Showing 204001 words to 207000 words out of 321579 words

Chapter 69 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

koma asibitin don duba lafiyarta, sai na tarar babu ita a Wakin da suka kwantar da ita, ko da na tambayi nurses sai suka ce kuWin gadon da muka biya sun ?are, in har ina so su mayar da ita dole saina biya wasu kudin. Hankalina ya tashi matu?a, na shiga nemanta, da ?yar na ganota a bakin wata bishiya ta asibitin kwance a ?asa, sai kuka take yi ta daddafe cikinta, wasu bayin Allah ne suka kewayeta suna tambayarta ina ?an uwanta? Wa ya kawo ta asibitin? Bata da kowa ne.?


Cikin sauri na je na daukota na koma da ita asibitin, na dinga ro?on su akan su taimaka mini su mayar da ita zan biya kudin zuwa gobe, da ?yar na samu suka amince zasu mayar da ita, amma suka gargaWe ni akan in har ban kawo ba zuwa gobe, babu wani uziri da zasu kar6a daga gare ni, bayan da suka mayar da ita kan gado, na baro asibitin na fara tunanin me zan siyar dan in biya kuWin aikin nata? Na duba na hango bani da komai, a lokacin ko gidan kaina ban mallaka ba, a gidan haya nake da zama, kadara Waya da nake da ita, mashin Wina, a ranar da nake shirin zuwa in siyar da shi, kwatsam sai ga kira ya shigo wayata da ba?uwar number.



Da farko ?in Wagawa na yi, anata kira sai daga baya na yi picking na kara a kunne tare da yin sallama.


Mutumin ya amsa min bayan mun gaisa na tambaye shi wanene saboda bangane me magana ba, na ga ba?uwar number.


Yace min eh dama yasan bazan gane shi ba, saboda ban san shi ba, amma shi ya sanni, maganar gaskiya ya ganni a asibiti ne, shima a lokacin ya je duba marasa lafiya, dama ya saba zuwa bada tallafi a asibitin, toh ya ji komai dake faruwa hatta matata da suka sauke daga kan gado duk yana a wurin yana bibiyar mu saboda mun bashi tausayi, shiyasa ma har ya kar6i contact Wina agurin nurse.


Na ce Allah sarki, na gode sosai da nuna damuwa akan mu.


Ya tambaye ni na samu kuWin da zan biya kudin aikin nata ne?



Nace masa a'a, ban samu ba, yanzu nake shirin zuwa in siyar da mashin Wina duk da kona siyarma ba isa zasu yi ba, amma inason in fara biyan rabi don suyi mata aikin daga baya na cika.


Yace min kar a yi haka, idan na siyar da mashin dina ni kuma da me zan dinga yawo? Ina ma amfanin siyarwar bayan kuWin ba isa za su yi ba, abun da za'a yi shi zai biya kudin komai harma da jari zai bani."


Na yi ?ar dariya na ce nasan ma wasa yake yi min, saboda nasan babu mai iya yi min wannan taimakon, duba da yadda taimako ya yi ?aranci."


Yace min wallahi da gaske yake yi, idan ina so in tabbatar da abun da yake faWa zai bani address dinsa in neme sa.."


Bayan mun yi sallama da shi, sai ga sa?on address ya shigo wayata, a lokacin hankalina bai kwanta da shi ba saina ?i neman shi, bayan da na tafi kasuwa don siyar da mashin Wina aka rasa samun wanda zai siye shi da daraja, sai tayin wulakanci da ake yi min, ga shi lokaci yana ta gudu har marece ya yi ina ta neman wanda zai siya da kirki ban samu ba, a ?arshe na sha wahalar banza na dawo gida, da na ga bani da mafita saina yanke shawarar kiran mutumin don in faWa masa zan zo.



Bayan mun yi waya, na shirya na tafi gidan da ya yi min kwatance.


A falo muka zauna ni da shi, ban iya ganin fuskarsa ba saboda ya saka mask, ya kuma sanya glass a idanunsa, bayan mun gaisa na gabatar masa da kaina.

Ya ce min ai ya gane ni, kar inji komai in saki jikina, ba kaina ya fara tallafawa marasa ?arfi ba, ya saba zuwa asibiti duba marasa lafiya har ma ya biya kuWin jinyar su, da ya faWi hakan saina ji hankali na ya kwanta sosai, ya ce min sai dai ya ji kuWin da za'a yi mata aikin suna da yawa, zai biya rabi kyauta amma rabin zai bani a matsayin bashi, cikin sauri na ce na amince amma idan har yana da aikin da zan yi masa ya faWa min in ya so cikin kuWin aikin sai ya dinga zare bashin da ya ke bina.


Ya yi murmushi ya ce min bashi da aikin da zai bani amma in har na amince zan bashi duk abun da ya ke so a matsayin biyan bashin toh zai bani.


Na ce masa bangane me yake nufi ba? Ya ce min kar in damu ba wani abu bane, kawai yana son mu yi yarjejeniya in har ya bani kuWin komai ya bu?ata zan bashi.


Da ya ke a bu?ace nake na amsa mashi da na amince in dai ina da abun, nan take ya shiga Waki ya dauko jaka ya mi?a min tare da cewa in Wauka miliyan biyar ne a ciki, na ruWe a lokacin na ce masa sun yi yawa bazan iya kar6a ba, kuma bani da hanyar da zan iya biyan shi, sai dai ya rage ya bani daidai kuWin da nake bu?ata, ya ce dama ce a gare ni, in yi amfani da ita tun kafin in rasa, da jin haka sai na yi masa godiya , daga bisani muka yi sallama na tafi.


Washe garin ranar, bayan da na je asibitin na biya kudin aikin ta. Cikin sa'a bayan an yi mata aiki ta ji sau?i kamar bata ta6a yin ciwo ba, bayan da suka sallame mu muka dawo gida, ban ta6a faWa mata game da yarjejeniyar kudin dana kar6a bashi ba.

Taj wlh sai da nayi danasani, ni bansan da mugun nufi ya shiga rayuwata ba, ban yi bincike akanshi ba, saboda kuWin nake cikin bu?ata bani da yadda zan yi Taj, tun bayan da ya ban kuWin ban ?ara jin Wuriyar shi ba, nama manta da batun bashin da na ci, da kudin na fara neman na kaina ina Wan ta6a kasuwanci harma na samu aiki a companyn kasuwanci. Lokaci Waya Allah ya buWe min kofofin samu, na mallaki gidan kaina, na sayi mota, a lokacin Uzair ya zama matashi na dawo da kai gidana, kwatsam! wata rana sai ga kiran mutumin nan ya zo yasa akai masa sallama da ni, bayan na fito na yi mamakin ganinsa still fuskarsa da takunkumi, bayan mun gaisa na yi masa iso muka shiga ciki, a bayan gidana muka zauna ya ce ya ji shiru kona manta da bashin shine, nace masa ban ta6a mantawa ba, da abun nake kwana a raina, saboda ina son in sauke hakkinsa dake a kaina, don haka yanzu tun da mun haWu ya faWamin da me zan biya shi?


Da buWar bakinsa sai cewa ya yi, "?a'?a yake so in biya shi da su." Na yi zaton zolaya ta yake yi, na yi dariya na ce don Allah ya daina zolaya ta, mu yi magana ta gaskiya, da me zan biya shi bashin, ya kuma ce min rai yake so, dana fahimci dagaske yake sai na ce masa ai ba a biyan bashi da rai, ban ta6a ji ba, kuma ni ban da ran da zan biya da shi, bama zai ta6a yiwuwa ba, in dai zan biya sa sai dai in biyasa da abun da ya bani ko ya fadi wani abun daban!

Girgiza kai ya yi da kakkausar murya ya ce, "Na manta yarjejeniyar mu ne? Idan nasan ba zan iya bashi abun da yake so ba meyasa na kar6i kuWinsa?" Raina a 6ace na ce, "Amma dai malam baka da hankali ko? Kawai saboda ka bani bashin kudi sai ka ce in baka rai? Kamar wani ran kaza? To wallahi bazan bayar ba, komai zai faru sai dai ya faru, a ina aka ta6a haka? Kudi sun isa su sayi darajar rai ne.. !" Na gaggaya masa maganganu cikin bacin rai saboda naga rainin wayon nasa ya yi yawa, cikin fushi ya ce oh shi zan ma butulci? Bayan halaccin da ya yi min? dama ba a gane halin talaka sai ya yi kuWi, wato yanzu na samu bakin gaya masa magana ko? Ba don shi Win ba ai da yanzu na rasa matata, amma shike nan zai tafi amma fa in sani zan biya abun da na yi masa.


Bayan fitarsa, abun ya dame ni, na yi ta tunanin meyasa yake son in biya shi bashi da rai? Me zai yi da ?a'?a? Gashi dai da hankalinsa ba mahaukaci bane balle in ce ko ya samu ta6in hankali ne, can kuma raina ya bani ko dai irin waWanda basa haihuwa ne waWanda Allah ke jarabtarsu da son ?a'?a.

Da sauri na bi bayan shi, a lokacin yana kokarin shiga motarshi na dakatar da shi na tambayesa meyasa ya ke son ya'ya? Cikin karyayyar murya ya ce,

Saboda rashin da ya yi, a lokacin baya yana da mata Waya da ?a'?a biyar, sanadin haWarin jirgin sama ya rasa su, shi kuma a lokacin ya samu matsalar haihuwa yanzu haka yana da aure amma bai ta6a samun haihuwa ba, yana son ya'ya sosai. Na tausaya mishi na ce mashi indai haka ne meyasa ba zai je gidan marayu ba ya yi adopting, sai ya ce min baya son ru?on maraya yana da wuya, kuma yawancin su basu jin magana, shi yasa ya fi son waWanda suke da iyaye, jarirai da zasu raina shi da matar shi, in yaso daga baya idan Allah Ya sa ya samu warakar lalurarsa zai mayarwa mai su, shiyasa ya bani bashin nan saboda yana so in taimaka masa in share masa hawayensa, har kuka sai da ya yi min.

Taj tausayin sa ne ya cika zuciyana, har bansan sa'adda na ce masa na amince da yarjejeniyar mu, a lokacin ban san meke damuna ba, idanuna sun makance burina kawai in taimake shi, ji nake in har ban taimaka masa ba, zan iya rasa raina.. " Taj da ke sauraron sa tsantsar ruWani ne akan fuskar sa.


_"A lokacin nasan idan na faWa ma hajiya Adama ko wani daga dangina ba zasu yarda ba shiyasa na yi shiru da baki na, a lokacin baku cika zama gida ba kuna zuwa makaranta. Sau biyu Adama tana haihuwa ina sace jariran tare da haWin bakin mutumin da likitansa, bata ta6a sani ba, sai dai ta ga ta haifi jariri ya zo babu rai, likitansa ne ke yi masu allurar da zasu yi kamar sun mutu, babu wanda yasan lokacin da muke aiwatar da hakan..."_


To fa!Kallo ya koma sama, hankalin Taj idan ya yi dubu toh ya tashi, tsantsar al'ajabi ne ya kama sa! A ransa ya ayyana ashe kurkukun ?addara bai bar kowa ba! Abun ya zo har takan Uncle dinsa!"



"?a'?a biyu na bashi, mace da namiji, a lissafina yanzu namijin zai kai shekara ashirin, macen kuma ba zata wuce shekara sha takwas ba idan suna a raye, Taj kamar bani da hankali, ban ta6a sanin gidansa ko wani nasa ba, yadda kasan an rufe min bakina na kasa tambayarsa hakan, wallahi ko fuskarsa bansani ba, kullum da takunkumi nake ganin sa, a duk lokacin da na yi yun?urin tambayarsa game da hakan sai in ji kamar an kulle min baki na..."

"kuma tun bayan da na bashi ya'yan ban ?ara marmarin in waiwaye su ba ko in tuntu6i mutumin in ji wani hali suke a ciki, gaba Waya namanta da babinsu, har tsawon shekaru, sai daga baya ne a lokacin kun 6ace babu ku, muka shiga mawuyacin hali na bu?atar ?a'?a, ga hajiya Adama ta daina haihuwa ko 6ari bata yi har asibiti muke ja docs suka ce matsala ta samu a mahaifarta ba lallai ta sake haihuwa ba, daga ni har ita mun shiga matsananciyar damuwa, na fi jin tausayinta saboda ni na cuce ta, na bayar da ya'yanta batare da sanin ta ba, ina jin fargaban ta ji maganar nan, nasan har rabuwa zata iya yi da ni, ni kuma banason duk wani abu da zai raba ni da ita. Taj lokacin da tunanin mutumin ya dawo min akaina, a lokacin na yi arzikin da zan iya biyansa kaf kuWinsa harma da ?ari batare dana girgiza ba, na sha kiran layinsa baya Wagawa, har sa?onni na tura masa baya min reply, har na fidda rai da zai Waga kira na, unexpected wata rana ina ?ara jaraba kiran shi ya Waga,

(Idan masu karatu zasu iya tunawa, a kwai lokacin da Hajiya Adama ta yi ma Abdallah la6e yana waya a Wakinsa har ta jiyo shi yana yin waya da wani mutumi, bari mu tariyo wayar da ya yi a wannan lokacin=?G?)



"Ka yi ha?uri nasan ba haka mukai da kai ba, na sa6a alkawari amma ka dubi halin da nake a ciki, lokaci Waya na rasa Wana bayan haka na rasa Wan yayana tare da ?arsa, na rasa yayana da kakata, kai kaWai ne zaka iya taimakona a halin da nake a ciki, wlh ni zan iya maida maka adadin kuWin dana kar6a a wurin ka saboda ka dawo mun da su in dai suna a raye na ?wammace na ?are rayuwata a talauci akan in ci gaba da ganin damuwarta akan rashin haihuwa..."

Muryarsa a marairaice ya yi maganar kamar zai yiwa mutumin da suke yin wayar sujjada tsabar yadda yake lalla6a shi yana yi masa magiya.



*Cigaban labari*



"Na rasa ya zan yi Taj, nasan na cuci kaina, na kuma cuci yaran dana basa, bansan me ya yi da su ba, saboda ina zargin komai da ya faWamin game da labarinsa ?arya yake yi min, damfarata ya yi, kuma ba hakanan ya ?yale ni ba. Ban tashi gane hakan ba, sai yau da na kalli news na ji labarin kurkukun ?addara da fursinonin cikinsa sai na dinga ji araina da wuya in mutumin nan ba yana a cikin matsafan ba, duk da bani da tabbaci, amma in har ya tabbata za'a iya samun yaran in suna raye.."



ya karashe labarin da hawaye a cikin idanunsa.


Numfasawa Taj ya yi cike da tausayinsa a cikin zuciyarsa ya ce, "Uncle na fahimci damfararka ya yi, kuma ya gusar maka da hankalinka daga tunaninsa da ya'yanka, babu tantama zai iya zama cikin matsafan.."


Cikin sanyin murya ya ce, "Taj, tayaya zamu iya sanin idan yana a cikin su? Tayaya ma za a iya gane yaran nawa idan suna a raye, bayan koni bansan kamannin su ba?"


"A labarin daka bani baka faWamin sunan mutumin ba"?


Girgiza kai ya yi cike da damuwa ya ce, "Sunansa dana sani wanda ya ta6a faWa min Alhaji Ja'afar Dila."


Jinjina kai Taj ya yi tare da kwantar masa da hankali ya ce in sha Allah zai yi magana da Dj, idan ma yana a cikin su za su gano shi, zai yi iya ?o?arinsa saboda shima yana son yaran ko dan ya samu cousins Win da zasu maye mashi gurbin Uzair"



Abdallah ya ce yana son su bar maganar nan a matsayin sirri tsakanin su, ko mutuwar Uzair baya son hajiya Adama ta sani, yafi son sai sun samu mutumin nan da ?a'?ansa sai su faWa mata komai, yasan koda zata ji zafi ba za ta yi fushi da shi ba, zata yafe masa saboda tana da ha?uri kuma tana son shi sosai.



Abun da basu sani ba, gaba Waya firar da suka tattauna a kan kunnan Hajiya Adama da ke yi musu la6e, kuka mai cin rai ta ke yi, ta toshe bakinta da tafukanta duk don kada sauti ya fito su jiyo ta, sai da taga sun mi?e ta watsa da gudu ta koma cikin gidan ta shiga toilet, ta wanke fuskarta don kar su gano ta, baiwar Allah ta ji zafin mutuwar Uzair sosai, ?unci da ba?in ciki suka mamaye zuciyarta, ta dinga karanta addu'o'in neman sassauci a cikin zuciyarta, kwata kwata bata ji haushin abun da Abdallah ya yi mata ba, duk da bai kyauta mata ba da ya 6oye mata ya'yanta da ya bayar, kamar baisan irin yadda mata ke shan wahalar na?uda kafin su haihu ba, wata tara ta raini ciki, ya dauka ya ba wani? Batare da sanin ta ba? Kamar ta ce masa batason ?a'?an! Amma ta yi masa uziri saboda ta fahimci mutumin yaudararsa ya yi kuma hada asiri ya yi ma shi, bayan haka komai ya yi saboda son da yake yi mata ne, fatanta Allah yasa su gano mutumin nan don ya basu ?a'?an su, Allah yasa suna a raye shi kaWai ne hope Win da take da shi a yanzu.



Kafin tafiyar Taj saida suka shigo ciki, ta fito suka ?ara Wan ta6a hira cike da ?arfin hali, kafin suka rako shi har bakin motar shi ya yi masu sallama, suna ta ?ara tuna mashi suna son ganin Unaisah ya ce zai kawo masu ita in sha Allah. Bayan da ya tafi ko bayan da suka koma cikin gidan hajiya Adama bata bari Abdallah ya gane ta ji komai ba, a 6oye take shan kukanta, tsoffin hotunan Uzair ta dinga Waukowa tana kallonsu, da su take kwana da su take ta shi..



~__________________________________=?%?=ث?~


A bangaren Natasha kowa ya manta da batun ta saboda halin da suka shiga, amma kullum ne sai chef Win da dg ya ba Wawainiyar kula da ita ya je kai mata abinci sau uku a rana, daga bisani dg ya kira Ummi ya dam?a mata wasi?ar Unaizah da ya kar6a a hannun Unaisah, ya ce ta kai ma Natasha sannan ta faWa mata wanene Musa, da kuma miyagun ayyukan da yake aikatawa.



Bayan da Ummi ta je Wakin bata saurari haukan Natasha ba, ta zauna ta fyaWe mata komai game da Musa tun daga biri har wutsiyar sa, Ya salam! Natasha ta razana sosai, hankalinta ya tashi matu?a, ta ji ba?in ciki da takaicin cin amanar da Musa ya yi mata, sai yanzu ta gane dalilin da yasa baya son ta san kowa nashi, ta daWe tana mamakin dukiyar shi, saboda baya gajiya da basu kuWi ita da Unaizah, ashe ba mutumin kirki bane Wan blood cults ne, ba komai ya fi karya mata zuciya ba,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login