Showing 105001 words to 108000 words out of 321579 words

Chapter 36 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

da baby pretty ban ta6a cutar da ita ba, na bata kulawa, na bata tarbiya na kuma bata farin ciki, komai takeso inayi mata shi)

"duk da bani na haifeta ba, bata ta6a sanin bani na haifeta ba, saboda ya gargaWeni akan bayason ta sani kuma nayi hakan saboda yarjejeniyace a tsakanin mu, KuWi ya ke biyana.."


_cike da takaici Chief ya dafe kansa bakin cikine ya cika zuciyar shi, komai daya faru ubanta ne yaja mata, maganar Natasha gaskiya ne, da ace bai kai mata ita ba da duk hakan bai faru ba, kuma da ace ya kwa6e ta akanta da bata 6atata ba, amma dayake dama da biyu ya kai ta saboda ya riga daya sadaukar da ita bata da amfani a gare sa, bayan haka Natasha baturiya ce baturiyarma mai yanci kuma karuwa, dama wasunsu ba hankali gare su ba, gani suke indai jin dadin rayuwane komai da zasuyi don su faranta ransu mai kyau ko mara kyau ba laifi bane, suna da right din da zasuyi amma duk da haka bazai kyaleta ba, yadda Unaizah ta dandani zafin cin amanar da su kayi mata haka ya ke son kowan nan su ya danWani kwatankwacin raWadin da taji a cikin zuciyarta_

"Since last year, ya raba ni da ita, ya maidata gurin mamanta, yanzu haka wannan zuwan da nayi hada don inason naganta, in kuma rokesu su bani ita saboda bazan iya rayuwa batare da ita ba..." bata kare maganarba ya kwatsa mata tsawar da data razana ta

"Su baki ita don kicigaba da biyan bukatarki da ita ko"? Ya fada kamar zai rufeta da bugu.

Girgiza kai tayi"ba saboda haka nakeso ta dawo gurina ba, inason ta, ina jinta kamar yar dana haifa a ciki na, After that, I had a problem, I'll never give birth"

"Kina daukarta kamar ?a? Kina nufin har yarki ta cikin ki zaki iya kwanciya da ita.."? Cike da jin shakkar shi ta Waga mashi kai alamar eh

A zuciye ya Waga hannu zai mareta tayi saurin kare fuskatarta da hannun ta

"Ya isa haka! Nagaji! Ka daina mari na! Ko dan saboda girmana ya kamata ka girmama ni, na fahimci haushina kake ji, ka tsaneni, amma yakamata ka gane ni bani da laifi..."

"Ke kike ganin girma a tare dake, Ni kaskanci da jahilci nake gani a tare dake, baki da mutunci ko kima a idanuna, saboda ke din mara imani ce, dabba mara hankali.."

taji zafin kalamanshi sai dai kwata kwata bata nuna hakan ba.

"Yau ki ka zo nigeria, Kuma a yau kika shiga dakin yaran da baki hada alakar komai da su ba, ki kai yunkurin taba jikinsu saboda jaraba kuma a haka kike kiran kanki mara laifi? shiru tayi bata musu ma shi ba.


Jinjina kanshi yayi ji yake kamar ya binneta da ranta saboda haushinta da yake ji

"Kin ta6a haihuwa da shi"?

cikin fushi tace"I don't know, I'm tired of your questions, kamar nayi maka laifi saboda kawai nazo gidanka zaka tsareni da bugu kamar jaka.."

rufe shi da fada tayi ta inda take shiga bata nan take fita ba.

Sam ta manta da gun din hannunsa sai da taji ya har6i vase tayi kara taja baki tayi shiru a firgice.

"Zaki amsa min tambayata ko kuwa"?

Harara ta watsa mashi tana yatsina fuska tace"Na ta6a sau Waya, amma ba araye na haife su ba" a takure ta amsa tambayar..


"Mata ne ko maza"?


"No, they are mixed twins"

jinjina kan shi yayi da alama akwai abun da ya ke tunani aran shi.

Yanzu ya gane itama Ya ci amanarta batare da sanin ta ba, hakan yayi mashi dadi, saboda itama taji abun da uwa take ji idan wani ya cutar mata da, kuma zatayi danasanin komai da tayiwa Unaizah.

"Pls kada ka kara tambayana nagaji.." ta fada tana yatsina masa baki, fuskarta sai naso ta ke yi kamar Wanyen nama.

Jinjina kan shi yayi"Okay"

"Tunda na amsa maka tambayoyin ka, nima ka amsa mun nawa, wani laifi big boss ya aikata? Me kuma yasa ku ka kira ni? Sannan meyasa kake tambayana akan Unaizah? Kana da ala?a da ita ne?

"Zaki sani amma ba yanzu ba"

Juyawa yayi zai tafi tayi saurin bin bayanshi

Juyowa yayi"ina zuwa"?

"Zan koma ciki mana, in ba baka son ganina tafiya zanyi yanzun nan don ko mintuna banso in ?ara a gidan nan"

Murmushi Chief yayi"nan ne masaukinki a gidan nan, babu ke babu fita, za'a dinga kawo maki abinci, da kuma suturar sanyawa, akwai toilet in bukata ta kamaki .."

arude tace"bangane ba? Me kake nufi? Garkuwa kukayi dani ko kuwa na aikata laifin daya cancanta ku kulle ni ne? ..."

bai tsaya sauraranta ba, ya fuce tana kokari fita kofar ta datse kanta.

Bugun kofar ta din ga yi da kafarta da hannunta, kamar zata balleta, a karshe data galabaita, agajiye ta sulale kasa ta jingine kanta jikin kofar, zuciyarta a cunkushe take da bakin cikin cin amanarta da ummi tayi, gayanan taja mata bala'e da ta sani da bata zo ba =??


(=?%?UNEXPECTED CALL OF HAJJATY=?%?)


Around ?arfe 2 da rabi na dare suna akwance kan gadonsu, rabin jikinsu lullu6e yake da duvet, babu wadataccen haske a dakin nasu, kasantuwar sun kashe light din before su kwanta sai dai hasken Bedside lap da su ka bari a kunne..

Ringing din waya ne ya takura baccin nasu..

Wayar sai ruri take daga kiran ya katse wani ke shigowa.

Farkawa tayi bakin ta dauke da addu'ar ta shi daga bacci, a hankali ta buWe idanunta da suka kada ja saboda bacci ta dube shi da su..

Murmushi tayi, ganin ya samu bacci yau.

Tana tsaka da kallon fuskar shi, Ringing din wayar ya katse ta.

Sam ta manta me ya tayar da ita daga bacci sai da taji ringing din

Gabanta ne ya fadi da rudu akan fuskarta ta furta wanene ke kira na da tsakar daren nan?

Kasa motsawa tayi saboda tsoro ne da ita, tayi lamo a kirjin Mijin nata.

Sai da taji an?i daina kiran wayar nata ne yasa ta fara tunanin ko dai wani muhimmin abu ne yasa aka kira ta? Wata kil ma na cikin gidan ne ke kira.

A hankali ta raba jikinta da ga nashi, ta sauko daga kan gadon cikin sanda ta Wau wayar, duk don kada ta tada shi daga bacci.
Juya ta nufi can cikin dakin daga bangaren walk-in closet din su.
Screen din wayar ta duba, missed calls ta gani daga new number

Hakanan ta dinga jin fargaba, kamar karta daga kiran, amma zuciyarta ta matsa mata akan ta daga taji wanene..

Adaidai lokacin an sake kira, yatsun hannunta na kerma ta yi picking ta kara wayar a kunne unexpected taji yo muryar Hajjaty tana yin magana cikin muryar raWa

"Kina jina? Taji ta ambata.

Wata ajiyar zuciya ta sauke dadi ya lullu6eta kamar zata saka kuka tace"hajjaty ina kika shiga? Meyasa zaki gudu batare da kin neme ni ba? Kin kuwa san halin dana shiga? Kullum tunanina wani hali kike ciki..." bata kare maganar ba ta katse ta..

"Pls, bana so wani yasan na kira ki, ke ka Wai ce ko kina a tare da Oga"

"Ni kadaice hajjaty, babu kowa a kusa dani" tana jiyo ajiyar zuciyarta.

"Ki fada min meyasa kika gudu? Ta tambaya kamar batasan komai ba.

Fashe mata tayi d????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? a kuka"kina nufin baki ji komai ba"?

"Banji ba, nadai ji labarin kin gudu"

Saboda ta aminta da ita yasa ta faWa mata komai da Pravin ya sanar da ita, turai ta ruWe da jin labarin yasha banban da wanda ita ta sani.

"Ki yi hakuri ban ta6a sanar dake ba, yanzun ma tura ce takai bango, bani da mafita daya wu ce in sanar dake gaskiya, Pravin ya matsa mu bar kasar saboda yana jin tsoron hukuncin da zamu fuskanta agurin Hajiya saratu da yayyanta, ni kuma banaso mu tafi saboda ya'yan shi da matar shi, ni ma kuma na saba da ahlin obie, nayi nayi da Pravin ya bari muzo mu nemi yafiyar su amma ya?iya, kwat kwata baison wani yasan inda muke, ko fita zaiyi da mask a fuska ya ke fita, na rasa ya zanyi in shawo kanshi, yanzu haka da nake maki magana baisan na saci wayar shi na kira ba, Yana adaki yana bacci.."

"Hajjaty, ki kwantar da hankalin ki, Naji komai tabbas baku kyauta ba, da kuka zauna tsawon shekaru kuna boye musu alakar dake atsakanin ku, da tun farko kun fada masu komai da duk hakan bata faru ba, amma yanzu abun da nakeso dake, Karki bari Pravin yasan kin dauki wayarsa, ko kinyi waya dani, tun da na fahimci tsoro ya ke ji, kawai idan mun gama magana ki goge number ta, kada ki kara kira kuma kada ki ta6a ta, ni duk zanji da komai, In sha Allah zan yi kokarin sulhunta tsakanin ku da su.."

"Nagode Aminiyana, dama nasan ke kadaice zaki iya share min hawaye na, amma taya zaki tuntu6e mu idan sun yafe mana? gobe fa zamu tafi"

"Kin san sunan anguwan da kuke ne?

"Bansan komai ba, lokacin daya kawo ni bana a hayyacina"

"Okay, Kiyi yadda nace maki, ki ajiye wayar" zan sake kira amma ki kwanta kinji"? Amsawa tayi da toh"amma pls kiyi sauri ki kira kafin ya farka, wlh idan yaga na kira ransa zai baci"

"Toh" daga haka su ka yi sallama.

Juyawa tayi cikin sauri ta koma kan gadon su.

"Babe, ka tashi, Hajjaty, ta kira ni, ka tashi pls! Gobe zasu bar kasar" dakyar ta samu ya farka yana yamitsa fuska idanunsa a rufe yace"pls kada ki takura min, Ki kyaleni.." saitin kunnanshi takai bakinta"hajjaty ta kira yanzun nan.." bata kare maganar ba, taga ya ware idanunsa tare da mikewa yana tambayar ta wace hajjatyn?

"Hajjaty dai daka sani, ba ka ce nemanta ku ke yi ba, To ta kirani da bakuwar number yanzun nan"

Bai tsaya sauraron karashen zancen ba Yace Ina number din data kira da ita, Wayar ta mika masa yasa hannu ya kar6a, ya na dubawa..

Me kuka tattauna da ita..

Zayyana masa tayi, ta dan marairaice fuska tace"babe, na rasa gane kan zancen, a maganar hajjaty bata nuna tasan wani abu game da ciwon hajiya saratu ba, ku kuma kunce kuna zargin faWane ya haWa su! Ban dai tambayeta komai ba ban kuma fada mata meya faru da hajiya saratu ba, gudun kada in daga hankalin ta, amma tayaya akai hajiya saratu tasan da aure atsakanin su? anya Praveen yana da gaskiya kuwa? Na fara zargin shi, meyasa zai matsa akan su bar kasar nan? Bayan ga matar shi nan rai hannun Allah, ga kuma ya'yansa kuma meyasa pravin yakeso su bar kasar akan abunda bai kai ya kawo ba? Tun da ta fara maganar bai kula ta ba, yana ta danna wayarta.

"Dan Allah kayi kokari ka taimaka masu nasan sun tsoratane shiyasa zasu gudu, tun da sun gane kuskurensu a kira su aji meya faru, ni bana zargin su, pls muyi wani abu, kafin gobe"


Wani kallo Sir mubarak yai mata, tuni taja baki tayi shiru

"Kin cikani da surutu kamar aku, zaki kwanta ko saina matseki"

ya fada da zolaya, dariya tayi tare da kwantar da kanta, yaja mata bargo ya lullu6eta duka har kanta

Daga cikin bargon taci gaba yi masa magiya akan ya taimaka ya dawo mata da yar kawarta gida.. "

Saukowa yayi daga Kan gadon, daga shi sai dan short, ya nufi walk-in closet nasu jim kadan ya dawo, sanye da jallabiya a jikin shi, har ya fuce daga dakin bata sani ba sai bayan tafiyar shi ta Wan leko daga cikin bargon tayi mamakin ganin babu shi kuma bai aje mata wayar ba, fatan ta Allah yasa za su je su dawo da su hajjaty ne.

________________________=?%?


*ANEELERH=?%?*


Around ?arfe sha biyu na safe ta farka daga guntun baccin daya dauke ta tun bayan da suka kammala breakfast, Mi?a ta yi tare da yin hamma kafin ta sauko daga kan gadon jikinta sanye da jallabiya, ta lullu6e kanta da hula, doguwar sumar kanta ta sauka gefe da gefen kafaWarta, bata damu da rashin ganin junaid a bedroom din ba, tasan bazai wuce dakin mami ba ko na zahra, cos yau ba school weekend ne, har ta juya zata fuce daga dakin wayar ta dake ajiye kan bedside drawer ta fara ruri juyawa tayi cikin nutsuwa takai hannu ta Wauki wayar ganin sunan Benazir ya bayyana akan screen din yasa ta sakin murmushi cike da zumuWi tayi picking call din tare da kara wayar a kunnanta.

"Amarya kuma uwar gida agurin Taj, ya kike? Ya su mami? fatan kuna lafiya..."

On the other hand sautin dariyar Benazir ya cika kunnanta"har kinsa naji wani sanyi araina da kika ambaci Taj, da ace muna a kusa har tukuici zan baki saboda faranta min rai da ki kayi..."

murmushi Anila ta saki, bayan sun gama gaisawa Anila tace"yaushe zamu sake komawa gidan Dj ne? Nayi missing din Aisha, Inaso na sake ganinta, kullum da tunanin ta nake wuni, gashi har yanzu bata Waga kirana ...."

Benazir tace"wallahi nima har yanzu bata Waga kirana, bansan me mukayi mata ba, shima ya shureim bata Waga kiran shi, saboda yadda na damu da ita har mafarkinta nakeyi..."

bata ?are maganar ba Anila ta katse ta da cewa"bakya tunanin akwai wani dalili dayasa take fushi da mu? In ba haka ba me mukayi mata"? Ta faWa fuskarta a yamutse kamar tana a kusa da Benazir din.

"Anila ni kaina saida nayi wannan tunanin, amma na rasa gane laifin me mukayi mata? In ma saboda abunda ya shureim yayi mata ne yakamata ace komai ya wuce yanzu, bawan Allah nan har hakuri ya bata, mu ma mun bata hakuri, abu fin shekaru tana rukon shi a zuciyarta..."

Anila tace"har yanzu bana ganin laifinta, kinsan zuciya bata da ?ashi, Aisha tasha wahalar rayuwa, in har zata dinga tuna bakin cikin data kunsa silar abun daya shiga tsakaninta da ya shureim ba lallai ta yafe masa ba, ni wallahi abun daya daga hankalina game da ita, canzawar da tayi, bansan wata irin rayuwa Aisha tayi a america ba, amma kallo daya zaki mata ki gane ba ustatha bace, zato zunubi amma kammanninta kamar irin na tantiran yan barikin nan, idanunta sun buWe, dai dai da tafiyarta bata uztazai bace..."

bata kare maganar ba jin shesshekar kukan Benazir

"Koma meya faru da Aisha mune ne sila"

lallashin ta Anila tayi har saida ta samu tayi shiru na Wan wani lokaci kafin Anila ta ce"sun ce zasu neme mu, amma naji shiru har yau basu kira mu ba, nifa kawai ina rayuwa a cikin gidan nan ne saboda iyayena suna a cikin sa, amma wallahi kullum cikin fargaba nake saboda Uncle dan iya, ko haWa hanya da shi bansan yi, mutumin ya fita araina na tsane shi, shiyasa na kosa su gama binciken su akan videon ana, suzo su kama shi kawai kowa ya huta"

Cikin sanyin murya Benazir tace"nima din hankalina ba a kwance ya ke ba, koda yaushe cikin fargaba nake, tun da na fitar da sirrin abun da na sani game da Uncle musa, dama ina zargin shine ke yunkurin kashe ni, shiyasa time da nayi ciwo nai ta pretending kamar bana acikin hayyacinta saboda na fahimci bai hakura ba, har yanzu yana akan bakansa na daukar mataki akai na, Anila bansan ya zanyi ba, banaso wani abu ya samu iyayena da ya shureim, gashi duk muna a karkashin ikon shi, in har ya gane na fitar da sirrin wlh zai iya binne mu da ranmu tun da ba imani ne da shi ba.."

gaba daya sun shiga damuwa.

"Benazir, mu dai bamu yi dacen kawunnai ba, wallahi ban taba zaton Uncle dan iya zai iya aikata rashin imanin nan ba, mutumin banza me fuska biyu, Allah kadai yasan ina yakai Ana, na rasa gane kashe ta yayi ne ko kuwa wani gurin ya kulleta, daurewa kawai nakeyi amma duk idan na ganshi ji nake kamar in kama gemun shege in tsistsinka shi,...." ?yal?yalewa da dariya Benazir tayi jin abun da Anila tace.

"ni wallahi abun dayafi damuna Su zahra, yara masu kirki sai dai kash ba su yi dacen uba ba.."

"Hmm ke dai bari, Idan suka san mugun abun da fasikin ubansu ke aikatawa ay wlh sai sun kusa zaucewa..." Benazir ce ta fada can kuma tace

"Anila, kin tuna abun da Dj ya gargademu akai? Ki daina daga murya kada wani ya ji yo ki, Ina fata ke kaWaice a dakin nan don na ji kamar motsin wani a cikin kunne na.."

Zaro idanu Anila tayi cike da fargaba, can kuma ta saki dariya"wlh kin tsoratar dani, har kinsa gabana ya faWi, idan Uncle dan iya ya kamani ina yin wayar wlh na mutu"

dariya Benazir tayi"yaya shureim yana kira na sai anjima zamuyi magana.."

sallama su ka yi, fuskarta Wauke da murmushi ta Waura wayar saman mirror tare da sauke ajiyar zuciya, ta Wan lumshe idanunta, kwatsam ta tsinkayi motsin mutum adakin ta, tayi azan junaid ne hakan yasa ta furta "my baby boy, ina ka shiga na farka daga bacci bangan ka a kusa ba"?

Ta faWa ba tare data buWe idanunta ba, ga kuma motsin yana cigaba da tunkarota.

"Babyn mommy ka yi min magana mana, nayi missing dinka, zo nan kusa da ni..."

ta faWa tana mi?a hannunta.

shiru taji ba'a tanka mata ba, In har junaid ne tasan bazai ta6a share ta ba, tunawa tayi da maganar Benazir

_ina fata ke kadaice a dakin nan don naji kamar motsin wani_


Cikin sauri ta buWe idanunta kaitsaye suka sauka acikin na shi ta cikin madubi, wata irin zabura tayi kamar wadda taga dodo, ta zazzare idanun ta cike da tashin hankali, kwata kwata bata tsammaci zata ga mutun adakin ba, me ya kawo shi dakin ta? abun da take ma fargaba kada ace yaji wayar da tayi da Benazir, kirjinta kamar ana luguden ta6are, da wata irin faduwar gaba ta zabura jikinta na kerma ta mi?e tsaye tana ?are masa kallo daga ?asa har sama ta cikin madubin batare data waiwayo ta fuskance shi ba.


Yana a tsaye ya ruke qugunsa da hannunsa na dama, yar shara da gajeran wando ne a jikin shi, kwata kwata fuskarsa ba walwala ko miskala zarratin, fuskarsa sai naso take ga wani uban shade fari daya ?wama a idanun shi ya sauko har ta kan karan bajajjen


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login