamata, bayan haka maganganun da Chief ya faWa a game da shi sun tsaya mata a ?ahon zuciya, tabbas diary din baby preety ne, agurin ta kaWai za'a samu hotunansu, wani abu da ya ?ara ruWar da ita nickname dinsa da ta gani a rubuce cikin diary din Preety, kuma a labarin da Unaisah ta basu ta fadi sunan mahaifin Unaizah yar gidan daddy, gaba Waya dai kanta ya Waure tamau, kwakwalwarta ta rikice sai tufka da warwara ta ke yi.


"Ummi, kun gama magana da Chief dinne?" Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Taj, a firgice ta dube shi yana zaune kan wheelchair dinsa, danne damuwarta ta yi ta kakaro murmushi kan fuskarta, "Eh mun gama magana da shi, shine ma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login