Showing 258001 words to 261000 words out of 321579 words

Chapter 87 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

Allah SAW ki buWe min ?ofar Wakina! Inaso naje gurin Unaisah! Inaso na hadu da yan uwana gurin biki, wallahi na ha?ura da bridal gown din zan sanya ankon amarya, bazan ?aracewa inason wani abu kalar nata ba"

tsantsar tausayinta ne Ya mamaye zuciyar ummin nata, sai dai bata jin zata Iya buWe mota ?ofa, Batool nema take taja masu abun kunya.

Idanunta ne suka cicciko tab da kwalla, ta jingina kanta jikin kofar tana jiyo kukan Batool dake karya mata zuciya..

"Laifinki ne Batool, ke kika ja na rufe ki, bada son raina ba, meyasa baki jin maganata? Meyasa kikeso kija mana abun kunya ne"?

"Bazan kara ba Ummina, na daina ki yafe min, ni ma bansan meke damuna ba!, bansan meyasa nakeson komai irin na Unaisah ba, banaso naga tafi ni da wani abu, nafison komai namu iri Waya"


Da rudu Ummi ta saki baki sototo tana sauraron ta..

"Batool why why? Ba fa ciki daya kuka fito ba, sister dinki ce but ki sani don kuna yan'uwa ba hakan yana nufin kaddararku iri Waya ba, kowa da yadda Allah ya tsara mashi rayuwarshi, ni na narasa gane Kishi kike da ita? Ko hassada kike mata? Ko kuwa kawai gasa ne"? ta fada idanunta na fitar da ?walla..

"Ko kinyi tunanin bansan komai bane? Kinyi henna irin nata, kinyi gyaran gashi irin nata, komai na gyaran jiki da akai mata kema saida akai maki sai kace ku biyu za'a aurar? Angaya maki komai akeso mutun yayi irin na amarya? Ta karashe maganar tare da bugun kofar cikin 6acin rai


"Why Batool? Kin Waga min hankali, na tsani hassada arayuwana, mugun ciwo ce dake kashe rayuwar mutun Ya gur6ata masa tunani, bana so ki zama daya daga cikin wadanda zasu nakasa rayuwarsu da hassada..."

"Ki fahimce ni ummina, Wallahi ba hassada nake ma Unaisah ba, kuma bana kishi da ita, sannan ba gasa nake da ita ba, nima bansan meke damuna ba, Ina jin haushin abun da nakeyi, na tsani kaina.." cikin shesshekar kuka ta ?arashe maganar..

"Batool na fahimce ki, Ki daina kuka bana sonji" amsawa tayi da toh..

Zurfin tunani ta shiga, tabbas ta yarda da maganar Batool amma meyasa take mata haka?

Zuciyarta ce ta bata amsa da cewa"ko dai son Owais ta ke yi shiyasa ta ke yin komai irin na Unaisah donta burge shi kamar yadda Unaisah zata burge shi .."

gabanta ne Ya fadi daram.

Arude ta furta"batool Kina jina!
"Inaji ummina"

"Ki ji tsoron Allah ki faWamin gaskiya! Ko dai Dg kike so"?

"Ni ba sonshi nake ba.."_ bata kare maganarba Ta katse ta"naji bakison shi, amma baki tunanin shi? Ko jin faduwar gaba idan kika gan shi"?

Shiru tayi kamar bataji me tace ba.

Knocking kofar tayi"baki bani amsa ba, nasan kina jina, pls ki faWamin zan nema maki mafita ne"

"Duk abun da kika tambaya inayi, sai nayi tunaninshi nake jin dadi araina, ko 6atamun rai akayi da zarar na tuna shi nake mantawa da komai, kuma bana jin dadi idan Unaisah ta fadamin ya siya mata abu, ni bai siya min ba, ko inji suna waya, wlh haushi nakeji kamar in haWiyi zuciyata, amma inason unaisah, kawai ni banason kulawar da suke ba Juna ita da Chief, .."

kasa ?arasa maganar tayi jin Sallallamin da Ummi ke yi..

"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, abun da nake gudun ya faru ya faru! Batool son shi ki ke yi! Shiyasa kike kishi da Yar uwarki, ki faWa min tun yaushe kike son shi"?

"Ummi ba son shi nike ba, Ni bazan iya son mijin Unaisah ba, kuma na daWe inajin shi araina, tun kafin nasan yana son Unaisah ..."

wani irin sarawar ciwon kai Ummi taji, ji take inama zata Iya cika ma batool burinta, saboda batason ta nemi wani abu ta rasa amma wannan karan tazo da abun daya fi karfin su.

"Batool, Kiyi hakuri, nasan da ciwo, amma ki daure, ki cire shi aranki, nasan kin sani, Unaisah itace Second wife din shi, ba lallai In yana da ra'ayin ?ara aure ba, kuma ni bana so ma kaddarar aure ta hadaki da Unaisah, saboda zaku yi ta samun sabani ne, in sha Allah zan tayaki da addu'a Allah ya za6a maki mafi alkhairi cikin samarin dake zuwa neman auren ki. .."

bata karashe maganar ba, Batool Ta rushe da kuka kamar ranta zai fita..

Itama kukanne ke nema Ya kwace mata..

"Zan tafi Batool, ummu Unaisah tana jira na, kada su ji ni shiru, nasan zaki kuntata amma bazan iya bude ki ba, zamanki agida sai yafi mana kwanciyar hankali please, Kiyi hakuri ki daina kuka banaso, kici breakfast din dana ajiye maki akan table"

tana karashe maganar ta juya da dan gudunta ta sauko down tana kuka ta nufi Waki don ta shirya.

A bangaren Batool, tana ta bubbuga kofar, hawaye sun wanke fuskarta, ?unci da bakin ciki suka mamaye zuciyarta, gaba daya ta haukace ta koma bubbuga kanta jikin kofar, nan take hancin ta ya soma bleeding, fatar goshinta tayi jawur tana barazanar fashewa saboda buguwar da ta yi, lokaci daya wani azababben ciwon 6arin kai Ya ziyarce ta, wani irin jiri ne ya kwasheta bata sa'adda ta yanke jiki ta kife kan floor ba, ga wani irin chest pain daya fara addabarta, gaba daya ta fita hayyacin ta, cikin karyayyar murya ta soma sambatu


_mutuwa zanyi in ban same shi ba, na fita son shi, ita bashi take so ba, ni nake son shi.. " =ؔ?



Alhamdulillah, Aure Ya Wauru, bayan kammala Sallar Juma'a Dubban Jama'a Sun shaida Waurin auren Director General Owais Sharafudeen Obinna tare da Amaryarsa Unaisah Zaheer Tajudeen, Wanda aka gudanar A Masallacin Sheikh Imam malik, duniya ce ta shaida daurin Auran Unaisah, ba'a taba daurin auren daya yaWu irin nata ba, in a short time Labarin auranta ya karaWe duniya,Yan jarida suka dinga magana akan shi, Social media ko'ina zancen auran ta ake yi, abu biyune Yasa Aurensu Yayi shura, Na farko kowa yasan Dg da Unaisah tun lokacin da asirin kurkukun kaddara ya tonu su ka yi farin jini na fitar shari'a.

Abu na biyu dayasa Auran Unaisah Ya shahara a fadin duniya, bakomai bane fa ce Expensive Downry dinta, yana Waya daga cikin sadaki mafi tsada a duniya, sadakin da kowa ya ke ta jira yaji menene, Taj Bai bayyana ba ko ita Unaisan da mommynta basu sani ba, ya boye ne saboda baison surutun mutane, baima so sadakin ya kai haka tsada ba, ba yadda zaiyi ne saboda mahaifiyar ango ce ta biya sadakin shalelenta, sai agurin Waurin auren, shiekh Imam Malik Ya zayyana sadakin Unaisah tiryan tiryan kowa yaji kuma ya shaida.


Sadakin Unaisah dai an biya shine da 50-carat Heart-Shaped Diamond Pendant mai darajar gaske.


su nan wannan sadakin burin kowace ?a mace, dole mutane suyi tsegumi, Labarin sadakin Unaisah Ya zama ruwan dare ko'ina zancen shi akeyi, Mutane har sun fara tunanin yaya gidanta zai kasance! Don sun fahimci angonta ashirye yake da ya ?arar da tattalin arzikinsa akanta, ganin yadda yake almubazzaranci da dukiya akan amaryarsa, kamar baison zafin neman ta ba, ya siyeta da darajarta tun da aka fara shagalin bai kashe abun da yayi kasa da dala dubu ba, al'umar duniya sun ruWe.

Gidajen Talabijin da radio sai taWin auren su a ke yi..


Kwata kwata Unaisah batasan Auranta ya kammalu ba, sai dai faduwar gaba da take taji, a lokacin designer din ta gama shiryata, Unexpected wayarta da ke ajiye kan drawer ta soma ruri.


da sauri madam ta mika mata wayar, ta kar6a tare da duban me kiran nata.

"Murmushi tayi, cike da zullumin mai zai faWa mata tayi picking call Win ta kara a kunnanta..

Sanyayyar muryarsa ce ta ratsa kunnanta"Alhamdulillah Unaisah my Angel, kin zama mallaki na, halak malak, ke tawa ce, burina ya cika na ganin ranar dana daWe ina jiran ta..."

nutsuwa tayi tana sauraron shi aranta ta ayyana wai dagaske auranta ya Wauru? Yanzu ita matar yaya Owais ce? Kishiyar Nazli? Ya Allah

Idanunta ne suka cuccuko da kwalla cikin rawar murya ta furta"yaya Owais, ina tayamu murna, Alhamdulillah.... "

cikin shesshekar kuka ta yi maganar, tana so ta zukunna tayi sujuddusshukur sai dai gown din jikinta ta matse ta..

Kamar daga sama ta tsinkayi miryoyinsu a cikin kunnuwanta..

Wata irin buWa suke rangwaWawa cikin zazza?ar muryarsu, daga can cikin gidan ayyyiririiiiiiii..



"You're no longer Unaisah Zaheer Tajuddeen! You're now Mrs Owais, Come and take your crown, our bride queen! His princess, Yeeehhhhhhh"


A lokacin kiran nasa har ya katse, godiya tayi mata designer din, sukayi sallama da juna ta tafi.

A tsanake ta soma tafiya zata fuce daga Wakin cikin sauri.


Tana fitowa taci karo da bridemates suna tunkaro inda ta ke, gaba daya sun razana da ganin adon jikin ta, tayi masu kyau, fuskokin su Wauke da fara'a sai murna su ke yi, gaba Wayan su sun sanya anko din su, sun daura Red Aso ke headband akan su, sunyi kyau sosai.

suna tafiya suna ta ka rawa yayin da su ke bin wa?ar.

_Ta zamo amarya
Badan tayi daukaka ba
Ta zamo amarya
Ba domin tafi kyau ba
Ta zamo amarya
Ba domin itace ba
Sai dan mijinta nasan ta
Ashe kaunace_

Baby yau ko gobe (baby)
Ya zamo angon ki (eh)
Amarya ta zama taka (baby)
Kar kayi mata wayo (eh)
Baby yau ko gobe (baby)
Ya zamo angon ki (eh)
Amarya ta zama taka (baby)
Kar kayi mata wayo..

Kunyace ta kama ta ta juya zata koma inda ta fito, da sauri su ka yi mata ?awanya suka cigaba da
Wa?e ta suna kewaye ta sai ti?ar rawa su ke yi.

Farin ciki ne ya cika ta, har ta kasa rufe bakin ta, ta dinga sakin dariya tana bin su da kallo Waya bayan Waya.


Walwalar fuskarta ce ta Wauke, lokacin da ta lura babu Aminiyarta a cikin su..

"Ina Batool? Batazo ba? Ko tana a cikin gida"?

ta tambaya tana duban su, Parveen tace"ba tazo ba, tun Wazu muke nemanta bamu ganta ba.. "

"May be bata gama shiryawa bane" acewar Sajeeda.


"Kun tambayi mommynta"? ta faWa fuskarta a yamutse.

"A'a bamu tambayeta ba" suka haWa baki gurin furtawa..

Nan take ranta ya bata akwai wani abu daya faru wanda ya hana Batool zuwa, zaiyi wuya in ba maganar jiya bace..


Cikin sauri ta soma tafiya suka bi bayanta kaitsaye suka nufi main Falo na gidan, tun kan su shiga suka soma jiyo haniyar al'umma da ta cika gidan, ga sautin kiWan ?warya daya karaWe kunnuwan su.


Suna shiga ciki gaba Waya idanu su ka dawo kan Amarya Unaisah, kowa ya zare idanu haWi da buWe baki suna bin ta da kallo kamar zasu haWiyeta saboda kyawun da ta yi.


Jemimah da ke ruke da hannunta ta dinga rada mata ta dinga fadin Tubarkallah kar su cinye mata kurwarta, batasan sa'adda ta saki dariya ba.


Aikuwa kowa yayi ta santin ta suna yaba kyanta, duk ta kasa sa?ewa dakyar take iya kallon su cike da jin kunya, Ankon da iyaye mata suka sanya tsadaddar atampa ce chiganvy, kowacce ta kashe Waurin kallabin ta abun sai wanda ya gani, gida ya cika makil wasu suna ta taka rawa, yayin da wasu suke cin abinci, wasu fira su ke yi cikin nishaWi.


Hajiya adama ce ta nufosu tana karasowa ta rungume Unaisah tare da shafa bayanta tana fadin"Masha Allah Unaisah, My baby Angel, Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya, Allah Ya baku zuri'a Wayyiba..." a hankali take amsawa da ameen ameen mommy.
.
"Kai Masha Allah, tubarakallahu Ahsanul khalikin, Ayyiriyiriiiii! Amarsu Ta Ango! amarya Bakya laifi ko kin kashe Wan masu gida!, Dan Allah ku bani guri, In rungumi ji?ata, adinga hadawa da tubarkallah.." muryar Hajiya layla suka jiyo tana magana cikin raha, kowa dake agurin ya kama dariya, murmushi Unaisah tasaki tana kallon grandma Win ta dake tunkaro su hannun ta ru?e da juice da take sha, tana karasowa ta rungumeta tana shi mata albarka tare da fatan Alkhairi tana amsawa da ameen ameen hadi da yi mata godiya.

Unexpected suka tsinkayi Muryar Sister Zahra tana yi mata kirari

"farin wata sha kallo, tauraruwar dake haskaka sararin samaniya, dawisu sarkin ado, the Dg's wife, nan gani nan bari, dukiyar dg ce... "

gaba Waya suka sanya dariya, suna kallon ta yayin da take shigowa ta ?ofar falo, ankon yan matan amarya ne a jikin ta, kana kallon ta zaka gane akwai ciki a jikin ta, tayi ?iba hutu ya zauna mata, Unaisah taji dadin kirarin da tayi mata, tana ?arasowa ta rungume Unaisah kamar zata mayar da ita cikin ta.

"Unaisah ina yi maki fatan Alkhairi, Allah yasa mutuwa kadai zata raba... " amsawa tayi da ameen nagode Aunty Zahrana, Allah ya sauke ki lafiya.
"Ameen nagode Unaisahna"

"Ina Aunty Aneelerh"?

Zahra tace"suna acan dakin Uwar Amarya..."

"Nagode Aunty Zahra, bari naje na same su... " ta faWa tare da juyawa ta nufi dakin mommyn ta.

A bangaren Benazir, bayan da Taj ya kira wayarta ya faWa mata aure ya Wauru..

bai ?are maganar ba, tayi rejecting call din ta zauna gefen gado, batasan sa'adda ta fashe da kuka ba saboda bata shirya rabuwa da Unaisah ba, tana jin kewarta tunkafin zuwan wannan ranar, Aisha da Aneelerh sun taru akanta, suna ta lallashinta tare da bata ba ki.


"Haba mana, Unaisah ba wata uwa duniya zataje ba, a cikin estate din nan gidan ta ya ke, ko ihu kikayi zata jiyo ki ne, sunna fa zata raya, ke ba abun farin cikin ki bane? Yar ki tayi aure, ta auri nagartaccen namiji Wan babban gida, da kowa ke burin ya haWa zuri'a da su... "

Aisha ce ta fada cikin sanyin murya.

Tana shesshekar kuka tace"hmm ba za ku gane ba, ni banyi wata rayuwa mai tsayi da Unaisah ba, duka fa baifi shekaru ?alilan ba da mukayi atare, yanzu kuma tayi aure, zata koma gidan mijinta da zama, ita kadaice fa gareni, ina sonta a kusa dani, gani nake kamar in ta tafi ba lallai ta samu kulawar da muke bata agida ba, har yanzu yarince fa, ku duba kuka ga irin kishiyar da zata zauna da ita, ina jin duk ba daWi, bansan ya zanyi ba..."

Aneelerh tace"please ki daina wannan maganar, kin san yadda dg ke sonta, in sha Allah Unaisah zata samu kulawarsa, karki wani damu da kishiyarta, bata fi Unaisah da komai ba, kuma kowa da matsayinsa a wurin dg, ni nasan zaiyi adalci a tsakanin su in sha Allah"

Cigaba da share kwalla tayi tana sauraron su

"Hakuri zakiyi Benazir, kowa fa haka akayi masa auran ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?nan, kin sani kema, ni banaso Unaisah tazo ta sameki kina kukan nan wallahi zaki daga mata hankali ne..." jinjina kai ta danyi ta soma share hawayen ta da hanky.

"Yawwa ko kefa, bari na gyara maki daurin Wan kwalin..." ta fada tana gyara mata head Win ta daya karkace.

gaba dayansu sunyi kyau cikin ankonsu..

Aisha tace"farin ciki yakamata muyi Benazir, tun da aka fara bikin nan dg ke 6arin dollars akan Unaisah, kamar baisan zafin neman su ba, sai fa kana son abu kake siyansa da daraja, maganar kishiya mu aje ta gefe, Unaisah fa babu mai iya ja da ita wallahi, ita da take da mu? Babu wani lagwon namiji da ban sani ba, Allah idan dg ya shiga tafin hannun Unaisah mai ?watarsa sai ya shirya...."

gaba Waya suka sanya dariya..

Anilah tace"godiya yakamata muyi wa Allah, Wallahi Unaisah tayi dacen miji, ga kyawawan halaye, komai Allah ya basa! kinji kuwa yadda al'umar duniya ke taWin bikin Unaisah"?

Murmushi Benazir tayi"mungode ma Allah, Wiyar mu tayi goshi, Ina alfahari da dg, na yarda da son da ya ke yi mata, fatana Allah ya basu zaman lafiya da ita da mijinta da kishiyar ta... "

Gaba Waya suka amsa mata da ameen.

"Ummm Itama dai Unaisah zataje taji abun da mu ka ji A first night din mu.."

waro ido su ka yi jin abun da Benazir tace, aikuwa suka tuntsire da dariya, Aisha tace"Allah ya shirya ki Benazir, me hali bazai ta6a canzawa ba, har yanzu kina nan da rashin kunyarki, yanzu nan fa kika gama kukan munafurcin za'a rabaki da ?ar?i..." dariya Benazir tayi"to ya zanyi Aisha! Abun nan fa ya riga daya faru, dole Unaisah ta tafi gidan mijin ta shikenan ba zanyi raha ba.."

Aneelerh tace"baiwar Allah, tun kafin ta mallaki hankalinta take da burin yin aure, tunkan tasan ma'anar auren, ba dan komai ba sai don saboda ganin irin rayuwar farin cikin da mu ke yi Nida Uzair a lokacin, ni dai fatana Allah yasa Unaisah ta more rayuwar auranta kamar yadda take saran zataji dadi idan tayi aure, Allah yasa kar tayi danasani, saboda inason ta cika burin ta"

idanunta cike tab da kwalla tayi maganar tunawa da marigayi Uzair.

gaba daya jikin su yayi sanyi..

In a broken Voice Benazir da Anila suka hada baki gurin furta"ubangiji Allah yaji?an Uzair, Allah yakai rahama kabarinsa"

"cikin sanyin murya ta amsa masu da Ameen"

Shiru su ka yi na Wan wani lokaci babu wanda ya ?ara furta kalma.

"Yakamata mu fita kar aji uwar amarya shiru bata le?o waje ba, kuma mun bar su mami da aikin tar6ar baki"

Aneelerh tace ta faWa tana mikewa Ummi tace"in da Allah ya rufa mana asiri sai bayan biki da sati Waya za'ayi dinner, kafin ranar zamu ?ara shiri"

"Ni dai ba haka naso ba wallahi, banji dadi da Owais ya tsara dinner har sai bayan sati daya da yin auren ba, dama dai agida zata zauna kafin ranar dinner din da naji dadi, kuma wai ba gidanta za'a fara kaita ba, gidan iyayensa za'a wuce da ita, jiya Taj ya ke faWa min, na rasa gane meyasa suka za6i su yi hakan? Bansan ko haka suke yin auren su ba, Ni dai a asanina amarya gidanta ake fara kaita bayan biki"

Ummi tace"wannan duk ba abun tashin hankali bane, munsan mutanan nan, sunyi mana halaccin da ba zamu iya biyan su ba, komai suka yanke akan Unaisah muyi masu kyakkyawan zato"

Ajiyar zuciya ta sauke"hakane kuma, nima na faWa ne kawai ba dan ina nufin wani ba"

Aneelerh tace"ni nafi tunanin Owais ne a bayan komai, may be akwai wani surprise da zaiyi ma Unaisah shiyasa bayason kowa nata ya rakata gidanta, saboda ita ya ke son ta fara zuwa, shiyasa ya tsara a fara kaita gidan su daga can sai ya Wauke ta yakaita gidan sa... " ta kare maganar idanunta a cikin na Benazir dake kallonta..

Ummi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login