Showing 252001 words to 255000 words out of 321579 words

Chapter 85 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

tafiya ya ka baro uncle Muhsin din? Ina fata ya samu lafiya"?

"Alhamdulillah My Angel, nayi missing naki nima, Muhsin yana gaishe da ku, jikinshi da sau?i fatan na same ku lafiya, Ya shirye shiryen biki" cike da jin kunyarshi tace"Alhamdulillah."

Kallonta yayi da kyau"masha Allah daughter, umminta me kike batane naga ta sauya min tayi kyau kamar lu'u lu'u ..."

Dariya Benazir tayi"Sirrin mune na mata, kaima lokacin da zaka aure ni ba haka ka rude ba duk ka susuce da ganin yadda nayi kyau..."

bata ?are maganar ba ya galla mata harara afakaice kasa kasa da murya yace"meye haka pls"?

Yar dariya tayi"me kuma ya rage Tajo, ai daga gobe ta wuce Unaisah zatasan komai.."

ta fada tana Wage masa gira.

throw pillow ya janyo Ya wurga mata tayi saurin cabe shi a hannun ta

"babu wani boye boye Tajo, daga gobe ne"

"Ummu unaisah ki daina! Aa wai meke damunki ne"!

Bushewa tayi da dariya, Unaisah data langwa6e kanta saman kafadar shi tayi shiru tana sauraron su.

"Wai ya maganar sadakinta ne? Ko yayi tunanin kyauta zamu bashi ita ne? Naji shiru tun satin da aka sanya bikin naketa jira inji ance ga sadakin Unaisah amma shiru kakeji wai malam yaci shirwa"

"Mun yafe masu sadaki, salatin annabi za'ayi don auren yayi albarka ko Unaisahna" ya faWa tare da leken fuskarta.

murmushi tayi tare da jinjina mashi kai.

"Hmm Yanzu mutun yayi magana ace ya yi sa6o, ko ya kafurta amma taj meya kawo wannan maganar? In albarkar aure akeso nima in na saka mata ya wadatar ko"

?yal?yacewa su ka yi da dariya gaba Wayan su cike da nishadi su ke yin firar su..


*AGIDAN DR SHUREIM=?%?*


A hankali Motar shi ta kunna kai cikin harabar gidansa, a tsanake ya ke yin driving yana bin karatun alqur'anin da ya kunna..

Bayan yayi Parking din motar ya kasheta, A hankali ya fito as usual sanye da arab dress dinsa..

Fitowa Ummi tayi daga cikin gidan, ta nufe shi da sauri tana karasowa sukayi hugging din juna kamar sun shekara basu hadu ba..

Dagowa tayi ta sumbaci kuncin shi"Welcome back habibina, ya kake ya aiki? Ina fata kana lafiya? Ta faWa tare da kar6e jakar hannunsa..

Fuskarsa dauke da murmushi yace"mar'atussaliha, Alhamdulillah Ina lafiya, fatan na same ki lafiya.."
"Lafiyalou"
Ru?o hannunsa tayi a cikin nata"mu shiga daga ciki.."

A bedroom dinsa suka tsaya ta taimaka mashi ya rage kayan jikin shi.

"His excellency, wanka ko abinci wanne kafi bukata in taimaka maka da shi .." ta tambaya tana kallonsa yayin da ya ke a zaune gefen gadon sa.

"Ke" ya bata amsa a takaice
Kayataccen murmushi tasakar ma shi" ta matsa kusa da shi bai aune ba yaji ta fara kissing nashi sai da tabari ya fara hawa kan network tayi saurin raba jikinta daga na shi.

"Nasan akwai gajiya a tare dakai da kuma yunwa, bari na kawo maka abinci..." wani marayan kallo ya bita da shi yana hadiyar yawu.

Kashe mashi ido daya tayi ta juya yabi bayanta da kallo mai cike da shauki, har saida ta bace ma kallonshi tukunna ya jingine kansa jikin pillow, yana mai kara godewa Allah daya mallaka masa ummi amatsayin matarsa, dadinta yakeji fiye da komai na duniyar nan, idan yana atare da ita mantawa ya ke yi da komai.

Har ta shigo bai dawo daga duniyar tunanin da yake yi ba, a saman table ta daura tray din hannunta mai dauke da lunch dinsa.

"Mijin so, am back, ka tashi in ciyar dakai girkina" murmushi yayi tare da mikewa ta janyo table din agabansa.

Yana niyar bude baki yayi magana tayi saurin daukar glass na juice ta kafa mashi abaki ya dan kur6a yana jinjina kanshi alamar yayi dadi.

Abaki ta dinga bashi abincin yana ci.

"Ina Batool ne? Batasan na dawo bane? Ko ta tafi gidan Bikin ne"? Girgiza kai tayi"a'a bataje ko'ina ba, may be tana a bedroom din ta"

"Taci abinci?

"Nayi nayi da ita tace min bata jin yunwa, dana matsa mata sai tace min da anjima idan ta shiga gurin Unaisah zasuci a atare"

Shiru ya danyi jimm kafin yace"kira min ita"

"Okay Sir" aje spoon din tayi ta juya tana tafiya da rangwaWa dagangan take yi don ta rikita shi.

Murmushi yayi tare da dan girgiza kan shi..

A cikin kunnanta ta tsinkayi shesshekar kukan Batool, wani irin faduwar gaba taji, da karfi ta shiga bubbuga kofar dakin ta"babe! Babe! Me kike ma kuka ne? Zo ki bude mun kofa!

Shiru taji ta daina kukan kuma babu alamun zata bude kofar.

"Babe! Kina jina kika shareni? Ba zaki bude min kofa ba"? ta fada da damuwa akan fuskarta.

Dakyar ta samu batool ta buWe mata kofar dakin, bin ta da kallo tayi, idanunta sunyi jawur sun kumbura, Cheeks dinta sunyi jajir alamar tasha kuka, sumar kanta duk ta hargitse
Hankalin ummi idan yai dubu to ya tashi.

Dafa kafadunta tayi"meke damunki? Baki da lafiya ne? Waya ta6a min ke? Meyasa ki kuka.."?

Duk tabi ta rude..
Cikin sanyin murya batool tace"babu komai, bana jin dadi jikina ne" girgiza kai ummi tayi"ban yarda ba batool, dole akwai abunda ke damunki, Mu shiga ciki ki fada min.." ta fada tare da jan hannunta suka shiga ciki ta zaunar da ita gefen gadon itama ta zauna.

"Kada ki boyemin Batool dina, ki fadamin abun da ke damunki zan taimaka maki mu nemi mafita"!


Kasa sanar da ita tayi saboda tana fargaban yadda zata dauki abun idan taji.

Amma ya zatayi bata da mafita..
lallashin ta ummi ta soma yi tana lalla6ata don ta faWa mata.

Har saida taji zata iya sanar da ita.

"Ummina, bana son kayan da aka raba mana na yan matan amarya, ni bazan sanyasu ba, nafison kalar rigar da Unaisah zata sanya a ranar bikin ta.. "

kasa karasa maganar tayi ganin yadda Ummi ta saki baki sototo alamar mamaki ya kamata..

"Nasan zaki fahimce ni shiyasa na fada maki, wallahi in har ban samu kalar rigar Unaisah ba, ba zanje gidan bikin ba ranar auran ta.."

ruWune tsantsa akan fuskar Ummi"batool kinsan me kike fada kuwa? Dagaske kike ko wasa kike min" fuskarta babu annuri tace"wallahi dagaske nake maki, dan Allah ki siyamin kalar rigarta komai da komai"

"Batool zan iya yi maki komai a dunyar nan indai baifi karfina ba, amma in banda abunki tayaya zaki ce irin bridal gown din Unaisah ki ke so? Batool tafi karfin mu, bamu da kudin da zamu iya siya maki ita, har yau ni banma ga rigar ido da ido ba, a hoto Benazir ta nuna min ita, ba'a kaiga kawota gidan ba! Sai zuwa gobe"



kwata kwata Batool bata fahimtar bayanin ta"ummina ba za ku iya siya min irin ta ba? Shikenan ni bazan iya mallakar komai da Unaisah ta samu ba?

Idanunta cike tab da kwalla ta karashe maganar, arude ummi ke dubanta cike da fargaban kada abunda take kokwanto ya tabbata akan ta.

"Ki fahimce ni Batool, bamu da halin da zamu iya siya maki ita!tafi karfin arzikin mu, kuma babu yadda za'ai ki sanya kalar rigar Unaisah aranar auranta, zakija mana surutu tun da ba auranki akeyi ba"

"amma ki canza wata rigar mai saukin kuWi in sha Allah zamu siya maki, amma dan Allah kidaina fadin ba zaki iya mallakar komai da Unaisah ta samu ba, kema zaki iya samun fiye da shi amma kinga wannan bridal gown din da kike magana akai ba iyayen ta bane suka siya mata ba, Mijin da zata aurane ya siya mata..." bata kare maganar ba, taga ta zabura ta mike tsaye jikinta ya hau yin kerma cikin muryar fushi mai tattare da bacin rai tace"zanje na fadawa Abbana, nasan zai siya min irin ta.." fucewa tayi daga dakin.



A rude Ummi tamike tabi bayanta gabanta naci gaba da faduwa ta rasa gane meke damun Batool ne? kamar ?amar yarinya, Meyasa takeson irin rigar Unaisah? Maganganunta kamar suna nufin tana hassada da ita, wallah bata fata abun da take hasashe ya zamana gaskiya.

Ko sallama ba tayi ba ta shigo dakin, abun da ba dabi'arta ba, motsinta yasa shureim dagowa ya dubeta, kwata kwata bai lura da moods din fuskarta ba.

Zama tayi gefenshi ko gaishe da shi batayi ba cikin shesshekar kuka tace"Abbana dan Allah, dan sonka da annabi, ka siya min irin rigar Unaisah ta aure! Wallahi ita nakeso Abba" bai san sa'adda ya furzar da ruwan lemun daya kur6a abakinsa ba, da sauri Ya aje cup din kan table ya dubeta da idon basira.

"Batool me ke damunki? Ba kiyi min sallama ba, ko gaishe ni bakiyi ba, ba sannu da dawowa kuma ki rasa da wani zance zaki tarbeni sai da wannan"? Ya fada fuskarsa a yamutse.

Bata kaiga furta kalma ba, Ummu ta shigo dakin, anan ta fayyace masa komai..

"Haba Batool, wallah idan akan farin cikinki ne sai inda karfinmu ya kare, ba abunda ba zamu iyayi maki ba, amma ki gane rigar Unaisah tafi karfin mu, kuma in banda abunki ai babu me sanya irin rigar amarya ita nata dabanne, kuma ba an baku kyautar anko na kawayen amarya ba? kiyi hakuri ki sanya su mana.."


bai kare maganarba, ta fashe masu da kuka kamar ranta zai fita, gaba daya ta daga masu hankali, suka rasa shawo kanta, dr shureim daya rude yayi zaton iskane suka shigeta nan take ya fara yi mata rukiya


Cikin shesshekar murya ta furta"abba da hankalina! Ni ce batool, babu wani aljani a jikina, Ku dainayi min ru?iya kawai kuyi min abunda nakeso, ban taba tambayarku wani abu kun kasa yi min ba, meyasa ba zaku iya siya min kalar rigarta ba! Tayaya zan yarda kuna sona?

Maganganunta sun daga hankulansu.

Tsawa dr shureim Ya daka mata ganin taki ta saurare su

"Ya isa haka Batool, na fahimci rashin wayau ke damunki, karki kuskura ki kara wata magana anan idan ba so kike ranki ya 6aci ba! Haba sai kace yarinyar goye? Kodan kinga muna lallashin ki shiyasa kike mana abunda kika ga dama? In banda rigima me zakiyi da rigar amarya? Ke za'ay ma aure ne?

Ummi ce ta balbaleta da fada ta inda take shiga bata nan take fita ba, Dr shureim sai kokarin dakatar da ita yakeyi saboda baisan 6acin ran batool dinsa.

Mi?ewa tayi fuskarta sharkaf da hawaye cikin fushi ta fuce daga dakin, suka biyota da sauri suna ambaton sunanta kafin su karaso tuni ta shige daki ta kulle kanta.

Bubbuga kofar suka dinga yi suna lallashinta akan ta buWe ma su ?ofa, tana ji tayi banza ta kyalesu, gaba daya tsoro sukeji kada ta lahanta kanta.

Da suka gaji da buga kofar, a kan stairs suka zauna ransu duk ajagule.

"Ina ma ace zan iya siya mata rigarnan wlh dana siya mata, saboda banason bacin ran batool, Idan tana kuka har cikin raina nake jin Waci, saboda tana tuna min lokacin da tana jinjira"

hawayen da suka cika idanun shi suka soma kokarin saukowa kan kuncinsa da sauri ummi ta sharesu da yatsunta.

"Pls, kada ka sanya damuwa aranka, ni kaina nayi fatan hakan amma ba zamu iyaba, dole sai mun danne son da muke mata mun koya mata hakuri da babu idan ba haka ba zamuci wahalarta agaba.."

GyaWa kansa yayi"ni lamarin ma tsoro ya bani wlh, lokaci daya ta sauya dabi'unta irin na yara amma meyasa takeson dolin doliya sai irin rigar Unaisah"?

Ya tambaya yana duban ummi.

"Kasan wani abu, nifa ba tun yau ba, na lura da wani abu, Batool tana kwaikwayon komai na rayuwar Unaisah, na rasa gane gasa ta ke yi da itane? Kishi ne ko hassada.."

bata kare maganarba ya katseta"bana tunanin haka, pls mu kyautata mata tazo"

Ummi tace"dole fa sai munsan meke damunta tukunna zamu kamo bakin zaren, Batool fa saboda bedroom din Unaisah yana a upstairs yasa itama ta nace mana akan mu maida mata bedroom dinta up, sannan ta matsa mana akan mu maidata jami'a don tayi graduation tare da su Unaisah, ka lura da kyau yanzu haka zanan kunshin hannunsu iri Waya ne babu banbanci"

Ta fada tana duban shi, abun duniya ya ishe shi.

"Aisha, bansan ya zanyi ba! Wai menene dalilin dayasa take son komai irin na Unaisah ne? Ummi tace"nima abun da nakeso na sani kenan, dole akwai abunda take mawa.."

gaba daya sun rasa mafita.

Gashi ta kulla kanta adaki tun safe su ke ta kokarin shawo kanta amma abun yaci tura, ba ci ba sha, har marece ya yi Batool bata fito ba, ko magana batayi gaba daya ta daga hankulansu.

Suna a zaune cikin falo kan sofas sun zagba tagumi, kwatsam sallamar Unaisah ta katse su cikin sauri suka dubi kofar falon, Shigowa tayi sanye da hijab ta ruke lunch box a hannunta.

Tuni kamshinta ya cika hancinan su.

"Unaisah.."

"Na'am Aunty Ummi, Uncle shureim ya ku ke? Ina fata kun wuni lafiya.."

murmushin ya?e suka sakar mata"lafiyalou Unaisah, Ya shirye shiryen biki"

"Alhamdulillah, munji shiru baku leko ba, Nima gurin yar uwata nazo duk yau banji duriyarta ba"

walwalar fuskar su ce ta dauke duff, damuwar da suke boyewa ta bayyana akan fuskokinsu.

"Ina Batool din? Ko tana daki"?
Har suna hada baki gurin furta"tana aWa.. Au bata nan ta tafi unguwa.." kallon juna su ka yi.

Da ruWu Unaisah take dubansu jin yadda suka bada amsa daban daban.

"Aunty Ummi, meke faruwa ne? Ina Batool? Ko wani abu ya faru da itane"?

?wafa Ummi tayi"Unaisah, Batool tana a daki, amma bata jin dadi, bacci takeyi, ki bari zuwa anjima zamu leko gidan tare da ita.."

girgiza kai tayi"i'm sorry Aunty Ummi bazan iya tafiya banganta ba, Inaji araina wani abu na faru badaidai ba, gaba dayanku da damuwa akan fuskokin ku, bayan haka tunda bikina ya matso Batool kullum tana a tare dani, amma yau ko kadan bata leko ni ba, tayaya hankalina zai kwanta? Dan Allah kubarni naga yar uwata.."

ta fada tana kokarin wucewa ciki da sauri suka sha gabanta kamar mara sa gaskiya duk sunbi sun rude, kwata kwata basu san tasan meke faruwa saboda sunsan son da take ma yar uwata zata iyayi mata komai donta faranta mata rai su kuma basu san hakan ya faru zataja masu abun kunya ne.

"Dan Allah Uncle shureim ku fada min meke faruwa? Kada ku boyemin abunda ke damun ku.. "

idanunta cike tab da kwalla tayi maganar.

Kallon juna su kayi, Ummi ta dinga girgiza mashi kai donta lura kamar so ya ke ya fada mata.

"Unaisah, dan Allah kiyi hakuri ki koma gida, wallahi bamu son kiji abunda ke faruwa, ba zakiji dadi ba,"

Gyada kai tayi"tunda ba zaku fadamin ba, zanje na fadawa mommyna da daddyna, nasan su zaku iya fada musu..."

juyawa tayi cikin sauri suka tarota.

"Unaisah, abun kunyane, Mun rasa gane kan Batool, ta canza mana, rigima takeyi mana kamar karamar yarinya, saboda kawai tace mu siya mata irin gown din auranki munce mata bamu da halin da zamu siya mata shine ta kama fushi damu, taita kuka, tun safe ta kulle kanta adaki, baci ba sha, munyi munyi da ita akan ta bude mana kofar dakin ta ?iya.." dr shureim ne yayi maganar.

Ummi tace"dan Allah karki damu kanki Unaisah, in banda abun Batool ai abun amarya na dabanne babu mai yin irin shigarta.."

Gabanta ne ya fadi, damuwa ta mamaye zuciyarta, dama sai da tayi fargaban hakan cos tun shekaran jiya da aka raba ma su Invitation bags ta lura Batool bata gode ba.

"Dan Allah Unaisah kada ki fadama kowa, daga mu sai ke, yadda mukayi maganar anan mu binneta anan pls, wlh abun kunyane maganar nan ta fita, kema mun fada maki ne saboda ba mu da mafita"

Cikin karyayyar murya tace"Batool bata kyautamin ba, kawai saboda tana son rigar aure na shine ta haramtawa kanta zuwa gurina, Ta kulle kanta adaki? ta tambaya cike da takaici.

"Bana fata Allah ya nuna min ranar da Batool zata nemi wani abu agurina in gaza yi mata shi, tafi karfin komai wallahi, zan iya hakura da komai in bar mata"

waro idanu waje sukayi cike da mamakin maganarta, juyawa tayi da sauri ta nufi up, suka bi bayanta da sauri.

Knocking kofar tayi"Ukhty Batool BuWe mun ?ofa, Nayi missing naki, Inason ganin ki"

A cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Unaisah daga waje, tana a zaune kan couch ta yi kuka har ta gaji, jikinta sai kerma ya ke yi saboda zazza6in daya kamata.

taji dadin jin muryar Unaisah saboda tayi kewar ganinta, sai dai batajin zata iya hada ido da ita..

"Nasan kina jina Batool, Dan Allah ki bude min ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????kofa kinji"?

Magiya ta dinga yi mata, dakyar ta samu Batool ta buWe mata kofa..

Kallo daya da Unaisah tayi mata sai da taji tausayinta ya kamata, daga gani ko wanka batayi ba, rigar jikinta ta yamitse kamar wadda aka kwato daga bakin kura.

bataji dadin halin da batool ta jefa kanta ba saboda kawai tana son irin rigarta?

Ruko hannunta tayi suka koma ciki, a saman gado suka zauna suna fuskantar Juna.

Ummi da shureim suna daga waje suna sauraron su.

"Meyasa bakizo gidanmu ba? Kin barni da tunanin wani hali kike a ciki ." ta faWa tana dan jifarta da harara.

Duk ta kame kanta, kamar wadda tayiwa sarki karya fadawa suka turketa.

"Um.. Bana jin daWine, amma kina araina.."

"Meke damunkine Batool?Dubarki dan Allah, daga gani ko wanka bakiyi ba.." ta fada tana bude Lunch box din data kawo mata.

"Ba abunda ke damuna.."

"Okay Aunty Ummi ta fada min baki ci abinci ba, ga lunch na kawo maki, abincin da mommy tayi ma daddyne na debo maki"

murmushi ta danyi fuskarta ba walwala.

"Naji dadi ya dawo lafiya, da anjima zan shiga na gaida shi, bari na wanko bakina"

"Kina nufin ko brush baki ba" daga mata kai tay, ta sauko ta shige toilet, ajiyar zuciya Unaisah ta sauke a ranta tana mai mamakin ta.

Jim kaWan ta fito ta dawo kan gadon ta zauna, Unaisah ta soma bata abaki tana ci..

Duk akan idon su Aisha, jikinsu yayi sanyi sosai..

Saida taci ta koshi tana ta santin abincin, daga bisani Unaisah ta karasa cinye sauran data rage..

Ta daura lunch box din gefe Waya.

Ruko hannunta Unaisah tayi a cikin nata, idanunsu a cikin na juna..

"Bayan rigar aurena sai me kikeso nawa"? Gabantane Ya fadi wata irin kunya ce ta kamata adabarbarce ta furta"um..waw..waya fada maki? Ni bance ina son rigar auren ki ba, cewa kawai nayi kalarta nakeso ba taki ba. "

murmushi Unaisah tayi"meye na daga hankali aciki? Tambayarki nayi kawai ki bani amsa, banaso gobe ki ga wani abu nawa a ?urarren


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login