Showing 282001 words to 285000 words out of 321579 words

Chapter 95 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

baison kowa ya rasa ran shi,..."

Dg yace "Kusan kullum sai Uncle Hateem ya kira ni ya tambayeni Ina baby boy dinsa, sai in rasa amsar da zan ba shi, kasan ya kwallafa rai akan Danish, pls Commender ka bani shawara, tayaya zan san idan yana araye koya mutu"? Ya tambaya yana kallon Haroon daya yayi shiru yana kallon shi.

Numfasawa yayi kafin yace"me zai hana mu sake yin meeting, idan komawar ta kama muyi sai muje, saboda ko da ace Danish Ya ku6uta tayaya za'ae mu iya sani mu? Yaron da baisan komai ba? Bazai iya kawo kan shi gidanka ba Sir, zai ma Iya fadawa wani gurin"!

Maganar Haroon Ta Waga hankalinsa, Harya bude baki zai kuma yin magana kwatsam Wayarsa dake akan table ta hau yin ruri, janyo ta yayi tare da duba screen din, ya mutsa fuskarsa yayi batare da yayi picking ba..

"Sir, tun da muka fara magana ake ta kiranka awaya, yakamata ka daga kaji wanene"? Girgiza kai yayi"haroon, kasan bana Waga bakuwar number, babu wanda yayi requesting yana son magana dani wannan layin special ne ba kowa yake dashi ba, kuma numbar daga kasar benin ne tayaya zan Waga? May be wrong number ne tun jiya suke kira"

Commender Yace"Sir, kayi hakuri ka daga kiran nan, Ni inaji araina kira ne mai mahimmanci, kuma saboda kai akayi shi, kamar yadda kace Contact dinka special ne, babu wanda zai iya hasashen numbarka in ba wanda ya ta6a gani ba, bana so rashin dagawarka ya zama silar da zamuyi danasanin rasa abun da wanda ke kira zai faWa maka"!



har kiran ya katse baiyi picking ba, Commender haroon ne Ya matsa mashi akan ya daga kiran, yana kokarin bin kiran sai ga sakon da Khala ta turo mashi, wata irin zabura yayi tare da mikewa yana zare idanunsa yayin da ya ke karanta sakon.

A sukwane commender Haroon Ya mike tsaye yana tambayar shi lafiya? Meya faru"? Muryar shi na rawa ya furta"Khala da Danish suna araye! Ina tunanin su ne suke kira na"!

washe baki Haroon yayi, tsantsar farin Ciki da al'ajabi ne akan fuskokin su..

Jikin shi na kerma Ya kira layin, kiran na shiga aka Waga.

Cike da zumudi Ya furta"wanene ke magana"?

Muryar Danish ce ta ratsa kunnuwan shi.

"Chief, it's me Danish.."

tsantsar al'ajabi ne ya ruke shi tamau, idanunsa azare, baisan sa'adda Ya yi sujjada ba tare da furta"Alhamdulillah Alhamdulillah.."

mi?ewa yayi ya kanga wayar a kunnansa" Danish dama kana araye? Danish Kana Ina yanzu? Tayaya zan hadu da kai"?

Shiru bai bashi amsa ba, yana ta kiran sunan shi har ya yi tsammanin kiran ne ya katse Unexpected yaji muryar dattijo na magana da turanci

"Barka yalla6ai, kana magana da adamu ne, daga nan Abomey-calavi benin".


gaba daya tsohon ya zayyana masa ta yadda suka taimakesu a daji..

wani irin farin ciki ne Ya cika Chief Owais Ya ce ma tsohon su kula da su, zai basu ko nawa su ke bu?ata, bai son komai ya same su, yau zai shigo ?asar.."

Dattijon Yace mashi Toh, Allah ya kawo shi lafiya.."

yana gama wayar, Ya fayyace ma Haroon komai da suka tattauna da dattijon, Waga hannayensa sama yayi Tare da yin hamdala Yace dama shi saida ranshi ya bashi kiran nan mai mahimmanci ne shiyasa ya matsa masa akan yayi picking, yanzu abun daya kama suyi shine su kira Pilot dinsu .

Batare da bata lokaci ba, nan take Chief Owais Ya kira jet Pilot din su.

Bugu Waya yayi picking,

"Captain I need you to prepare the jet for immediate departure."

"Destination, sir?"

"Abomey calavi benin, to be precise."

"Benin Republic, sir?"

"Yes, I have urgent business to attend to, Ensure all necessary clearances are obtained."

"Understood, sir, What's the estimated departure time?"

"Two hours from now, Make sure we have sufficient fuel for a return trip."

"Consider it done, sir Will there be any passengers accompanying you?"

"Yeah, ni da Commender Haroon ne"

"Okay sir"


Daga haka sukayi sallama, Ya mayar da wayar a cikin aljihunsa, Ruke hannun Haroon yayi a hanzarce suka fito daga office din tsabar sauri lift suka hau ta sauke su down, Suna futowa suka nufi parking space tun kan su karasa SA ya buWe masu mota, a back seat suka zauna, SA din Ya shiga Ciki, Chief yace Ya wuce da su NAI Aiport, da matsakaicin gudu motar su ta fuce daga Headquarter din..

Lokacin da jirginsu yayi landing a Airpot din dake a cikin birnin abomey calavi..

Bayan sun fito daga Airpot din, Ya kira layin Adamu Ya fada ma shi Location din da zasu same shi.

Bada jimawa ba, Sai ga Motar dattijan ta karaso inda suke, basu sha wahalar gane su ba, saboda Chief ya kwatanta ma adamu kakin da ke a jikinsu.

Bayan sun Waukosu a motar suka nufi Gidan Gonar da su, kowa da abun da yake sa?awa aran shi, su suna Allah Allah aransu su isa don suga Idan sune, yayin da su kuma dattijan suke ta ayyana kudaden da zasu samu agurinsu, tun da suka ga yanayin shigarsu suka fahimci akwai arzi?i atare da su.

Lokacin da suka karaso gidan Gonar, bayan motar tayi parking, suka fito gaba dayansu cike da zumudi Chief ya tambayi suna Ina.

Dattijan sukace ya fara biyan su tukunna su nuna masu inda suke!

Commender Haroon yace"karsu raina masu hankali, basu ga kakin dake a jikin su ba? harara daya daga cikinsu Ya watsa masu Yace"Idan har ba zasu biya su ba, to su koma inda suka fito.."

Chief yace su fadi ko nawa suke so, zai biya su da dollar.

Commender Yace ba zasu basu ko sisi ba, ya ma daina maganar zai biya su, kamar fa sunyi kidnapping dinsu ne, wanda hakan Ya sa6a ma doka a matsayinsu na jami'ae su biya kudin garkuwa.."

Chief yace"bazai iya jurewa bane, Yana son ya gan su"

Commender Yace"har yanzu bai yarda da su ba, kada sai sun biya su kudin su ki nuna masu su.." da harshen hausa sukayi maganar hakan yasa dattijan basu iya gane me suke cewa ba..

Haroon Ya ce"sunji zasu biya su ko nawa suke so, amma su fara nuna masu koda hotunan su ne, don su gasgata ba karya suke masu ba"

da sauri adamu ya zaro wayarsa daga aljihu Ya buWo hoton Danish daya dauka batare da sanin shi ba a lokacin dayake bacci shida khala Ya nuna masu


Farin ciki ne ya lullu6e Zuciyoyin su, nan take Chief ya kar6i account number dinsu saida ya fara canza masu kudin da wayarsa Ya maida kudin kasar su tukunna Ya tura masu kimanin miliyan biyar"


koda suka ga kudin sun sauka a cikin account dinsu, tsabar murna yasa suka zube kan gwiwowinsu sunayi mashi godiya kamar zasu kai goshin su kasa, daga gani Shegen son kudi gare su, gashi daga taimako sun samu kudin da sai sunyi shekaru zasu iya tara su..

Rakiya sukayi masu har zuwa dakin da suke.

Chief ne Ya fara shiga dakin, kaitsaye idanunsa suka sauka akan Danish dake a kwance kan katifa Yana bacci, shi kadai

A hankali Ya zauna daga gefen katifar, Commender Haroon Ya zu?unna gefe Waya, Yayin da dattijan suke atsaye bakin kofar dakin suna kallon su sai faman washe baki su ke yi.


Harara Haroon ya watsa ma su yace "ku rasa a ina zaku aje mai rai sai a wannan kongon gidan" ya fada Yana jifar su da harara, hakuri suka hau ba shi dayake sun basu kuWi.

Hankalin Chief baya akansu, Zuciyarshi ta karaya da ganin halin da Danish Yake a ciki..

A hankali Ya shafa gefen fuskarshi, ya Wan bubbuga kirjin shi, numfashi Yaja tare da kokarin bude idanun shi da suka disashe saboda bacci..

"Danish, Chief ne, ka tashi kaganni, Ina atare dakai"

a cikin kunnansa ya tsinkayi muryar Chief, Firgigit ya karasa ware idanunsa da suka kada jawur, yana ganin Chief jikinshi na 6ari Ya mi?e zaune tare da janyo shi suka rungume juna kamar zasu koma mutum Waya, gaba daya hannayen chief na a saman bayan Danish, Cikin sigar lallashi ya ke shafa bayansa.


"Ina tsohuwar take? Ko itama sai mun biya zaku nuna mana ita"?

Haroon ne ya fada yana jifar su da harara.

kafin su furta Kalma sai ga Khala ta fito daga Cikin toilet din dakin, dakyar take taka kafarta koda idanunta su ka yi mata tazoli da Chief dake a rungume Da danish sai taji wani irin farin ciki ya lullu6e ta kamar ta zuba ruwa kasa ta sha.


Cikin rawar murya tace "Owais! Danish cousin dinka ne, shine babyn Hateem na karshe da Sheikha mujeeda ta haifa masa, na fada masa komai game da iyayensa"

lokacin da yaji wannan maganar daga bakin Khala baisan sa'adda ya kara matse danish a kirjin shi ba, wani kuka ne ya balle masa, daga shi har danish din aka rasa mai lallashin wani a cikin su.

murmushin farin ciki Haroon Ya saki bayan ya gaishe da khala, Ya juya ya kalli dattijan da suka kura masu ido Yace"pls tun da kun kawo mu mun gansu, ku dan bamu wuri zamuyi magana ta sirri"


Har suna haWa baki gurin cewa dama abun dayasa suka tsaya suna son suji idan nan zasu kwana, don su kawo masu wata katifar da kuma abunda zasu ci"

cike da kyankyami Haroon Yace"kasan su wanene mu kuwa? Kana nufin a wannan kongon zamu zauna"?

Look bamu bukatar komai daga gare ku, mungode da taimakon da ku ka yi mana, Allah yasaka maku da Alkhairi, ga kuma kudi kun samu, don haka ku tafi, Idan mu ka gama tattaunawa, zamu bar maku gidan gonar ku.."

amsawa sukayi da toh sunata washe baki sufa yau ashar dinsu kakarsu ta yanke saka.

Har suka bar dakin Chief bai raba jikinshi daga na Danish ba, sun ki sakin juna..

Da murmushi akan fuskar Haroon Yace"finally Chief ya haWu da cousin brother dinsa da ya rasa, dan uwansa mai kama da shi, me jarumta irin tashi."

Cike da farin Cik???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i khala tace"tana tayasu murnar sake haWuwa da juna, suyi kuka son ran su, suji Wumun junansu, babu abun da zai sake raba su in sha Allah"

kalamai masu dadi da karfafa gwiwa ta shiga gaggaya masu.

Lokacin da suka raba jikinsu daga na juna wata irin zuface ta wanke fuskokinsu da jikinsu, ga wani zafi da jikin nasu ya dau ka, Idanun su cikin na juna, yayin da hawaye ke cigaba da shararowa kan kuncin kowannansu.

Cikin shesshekar murya Chief yace"am really sorry danish! Nayi zaton kun mutu, wallahi Bansan kune kuke kirana ba, da tun ranar farko nazo na tafi daku, bansan kana araye ba, Danish kana araina dakai nake kwana dakai nake tashi, saboda yadda na damu dakai har mafarkin ka nakeyi, Danish ashe da rabon zamu sake ganin Juna? ....."

Nan take ya labarta masa komai daya faru, Hankalin Danish Ya kwanta da jin cewa Daddyn Unaisah da salsabeel dinsa suna araye sai dai baiji dadin nasarar da basuyi ba akan Elders..

"Ku faWa mana tayaya akai kuka ku6uta daga Kurkukun kaddara..." Haroon ne ya tambaya.

"Owais Ni baka ganni ba"? Khala ce ta fada mikewa yayi tare da duban ta..

"Ina sane dake, kema kina araina tun ranar dana fara ganinki da kuma maganar da kika fada akaina, kamar kin sanni! Pls ki fada min wacece ke? Kamar na sanki, Inaso na sani!"

"Owais baka gane ni ba har yanzu? Ka dubeni dakyau, duk da nasan tsufa ya boye ainihin kamannina.." kura mata idanun shi yayi sosai"wadda kike min kama da ita, ta mutu yanzu bata araye,"

Murmushin takaici tayi"owais, zan fada maka abun da kake son ji akaina, ba yanzu ba, saboda a halin yanzu Daga ni har Danish muna bukatar kulawar likitoci saboda ba lafiya gare mu ba..."

nan take ta fayyace masu komai daya faru bayan Elder Ya ritsa da ita.

Hankalin su Ya tashi matuka sun kuma tausaya mata, sun jima suna fira a tsakanin su.


A ranar suka bar gidan gonar, Commender Haroon ne yayi masu booking Hotel Rooms din da zasu zauna, da taimakon adamu da ya shige masu agaba shi da yasan takan Birnin nasu..

Saida khala ta yi jinya a asibiti, na tsawon kwana biyu docs suna yi mata treatment na konuwar da kanta ya yi, Chief bai mi?a danish Asibiti ba saboda baya son ma wani ya gan shi, yasan yadda yake da jan hankali mutane zasu iya daukar hoton shi a boye wanda yin hakan zai iya jaza mashi matsala, tun da idan har Elders suka san suna araye, zasu nemi hanyar da zasu salwantar da rayuwarsu ne, sai dai ya dauki hayar Likitan da zai duba shi a boye, Cikin kwana ki biyu ya dan ji saukin jikin shi.

Ganin sun murmure Yasa Chief Ya fara tunanin Komawa da su Nigeria, koda ya tuntu6i Haroon da maganar komawar su bai goyi bayan su koma tare da su ba, saboda rayuwarsu tana a cikin haWari, In har Elders suka san suna araye sai sun nemi hanyar da zasu kashe su saboda sune silar da aka kai musu farmaki, kuma yadda suka ci amanar su ba zasu ta6a ?yale su ba, dole su dauki fansa akan shi ?wara su nisanta su daga Nigeria har zuwa lokacin da zasu kawo ?arshen Elders.


Maganar Haroon ta ankarar da shi kuskuren da ya ke kokarin yi dama yana zargin akwai sa hannun nashi a ciki! In har ya koma da danish cikin yan uwansa Elders zasu iya sani tun da yasan suna da yan le?en asiri.

basu gama yanke shawarar inda zasu boye su ba, Chief Ya ce ma Haroon zai nemi shawarar khala ya ji ra'ayinta.



Bayan daya samu Khala a dakin ta, ya fada mata abun da suka tattauna da Haroon cike da damuwa tace sunyi tunani mai kyau tabbas idan Elders suka san suna araye zasu kashe su ne! Amma tana neman alfarma agurinsa, Ya taimaka Ya haWa Danish da Iyayen sa! Tana son ya cika burinsa, rayuwa ba tabbas batason ya mutu bai gan su ba"!

Shi kanshi baida burin daya wuce danish Ya haWu da iyayen sa, sai dai baya jin zai iya haWa shi da mahaifinsa tun da har yanzu bai kai ga gano su wanene ke da sanya hannu a kurkukun kaddara cikin Uncles din sa ba, wannan dalilin ne yasa shi yanke shawarar zai hada shi da mommyn shi amma fa ba zai hada shi da daddynsa ba har sai zuwa lokacin da suka kammala bincike.

kwata kwata Khala bata nuna mashi tasan wanene Elder ba, ba irin magiyar da baiyi mata ba akan ta faWa masa wadanda ta sani a cikin Elders ! Kuma yana son yasan tayaya akai tasan Danish cousin dinsa ne dan uncle Hateem! amma ta?i ta sanar da shi, daya matsa lamba tace in har yana son yaji amsoshin tambayoyin shi toh ya koma da ita Nigeria ya kuma hada kowa na family dinsa a estate dinsu, ita kuma tayi masa alkawarin a wannan lokacin ne zata fayyace mashi wacece ita sannan kuma zata tona wani sirri na family din su agaban kowa"!

maganarta ta Waure mashi kai, Ya rude ba kadan ba, amma bai musa mata ba,


Abun daya sa khala ta?i ta sanar da shi ta za6i ya koma da ita Nigeria ya kuma tara kowa na family dinsa, badan komai ba sai don tana son ta cika burinta na ganin ta tonawa Elder asirin agaban Ahlin sa.

Masu karatu kunji dalilin dayasa Owais Ya roki alfarmar yana son ayi family meeting a ranar birthday dinsa, saboda bazai iya jira har sai date din family meeting yazo ba, kuma yana son kowa na family dinsu ya halarta duk don ya cika sharuddan Khala! Hakan na nufin dama can Owais Ya san da zuwan Khala.




___________________________=?%?



Bayan daya faWa ma Haroon yadda su ka yi da Khala, shima ya goyi bayan ya hada Danish da mommynsa a boye, tun da ba'a Nigeria ta ke da zama ba, ita kuma khala ya bashi shawarar in sun koma Nigeria da ita su boye ta a guest house din sa kafin zuwan ranar da zai kaita estate din su, Chief yaji dadin shawarar Haroon.



Su uku suka san da wannan maganar, batare da 6ata lokaci ba, Dg Ya kira Sheikha Mujeedat awaya bayan sun gaisa ya fada mata cewa game da binciken da ya ke yi akan Danish, Ya gano cewa dagaske babynta ne da ta haifa babu rai shekara ashirin da suka wuce, yana tunanin akwai wadanda suka kulla makirci gurin raba su da shi.."

Bai ?are maganar ba, ta katse shi da cewa dama ita tajima da ji aranta jininta ne, saboda kaunar da Hateem ke yi masa da kuma kamanninsa da Hateem! shiyasa ta yi dna test din nan, amma tana so tasan su wanene suka rabata da shi? Meyasa su ka yi hakan? Laifin me tayi masu da har yasa suka rabata da yaronta tsawon shekara ashirin, bata san yana araye ba, daga haihuwarsa ko Wumin jikinta bai ji ba, ba'a bari ta gan shi ba aka rabata da shi, akayi mata ?aryar ya mutu! ita kawai so take ta san su wanene su ka yi mata aika aikar nan"!

cikin lallashi chief yace tayi hakuri, ta kwantar da hankalin ta, Sun kusa kammala bincike akan wadanda suke zargin sun raba ta da shi, Yanzu haka da ya ke yi mata magana yana a tare da Omair dinta, sun riga sun faWa masa cewa itace mommynsa, kuma tun da yaji hakan ya matsa lamba akan su haWa shi da mamansa, ta taimaka in zai yiwu yana son ta haWu da shi, amma baya son kowa ya sani! saboda rayuwar yaron tana a cikin haWari, miyagun da suka rabashi da su suna nan suna farautar rayuwarsa, ya zamana komai cikin sirri zasuyi shi.

kusan ruWewa tayi saboda farin cikin jin cewa zai hada ta da dan ta.

Cike da zumudi tace karya damu, in sha Allah zata kula da komai, ba zata bari kowa ya sani ba, yanzu ya fada mata da yaushe zai turo shi canada"?


Chief yace "ba a Canada ya ke son su haWu ba, yafi son ta hadu da shi a dubai, zaifi sirri, Yanzu haka suna a abomey-calabi benin, Zuwa jibi, zai kammala yi masa travel arrangment, kafin ya karaso ta tanadi private docs din da zasu duba lafiyar shi"

Bai kare maganar ba, tace"ba zata iya jiya har sai jibi ba, yanaso ta kasa rintsawa ne?

Dariya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login