Showing 54001 words to 57000 words out of 321579 words

Chapter 19 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

taba yin dariya ba.

Ta fahimci indai zata yi mata maganar Benazir ko Anila bata farin ciki, shiyasa ta kasa faWa mata tasan tarihin rayuwarsu.


"Sai dai ki Wauki wasu hotunan keda Batool ki tura masu amma banda nawa.." ta fada fuskarta a Waure ba annuri..



"Meyasa Aunty Ummi?" Batool ce ta tambaya,

"baku ga babu mayafi a jikina ba? Bai dace a ganni haka ba koda a hotone"


Ta ?arashe maganar tare da mi?ewa ta juya ta nufi Up, bin ta da kallo Unaisah tayi harta hau kan stairs ta Wan dakata da yin tafiyar, ta rasa meyasa take ji aranta kamar sakacin su Benazir ne ya ja ta rasa babynta, Zuciyarta ce ke tunzurata akan manufarta shiyasa ko sun kira bata Waga kiran su, sa?onnin da suka tura mata sun kai Wari amman ko Waya bata buWe ba balle tasan me suka rubuta a ciki, Shureim ne kaWai idan ya yi mata sako take dubawa saboda har yanzu akwai ?aunarsa a cikin zuciyarta.



Har bayan sallar Isha'i ba Chief ba labarin sa, hankalinsu ya tashi matu?a, saboda damuwar rashin dawowar shi da tayi masu katutu acikin zuciya, hakan yasa bacci ya ?auracewa idanunsu, hankalinsu ya ?i kwanciya, gani suke kamar wani abunne ke faruwa da shi, a falo suka raba dare gaba Wayan su harda Taj, ko cake din da aka kawo masu basu ci ba.



Lokacin da bacci ya fara cin karfin su, Ummi da Batool har sun fara gyangyaWi, Unaisah dai ba alamun bacci atattare da ita, ta kasa ta tsare sai Chief ya dawo.


"Ummi ku tashi kuje ku kwanta, dare yayi sosai" Taj ne ya fada yana duban su..

Sun langwa6e kansu jikin Sofa, girgiza kai Ummi ta yi, "Bana tunanin zan iya runtsawa in har Chief bai dawo ba, wlh na damu Boss, ace ko waya baya picking?"

Ta faWa fuskarta a yamutse.

Da damuwa akan fuskarshi ya ce, "Ku yi hakuri kuje ku kwanta, in sha Allah ba abun da zai faru da shi, bafa wata uwa duniya ya tafi ba, yana agidan grandpa dinsa dake a cikin estate din nan, may be yan uwansa ne suka ru?e shi, amma nasan in sha Allah da asuba zai dawo nan din.."


"Amma in har lafiya, meyasa munata kiran sa baya picking? bayan shi da kan shi yace mu shirya idan ya dawo zamuyi celebration a gida.."



"At least in ma bazai dawo ba, yakamata ya kira a waya ya faWa mana.."



"Ummi, kuyi masa uziri, Allah kadai yasan me ya tsayar da shi, a sanina da Chief bai cika mantuwa ba, mutunne mai son cika alkawari, sai dai bansan meyasa bai dawo ba, kuma bansan abinda ya hana shi kiran mu ba, amma mu yi hakuri mu jira zuwa gobe.."

Ummi ta ce, "Ni ba rashin dawowar shi bane ya Waga min hankalina, kawai muna so muji in yana lafiya sai hankalin mu ya kwanta.."

Dakyar Taj ya samu ya lallashe su har suka hakura da jiran na shi kowa ya nufi bedroom dinsa don ya kwanta.


~______________________________~


ELDERS=?%?




Duhu ne ya mamaye ko'ina, ba zaka iya ganin komai dake a kewayen wurin ba.


Yayin da yake a tsaye cikin shiga ta doguwar riga ba?a ta sauka har ?asan kafafunsa dake a sanye cikin bakaken takalma na fata, Ya lullu6e sumar kansa da hular rigar tasa, baka iya ganin komai na jikinsa in ba ?wayar idanunsa ba, hatta fuskarsa a lullu6e take da ba?in takunkumi, yayin da ya ru?e sandar sa a hannun shi na dama.



Tun daga yanayin tsayuwarsa zaka fahimci babu ?oshin lafiya atare da shi, akwai rauni da karayar zuciya atattare da shi..


Unexpected hasken wutar candles dake a kewayen wurin ya soma kunna kansa, hakan ya bani damar ganin sauran bil'adaman dake a cikin katafaren Wakin, har saida na firgita da ganin wasu irin dogayen mutane masu ?irar ?arfi a jikin su, gaba dayansu suna a zaune kan armchairs din dake a kewaye da shi.



Shigar jikinsu bata da bambanci da tashi, bakaken dogayen riguna ne a jikinsu, sun rufe kansu da hulunan rigunan, kowannansu yana a ruke da sandar shi ta alfarma, gaba daya sun sadda kansu ?asa.


Hankalinsu ya dugunzuma ainun, basu ta6a shiga mawuyacin hali na farga irin wannan ranar ba, tun da Elder ya fada musu abun da ya faru da shi hankulansu sun tashi matu?a, wlh sun kaWu da jin asirin Elder ya tonu, dole su razana saboda basu taba tsammanin asirin shi zai tonu cikin sau?i ba, shi da yake shugaban su, ina ga su na ?asa da shi.


Abun da ya daure musu kai ta yadda har sihirin shi ya?i tasiri a lokacin da khala take tona mishi asiri, bayan haka sun yi mamakin tabya akai ta rayu bayan Elder ya tabbatar musu da mutuwar taS'

A ?alla Elders din dake a dakin sun kai su goma sha Waya, gaba daya sun tattara nutsuwarsu sun mayar da hankulansu akan Elder da ke kora musu jawabi cikin harshen su na matsafa..


"Ha?i?a yau na ji kunyar da ban ta6a jin taba a rayuwata, nasan da zuwan wannan ranar amma ban ta6a zaton zata yi silar da zan ji danasani atare da ni ba, hankalina ya tashi, zuciyata ta karaya, fargaba da tsoro sun mamaye zuciyata, bawai don asirina ya tonu ba, sai don halin da na jefa rayuwar ya'yana da suka aminta da ni, nine silar Waukakarsu, nine ?ashin bayansu kuma jigo sannan jagora na rayuwar su, kuma nine abu mafi soyuwa agare su, kamar yadda nima na Wauke su dangina, bugun zuciyata, sune nake gani in ji dadi a raina, sune farin cikina kuma jin dadin rayuwana, amma a yau da asirina ya tonu a gaban idanunsu, na muzanta na ji kunyar da banta6a jin ta ba a rayuwana, na karaya da ganin yadda suke kukan bakin ciki saboda zaluncin dana aikata ma ya'yan su da kuma ha'intar su da na yi a matsayina na uba a gare su, na cuce su na cuci kaina, na kuma cuci ya'yan su dana sadaukar......."


Tun da Elder ya fara maganar sauran Elders din suka kafe shi da idanunsu da suka cika da tsantsar al'ajabi da rudanin maganarsa, gani suke kamar mafarki ne ba gaske ba, jin maganganun da suke fitowa daga bakin shi, asanin su da Elder mutunne mai taurin zuciya, bai ta6a karaya ba, kuma bai ta6a danasanin abunda ya ke aikatawa ba sai yau? Abun ya Waure musu kai tamau har sun fara kokwanton anya Elder din su ne? Ko dai musayarsa aka yi musu? Taya ya karaya cikin sauki ya ajiye makaman ya?insa?" Gaba daya sun ruWe matu?a.



"Harshe na bazai iya misalta muku irin kuncin da na ji a cikin zuciyata ba, naji bakin ciki da takaici mara misaltuwa, na ji radadin da yafi na ?unar wuta zafi acikin zuciyata, nayi fatan ace na mutu kafin zuwan wannan ba?ar ranar"



Ya faWa cikin raunanniyar muryarsa, a hankali ya dafe saitin zuciyar shi da tafin hannunsa.



Kafin ya Waura da cewa, "Jikana dana fi kauna yau da kansa ya sha?i wuyan rigata kamar zai doke ni, mutuncina ya zube a idanunsu, na yi musu mummunan tabon da har bayan ransu bazai ta6a goguwa ba, na yi zaton tsafina da dukiyata zasu sama min komai na duniyar nan, ban ta6a zaton akwai ranar da tsafina bazai amfane ni ba, a yau na raina karfin sirihina saboda na gane cewa shima tsafin ba gaskiya bane yaudarar kaine, akwai wanda yake da iko da masu tsafin da shi kanshi tsafin wanda idan ya so cikin da?i?a zai kar6e sihirin daga gare mu, kamar yadda dangina suka mutu a fagen fama, lokacin da ma?iya suka kawo mana farmakin bazata, mu tsafi gare mu sukuma basu da wannan tsafin amma a haka suka ci galaba akan dangina suka kashe kowa baifi mu shida muka rage ba a lokacin, In har tsafi bazai hana matsafi fuskantar mummunar kaddara ba, kuma bazai hana matsafi mutuwa ba, me hakan ke nufi....."? Ya karashe maganar cikin raunanniyar murya yana duban Elders din dake sauraron shi ..W'


"Bamu gane abunda kake nufi ba Elder! Kalaman ka suna nema su rikita tunaninmu, mun rasa gane ina ka dosa! maganganunka sun jefa mu a ruWani..." Jan le6e ne ya yi maganar..



"Ka gafarce ni Elder, amma na yi mamakin yadda kayi saurin karaya saboda kawai asirinka ya tonu a gaban ya'yanka? Kada ka bamu kunya mana, Faduwa ba taka bace Elder! Ba'asan Elder da rauni ba, kuma ba'a san su da saurin karaya ba, a sanin mu da kai jarumin namiji ne, wanda ba'a halicci zuciyarsa da imani ko tausayi ba, kaine kake ?arfafa mana gwiwa akan karmu kuskura mu bari zuciyar mu tayi raunin da zamu ji tausayin wani ko mu karaya.." A cewar Jan Ido...



Da kakkausar murya Jan Wuya ya ce, "Ni kuma baka ta6a bani kunya irin na yau ba Elder! Ina hankalinka da tunaninka suke? Ina dakakkar zuciyar ka take? Ina izzarka da zaluncinka suke! Kaine fa dodon dake tsoratar da wasu Yau kuma kaida kanka ka tsorata saboda asirin ka ya tonu a gaban ya'yanka uhum?"


Ya fada rai a 6ace, "kada ka bari son ya'ya ya rufe maka ido har ka yi abin da zaka yi danasani Elder! Idan ma kana tunanin ajiye kambun zalunci ka ne to ka daina! Saboda ka riga da ka makaro Elder! Tubanka bazai kar6u ba Elder saboda tarin Wumbun zunuban da ka aikata, Koda ka shiryu hukuma da al'ummar duniya bazasu kyale ka ba, mutuncin nan naka da ?imarka zasu ruguje za'a cigaba da tsangwamarka kaida ahalinka har sai ba?in ciki ya yi silar barin ku duniya, ka tuna kana da ma?iya kaida ya'yan ka, me kake tunanin zai biyo baya idan suka ji abunda ka aikata? Zasu yi amfani da wannan damar ne gurin cuzguna muku!"

Ya faWa da kakkausar murya hadi da dun?ule yatsunsa,



"Kuma idan hukuma ta dam?e ka sai ka yi danasanin zuwanka duniya saboda azabtarwar da zasu yi maka, bayan haka idan mutuncin ka ya zube, zaka tashi daga dattijon arziki ka koma ?as?antacce, mugu, kuma tantirin Wan ta'adda a idon jama'a, za'a cigaba da aibata ka ne..."



Ya faWa yana sakin dariyar sha?iyanci da alama shi ko a jikin shi bai damu da halin da Elder ya ke a ciki ba, shiru Elder ya yi bai tanka masa ba, hakan ya bashi damar cigaba da yin maganarsa, "Yanzu ya rage naka Elder, ka zauna kayi tunani kafin ka yanke shawara, har yanzu muna da damar da zamu farfaWo da gidan kurkukun ?addara, ka kashe kowa naka da ya san sirrinka, mu cika sharuWWan allon tsafin mu, a ganina ba dole saida Iyalanka zaka cigaba da rayuwa ba, kabar kowa naka, mu canza she?a...."



"Aminina, ni ina ganin mu Wauki shawarar Jan Wuya, ita kaWai ce mafitar dake gare mu, Ba zan so Waya daga cikin abunda ya faWa ya faru da mu ba, ina jiye mana tsoron kalubalen da zamu fuskanta, ni bazan baka shawarar ka kashe ya'yanka ba, amma mu yi nesa da duniyar mutane, inda babu wani mahalukin da ya isa ya tunkare mu koda ba zamu cigaba da yin tsafin ba.." Jan Harshe ne ya yi maganar cikin tausasa murya...



"Har yanzu baku fahimce ni ba, Na lura wasu daga cikin ku basu damu da halin da nake a ciki ba..." ya faWa yana jan numfashi gami da furzar da shi..



"Ba haka bane Elder, Mun fahimce ka, sai dai mu ba zamu mi?a wuya ba, koda kai zaka yi murabus daga kan mu?amin ka na Elder, Mu muna akan bakanmu, tsafi da rainon yara yanzu muka fara, babu wani mahalukin daya isa yasa mu ajiye makaman yakin mu..."

Wani Elder ne daga cikin su yayi maganar..



Jan Ido ya ce,"Fatan mu shine, ko da ka ji ka gani kana son yin murabus, Ka rufa mana asiri tun da mu bata kaiga faWin sunayen mu, ko a cikin Elders ba kowa ta sani ba! na gidan kurkukun ?addara kaWai ne ta sani, don haka muna rokanka alfarma ta ?arshe, a matsayinka na shugabanmu wanda ya yi silar Waukakarmu, kuma ?ashin bayan Elders na gidan kurkukun ?addara, wanda har abada ba zamu manta da kai ba, saboda kayi mana halaccin da har abada ba zamu iya biyanka ba, mu a wurinmu ka fiye mana kowa na duniyar nan, bauta maka ne kaWai bamu yi ba, amma ka cancanta har bautar ma mu yi maka..." Elder din da ya Wauko maganar bai kaiga dire ta ba, sakamakon buga sandar da Elder ya yi da ?arfi akan floor, tuni kowannansu yasha jinin jikin shi, magana yake son yi saidai ya kasa furta ta saboda raunin da zuciyar shi ta yi..


Da?yar ya tattara ?warin gwiwarsa ya ?arfafa zuciyar shi gurin furta, "Ni bazan Wauki huWubar ku ba, na riga da na gane kuskure na, na yi danasani kuma zan mi?a wuya a gare su, saboda inason su dauki fansar abunda na aikata ma ya'yan su, wata?il ta silar hakan su yafe mini, kuma a shirye nake da in fuskanci ?alubale in dai akan su ne..."

Ya Wan dakata yana jan numfashi kafin ya Waura da cewa, " Kuma ina baku umarni! tun wuri ku ajiye makaman ya?in ku, zaku iya guduwa ku nemi mafaka don ku kare kanku, amma kada ku cigaba da aikata miyagun ayyukan da kuke yi, yakamata ku dauki darasi a kaina, kuna gani dai sihirina bai amfane ni da komai ba...."

Bai ?are maganar ba, Jan Wuya ya katse shi abun da bai ta6a yi masa ba, yana huci ya ce, "Ya isah haka Elder! Yakamata ka san mi zaka faWi! Bai kamata kana tursasa mana akan mu bi ra'ayin ka ba, bayan kaine ka janyo mu cikin harkar, ka lasa mana zuma a baki, don haka mu ba zamu fasa ba, ba gudu ba ja da baya, kawai abunda muke so kayi mana shine karka kuskura ka tona mana asiri, tun da mu asirinmu a rufe ya ke, bata fallasa mu ba, kai tun da ka ji zaka iya ha?ura saboda zuciyarka ta mutu akan son ya'yanka to ka je ka mika wuya, wanda ya ?i ji ba zai ki gani ba....!"


Bai karasa maganar ba, Elders suka dakatar da shi ta hanyar daka mashi tsawa, yana huci ya ja baki yayi shiru badan ya so ba..

Cikin fusatacciyar murya Jan Harshe ya ce, "Ka fara wuce gona da iri Jan Wuya! Ka iya bakin ka! in ba so kake in canza maka kamanni a gurin nan ba, tun kan aje ko'ina har ka fara yi mashi magana da tsawa! Wanene kai? Bana tunanin ko darajar takalman ?afarsa ka kai, kai din ba bawansa bane da ya Waukaka ya baka mu?ami? Zaka iya biyansa abunda ya yi maka ne?"

Ya faWa a tsawace yana kallonshi, Maganar Jan Harshe ta ?ona masa rai, Zuciyarsa ta zo wuya, har wani gurnani yake fitarwa saboda 6acin rai..



"Koda Elder ya aje mu?aminsa hakan ba yana nufin ya zama abun wula?antawa a gurin mu ba, har abada shine Elder na kurkukun ?addara, da izininsa komai ke faruwa, idan ya so cikin da?i?a zai ?wace sihirin dake a jikin kowannanku! Ya kamata ku san da wannan, gargadi ne na yi maku, idan ma akwai wanda ke da wani mummunan kudiri a cikin ku...." Ya fada yana nuna su da sandar hannunsa.


Gaba daya suka sha jinin jikinsu hatta Jan wuya da yake ta tada jijiyoyin wuya saida ya sha jinin jikin shi saboda baida wani ?arfi in har Elder ya kwace sihirin jikin sa, dama da shi ya ke ta?ama, lokaci Waya suka sauko daga kan kujerunsu suka zube kan gwiwowinsu, kamar zasu yi mashi sujjada ?iris ya rage goshinansu su ta6a ?asa...



Atare suka hada baki gurin furta,

"dodon tsafi ya huci zuciyarka Elder, a gafarce mu Elder, tuba muke Elder, kanmu bisa wuyan mu, zamu yi biyayya agare ka, ka rufa mana asiri kada ka rabamu da sihirin da ke a jikin mu"

Mutum Waya ne bai zu?unna ba a cikin su, Mi?ewa ya yi daga kan kujararsa ya nufi Elder da ya sadda kanshi ?asa, hannunshi da ya ru?e sandar shi da ita sai kerma yake yi..


Dafa kafaWunsa Jan Harshe ya yi da tafukansa, tun kafin ya yi magana Elder ya riga shi cewa, "Kada ka ce min komai, ka barni kawai, bazan canza ra'ayina ba, zan bar maka komai har mu?amina, amma ni bazan bar ?a'?ana ba, dame za su ji idan na gudu? Ya faWa cikin rawar murya....

"Rashin ganina zai ?ara jefa su cikin mawuyacin hali, ni dai koda zasu tsane ni ne na ?wammace in zauna atare da su..."


Kasa ?arasa maganar ya yi saboda kukan da ya sar?e makoshin shi.." Cikin raunaniyar murya Jan Harshe ya ce, "Bazan misalta maka tashin hankalin dana shiga ba, naji kwatankwacin raWaWin da ka ji acikin zuciyarka, kamar yadda kayi danasani nima na yi danasani aminina, kuskure ne mun riga da mun tabka shi!" Ya fada cike da takaici....

"Amma na Waurawa kaina alhakin kowani laifi da ka aikata saboda nine sila, lokacin da ka ?yamaci abun a zuciyarka, ka nuna cewa ba dole saida tsafi zamu cimma burinmu ba, akwai wasu sana'o'in da zamu iya yi, ni ne na tunzuraka da cewa ba zamu ta6a samun abunda muke so ta cikin sau?i ba sai ta wannan hanyar, kuma gadonka ne da iyayenka suka bar maka, bai kamata ka yi watsi da shi ba, a lokacin na matsa maka har saida ka dauki shawarata ka ha?a sihirin ka maida shi a jikin ka, wanda nayi imanin da ace babu Evils a jikinka ba zaka ta6a iya kashe rai ba...." Kifa kan shi ya yi akan kafaWar amininsa sosai ya fashe da kuka mai tsuma zuciya..


Hakan ba ?aramin Waga hankulan Elders ya yi ba, jin kukan Elder, tun da suke da shi ba su taba ganin ko da Wigo na hawayen shi ba, tabbas sun razana sosai, faWuwar gaba ta darsu a zukatansu..


"Ka yi hakuri na cutar da rayuwarka, na jefa ka a tsaka mai wuya, amma ka jure ka dauki shawarar Jan wuya, mu yi nesa da duniyar mutane, saboda ina jiye mana tsoron azabtarwar da zamu fuskanta agurin hukuma da kuma tozartar da zamu yi a idon duniya, in ya so idan muka gudu sai mu bar harkar tsafin mu tuba..."



A hankali ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login