Showing 93001 words to 96000 words out of 321579 words

Chapter 32 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

ka bani mamaki, ban taba zaton zaka iya furta wannan maganar akan kakan ba, kafi mu sanin wanene shi, amma ko mu kanmu da muke abokanka mun yi imanin baba Obie bashi bane Elder, Mutumin mai kyawawan halaye da tausayi irinsa bazai iya aikata abun da Elders suke yi ba...

"Ni dai danasan zaka fada mana wannan almaran da ba abun da zaisa in halarci meeting Win nan, sai dai ka yi hakuri Chief amma yau ka 6ata min rai, ka ce Elder ne kakan ka, Wanda ya haifi baba, gaskiya sir kwakwalwarka bata aiki yadda ya dace kana bukatar a duba ka.." Coo ne ya fada tare da zame glass din kan fuskarsa ya zaro hanky yana sharce gumin dake tsastsafo masa.

Kasa juyowa ya yi ya fuskance su, baisan taya zai yi musu bayani ba, baba Obie ya cuci kansa ya yaudari mutanan da suka yarda da shi, gayanan duk wanda aka faWamawa sai anyi da gaske kafin ya yarda..

Taj Tuni hawaye sun wanke fuskarsa, dama saida ranshi ya bashi hakan, wata irin karaya ya ji, baba Obie ya bashi mamaki, ba tun yanzu ba ya jima yana al'ajabin dukiyarsa da Waukakar ahlinsa ashe bana Allah da Annabi bane, ha?i?a bai kyauta ma rayuwarsu ba, ya zalunce su wata shari'ar sai A lahira...

"Tun da nake daku na taba yi maku ?arya? Mutumin nan kakana ne nafi ku sanin wanene shi! Miye ribana in na mashi kazafi? Tun da na ce maku shi ne ku yarda kawai, kakana ne Elder!"

Ya faWa cikin shesshekar murya ba tare da ya juya ya fuskance su ba,

Wannan karon kusan suman tsaye suka yi saboda sun fara karaya da maganarsa jin kamar yana shesshekar kuka...

"Ba shaye shaye na yi ba, da hankalina da tunanina, Ni ba mahaukaci bane, ba kuma kazafi na yi masa ba, zan sake maimaita maku, Kakana Obinna shine Elder, azzalumin da ya ke azabtar da rayuwar yaran da ba su ji ba basu gani ba a gidan kurkukunsa, mutumin da muke nema ruwa a jallo, ashe daga tsatsonsa na fito, ban ga laifinku ba da kuka kasa yarda da maganata saboda muma lokacin da muka ji hauka ne kaWai bamu yi ba, na yi fatan ace ban kai wannan lokacin a raye ba, gaba Waya mun yi danasanin kasantuwar mu jininsa, amma ba yadda zamu yi haka Allah ya ?addara mana, Allah yana fitar da rayyayye daga jikin matacce, Ga misali nan akan mu, Kakanmu gurbatacce ne, mai fuska biyu, mu kuma ba haka muke ba, gaba Waya uncles dina da mahaifina babu sa hannunsu a ciki, hasalima basu taba jin wani abu mai suna kurkukun kaddara ba, a ranar da asirin ya tonu, abun ya daure mun kaina, sai na ga kamar ban ma taba sanin shi ba saboda na ji abubuwa game da kakana wanda ni ko iyayenmu babu wanda ya taba sani..."



Jikin ta?aura fa ya yi la'asar, tuni annurin fuskokinsu ya Wauke duff kamar basu taba dariya ba, zuciyarsu ta karaya, ga ba?in cikin da ya mamaye su, hankalinsu ya tashi, har basu san sa'adda suka cire hulunan kakin da ke akansu suka WaWWaura su gaban table ba, a Wimauce suka koma kan kujerun suka zauna tare da sadda kansu ?asa..

Har tsawon mintuna ashirin cuf babu wanda ya furta kalma daga cikin su saboda matsananciyar damuwar da suka shiga, kwata kwata meeting din yau bai yi musu dadi ba, saboda jin abun da basu taba zata ba, basu ji dadin maganganun da suka faWa akan kakansa ba, wannan ne karo na biyu da suka ga raunin Chief, ranar da Danish ya faWa rijiya da kuma yau, wlh sun tausaya masa sosai, sun ma ga kokarinsa da ya iya jurewa in wani ne tuni zuciyarsa zata buga ya mutu ko ya halaka kansa saboda ba?in ciki..=ؔ?


Mi?ewa Commender ya yi ya nufe shi tare da ru?o hannunsa ya juyo da shi, hankalinsu ya tashi da ganin siraran hawayen dake zarya kan kuncin sa.


_Zaunar da shi kan kujera Commender ya yi, tare da zaro Hanky ya share mashi ?wallar shi, mikewa sauran suka yi gaba Waya suka kewaye sa duk da raunin da suka yi hakan bai hana su ?arfafa zuciyarsu gurin lallashin shi da bashi baki akan ?addarar data same su, babu wanda bai tofa albarkacin bakinsa ba gurin kwantar masa da hankali, su ka ce ya yi hakuri ya jure radaWin da ya ke ji, sun san abun da ciwo, dole zai shiga mawuyacin hali amma ya yi hakuri, kada ya ji komai su masu fahimtar shi ne, tabbas su kansu sun karaya sun kuma razana da jin cewa kakansa ne, amma ya zasu yi babu wanda ya isa ya canza abun da Allah ya riga ya kaddara faruwarsa, wlh saboda tausayin da ya basu da suna da halin da zasu cire mashi damuwar shi da ba abun da zai hana su yi hakan kodan su sau?a?a mashi radadin da yake ji, amma ba zasu bar shi ba, zasu kasance a tare da shi, No matter what, shi Chief dinsu ne na har abada, su sun yarda da shi fiye da yadda suka yarda da kansu, don haka kada ya ji komai, laifin kakansa ba zai taba shafarsa da ahlinsa ba, zasu tsaya masu tsayin daka don ganin basu tozarta a idon duniya ba, bashi kadai zai yi fadan ba, ya sani yana da su zasu taya shi yin fighting Win duk wani wanda yayi yunkurin cin zarafin ahlinsa ta hanyar amfani da abun da kakansa ya aikata! Bayan haka basu san rauninsa, yana Waga masu hankali, abun da suke so da shi ya yi ?o?arin cire damuwar da ke aransa, saboda zata iya haifar masa da rauni wanda kuma hakan faduwa ne a gare su, sun san Chief Winsu jarumin namiji ne, mai dakakkar zuciya, kuma mai tawakkali, basu so ya canza daga yadda ya ke a da, ya sawa ransa cewa zai iya, ya manta da cewa kakansa ne Elder, ta haka ne zai kore damuwarsa har su samu su ?arasa aikin su."_

Maganganu masu daWi da ?arfafa gwiwa suka gaggaya masa har saida
ya ji karfi a jikin shi, sun faranta ranshi, kuma dama abun da ya kamata kenan idan mutun ya shiga wani hali a tausaya masa, a ja shi a jiki, bawai a dinga cuzguna masa ba saboda wata ?addara ta same shi, wasu har daWi suke ji su dinga bullying Winka don su ba?anta maka rai, su ja depression ya kama mutun daga haka har ya lahanta kan shi, wa'iyazubilla..=ؔ?

Tun suna share mashi ?wallar da ke gangarowa kan kuncinsa har ta kai ga sun fara tsokanar shi, baisan sa'adda ya fara sakin murmushi ba, saboda dadin da ya ji har godiya ya yi musu, su ka ce kada ya damu hakkinsu ne su bashi kulawa, yanzu tunda sun fahimci ba ya jin dadi yana bukatar ya ga likita saboda lafiyarsa, don haka zasu Waga meeting din, zuwa lokacin da zai ji sau?i.


Ya ce masu bai ?i shawarar su ba, amma bazai yiwu a Wage meeting ba, akwai muhimman abubuwan da yakamata su tattauna akai idan ba haka ba zasu iya fuskantar matsala, hankalinsu ya tashi da jin hakan, suka ce tun da haka ne, zasu tafi hutun awa uku saboda sun damu da lafiyarsa suna so ya huta...

A cikin yan mintuna suka kira Isod docs suka bincika lafiyarsa anan cikin medical room Win su, bayan sun tabbatar da ciwon dake damunsa ya gargaWe su akan kada su faWa musu sakamakon saboda baya son kowa ya sani...

Lokacin da suka koma zaman meeting din, ba laifi sun ga ya Wan saki jikinshi da walwala akan fuskarsa, A tsanake ya fayyace musu komai da ya faru bayan zuwan Khala..

Sun yi matukar mamakin jin cewa kakarsa ce, kuma Obie ne ya yi ?aryar mutuwarta ya kai ta kurkukun kaddara, duk ba wannan ba, abun da ya basu haushi da takaici abun da Pravin ya aikata, ashe shima???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? Elder ne na gidan kurkukun kaddara, lallai Obie Family sun haWa giggan ?an ta'adda acikin su.

Bayan sun taya shi murnar ganin grandma Winsa, da jimamin abun da ya faru da familyn sa Commender James ya ce,

"Yanzu ta ya za'ai mu iya gano sauran Elders? Kana ganin grandma Winka zata iya samun sau?i nan kusa!" Girgiza kai ya yi, "Bakowa ta sani a cikin su ba, yanzu haka da ita da aunt Win nawa an kwantar da su asibiti basu san inda kansu yake ba, amma suna samun kulawar likita.."

"Me zai hana mu tuntubi shi Elde...Au, afwan sir grandpa nake so na ce,..." murmushi chief ya yi tare da kallon CI da ya yi maganar. "Duk yadda ma ka faWa daidai ne CI, already na yi masa magana akan ya fada mun sauran Elders din amma ya ?i sanar da ni...." Nan ya labarta musu abun da suka tattauna tsakaninshi da baba Obie.

Kallon kallo suka jefawa junan su cike da tashin hankali, Agent Jabeer Osman ya ce, "Akwai sauran rina a kaba kenan, In har bamu yi gaggawar kamasu ba zasu iya mayar da hannun agogo baya, nasan iwar haka suna nan suna shirin kawo mana farmaki."

Gaba Waya sunyi amanna da maganarsa, Agent Zahra ya ce, "Ni damuwana ina zasu farmaka? ya tambaya yana duban su,

"Hankalina ya fi karkata akan fursinonin da muka baro a Csh."

Taj ya ce,"Asibitin yana da tsaro tunda na sojoji ne, amma fa kada mu dogara da hakan, mun riga da mun san su wanene Evil Giants, in har suka farmake mu da su, toh Allah ne kaWai zai iya ?watar mu, za su iya amfani da sihiri su kashe sojojin dake tsaron su, su kwashe yaran abunda ba a fata, amma menene mafita...?"

gaba Waya suka zurfafa tunaninsu kowa na tunanin abun da yakamata a yi.

"Kuskuren da muka yi tun farko shine barin makaman da grandma ta bamu, da mun sani mun taho da su, saboda da su kaWai ne za'a iya ya?ar su.."

A cewar Captain..

Cike da takaici Canal ya daki gaban table dinsa yama rasa abun cewa..

Jackson ya ce,"Akwai gagarumar matsala, dole fa mu fara kai masu farmaki kafin su kawo mana idan ba haka ba, ba zasu yi mana da dadi ba, bamu san ina zasu farmaka ba!"

Lieutenant Thompson ya ce, "Ni dai a nawa ganin shawara Waya ce, Chief grandpa shine mafita, shi kaWaine makamin da muke da shi a yanzu, tun da ya ce zai mika wuya toh ya taimaka ya faWa mana komai idan ba haka ba, ba zamu iya cin galaba a kansu ba, a kowani lokaci zasu iya kawo mana farmakin bazata..."

Girgiza kai Chief Owais ya yi, "mu yi hakuri mu nemi wata mafitar, saboda ba irin magiyar da ban yi masa ba amma ya ?i fada mun, ya ce a dokar aikinsu wani baya tona asirin wani, alkawari ne suka Waukarwa junansu, kuma shi ba zai ci amanarsu ba, tun da har ya fadi hakan bai duba ?aunar da yake yi mini ba, toh wlh ba zai ta6a bamu hadin kai ba, koda zamu azabtar da shi ne, amma a maganarsa ya ce in har aka kawo mana farmaki mu sanar da shi, amma wannan ba mafita bane, tayaya za a yi mu san za'a kawo mana farmakin?"

Da damuwa ya jefa musu tambayar, gaba daya sun shiga tashin hankali..

"Ni a ganina mu fara nemo wadanda grandma ta fadi sunayen su? In ya so sai muci ubansu mu azabtar da su har sai sun faWa mana su wanene sauran Elders din..." Taj ne ya fada yana huci zuciya ta kai wuya..!

General Noah ya ce, "No ba zamu iya kama su ba, har yanzu bamu da isassun hujjojin yin hakan!"



"Sir, muna da isassun hujjojin da zamu iya kama su..."

Gaba Waya suka maida hankali akan Taj da ya yi maganar har suna haWa baki gurin tambayar wata hujja ce? Bai jira Chief ya bashi umarnin ya faWa ba, ya fara zayyana musu komai da ya faru tun daga kan labarin Ummi har izuwa labarin da Benazir ta bashi akan Alhaji Musa.

Lamarin ya Waure musu kai, basu gama shan mamaki ba, sai da Chief ya samu ?warin giwar tunawa da wata hujjar da yake da ita, nan shima ya labarta musu komai da ya gano game da shi tun daga kan hotansa dake a cikin diary din Unaizah, ya ?ara da cewa, "Har yanzu bai rabu da Ummi ba, bayan ya rabata da kowa nata ya maidata karuwarsa, shine ya tafi da ita America..." A rude U.s armies suke jefawa junansu kallo mai cike da tsantsar al'jabi, Ummi dai da suka sani tantiriyar karuwa yau sun ji asalin labarinta da kuma azzulumin da ya yi silar canza rayuwarta, gaba Waya basu ji daWin abun daya faru da ita ba, tausayinta ne tsantsa a kan fuskokinsu, ba su kaWai ba hatta General Noah dana hannun daman Chief sun nuna tausayawar su a gare ta, labarinta ya taba zukatansu, kuma basu taba ganin mugun mutun irin Musa ba, labarin yarinyar da ya sa su zubda ?walla ashe shine Ubanta, sun ma riga da sun yanke ma kansu shine JAN WUYA mutumin da suke nema ruwa a jallo..

Chief Owais bai dakata ba, ya Waura da basu labarin da Sheikh Imam ya ba shi ...

Taj ya ce, "dama sai da raina ya bani, sune suka kashe Uzair..." Ya faWa cikin ?unci da ba?in ciki.

General Noah ya ce, "Wai ni Musan nan bashi bane former president ba? Mahaifin Ddg? Kuma ?anwarsa tana auran daddynka ko?" Jinjina mashi kai Taj ya yi.

Cikin fushi Noah ya buga saman table rai a 6ace ya ce, "Babu tantama zai aika, Ni dama bai ta6a burgeni ba, mutun sai girman kai da izza ashe dukiyar tasa ta kungiyar asiri ce, shi dama karen yan siyasar nan na daWe ina zargin sa saboda mugun munafuki ne.."

CI ya ce, "Zai yi wuya in ba daga tsatson fir'auna ya fito ba, mutun ba imani ba tausayi! Zalunci da mugunta kaWai yasa gaba, aikuwa dubunsa ta cika, da?i?in kwata kwata baya amfani da kwakwalwarsa, gashi nan cikin rashin sani ya tabka kuskuren da ya yi silar tonuwar asirin sa..."

Coo ya ce, "Wlh ikon Allah ne, ka duba yadda ya daWe yana she?e ayarsa tsawon lokaci batare da an iya kamasa ba, wai a haka har matsayin president ya taka, ko da yake ya samu Waurin gindi ne..." Bai ?are maganar ba, Taj ya yi masa gyaran murya tare da furta "Hattara dai.." Cike da jin kunyar Chief CI ya sunnar da kansa, bawan Allah Chief Wan murmushi ya saki tare da Wan girgiza kan kanshi.

"Sir, Yanzu meye abun yi tunda muna da isassun hujjojin da zamu iya kama su? Taj ne ya faWa yana dubansu..

Commender James ya ce, "Babu bukatar 6ata lokaci, mu kama su kawai su fara kar6ar sakamakon zunubin da suka aikata..."

General Noah ya ce, "da shi Wan iyan, da Musan, da pravin da aminnan grandpa, da likitocin da momma ta faWa suna da sanya hannu suma a kama su, sannan kada a kuskura abar pravin ya ?etare kasar nan, nasan iwarhaka yana neman hanyar da zai gudu, watakil ma ya gudun, shiyasa banso kuka Wauki lokaci baku sanar damu ba, wlh da kun faWa mana tun ranar da abun ya faru zamu bi diddiginsa mu kama Wan iskan, amma na yi maka uziri nasan alhinine ya hana ka sanar mana..."

Chief ya ce, "Mun tattauna da Uncles dina, suma zasu bada gudummuwarsu..." Nan ya labarta masu abunda suka tattauna da Uncles Winsu, sunji dadi kuma sun ?ara jin kwarin gwiwa a tare da su..


"Bayan haka tun ranar da ya gudu nake ta trying layinsa a kashe yake, har jaraba bin diddiginsa na yi amma ban iya gano komai ba, ina tunanin ya jefar da wayar ne don kada mu bi diddiginsa."

Agent Zahra ya ce, "Zai iya yiwuwa ya canza layi, in kuwa yayi kuskuren zuwa yin register zamu iya samun bayanansa."

"Ita yar'uwar tashi ka kira layinta ne?" James ne ya tambaya..

"A Waki tabar wayar, na kar6i number dinta a hannun yan uwanta maids, dana kira sai na gano location din wayar a cikin gidan ya ke, da kaina na shiga na dudduba dakin har na gano wayar nata."

Taj ya ce, "Za mu iya haWa baki da abokan aikin nata, ita Hajjatyn zata iya yin kuskuren kiran wani daga cikin su tun da ta yarda da su atare suke aiki, ko basu ba mu nemi aminiyarta ta ?ut da ?ut, wadda muke da tabbacin zata iya kiran ta, sannan mu haWa baki da ita, da zarar ta kira ta tayi hanzarin sanar damu, mu kuma sai muyi kokarin bin diddigin su..." Shawarar da Taj ya kawo ta yi masu daWi..



Ya kuma cewa, "Amma ni abun da ya Waure mun kai, Ita hajjatyn tasan abun da ya aikata kuma ta bi shi suka gudu? Ko dai dama a tare suke aikata 6arna ta bayan fage..."

Amma da kamar wuya saboda Hajjaty mutuniyar kirki ce .." Wani marayan kallo Chief ya yi masa..

"Mugu bashi da kama Taj, abun da ya faru da ni ya isa yasa ka dauki darasi, ba kowani nagari bane mutumin kirki, akwai masu fuska biyu, a fili Musa a zuci fir'auna, ni bana zargin ta, amma ta aikata babban kuskure da ta haura ?afa ta bi shi suka gudu, in har muka gano da sa hannunta akan abun da ya faru da auntyna, kuma tasan abunda yake aikatawa wlh na lahira sai ya fi ta jin daWi, dole mu hukuntata daidai da abun da ta aikata, babu wanda zamu ragamawa kamar yadda bazan raga ma kakana ba, dole kowan nan su ya gir6i abun da ya shuka..."

Ya faWa tare da bugun kan table din gaban su, gaba daya idanunsu akan fuskarsa, maganarsa ta burge su, suna alfahari da shi, ya cancanci su yaba mashi saboda jajircewar shi akan gaskiya, a dai yadda duniyar nan ta baci da rashin son gaskiya, da wani mai son kan ne idan yasan nashi ne yake aikatawa 6oyewa zai yi, ko ya bashi hadin kai ya gudu don kada a kama sa, ko kada su kunyata a idon duniya, gaskiya samun mutun mai irin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login