Showing 66001 words to 69000 words out of 321579 words

Chapter 23 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

kawo masa mafita acikin lamuransa, badan sun so ba, suka amsa ma shi da toh, kuma su ka daukar mashi alkawarin zasuyi mashi addu'a, yayi wannan maganar ne acikin dakinsa yayin da suke awaje suna sauraron shi, Zuciyar su ta karaya ba kaWan ba.


Almost hours, Chief bai le?o daga part dinsa ba.

Wuni su ka yi kamar marasa lafiya, saboda damuwar da su ka yi da shi.

Ko sun kira layin shi baya yin picking.

__________________________________ELDERS=?%?

gaba Wayan su suna a kwakkwance kan wasu hadaddun Plush poolside loungers dake a cikin Katafaren Gidan Gonar su, aljanar duniya an kawata shi da kayan alatu kamar ba za'a mutu a barshi ba, kwata kwata babu riguna a jikinsu sai short, kirjinsu da bayansu a zane yake da tattoo na tambarin kurkukun ?addara, sun rufe rabin fuskokin su da gold mask su shida ne gefe da gefen su matasan yan mata ne masu jini a jiki sanye da short gown a jikin su, launin ja, sun saki gashin kansu ta baya, hannayen su ruke da madaidaicin tray mai dauke da expensive bottles na whisky wanda a kalla farashin kowace kwalba yakai 1.5 million dollars, cikin kulawa su ke yi serving dinsu a cikin wasu hadaddun crystal glasses yayin da wasu daga cikin yan matan suke yi masu tausar kafadun su.

daga gabansu wani tankameman Swimming pool ne makil da ruwa launin pure blue sky, ga wasu haWaWWun Floating bean bags da ke shawagi saman ruwan, tantiran karuwai ne kwance asaman su masu dirarran jiki, sanye da swim suit da suka bayyana tsiraicin su, kowaccensu ta manna Sunglasses a idanun ta, saboda haduwar su idan ka kallesu saika sake kallon, sukai su goma sha biyar, daga ganinsu ba jinsi da ya bane, hankalinsu kwance suke shakatawarsu ga iska dake ratsa fatar su..

A hankali ya ke zukar cigarettes din dake a hannunsa idan ya sha?a har ta hanci yake buso hayakin ta tsabar kwarewa...

"Maganar da Jan harshe ya faWa ta kona min rai, na kwana da ita acikin zuciyata, arayuwata na tsani mutumin da zai yi min magana da tsawa, bayan haka ya kira ni da kaskantacce, har ni zaice wai ban kai darajar takalmin Elder ba? Kawai saboda sun taba taimakona arayuwa nayi aiki a karkashinsu shine har suka samu damar da zasu yi min gori...." rai abace ya faWa.

Jan le6e yace"ni banga abun damuwa ba, yanzu fa tasu ta ?are, kabarsu suji da kunyar duniya, ai sun tabka babban kuskure da suka amince zasu mika wuya, ban taba sanin elder maloho bane sai wannan karon da ya karaya, saboda son ya'ya ya rufe mashi ido, har shawara ka basu basu dauka ba, saboda dakikanci da shafewar basira, ka jira ka gani da kansu zasuyi danasani...."

gaba Waya suka bushe da dariya da wannan budaddiyar muryar tasu mara dadin ji...

Jan Ido yace"ni abun daya bata min rai, meyasa suka ki bamu sihirinsu bayan sunce sun tuba? Anya ba tuban muzuru su ka yi ba? saboda nayi mamaki wallahi, Mutanan da suka gaji sihiri suka san dadin shi zaiyi wuya su tuba ta cikin sau?i"

Ya ?arashe maganar yayin da yake mi?a ma matashiyar dake a gafensa hannu cikin sauri ta tsiyaya masa whisky a glass ta mi?a masa ya kar6a tare da kaiwa baki yana kur6a.

"Bakin ciki ne da hassada don kada mu samu cigaba, Watakil kuma saboda suna jin fargaban mu farfado da ran kurkukun kaddara, ko kuma suna jin tsoron mu ci amanar su..."

acewar jan le6e, wata yar iskar dariya suka sanya..

A hankali jan wuya ya kur6i whisky din dake a hannunsa kafin yace"yakamata mu san abunyi, ni hankalina bai kwanta da alkawarin da Elder ya Waukar mana ba na cewa bazai tona mana asiri ba, yadda ya mutu akan kaunar jikan nan nashi kuna tunanin ba zai iya fada masa komai ba idan ya matsa masa? kuma ina kokwanto dakyar in ba makirar tsohuwar nan tasan ni ba, Kada sai mun saki jiki su fallasa mu..." maganarsa ta dan daga hankalin Sauran Elders din..

Jan Le6e yace"bana tunanin Elder zai iya cin amanar mu, mun riga da munsan halin shi mutunne mai rukon amana, ko da zasu azabtar da shi, bazai faWi sunayen mu ba,...."

bai ?are maganar ba, Jan wuya yace"hmmm dan adam ba abun yarda bane, ni ban yarda da kowa ba, kawai mu nema ma kanmu mafita..." bai kare maganar ba, jan ido yace"me kake nufi"? Wani makirin murmushin gefen fuska ya saki tare da kallon su, sai da Ya zuki tabar hannunsa kafin yace"ku yi amfani da brain dinku mana, idan har muna so mu zauna lafiya batare da fargabar wani abu ba, to fa dole sai mun kawar da Obie family, saboda sun san komai game da kurkukun kaddara da kuma sirrinmu, tun kafin labarin ya fita duniya ta sani, muyi gaggawar tura masu Evil giants under cover of night, su kashe su duka batare da sanin kowa ba, and no one will suspect a thing, kunga daga nan zamu ci gaba da cin karen mu babu babbaka...."

har ya ?are maganar tashi elders din basu tanka mashi ba, kamar shawarar tashi ba ta kwanta masu arai ba..

Jan le6e yace"wannan shawarar daka bamu bamai 6ullewa bace, ko kamanta gargadin da jan harshe yayi mana"?

ya tambaya yana kallonsa bai jira amsar shi ba ya dasa da cewa"Idan ka manta bari na tuna maka, Har yanzu Elder shi ke a ruke da masarrafinmu, idan muka kuskura muka ce zamu ci amanar shi wallahi zai yi mana tsiya ne! elder zai iya rufa mana asiri amma abu dayane zaisa ya tona mana asiri ya kuma ?wace sirihin jikinmu shine idan muka ci amanarsa, Saboda shi baya yafewa wanda ya ci amanarsa, Kuma kai kana tunanin Evil giants zasu Iya farmakar Ahlin Obie bayan Elder Yana araye..."? Ya jefa masa tambayar, nan da nan annurin fuskarsa ya Wauke Wuff..

Jan ido yace"kayi tunani mai kyau Jan le6e, ba zamu iya cin galaba akan ahlin Obie ba har sai bayan ransa.."

Shiru su ka yi na Wan wani lokaci, young ladies din da ke a kewaye da su sun yi zururu da idanun su, ga gajiyar da suka farayi da tsayuwa ba halin su ce zasu zukunna..

"Abun da ya kamata mu maida hankali akai yanzu, shi ne Mu nemo Jan kunne duk inda ya shiga acikin garin nan, saboda shine mai rauni a cikin mu, Idan mukayi kuskuren da Jami'an isod suka riga mu kama shi zai tona mana asiri ne da zarar sun fara azabtar da shi saboda ba shi da juriya ko kaWan...."

acewar jan le6e, kusan atare suke mike daga kishingiden da suke sam sun manta da batun wani jan kunne dama bawani mahimmanci suke bashi ba, saboda Obie yasa suke tarayya da shi...

"jan kunne baida amfani agurinmu, ko da mun kama shi sai dai mu kashe shi, tun da asirin shi ya riga daya tonu..." jan wuya ne ya faWa da kakkausar muryarsa.

Jan ido yace"wayarsa a kashe take, wata?il ya jefar da ita wani gurin don kada jami'ae su bi diddiginsa, duk da sakarcin shi wani lokacin yana da wayau, amma hakan bashi zai hana mu ?yale shi ba, dole mu kashe shi..." ya karashe maganar tare da kur6ar giyar dake a hannun sa...

"Ranar da muka yi zaman tattaunawa a mafarki, shi kadai ne bai halarta ba, zai iya yiwuwa ya gudu yabar kasar ne.." ya faWa yana kur6ar whisky dinsa..

"ba zai yi mana saukin kamawa ba, saboda karfin sihirinsa ?ayane da namu"! Jan le6e ne ya fada rai a6ace..

Jan wuya yace"kubar komai a hannuna, zan nemo shi da kaina, Kuma zan kashe shi..." tuntsirewa sukayi da dariya hahahaha...

"Ya batun dawo da ran gidan kurkukun ?addara? Kada ku manta Har yanzu muna da sauran dama fa, idan har muka cika sharuWWan da ake bu?ata zamu jefi tsuntsu biyu ne da dutse Waya, na farko zamu iya canza location din gidan kurkukun ?addara, abu na biyu in har mukayi nasarar cika sharuddan karfin sihirinmu zai ?aru, ta yadda ko Elder bazai Iya ja da mu ba, ..." wani irin annurin farin cikine Ya cika su, jin abun da Jan le6e ya fada, Jan ido yace"tayaya hakan zai yiwu"? Shu'umun murmushi jan le6e yayi"kada ku manta, tun kafin ku san Elder na riga ku sanin shi, atare mukayi yawan duniyancin mu, duk wani sirrin shi na sani, wannan maganar dana faWa naganta ne a rubuce cikin tarik sijnil ?adar wanda mahaifin Elder ne ya rubuta littafin da al?alamin shi tun da dadewa..."

wata irin shewa suka sanya har saida suka tsorata matasan yan matan dake yi masu hidima.

"Amma fa wanda ya riga cike sharuddan a cikin mu, shine zai maye gurbin Elder, shi kuma Elder zai rasa karfin sihirin sa ta yadda bazai iya sarrafa evils din jikin mu ba"

Wannan maganar da jan le6e ya faWa ta faranta ran Jan wuya, sai faman sakin shu'umun murmushi yakeyi aransa harya fara tunanin yadda zai riga su aiwatarwa saboda ya samu karfin ikon Elder, tsabar hadamarsa yafi so yafi kowan nan su karfin sihiri, ta hakane kadai zai iya mayar da su karkashin ikon shi, don ya cigaba da juyasu son ran shi =?3?

*=ؘ?UNAISA ANGEL=؋?*

A cikin kunnanta ta jiyo sautin dirar Mota a gidan, baiwar Allah a lokaci bacci ne ke kokarin Waukarta, tana a kudundune cikin duvet dinta ta kasa runtsawa saboda tunaninsa, ranta ne ya bata shi ne ya shigo gidan..


Jikinta na 6ari ta sauko daga kan gadon, Batool tana akwance gefe daya tayi nisa a baccinta, ta kudundune kanta cikin duvet din ta, Night gown ce a jikin ta Ja, Mayafi ta dauka ta yafa ma kanta, ko takalma bata saka ba, garin saurin ta fita daga dakin har tuntube tayi amma hakan bai dame ta ba, burinta kawai ta je ta dubo in shi ne.



Tana fitowa daga dakinsu ta nufi main falo unexpected Ta hango shi yayin da yake tafiya akan stairs, aranta ta ayyana dama yana fita a irin wannan lokacin idan sunyi bacci?

tayi kewarsa cikin kwanakin nan daya juya masu baya, daga yanayin yadda yake tafiya ta fahimci babu kuzari atare da shi kamar wanda yasha ?waya, Cikin sauri tabi bayanshi sai dai kafin ta karasa tuni Ya shige bedroom dinsa, tana isowa bakin kofar room din tayi knocking shiru babu alamun zai bude mata, cigaba da bubbuga kofar tayi tana ambaton sunan shi tare da yi mashi magiya akan ya bude mata kofar.



abun daya Waga hankalinta sautin nishin da ya ke saki har cikin kunnanta take jin shi, ganin baida niyar bude mata kuma bai bata iznin shiga ba, hakan yasa batai wata wata ba, ta fara kokarin danna code din kofar da ya ke ya taba nuna mata tun farkon da suka fara shakuwa da junan su, abun daya sa bata taba gigin yi mashi katsadan din ta shiga batare da izninsa ba, saboda ba muharraminta bane, kuma bai dace ta fada masa daki batare da izninsa ba, batasan awani yanayi zata taras da shi ba.


Nishin da taji yanayi ne yasa ta razana har bata san sa'adda ta saka code din kofar ta bude ta, a fujajen ta dira kafafunta cikin dakin, wani irin burki taci, lokacin da idanunta suka hango mata shi, har ya cire kayan jikin shi, yana daga tsaye gaban gadonsa ya bata baya, boxer short ne kadai a jikin shi, Ya ru?e Syringe mai dauke da ruwan allura a cikin shi, yana kokarin caka ta a upper arm din sa..



"My hubby...." dakatawa yayi jin muryarta a cikin kunnan shi, kwata kwata baisan da zamanta adakin ba, hatta knocking din da ta dinga yi baiji ba saboda hankalin sa baya a tare da shi, kawai so yake yayi ma kansa allurar ko ya samu sassaucin radadin da zuciyar sa ke yi masa, kwana biyu rabon da yayi bacci saboda pressure din daya daura wa kansa na gano su wanene Elders, bai da wani kwanciyar hankali idan har ba gano su yayi ba.

A hankali take tafiya tana tunkarar shi, daga bayan shi ta tsaya tana duban gefen fuskarsa daya jike sharkaf da gumi..


"Me ke damun ka? Meyasa ka juya mana baya? Ka hana zuciyata sukuni, saboda kai ko bacci bana iyayi, na rasa gane kanka acikin kwanakin nan! ..." ta fada tana dan girgiza kanta idanunta sun cika da kwalla..

"Why would you inject yourself? Aren't you well? Ta fada araunace.



da wata irin kakkausar murya ya furta I don't want to see anyone close to me! Don't you dare take one step closer to me! ki fuce min daga daki..."

gabanta ne ya faWi a rude take kallon bayansa, kamar ba daga bakinsa kalaman ke fitowa ba.


Ta razana sosai, Cikin rawar murya tace"Husband to be, yau ni kake kora daga dakin ka? Me yake damunka ne? A tunani na damuwarka tawa ce, bai kamata ka boye min ba, Pls ka fadamin zan taimaka maka mu shawo kan matsalar..."





numfashi Yaja tare da furzar da shi, ganin taki tafiya yasa shi daka mata tsawar da ta tsoratar da ita


 Don t you dare make me repeat what I said! Get out of my room before I do something bad.


gyada kai tayi, idanun ta cike tab da kwalla ta soma ja da baya tana cigaba da kallon bayansa, ta lura ko kallon ta baison yi, abu kamar aikin asiri in a short time ya canza musu.



A hankali ta juya takai hannu zata buWe ?ofar, sai kuma ta fasa saboda zuciyarta dake azalzalarta akan kada ta tafi, ta tsaya taji meke damun sa.



Sakin handle din kofar tayi da tunanin tayi ko karta aikata abunda zuciyarta ke saqa mata, ga tunanin nasihar dadynta amma bata jin zata iya barin shi a halin da yake ciki, juyawa tayi slowly ta nufe shi tana karasawa batay wata wata ba, ta faWa kan bayansa, she slowly wrapped her arms around his waist, ta daura tafukanta a saman shafaffen cikinsa, lokaci Waya ya tsinci kanshi awani irin yanayi mai wuyar fassaruwa, har baisan sa'adda Ya saki sirinjin hannun sa ba, wata irin kasala ta haifar masa, lumshe idanun shi yayi a hankali yana jin bugun zuciyarta da hucin numfashinta on his neck.

Yatsunsa taji akan hannunta yana kokarin banbareta don ya rabata daga jikin shi, cikin sauri ta furta"na roke ka, dan Allah, dan soyayyar da kake yiwa manzon Allah SAW kada ka kore ni, ka barni atare dakai, inaso naji meke damunka, ko ban sama maka mafita ba, zan tayaka addu'a Allah ya yaye maka damuwarka, baka taba barin mu cikin damuwa ba, taya kake tunanin ni zan iya barin ka a mayuwacin hali irin wannan"?



Kalamanta sun sanyaya zuciyarshi, sai dai baya jin zai iya fada mata abunda ke damunsa, baisan ya zasu dauki abun ba idan suka ji cewa kakansa ne Elder mamallakin gidan kurkukun kaddara, mutumin daya azabtar da rayuwarsu, Ya Ilahi, Ji yake kamar kowa zai juya masa bayane..

wata irin kara mai tattare da bakin Ciki Ya fasa, tuni shatun jijiyoyin goshinsa dana wuyansa suka fito ruWu ruWu saman fatarsa, tun da ya yi tsawar gaban ta ya faWi rass hankalin ta ya ?ara ta shi duk tabi ta ruWe..



Nauyin jikin shi daya sakar mata ne yasa ta gaza jurewa saboda yafi karfinta nesa ba kusa ba, aikuwa gaba daya suka faWa saman bedmattress dinsa.


a rubda ciki ya faWa yayin da take akwance saman bayansa, sam sun kasa motsawa har na tsawon mintuna, dakyar ta yi kokarin raba jikin ta daga na shi, da wata irin kasala ta mike zaune tare da zuba mashi idanunta da suka cicciko da kwalla.


Duk da batasan meke damunsa ba, amma hankalinta ya tashi ta kuma ji tsantsar tausayin sa acikin zuciyar ta, jikinta harya fara daukar Wumi saboda zafin jikin shi da ta goga silar haWuwar da fatarsu tayi.


ya kasa jure radadin da yake ji ne, baiso ya bayyana rauninsa a fili ba, duk yadda yaso ya danne damuwarsa ya kasa bawan Allah.

Cikin shesshekar kuka ta dinga tambayar shi meke damunshi har ta ha?ura ta yi shiru saboda ya?i furta kalma, daidaita nutsuwarta tayi cikin sanyin murya ta fara zuba mashi kira'ar alqur'ani mai tsuma zuciya, lokaci Waya ya fara jin tamkar ana wanke damuwar da ke acikin zuciyarsa, bacci ne ya ziyar ce shi a hankali ya fara lumshe idanun..



bata kaiga dire ayar data janyo ba, kwatsam ta fara jin gyangyaWin bacci har bata san lokacin da ta sulale gefen sa ta kwanta ba, Kafin wani lokaci, wani wahalallan Bacci yayi awon gaba da su, ikon Allah kenan bai kaiga yin sedative injection din da ya so yayi ba, sai gashi silar karatun qur'anin da Unaisah tayi masa yasa shi yin bacci...=ؔ?


sai da suka shafe tsawon awanni bakwai suna yin baccin, tun karfe Waya da rabi na dare, har karfe bakwai na safe basu farka ba kamar wadanda suka sha sleeping pills.


Tun da garin Allah ya waye Batool taga babu Unaisah a dakin, har toilet ta duba bata ganta ba, hankali atashe ta nufi dakin aunty ummi don ta dubo ko taje can, tana zuwa taga babu unaisah nan ta fada ma Aunty ummi bata ganta adaki ba, hankalinsu atashe suka fito neman ta, sako da lungu na gidan sun duba basu ganta ba, kuma basu kawo ma ransu tana adakin Chief ba, har dakin Taj suka shiga a lokacin yana a zaune kan darduma Yana jan cazbaha bayan sun gaishe da shi, Ummi ta tambaye shi Unaisah batazo nan ba, yace musu ko gifcin ta bai gani ba amma kada su damu yasan duk inda taje ba zata wuce cikin gidan ba, ya fada tare da dauko wayarsa ya danna mata kira tana ta ringing ba'ay picking ba..

__________________________________=?%?=؋?

A hankali ya soma kokarin bude idanunsa da sukayi mashi nauyi ga wata kasala data baibaiye jikin shi, jin hucin numfashin mutun a gefen shi kasa kasa cikin natsuwa ya ke fita, yasa shi saurin karasa bude idanun nasa.



tamkar wanda ya yi loosing memory dinsa, ya Wan razana da ganin mace a kwance saman gadon shi tana bacci, kuma suna fuskantar juna, kitson kanta yabi da kwallo,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login