Showing 264001 words to 267000 words out of 321579 words

Chapter 89 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

mutunci da karamci_________ "

Hajiya adama ce tayi maganar cikin nutsuwa.

Gaba Wayan su murmushine akan fuskokinsu ga dukkan alamu sunji dadin maganarta.

Ta Waura da cewa"babu shakku ko fargaba a tare damu, saboda munsan hannun da ?ar mu ta faWo, toh ga ?arkunan Mun kawo maku amana, Allah ya tayaku ru?on ta.." ta faWa tare da nuna Unaisah da hannun ta..


Gyaran murya malika sarauta tayi, hankali ya dawo kanta, gently ta soma magana cikin ?asaita

"Mun kar6i amanarku da hannu bibbiyu, Gaba Wayan mu muna farin ciki da zuwan ku, kuma muna farin ciki da zuwan Unaisah cikin Family din mu, wannan abun alfahari ne agare mu, samun suruka irin Unaisah, wadda ta fito daga gida na mutunci da tarbiya zai yi wuya a duniyar nan, in sha Allah, alkawarine mukayi maku, Unaisah bazata ta6a maraicin barin gidan iyayenta ba, kuma bazata ta6a danasanin Auran Wan mu ba... " Kalamanta sun faranta ran su, aneelarh har taji ?warin gwiwa atare da ita tasan in ta bama benazir labari ba qaramin dadi zataji ba..



Hajiya saratu tace"Ai in sha Allah yadda Unaisah ta shigo family din nan, mutu karaba mu da ita, zamu tsaya tsayin daka don ganin ta zauna lafiya agidan mijinta, ko yaji bazai dawo da ita gidan iyayen ta ba..." ta ?arashe maganar tana cizgar fiffiken kaza..

Gaba Waya suka sanya dariya cikin raha..

Burin Unaisah gimbiya Mujeedat tayi magana, so take taji muryarta kota samu salama a cikin zuciyarta, saboda gaba daya muryarta irin ta Danish ce dan banbancin kadan ne shi yana namiji ita kuma mace..


Aikuwa Cikin sa'a ta tsinkayi muryar Mujeedat a cikin kunnanta, cikin harshen turanci ta ke yin maganar ta..

"yadda Unaisah ta nunama jinin mu ?auna, ta amince zata rayu da shi tabar gidan iyayenta da danginta saboda shi, ta dawo namu don ta raya sunnar ma'aiki, in sha Allah ba zamu bari tayi danasani ba, ba zamu ba ku kunya ba, Unaisah ?ace agurin mu, kuma lu'u lu'u ce mai daraja mai wuyar samuwa, da kowa ke burin ya mallaka amatsayin surukar sa, amma mu Allah ya azurtamu da samunta, iyayenta sun mana halaccin da ba zamu iya biyan su ba, sun dauki yarsu sun bamu badan isarmu ba, badan matsayinmu ba, badan sun gaji da ita ba, kuma badan basu sonta ba sai don suna son yarsu ta raya sunnar ma'aiki, tayi aure itama ta hayayyafa kamar yadda suma su ka yi, in sha Allah zamu ru?e Unaisah da hannu bibbiyu, zamu bata kulawarmu, soyayyarmu, goyon bayan mu, kamar yadda muke yiwa ya'yan mu, saboda itama Amana ce agare mu.. "

yadda ta ke yin magana cikin nutsuwa da kasaita tana watsa yatsun hannayenta dake asanye da zobban diamond ba karamin burgesu tayi ba, ta tafi da imanin su.

Baiwar Allah Unaisah kamar sakarya tuni ta shagala tana ta kallon tausasan la66an sheikha mujeedat, danish kawai take tunawa, ji take inama ace itace surukarta wayyo Allah..

Babu wanda yasan kallon ?urullan da takeyi mata saboda mayafin daya lullu6e fuskarta, falon yayi tsit kowa ya nutsu yana sauraron daddaWar muryar Sheikha mujeedat, basu taba zaton zata iya magana har haka ba, saboda izzarta..

Sarauta taji daWin jawabin Sheikha mujeedat, ta taimaka mata data ari bakin ta..

Matar akwai wayewa da tsantsar ilmi akan ta..


Basu bar gidan ba, anan suka tsaya saboda walimar da suka faWa masu za'ayi anan, da lokacin yin walimar ya yi, gagarumin shagali suka haWa masu, babu wanda bai nishaWantu ba, sun ji dadin karramawar da su ka yi ma su.


Bayan kammala walimar, around ?arfe shida, suka yi masu sallama zasu koma.

Unaisah kamar tayi hauka saboda zullumi da fargaban karsu tafi su barta, Har bakin motocin su suka rakosu, daddynta ya rungumota yana lallashinta, shi kanshi daurewa kawai yakeyi har kwalla sai da yaji ta cika idanun sa, ta rungume Aunty Aneelerh da aunty Ummi sunata lallashinta, duk saida tabi bridemaids ta rungume su, cikin shesshekar murya take yi musu godiya.

Kwata kwata babu wanda ya lura babu Batool a cikin su har suka kammala yin bankwana da Unaisah da zumar zasu sake haWuwa gurin dinner din ta bayan kowan nan su Ya shige cikin mota, akan idanun Unaisah motocin su ka tafi.

Kamar tayi hauka, kwata kwata ta manta da mutanan dake a bayanta ta fashe da kuka, batai aune ba, taji an rungumeta, har saida taji gabanta ya faWi jin kamar sheikha Mujeedat ce.

Shafa bayanta tayi"karki yi kuka, zaki 6ata makeup dinki, tun kan angon naki ya gani, kiyi hakuri kinji surukata, nasan ba daWi ka rabu da kowa naka ka shigo cikin dangin da baka taba rayuwa da su ba, amma ki kwantar da hankalin ki, mu ma da haka muka fara, nayi maki alkawarin zan share maki hawayen ki..."



ai tun da hancinta suka shakar mata turaren sheikha ta kuma tabbatarwa kanta itace ta rungumeta tuni ta nemi kukan da ta ke yi ta rasa, ita dai tana son maman danish din ta, duk da tana jin fargaban karta ta juya mata baya tun da mijin yar ta ta Aura, sai lokacin ma ta tuna da kishiyarta Nazli bata ganta agidan ba.

Komawa su ka yi da ita cikin gidan, Sarauta ta ru?e hannunta suka nufi dakinta, a kan gado tace ta zauna, jikinta asanyaye ta zauna tana ta jin faduwar gaba, har abinci tasa maids suka ka kawo mata, tace mata bata jin yunwa taci abinci agida.


Allah Allah take su mika ta gidan ta, saboda takasa sakewa anan gaba daya a matse ta ke, ta ?osa ta cire bridal gown din jikinta, ta matse ta sosai.

Around ?arfe shida na mare ce bayan anyi magrib, su ka fito da Unaisah daga cikin gidan, suka nufi jigunanniyar Motar sarauta da ita, gidan baya ta shiga ta zauna sanyin A.c ya daki fatarta, ta ruWe da ganin haWuwar motar, irin wadda sarakuna ke hawa, Sheikha mujeedat da hajiya malika ne a mazaunin gaba, tayi mamaki sosai, tayi zaton Owais ne zai zo ya tafi da ita, amma sai taga akasin hakan, tsabar gatanci su biyu zasu kaita gidan ta.

Gimbiya mujeedat ce ke sarrafa motar..

"Unaisah, Akwai gift boxes da muka ajiye maki a Wakin ki, Idan kin shiga zaki gani... " Sarauta ce ta faWa, cikin sanyin murya ta amsa da toh tare dayi mata godiya, tace batason godiya, babu wannan atsakanin su, sun zama Waya, murmushi tayi.


"Ko akwai abun da kike bu?ata"?

gimbiya Mujeedat ce ta tambayeta, a hankali ta sanya hannu ta yaye mayafin ta ta saci kallonta ta madubin motar dake fuskantar ta, kaitsaye idanun su suka shiga cikin na juna, wani irin faWuwar gaba taji ganin ta kashe mata ido Waya tare dage mata gira, cike da jin kunyarta ta sunnar da kanta ?asa adabarbarce ta furta"bana bu?atar komai, nagode da kulawar ku"

murmushin gefen fuska sheikha mujeedat tayi tare da kallon Sarauta itama da murmushi akan fuskarta.

"Kina ta farin ciki kamar ba ?arki akayima Kishiya ba" Saurata ce ta faWa da zolaya.


bushewa tayi da dariya"ba zaki gane ba, wallahi Sonta na ke yi, yarinyar tana da Qualities da nakeson inga mace da shi, gaskiya munyi dacen suruka, Owais Ya more mata.." ta faWa tana satar kallon Unaisah da ta sadda kanta ?asa, duk tasha jinin jikin ta, tun da sheikha ta kashe mata ido.



GIDAN AMARYA UNAISAH, wani kaya sai amale, Al?alamina ya girgiza, an kashe min bakina, saboda bazan Iya misalta HaWuwar Katafaren Gidan ba,

har motar tayi parking a parking space Unaisah bata Wago da idanun ta ba, saida taji alamun buWewar Cardoors din sannan ta lura.

Bata motsa ba, har saida suka rigata fitowa daga cikin motar, Sheikha mujeedat ta mi?a mata hannunta"mun ?araso gidan naki, my baby in-law, zaki iya tafiya kan ?afafunki, ko kinaso in goyaki in shigar da ke ciki.."?


murmushi tayi cikin sauri ta zura hannunta a cikin na sheikha, ta rukota ta fito waje, suka tsaya daga gaban ta, addu'o'i su ka soma yi mata tana amsawa da ameen daga bisani suka sanya mata albarka, tayi zaton zasu rakata cikin gidan ne amma sai taji akasin hakan.

"Ki shiga daga ciki, ki jira mijin ki yana akan hanya..." Sarauta ce ta faWa.

Jiki asanyaye ta amsa da toh hadi dayi masu godiya, walking slowly ta nufi ?ofar shiga falo...

A hankali ta ke satar kallon ginin kamar a mafarki saboda tagaza yarda gidan ta ne, ta razana da ganin haWuwarsa, wai anan zatayi rayuwa, hasken electricity ta ko'ina tamkar da rana...

Rantane ya bata basu tafi ba, slowly ta juya tare da kallon su, ile ko suna atsaye gaban motar su suna kallon ta.

Tarasa gane meyesa ba'abari kowa nata ya rakota ba, sai ita kadai? Kamar mara dangi? Ita a yadda ta sani kawayen amarya suna kwana a gidan amarya, amma ita ko rakiya babu wanda yayi mata, sai dai Uwar ango da matar Kawunsa suka rakota, duk da haka taji dadin gatantata da sukayi..

Tana isa bakin kofar, ta Waura hannunta jikin glass din da niyar ta tura nan take kofar ta soma zamiyewa, Unexpected tana dira ?afarta, ta tsinkayi muryar sa a cikin kunnanta.

_My baby bride, I've been counting the minutes until you walked through that door, I'm so glad you're home, I've got a whole night of love planned for us_

arazane ta zare idanunta ganin bata ga kowa ba, ranta ne ya bata muryar na'ura ce sai dai tayi sak irin ta Owais.

Numfasawa tayi tare da sauke nannauyar ajiyar Zuciya, tana ?arasa shiga ciki, ?ofar tayi locking kanta, Kamar 6arauniya cikin sanWa take tafiya sautin takunta na fita ?was!!?wass!

Batasan Ina zata Nufa ba, ganin hanyoyi daban daban Cikin falon, na ?asa dana stairs harda glass Lift..


again ta kuma tsinkayar muryar na'ura a cikin kunnanta tana yi mata kwatance inda zata ga bedroom Winta, a hankali ta nufi hannunta na dama, ta hau stairs ta 6ulo second floor, harta fara gajiya saboda matsewar da takalmanta su ka yi, rigar ma ta fitine ta, dakyar ta gano wata hadaddiyar ?ofa, nan take ranta ya bata shine bedroom Winta, ganin tana da security yasa ta Waura finger Winta, nan take ?ofar ta buWe a hankali, wani spiral stairs tayi aran gama da shi, cikin 6acin rai ta bubbuga kafafunta, aranta ta ayyana babu abun da zai hana ta tu6e bridal gown din nan ko yazo ko bai zo ba, sai ta cire ta..

Hawa tayi kan staircase din tana cikin tafiya kamar wadda kwai ya fashe mawa akai..

A matu?ar ruWe ta Wan dakata dayin tafiyar tana kallon abun daya daure mata kai, wato ainihi stairs din da take akan shi kaitsaye zai kaita cikin Bedroom Win ta daga inda ta ke atsaye kan staircase din tana hangen katafaren Master Bedroom Win.

Farawa da bismillah, a hankali take bin bedroom din da kallo tun daga kan katafaren Four poster bed din cikin sa irin na sarauniya, an ?awata shi da 24 karat gold leaf, and precious gems, gaba dayansa wasu dogayen curtains ne kewaye da shi shara shara with a velvet canopy, gefe da gefen gadon wasu dankara dankaran bedside drawers ne Wauke da crystal lamps, buWe baki tayi kamar shashasha tabi ceilling din dakin da kallo wasu kawatattun Feather pendant lamp ne da ke haskaka tsakar dakin, tun daga gaban gadon har izuwa interior din dakin an shimfide shi da tattausan Ivory shag rug, very fury, daga saman shi Glass candles ne a cikin kwalba sai ci suke da wuta gwanin ban sha'awa, ga wasu floor Lamps na tsaye a tsakar Wakin, daga can cikin kusurwar data kalli bangaren dama na bedroom Win seating area ne wata White corner couch ce zungureriya yar ubansu mai numfashi, an ?awata saman ta da throw pillows, gabanta glass tables ne mai dauke da crystal vase, ga wasu bean bag chairs dake a gurin Wumduma Wunduma jefi jefi take ganin gift boxes akan rug masu kyan gaske nan take ta fahimci kyaututtukan da Surukarta tace zata gani a Wakin ta ne, ko menene a cikin su?


wani ni'imtaccen sanyin A.c mai haWe da kamshin turaren Waki ne Ya ratsa kofofin hancin ta har saida ta lumshe idanun ta, tun da uwarta ta haife ta bata ta6a ganin tsantsararren bedroom irin wannan ba! Har ta fara kokwanton anya mallakin ta ne?


Saboda yafi karfinta, batajin zata iya kwana a cikin sa"

Ni kaina da nake rubutawa na jinjinawa haduwarsa, A hakan ma bakomai zan iya fayyace maku ba, saboda ina jin tsoron ruwan alkamina ya kare gurin zayyana maku komai.

A hankali ta ?arasa saukowa cikin bedroom Win wanda gaba Waya furnitures Win cikinsa launin Bold pink and navy ne, aranta sai santin bedroom din ta ke yi, tana kara jinjinawa haduwarsa, har wani jinjina kanta takeyi irin ta ruWen nan.

Bata nufi ko'ina ba sai gaban gadon daya tsone mata ido, saman shi tabi da kallo lumbutsetsiyar mattress ce shimfide da bedsheet, rabinta a lullu6e ya ke da lallausan duvet, gab??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a Waya kewayen mattress din an jera throw pillows a sama, daga tsakiyar mattress din furanni ne launin pink and Red masu ?amshin gaske..


Juyawa tayi baya tana karewa ko'ina kallo kamar wuyanta zai balle


"Hmmmmm " ta furta sautin tana ru?e qugun ta, gaba daya ta kasa furta kalma..



Wuce wa tayi ta nufi interior din dakin, daga cikinsa kana Iya hangen komai dake a cikin toilet ta cikin Glass wall, haka zalika data nufi ciki tayi arba da kofar dressing room wadda shima bangon glashinne tana hangen walk-in closet dinta, sha?e da suturun sanyawa kamar a company, ga wani faskeken dressing mirror Wan uban su...


Babu ce kadai ke babu adakin Amarya Unaisah, amma fa an zuba mata tsadaddun furnitures na gani na faWa.

Daga ganin fasalin Wakin zaka fahimci don masoya akayi shi..

A ?alla ta shafe rabin awa tana bin Wakin da kallon ?urulla batare da gajiyawa ba, daga bisani ta fara tunanin Ina mijin nata ya ke? Taji shiru babu motsin sa, gashi ta?osa tagan shi saboda idanunta sunyi maraicin ganin shi, ta yi kewar shi, tun bayan da aka sanya bikin su bata ?ara ganin sa ba, kamar yadda yayi al?awarin sai bayan auran su zai bayyana saboda ba zai iya jure kallon ta ba, still tana jin fargaban haWuwa dashi a matsayin mijin ta.

Tana tsaka da yin tufka da warwara, cikin ta ya fara kukan yunwa, ga wani irin baccin gajiya dake kokarin fisgarta har wani jiri jiri take gani a cikin idanun ta da ke lumshewa, a hankali ta dubi agogon bango, ?iris ya rage afara kiran sallar isha'i, baiwar Allah tana ta sa ran ganin shi shiru baizo ba, tunawa tayi da wayarta da sauri ta shasshafa jikinta, yamutsa fuska tayi tunawa da babu wayar atare da ita, ta mantata a gida, taji takaici kamar tayi kuka..


Matsawa ta yi daga gaban tamfatsetsen dressing mirror din Wakin, ta zauna kan kujerar gabansa, tana ta jiran ?arasowar yaya Owais, don su ci dinner a tare kamar yadda suka Waukarwa juna alkawarin zasuyi a karo na farko da suka kasance ma'aurata
Batasan sa'adda ta fara yin gyangyadi ba, ga wata jarababbiyar hamma data cuka bakin ta, ta Wan kishindiWa bayanta jikin kujerar..


A lokacin data fidda rai da zuwan angon nata, bacci ya yi awon gaba da ita, ta saki baki da hanci tana ta yin minsharin gajiya.



~_________________________________


*DG OWAIS=?%?*


Around ?arfe tara na dare daidai wata Hamshakiyar Mota ta biyo titin da zai sada ka da gidan Amarya.


Idanunsa suna a lumshe yayin da ya ke a hakimce cikin backseat na hamshakiyar motar shi, ya Wauki wankan dandatsetsiyar shadda Getzner wagambari Launin sky blue short sleeve shirt, da dogon wando, ya daura babbar riga ta alfarma daga sama, anyi mata aikin hannu har ?yalli ta ke yi.


ga wata haWaWWiyar Hula daya daura a kansa, hakan bai boye lallausar sumar kan shi ba, ta lullu6e ilahirin ?eyarsa har izuwa saman wuyansa.

Wuyan hannunsa na dama na asanye da tsadaddiyar agogo ?irar Rolex Daytona.

gaba Waya ?amshin turarensa ya buWe Motar, girma da kwanciyar hankali sun zauna masa, ta yadda ko fatarsa ka kalla zaka shaida hakan, sajen fuskarsa ya fi komai jan hankali, Yadda ya lumshe idanunsa sai ka yi zaton bacci ya ke yi alhalin kuwa idanunsa biyu tsabar qasaita ce ta angon Gimbiyar Izza.

Babban Amininsa big guy Omar yana a zaune saman seat din gefensa, ya tattara hankalinsa akan iphone dinsa da ya ke daddanawa, kusan shigar su kala daya banbancin su shi bai sanya babbar riga ba.

Wayarsa ce tayi ringing, picking yayi tare da kara wayar a kunnansa..

"Wifey, me ki ke yi har yanzu baki yi bacci ba"?

On the other hand tace"yaya Owais nake nema, Ina kiransa baya shiga, pls idan kuna a tare ka ba shi wayar" kallon Owais ya yi tare da cewa"Hindu ce, tana son magana dakai" batare daya buWe idanunsa ba ya mika masa hannu ya kar6i wayar ya kara a kunne..

Shiru yayi yana sauraron ta"big bro, ka yi hakuri ban shigo gida ba yau, bana jin dadine, inataso in tayaka Murna, Allah ya sanya alkhairi, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a Wayyiba..."

?asa ?asa da murya ya amsa da ameen My Lil' sis, nagode da addu'arki, karki damu, nasan halin da kike a ciki bai kamata kina fita ba, idan kinji sau?i ranar Dinner sai ki shigo"

"Okay yayana nakaina, nagode da kulawarka agareni, Ka gaishe min Amaryarmu"


"Zataji, nima ki kula min da kanki," amsawa tayi da toh kafin su kayi sallama ya mika ma Omar Wayar.


"Kamar kana da damuwa? nifa na lura da kai tun gurin Waurin aure babu annuri akan fuskarka"


Bai iya furta kalma ba, yayi shiru yanayin fuskarsa ba walwala.


"Owais, kar dai kace min har yanzu kana... " bai ?are maganar ba ya yi saurin katse shi da cewa"pls ba sai ka faWa ba, kamanta kawai, bana son ji"



jinjina kai Omar yayi batare daya ?ara furta kalma ba.



Officer din da ke driving dinsu kwata kwata bayajin abunda suke tattaunawa, Yana a driver's seat, a hankali Motar su ta ?ara so layin Gidan tana kokarin kunna kai ta main entrance, kamar ance ya dubi window glass din Motar, Unexpected idanunsa sukayi mashi Tozali da mutun ra6e jikin bangon gidansa kamar aljana.


Da ruWu akan fuskarsa ya furta"tsayar da motar anan.." nan take drivern ya tsaya..

Big guy yace"meya faru naji kace a tsaida motar bayan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login