Showing 171001 words to 174000 words out of 321579 words

Chapter 58 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

fargaba.


Kusan gaba Wayansu suna a falo cikin damuwa, kowa?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ka kalli fuskarshi babu annuri bacci su ke ji amma damuwa ta hana baccin ya Wauke su, sun kasa sun tsare suna jiran dawowar ?a'yan su, Sheikh imam ne ke tausarsu da nasiha mai ratsa zuciya, Taj ne kadai baya a falo bai jima da fita ba, ya je ya kwantar da baby Junaid da ya yi bacci, Benazir da Aisha da Anila Suna a zazzaune kan Sofas sun zabga tagumi suna sauraron Sheikh Imam, yayin da Dr shureim yake a gefen shi, shi kanshi Imam malik din ba ?oshin lafiya ne da shi ba, sosai yake jin Wacin abun da Musa ya yi mashi a ranshi, ya yi masa abun da har abada ba zai manta da ba?in cikin nan ba, amma ya Wauki dangana, kuma baya son rauninsa yasa suma su shiga damuwa ko dan Saboda al?awarin da ya Waukarwa Aisharsa.


*TAJ

Yana a zaune gefen gadonshi. Idanunshi akan baby Junaid dake ta sharar bacci, bakomai ne ya fado masa aran shi ba face wasu maganganun da suka ta6a yi da Uzair, Allah sarki ba rabon Uzair yaga gudan jininsa..

Tunawa ya yi da lokacin da Unaisah take yar jinjirarta, murmushi ya yi, yayin da hawaye suka cicciko idanunshi, baya jin zai iya rayuwa batare da ?ar shi Unaisah ba.


Shafa fuskar Junaid ya yi da tafin hannunsa, bai aune ba ya ji ya ka6e masa hannu cikin magagin bacci ya soma yin sambatu yana fadin, "Ni ka daina kallona, duk ka takura ni, ka tashi ka tafi tun da ka kwantar da ni."

baisan sa'adda ya yi dariya ba.

Ashe idanunshi buWe suke, sun yi ja sai cika yake yana batsewa.

"Baby Junaid, Ni ne fa? Daddy Taj."

Zum6ura masa pink lips dinsa ya yi, "Ni ba wani nan, kawai ma ka takura ni, Allah saina faWe mata abun da kake mini.."


ya faWa yana kokarin mi?ewa zaune da sauri Taj ya mayar da shi ya kwantar, ya janyo duvet ya lullu6e shi dukan shi.

"Pls ka yi hakuri ka yi bacci, ba zan ?ara damun ka ba"

"Toh ka tashi ka tafi." Murmushi ya yi tare da mi?ewa cikin sanWa ya fuce daga dakin.

Le?owa Junaid ya yi daga cikin bargo, ganin babu Taj yasa shi mayar da kansa ciki ya ci gaba da yin baccinsa.


Unexpected wayar Taj ta soma ruri, a lokacin yana gab da zai shiga falo, cikin sauri ya zaro wayar, ko da ganin sunan my in-law ya bayyana yasa shi saurin picking yatsunsa har kerma suke saboda zumuWin ya ji ya ake ciki, duk da yana fargaban me zai ji daga gare sa.



"In-law, Guess what? Muryar Chief ce ta katse shi.


?an zaro idanunsa ya yi cikin rudu ya ce, "Chief, bangane me ka ke nufi ba? Kun samo su um?"


Sautin dariyar Chief Owais ya jiyo, "Ka fara yin sujudusshukr kafin in sanar da kai." Cikin sauri ya fuskanci alkibla ya yi sujjada, kafin ya mi?e yana tambayar shi meya faru?"


Nan take Chief ya zayyana mashi komai da ya faru a gidan Kurkukun kaddara! Ya Ilahi ji ya yi kamar a mafarki.


Ya ?ara da cewa, "Yanzu haka Elders suna a CSH ana yi masu treatment saboda raunukan da suka ji, Unaisah da Batool kuma suna a cikin asibitin Headquarter din mu, lafiyarsu kalou, amma ana ?ara bincika lafiyarsu, saboda kwakwalwar Unaisah ta Wan ta6u sakamakon razanar da ta yi..."


Bai ?are sauraran Chief Owais ba ya arta a guje ya nufi main door zai fuce.


Gaba daya suka bi shi da kallo, muryar Benazir ce ta katse shi, "Taj, meya faru? Ina zaka je?"


Ya juyo fuskarsa Wauke da murmushin farin ciki ya ce, "Sun dawo. Sus.. Suna a headquarter Win mu! Unaisah da Batool..."

kusan a tare suka mi?e tsaye tare da bin bayan shi, tsabar ?aguwa kamar zasu bangaje juna.

Sheikh Imam da Aisha motar Dr Shureim suka shiga., Benazir da Anila suka shiga motar Taj, tare da Motocin Securities gaba da bayan nasu motocin.


A lokaci Waya motocin suka fuce daga villa din sai baza gudu suke yi saman titi kamar zasu tashi sama..




*ISOD HEADQUARTER=?%?*




Lokacin da motocin su suka ?araso Headquarter basu sha wahalar shiga ba, suna yin parking dinsu, cikin sauri suka fito daga ciki, Taj da Benazir ne a gaba, Ummi da Shureim suna a biye da bayansu, yayin da Sheikh Imam da Anila suke biye da su.


Isod Soldiers din dake zarya a tsakar headquarter din sai kallonsu suke yi, sai dai kwata kwata babu alamun sun ma san da zaman su saboda hankalinsu na akan abun da ke gaban su.


Da yake sun san da zuwansu kuma ga Taj a tare da su hakan yasa duk inda suka bi a hanzarce agents din dake a ciki suke darewa su basu hanya don su wuce.


Lokacin da suka karya kwanar da zata sada su da inda suke unexpected suka soma jiyo ihun Unaisah tana faWin, "Acid na watsa mashi akan fuska! Na ?ona masa fuska, ya mutu! Bazai ?yale ni ba, gayanan ina ganin shi, fatalwarsa ce, kashe ni zai yi..."

Tsantsar farin ciki da rudani ne akan fuskokinsu, cikin sauri suka faWa Private room din, Doc suka gani a bakin gadon da take, Chief Owais yana a zaune daga gefen gadon ya rurru?eta, sai ihu take tana firgita kamar mai aljanu.


"Babyna..." Benazir ce ta faWa, da gudu ta nufi gadon, Chief Owais ya mi?e ya bata guri, zama ta yi tare da janyota ta rungumeta akan kirjinta, batasan sa'adda ta saki kukan farin ciki ba.


Ta dinga shafa bayanta tana fadin, "Unaisah ki daina kuka, mommyki tana a tare da ke! Ina fata basu cutar min da ke ba.."

Jajayen idanunta ta Waura akan benazir, tana magana yawu na fita ta bakinta ga majina dake zalalowa ta hancin ta, "Acid na watsa mashi a saman fuskar shi, na ?ona shi, ina ganin shi da idanuna yana a cikin Wakin nan ya ce sai ya kashe ni, gashi nan zai ta6a ni...!"


da karfi ta faWa a rikice, shatun jijiyoyin wuyanta sun fito rudu rudu.

?an?ameta Benazir ta yi kamar zata mayar da ita cikin cikinta..

Babu wanda bai tausaya mata ba!

"A ina aka gan su? Ina Batool? Ina Musan? Bai cutar da su ba? Meke damun Unaisah ne?" Chief suke ma tambayoyin, Shureim sai baza idanunshi ya ke yi burinshi ya ga Batool dinsa haka itama Ummi ta kasa samun sukuni.


"Pls, ku kwantar da hankalinku, ba a cutar da su ba, Unaisah ta yi faWa da Musa harta yi nasarar watsa mashi acid a saman fuskarshi, shiyasa ta razana, kamar gizau ya ke yi mata tun Wazu muke ta kokarin mu shawo kanta mun kasa, ga docs nan ta ?i bari su duba ta, kowa ya kawo hannu zai ta6a ta sai ta fashe da ihu tana faWin gayanan zai kashe ta.."

Tsantsar mamaki ne da rudani akan fuskokinsu, akwai tambayoyi da dama da suke son yi mashi sai dai sun lura ba a cikin nutsuwar shi ya ke ba.


"Ina Batool? Itama hada ita kuka dawo?"


Dr Shureim ne ya tambaya cike da damuwa..

"Harda ita muka dawo, amma sai dai ku yi ha?uri..." Gaban su ne ya fadi, cikin rawar murya Ummi ta ce, "Pls ba sai ka fada ba, in dai ba alkhairi bane ka yi shiru, zuciyata zata iya bugawa in mutu!"


Fuskar Owais babu annuri ya ce, "Tun da baku bu?aci in fada ba ku biyo ni mu je ku gani da idanunku, amma pls komai zaku gani ku yi ha?uri."

gaba daya sun sha jinin jikinsu.


Bayan fitarsu daga Wakin ya rage saura Unaisah dake rungume a kirjin mommynta, Taj yana a zaune kan kujerar dake fuskantar su, addu'oi suke ta tottofa mata akan ta.


Doctor din da ya zo duba ta yana a tsaye yana jira su kammala shawo kanta don ya samu ya yi mata allura.


A gaban dakin da take suka tsaitsaya cirko cirko, saboda zullumi da farbagan abun da zasu taras ya sa kowannan su yake jin tsoron ya shiga ciki.


"Bismilla, mu shiga daga Ciki."

Chief ne ya faWa tare da bude masu ?ofar Wakin.


"Dan Allah sir, ka fara faWa mana a wani hali take ciki? Ina jin tsoron na ga abun da zai yi silar mutuwa ta!"

"Ummi, ke da kan ki kika ce inna san ba alkhairi bane kada na faWa, why zaki canza magana, kawai ki shiga ciki." Yanayin yadda yayi mata magana da walwala akan fuskarsa kamar ba Chief Owais ba.


Sheikh Imam ne kadai hankalinsa bai tashi ba saboda yasan Chief Owais ba zai ta6a bari su zo ganinta ba in har wani mummunan abun ya faru da ita..


Tura kofar sheikh Imam ya yi, ya shiga da bismillah a bakinsa, yana dira ?afarsa ya hango ta a kwance saman gado ta yi Wai Wai tana ta sharar baccin ta.

Wani irin annurin farin ciki ne ya lullu6esa da ?arfi ya furta, "Alhamdulillah, ku shigo ku ga jikata da ranta da lafiyarta ba abun da ya sameta..."


A hanzarce suka bankaWo cikin dakin, Ummi da Shureim suna Waura idanunsu akanta, wani irin daWine mai tattare da farin ciki ya cika zukatansu, kamar wadanda aka yi wa albishiri da gidan Aljanna, bakinsu ya ?i rufuwa, idanunsu sun cicciko tab da kwalla. Kewaye gadon suka yi, jikin Ummi na 6ari ta zauna daga gefe, ba zata iya jira ta farka ba, tallabo kanta ta yi tare da rungumeta a ?irjinta, batasan sa'adda kukan farin ciki ya 6alle mata ba, wallahi sai ta ji gaba daya kamar an yaye mata ba?in cikin da ke a cikin Zuciyarta.



Cusa yatsun hannayenta ta yi a cikin gashin Batool ta na yamutsawa kamar tana yi mata susa ta ?an?ameta, ta fara manna mata sumbata tun daga kan kuncinta har izuwa goshinta, kamar zata lashe ta, ta ma manta da sauran mutanan dake a Wakin, kowan nan su murmushin farin ciki ne Wauke akan fuskarshi, Dr Shureim sai washe baki ya ke yi, har sujudusshukr ya yi a dakin, lokacin da ya Wago hawaye ne sharkaf akan kuncinsa, sai kallonsu ya ke yi kamar zai haWiye su.


Matsewar da Ummi ta yi mata ne yasa ta farka daga bacci, tunkan ta buWe idanunta hancinta suka shakar mata ?amshin turaren Aunty Umminta wanda koda yaushe in kana a kusa da ita sai ka ji shi a jikin ta.

Cikin rawar murya ta shiga furta, "Aunty Ummi? Ke ce? Kece a kusa da ni? Aunty Ummi kamshin turarenki nake ji? Dan Allah in bacci nake yi kada ku farkar da ni, mommyna kawai nake so na kasance da ita har ?arshen rayuwata, dan Allah kada ku bari ya raba ni da ita, ina so na rayu saboda ita, ina so na sanya ta farin ciki..."

Sambatun da ta ke yi ba karamin karya musu zuciya yayi ba.
Shiekh Imam a fakaice yake sharce ?walla, bakomai yake tunawa ba, fa ce ranar da ya kar6eta cikin tsumma daga hannun Aunty Laura, ya jinjina ta ya kira ta da sunan shegiya a gidansa, Ya Ilahi! Ya yi danasanin furta kalmar nan.


Tallabo fuskarta Ummi ta yi da tafukan hannayenta, hawayen dake zarya kan kuncinta kaitsaye suke sauka akan kuncin Batool hakan ya tuna mata da ranar da ta haifeta irin hakan ta faru.


"Batool, ki saka idanunki a cikin nawa, ni ce a tare da ke, ba abun da zai faru da ke, kuma babu wanda zai ?ara raba ni da ke, ba zan sake maimaita kuskuren da na yi ba Batool, bazan ?ara tafiya na barki ba, ina sonki fiye da raina..."

A hankali ta soma buWe idanunta da suka yi mata nauyi saboda baccin da ta sha, har yanzu allurar da doc sukai mata bata sake ta ba, wata irin malalaciyar kasala take ji.


Dakyar ta iya tsayar da idanunta a cikin na ummi.


Cikin disasshiyar murya ta furta, "Aunty ummi na.. "

jinjina mata kai ta yi da murmushi ta ce, "Daga yau ba sunana aunty ummi ba, ni ba gwaggonki bace, kuma ba yayyarki bace, Mahaifiyarki ce, ki kira ni da Mommy, ko kira ni da Ummi"

gaba daya suka saka dariya cikin raha.

Sam ta kasa kawar da idanunta daga kallon fuskarta, gani take kamar mafarki ne.

Cike da so da ?auna suke kallon juna.


"Batool, ni baki ganni ba?" Dr shureim ne ya yi maganar cikin karyayyar murya, a hankali ta mayar da idanunta akan fuskar shi, lokaci Waya ta shiga tariyo maganganun Musa a cikin kunnanta, ta ji komai, ta ji irin ba?ar izayar da mahaifinta ya sha saboda ita.


Fashewa ta yi da kuka kamar ranta zai fita, gaba daya hankalinsu ya tashi matu?a, a tunaninsu wani abunne ya 6ata mata rai, lallashinta suka dinga yi, Dr Shureim har ya karaya, ya yi zaton saboda ta ji shine silar abun da ya faru da mommynta shiyasa ta ke kuka, kallon da take masa ya yi masa kama da kallon tsana.

Jiki a sanyaye ya juya zai bar Wakin batare da kowa ya lura ba, baisan idanunta a kan shi suke ba, ?wacewa ta yi daga jikin Ummi, duk da rashin kwarin jikinta a haka ta duro daga kan gadon, suna ta tambayarta ina zata je, Anila na kokari ru?ota ta ka6e hannunta, da gudu ta bi bayan shi, yana gab da zai fuce ya ji ta rungume shi ta baya ta zagayo da hannayenta kan cikin shi, sosai ta ?an?ameshi, wani sanyi ne ya ratsa zuciyar shi kamar kamar me.


cikin shesshekar kuka ta furta, "Daddy, ina zaka tafi ka barni? Bakasan na fi bukatar ku akan komai ba? Daddy ina son ka wllh, kaine bugun zuciyata, jagoran rayuwata, wanda ya tsaya mini tsayin daka don ganin ban yi maraicin uwa a tare da ni ba, uban da zai iya sadaukar da rayuwarsa saboda ?arsa ta rayu, idan babu kai babu ni daddy..."


Yayin da take furta masa kalaman nan, ji yayi kamar anyi mashi albishir da gidan Aljanna, farin ciki kamar zai kashe shi, gaba daya mutanan dake a dakin saida suka yaba da iya tsara kalaminta, ta burge su, ta kuma sace zuciyar su, especially Sheikh Imam da Chief Owais sun kasa dauke idanunsu daga kallon su.


A hankali ya ru?o yatsun hannayenta, yayin da yake tunawa da ranar da ya fara ganinta tana jinjirarta, a lokacin da Ummi ta kawo mashi ita cikin tsummanta.

Janyota ya yi ya dawo da ita ta gabanshi, ya sanya hannayenshi biyu ya yi hugging dinta tighly kamar zai mayar da ita cikinsa, a hankali yake shafa sumar kanta har izuwa saman kanta, so yake ya yi magana shesshekar kuka ta hana shi.


"Kun ga yadda Allah ke ikonsa ko? An raba ku saboda zalunci, Allah kuma ya sake haWaku ta yadda ku kanku baku ta6a tsammani ba, ribar hakuri da tawakkali kenan, mu run?a hakuri da kowace kaddara ko jarabawa da ta same mu, duk abun da Allah ya yi a rayuwarmu mai kyau ne, amma sai mun yi hakuri zamu gane hakan, kawai mu yi hakuri mu ci gaba da addu'a, mu kuma yi masa biyayya kada mu sare ko mu butulce masa, mu dinga tunawa da ni'imomin da ya yi mana kafin jarabawarsa ta riske mu..."


Anila ce ta yi maganar fuskarta Wauke da murmushi, hawaye sun ciko idanunta abun ya ta6a zuciyarta.

"Zan iya cewa, yau ce rana ta huWu da na yi farin ciki mara misaltuwa a rayuwata, ranar dana ga su Taj a raye, da ranar dana ga Aisha da Benazir da ransu da lafiyarsu, sai kuma yau da Allah ya nuna mini abun da ya fi komai faranta raina.."

murmushi suka yi gaba Wayansu.

Mi?ewa Aisha ta yi daga kan gadon ta je gaban Dr Shureim ta tsaya tana kallon su..

Ita shaida ce akan irin kaunar da yake ma Batool dinta.

Da kyar ya iya furta, "Ki yi hakuri Batool, bada son raina komai ya faru ba, bansan na binne ki ba, bana a hayyacina, kuma bansan kina a raye ba, da wlh har raina zan iya badawa don in ceto rayuwarki.."

?agowa ta yi da fuskarta dake a ji?e da hawaye, "Abba, zan ro?e ka alfarma Waya a duniyar nan."

Cikin sauri ya ce, "Zan yi maki, komai kike so ki faWi." Kowa ya nutsu yana jiran ya ji me zata ce.

"Pls, mu manta da abun da ya wuce, bana ganin kowan nan ku da laifi, komai da ya faru na sani bayin ku bane, na ji komai da kunnena, idan kuna yin magana akan abun da ya faru a baya baku tunanin zai haifar min da damuwa?"

Batool ba karamin kashe su ta yi da dadi ba, tun yanzu sun san wacece yar tasu, yarinya mai tawakkali, mai hankali da tunani jikar Imam Malik kenan, Wiya ga Ustatha Aisha bintu Imam da d
Dr.Shureim, lallai ta fito daga tushe mai daraja.


"Na yi maki wannan alfarmar Batool, mun daina, ba zamu ?ara ba." Ya fada yana share mata hawayenta.


Murmushi ta yi, "Nima yanzu ina da iyayen da zanyi alfahari da su, ina da gata, sannan daga yanzu za'a dinga kira na Batool Shureim kamar yadda ake kiran yar uwata da Unaisah Zaheer Tajudeen."

gaba Waya suka sanya tafi.


"Ina taya ku murna gaba Wayan ku, Allah raya mana Batool dinmu Allah kuma ya kare mana ita."


Anila ce ta fada tana nufar su, janyo batool ta yi ta rungumeta sosai.


"Nima ina taya ku murnar ganin ?ar ku, kuma in sha Allah, ba za ku sake rabuwa da ita ba."


Chief Owais ne ya faWa cikin sanyin murya.


Godiya suka yi ma shi, kafin ummi ta ja hannun Batool ta kaita gaban sheikh Imam malik, "Kin gane shi ko sai na yi maki bayani?" Murmushi ta yi, "Kakana ne, Baba Imam."

Rungumeta ya yi a kirjinshi ya fara saka mata albarka da yi mata addu'o'i yana jin sonta da ?aunarta na ratsa shi, ita ce jikar shi ta farko kuma Waya ?wallin ?wal daga gurin ?ar sa abun alfaharin sa.


Allah kaWai yasan Wumbin farin cikin da Batool ta ji a yau, wallah baya misaltuwa.

A hankali ta raba jikin ta daga na sheikh Imam Malik, Ummi ta ru?o hannunta ta kuma ru?o hannun sheikh Imam, ta ja su har gaban Chief Owais, ta yi ma Shureim da Anila alamar su matso kusa da su, duk yana a tsaye yana kallonsu ya harWe hannayen shi kan ?irjin shi ya rasa gane me zata yi.

"Assalamu alaikum."

Muryar Taj


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login