Showing 288001 words to 291000 words out of 321579 words

Chapter 97 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

hawaye suka cika idanunsu kafin suka fara zarya kan kuncinsu..

Unexpected yaga ta sanya red tongue dinta akan fuskarshi ta lashe hawayensa kamar yadda ta sabayiwa daddynsa a duk time da hawaye suka zuba daga idanunsa, wani sanyi yaji aransa kamar ta ?afe ruwan hawayen nan take suka daina zuba, kwanto da kansa tayi kan kirjinta, taci gaba da yamutsa sumar kanshi kamar tanayi mashi susar kadangare..


"I love you more than i love my self, more than everything.." ta faWa calmly

DaWi ne yayi masa yawa har bacci ya Wauke shi bata sani ba, sai da taji shiru tana ta ambaton sunan shi bai amsa mata ba, a hankali ta soma ?are masa kallo kamar zata lashe shi ita kanta santin Wan nata takeyi, abun da take ma zullumi tayaya royal family dinta zasu kar6e shi? Zasuyi farin ciki ko kuwa? Tayaya zatayi ma iyayenta bayanin Wanta ne kuma Jikansu"?


akagare take da Owaisa ya kammala bincikensa don ta samu hujjar fallasa baiyanar Omair dinta ga yan uwa da abokanan arzkinta tasan zasu yi al'ajabin ganin kyakkyawan Wan.



kamar ta samu tv haka ta dinga kallonsa, har saida ta fara jin bacci, a hankali tayi tighting dinsa a kirjinta donji take kamar za'a ?wace mata shi.


Tamfatsetsiyar wayarta dake ajiye kan bedside drawer ta fara ruri kamar ba zata yi picking ba saboda batason komai da zai rabata da jikin danta.

Gudun kada ringing din wayar ya katse mashi baccin shi yasa ta mi?e a hankali kamar wadda ta kwantar da jinjiri ta sauko daga kan gadon ta Wauki wayar ta duba sunan me kiran ta, My in-law ta gani.

Almost 30 misscalled yayi bata batare data sani ba, saboda hankalin ta na akan baby boy Winta.

Gently tayi picking tare da kara wayar a kunne.

"Danish ya ?araso"? Daga yanayin muryarsa ta fahimci hankalinsa ba akwance ya ke ba.

"Owais, calm down your mind, Omair Ya karaso, Yanzu haka Yana akwance kan gado yana bacci"

wata nannauyar ajiyar zuciya taji ya sauke tare da furta"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah na gode maka"

cikin karyayyar murya tace"Owais, bansan da wasu kalmomi zanyi amfani gurin yi maka godiya ba, Owais, I couldn't bear it, when I hugged him tightly, I felt an indescribable sense of unconditional love, Owais daga ni har shi munyi kuka tamkar ranmu zai bar gangar jikin mu, Owais na kasa jurewa, bazan matsa maka ba amma ka taimaka min, ku gano su wanene suka rabani da shi tsawon shekarun nan, wallahi bazan ?yale su ba, ko da hukumarku zata hukuntasu sai nayi ?arar su Owais, dole su fuskanci hukunci mai tsanani dai dai da abun da suka aikata mana" ta faWa da tsantsar 6acin rai akan fuskarta.


Bata jira taji me zaice ba taci gaba da cewa

"Owais wani irin rashin imani da tausayi ne? Bansan yana araye ba, shima baisan yana da iyaye ba, bamu san irin rayuwar da ya yi ba... "

tun da tafara magana yayi shiru yana sauraronta, saboda a halin yanzu tana bukatar wanda zata fada ma halin da take a ciki kota rage radadin dake a cikin zuciyarta..

bata kare maganarba ta fashe mashi da kuka mai tsuma zuciya..

Kasa magana Owais yayi saboda tashin hankalin da ya ke a ciki, bai ta6a jin kukan Sheikha Mujeedat ba sai yau, shi damuwar shi Idan taji labarin azabtarwar da Omair yasha agidan kurkukun kaddara baisan Ya za ta ji ba.

"Mommy, bansan tayaya zan lallashe ki ba, amma ki tuna Allah yana atare da masu ha?uri, nayi maki alkawarin zamu gano ko su wanene sukai maku aika aikar nan, kuma zamu dauki mataki akan su, pls mommy, ki kwantar da hankali, ki lallashi zuciyarki, mu godewa Allah daya bayyana mana shi da ranshi ta hanyar da bamu ta6a zata ba, Allah kadai yasan dalilin da komai ya faru mommy, a halin yanzu damuwa bata ki bace, baby Omair Yana bukatar kularki da lallashin ki, saboda baya da koshin lafiya...."

lumshe idanun ta tayi a hankali hawaye suke sauka kan kuncin ta masu Wumi.

nutsuwa tayi tana sauraron Owais dake lallashinta tare da bata baki.

Kwatsam ta soma jin nishi da gurnani cike da fargaba ta zare dara dara idanunta akan shi wani faduwar gaba taji, Ganin yadda ya ke birgima akan gadon, tafukan hannayensa daddafe da mararsa, gaba daya ilahirin jikinshi rawa ya ke yi, fatar jikin shi ta jike sharkaf da zufa, Idanunsa sun juye sun koma fari fat gwanin nan tsoro.


Da karfi ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un Om.. Omair! Meke damun ka"?

Chief owais dake sauraronta aruWe ya shiga tambayar meke faruwa da shi? Bata kaiga bashi amsa ba ta saki wayar ta fadi kasa, ta haye kan gadon tare da janyo shi yana ta hauka hauka, idanunsa sun kakkafe, lokacin Waya ya fara sakin ?ara mai sautin gaske, fuskarsa tayi jawur, duk yabi ya ciccije labbansa Ya faffasa su, gaba daya tabi ta rude, ta shiga tashin hankali mara misatuwa, Tana kuka Yana kuka tare da sakin kara, duk yadda ta kai ga ?okarin kwantar masa da hankali takasa, fargabanta kada ta rasa shi arana ta farko da ta fara ganinsa amatsayin gudan jinin ta, rungume shi tayi a kirjinta wani zafi da taji a skin dinsa saida ta nemi zaucewa, cikin harshen larabci ta dinga furta Omair Meke damunka? Me ke faruwa dakai! Ya Allah ka kawo masa sau?i, Omair kada ka mutu ka barni, Omair, dan Allah ka saurareni, inason ka, Ina ?aunarka Omair, bana so na rasa ka"!


Addu'o'i ta soma karantowa tana tottafa mashi akan sumar shi, ta dinga shafe mashi ita da tafin hannun ta, maimakon taga sauki atare da shi sai taga kamar ana kara masa Ciwon.

tunawa tayi da maganar Chief da yace bashi da koshin lafiya, ta tanadi likitocin da zasu kula da lafiyar shi, a hanzarce ta soma kokarin raba jikinta daga nashi, wani abu daya karya zuciyarta yadda ya ?an?ame hannayenta yaki bari ta matsa daga jikin shi, Sosai ta fashe da kuka cikin shesshekar murya ta furta"omair ba tafiya zanyi na barka ba! bazan jure ganinka a mawuyacin hali ba, lafiyarka tafiye min komai arayuwata.."

tana ?arasa maganar ta 6an6are hannayenta daga nashi, ta sauko daga kan gado tana faman share kwalla ta dauki wayar da ta jefar kasa, yatsun hannunta na kerma ta dannawa likitanta kira..=ؔ?


After few mins..


Ambulace ta shararowa da matsakaicin gudu zuwa cikin Gidan bayan Sunyi Parking, Medical team tare da nurses suka fara fitowa cikin sauri kowan nansu sanye da Uniform dinsa, wasu sun ruko emergency box a hannayen su..

A Falon suka iske gimbiya Mujeedat, da hannu tayi masu alamar su biyo bayanta, kaitsaye suka nufi bedroom din da Omair Ya ke, a lokacin kiris Ya rage ya ?undumo kasa daga kan Gadon sai jan numfashi ya ke yi kamar ransa zai fita, cikin zafin nama Gimbiya Mujeedat ta tallabo shi tare da taimakon Docs Suka mayar da shi kan gadon nata, kasa barin dakin tayi saboda zullumi da fargaban kada ta rasa shi, duk tabi ta ruWe, sai fadi take su taimaka mata kada ta rasa Wanta, bata so wani abu ya same shi, ji take kamar ta Wauke masa ciwon ya dawo jikin ta.

Su kansu Medical team din mamaki ne ya kamasu jin kalaman Sheikha Mujeedat akan Yaron da basu san wanene ba ko a zuri'arta basu san da zaman shi ba.

gaba Waya suka kewaye shi tare da bada himma gurin fara duba lafiyar jikin shi, duk da halin da suke a ciki na duba lafiyarsa hakan bai hana su yaba ?yanshi a cikin zuciyarsu ba.

Rage kayan jikin shi sukayi, suka bar mashi short da singlet fara, zanan tattoo dinsa Yasa su jin fargaba.

Komawa tayi daga kofar dakin ta tsaya tana kallon su, jininta akan akaifa takasa tsaye ta kasa zaune gani take kamar basa yin sauri.

Muryar team led din su ta tsinkaya a cikin kunnanta

"Oxygen mask, stat! We need to get his oxygen levels up, And someone get an IV started, saline drip, now!"

cikin sauri nurses din suka buWe akwatinan, wani nurse ya soma sanya masa oxygen mask over his face, while another inserted the IV needle into his vein.


Daga bisani docs suka fara Examining din shi.

"Pulse is 120, blood pressure's 90/60, Let's get a blood sample for lab tests." wani doc ne ya fada

Da sauri Nurses ya kar6i blood samples din Omair ya tura shi zuwa Lab..



A lokacin kwata kwata baya acikin hayyacinsa, baima san su wanene akan shi ba, sai kokarin buWe idanunsa yakeyi ya kasa saboda nauyin da sukayi ma shi.



Gimbiya mujeedat kasa zama dakin tayi saboda tausayin shi, fitowa tayi bakin kofar dakin, ta kifa kanta jikin kofar hawaye wasu nabin wasu akan fuskarta.


"Let's keep him under close observation, I want vital signs every 15 minutes." gaba daya maganganun Doc din a cikin kunnanta, baiwar Allah tasha kuka kamar ba gobe..


Da damuwa ta mamaye zuciyarta, duk in ta rufe idanunta fuskarshi take gani, Prayer room ta shiga, bayan tayi sallah ta dinga yi mash??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i addu'o'i tana kai kukan ta gurin Allah..

Babu gajiyawa, har sai da kiran Doc Ya riske ta, fitowa tayi daga dakin with respect dr din Ya soma buWe mata hotuna a tab din sa masu dauke da bayanan ciwon Omair.


Yana magana yana duban fuskar sheikha Mujeedat, Tashin hankaline Tsantsa da damuwa..

Bai karasa Maganar ba ta dakatar da shi, jikinta kerma ya ke yi saboda damuwa..


"Please, I want you to do everything medically possible to save my son.." ta fada idanunta cike tab da ?wallah

"Consider it done, Your Highness." ya amsa mata kafin ya koma bakin aikinsa.

Tun dare suke duba lafiyar shi, Har asuba ta rutsa da su, da suka bukaci zasu ?ara mashi jini, ita ta bada jinin ta duk da sun nuna in akwai namiji zasu so ace shi ya bada, amma ta kafe kan nata zasu diba, Dan a yadda takeji ko shine kadai jinin daya rage mata zata iya mallakama omair dinta, babu yadda suka iya duba da ganin lafiyayyar mace CE kuma zasu samu enough yadda suke buqata, bayan sunyi gwaji suka sanya mashi.


Kasa jurewa tayi ta nufi bedroom dinta ta dauko waya, anan ta ga miss calls na family din ta, Hada na Chief Owais, kira ta danna mashi after yayi picking yace"meke faru da shi ne? Meke damun shi? Inata kira baki daga ba, duk na damu"

Kuka ne yake kokarin kubce mata amma saboda jarumtakarta ta jure tare da numfasawa ta zayyana mashi sakamakon abunda ke damun shi Omair ta kara da cewa"Owais, bazan misalta maka tashin hankalin da nake aciki ba, pls ka fadamin garin yaya ciwuwwuka sukayi mashi mugun kamu? Bazan tuhume ka ba nasan kana iyakar kokarin ka amma Owais, ciwo kusan biyar duk a jikin bawa? Su wanene suka azabtar da shi"?


Tashin hankali da damuwa sun cika zuciyar Chief, Sai yaji duk ba dadi badan ?wararan dalilan dayasa Ya damka mata Omair ba, da yasani bai tura mata shi a haka ba, har sai ya samu lafiya yasan zuciyar uwa musamman akan Danta.

Hakuri Ya kara bata yace ta jure komai zata gani atare da shi, ya kuma tunasar da ita yace kada ta manta Allah yana kar6ar addu'ar uwa akan ya'yanta, don haka ta dage dayi masa addu'a in sha Allah Omair zai samu lafiya, sannan Amsar tambayoyin da tayi mashi zata same su a lokacin da suka kammala bincinken su, baiwar Allah bata musa ba tace mashi toh har ta yi mashi godiya.

Bayan ta katse kiran ta kira layin daddynta Sheikh Khalid after yayi picking cikin harshen larabci

yace meyasa yanata kiranta bata picking? yana fata tana lafiya"

rasa amsar da zata bashi tayi.


Jin tayi shiru bata bashi amsa ba yasa shi furta"amsarki nake jira," numfashi taja tare da daidaita nutsuwarta kafin cikin sanyin murya tace"Alhamdulillah, ina cikin koshin lafiya baba, ina fata kaima haka"!


daga yanayin muryarta Ya fahimci babu kwanciyar hankali atare da Gimbiyar tashi.


"Meke damunki? Naji muryarki da damuwa"

da sauri tace"babu abun da ke damuna, mura nakeyi, amma nasha magani, da sauki"

"Allah ya baki lafiya, ki kula min da kanki" ta amsa da ameen.

sun daWe suna yin waya kafin su ka yi sallama..

Mi?ewar da zatayi keda wuya sai ga khadima ta yi knocking kofa.

Fitowa tayi daga dakin Khadimar ta sanar da ita medical team zasu tafi suna jiranta, da sauri ta nufi Down, Khadimar ta take mata baya, tana karasa saukowa down ta iske medical team din, wannan karon da walwala akan fuskokin su ga dukkan alamu sunyi nasara.

Har suna haWa baki gurin sanar da ita cigaban da suka fara samu akan Lafiyarsa sannan sukace kullum zasu dinga zuwa duba shi har zuwa lokacin da zaiji sauki, godiya tayi masu tare da jinjina, bayan sunyi sallama har suka tafi basu daina santin kyan patient dinsu ba, sun kamu da kaunar shi, sun kosa ya samu lafiya don suyi magana da shi, ba dan suna jin nauyi da shakkar gimbiya mujeedat ba da sai sun tambayeta menene alakarta da shi saboda sunyi mamakin yadda ta rude akan shi, da kuma kamanninsa da Nazli asaninsu bata da Wa namiji amma sai gashi yau sunga wani zankaWeWan saurayi kyakkyawa daya tafi da imanin su, gashi ta gargaWesu akan bataso kowa ya san wani abu game da kiransu da tayi da kuma yaron, sirrine in har suka sa6a sharadin data gindaya masu zasu fuskanci hukunci, shiyasa ko gulmarsa suka kasa yi sai dai suka bar abun aran su.

Lokacin da tashiga dakin akwance ta same shii Yana sharar bacci, bawan Allah ya sha alllurai.

A hankali ta zauna daga gefen gadon, Ta ruko hannun shi a cikin nata, ta sumbace ce ta Wago tana kallon fuskarsa dake asanye da oxygen mask.

"Allah ya baka Lafiya Omair, Allah ya tashi kafadunka, ya Allah ka musanya lafiyarshi da tawa, ni kamayar mun da ciwon nashi a jiki na, saboda ba zan juri ganinsa a mawuyacin hali ba, na damu da kai bugun zuciyata..."



duk wani motsinsa akan idanunta, Owais ya kirata yafi sau akirga duk bayan mintuna saiya kira ya tambayi ya jikin Danish saboda ya damu da shi.


Tsantsar kulawa take bashi kamar jinjiri, Lokacin sallah kaWai ke sa tabar Wakin, ko motsi ya yi sai ta tambayi yana lafiya?

Ba ci ba sha ko da chefs suka faWa mata sun kammala shirya mata Lunch, tace masu bazata iya cin abinci ba, su tafi kawai, haka ta wuni har dare tana tare da shi.

A gefen shi ta kwana, ru?e da hannunsa a cikin nata..


A kwana a tashi ba wuya wurin Allah, Har Danish Yayi One Week Agurin Mommyn sa, jikinsa Ya murmure lafiya tafara samuwa a jikin shi, ta ko'ina kulawa yake samu daga bangarori biyu, docs din da ke zuwa duba lafiyarsa kullum da kuma Mommynsa dake tsaye akan sa, itace mutun ta farko da ya ke fara yin tozali da ita a duk lokacin daya farka daga bacci, saboda tsantsar kaunar da take masa da kulawa bata bari ya yi komai da kansa in ba shiga toilet ya kama sa ba, abinci abaki ta ke bashi ya ci, da kanta ta ke wanke mashi sumar kanshi ta gyara mashi ita, bata barin shi cikin kaWaici.

tun aranar daya samu sau?i ta lura bayayin sallah, ta kasa yin shiru har dai ta tambayeshi meyasa baya yin sallah yace'' mata in zai iya tunawa shi ba musulmi ba ne, tayi ba?in ciki da jin cewa ba musulmi bane shi, amma data tambayesa yana son ya musulunta babu gaddama yace mata eh yana so, nan take ta biya mashi shahada ya kar6i musulunci, Kuma duk ita ta koya mashi yadda zaiyi alwala da sallah.

Har fita ta ke yi da shi tana nuna mashi wuraren sha?awata da ke a cikin gidan, duk don ta faranta masa rai saboda tana son ya saki jiki da ita sosai, sannu a hankali suka fara sha?uwa kullum sai sun shiga Personal gym din gidan a tare suke motsa jikin su, sometimes su shiga Private lounge su sha?ata abunsu harma suyi fira cikin nishadi ta dinga janshi da fira tun yana jin nauyin yin magana da ita harya fara sakewa sosai, wani lokacin kuma takan shiga library da shi ta dauko masu story books tana karanta mashi, sometime su shiga private cinema dinta su kalli movies, ba karamin nishaWi da ilmi ya ke samu ba, in ka gansu suna wasa da dariya ya yin da su ke yin fira sai ka yi zaton sun daWe da sanin juna.

in a short time ta mantar da shi trauma din daya fuskanta abaya, gatanta shi ta ke kamar ranta, tarairayarsa takeyi kamar ?wai a cokali, bata son ko tari ya yi, idan dare yayi a kan bedroom counch ta ke kwana tana fuskantarsa yayin da ya ke yin bacci saman gadon ta, saboda bata iya barin shi a bedroom shi kaWai.

Saboda shi ta kira ma'aikatan gidan dukan su, ta tarasu a falo ta nuna masu shi ta gargaWe su akan karsu kuskura suyi ganganci gurin kula da shi, su Wauke shi tamkar ran su, batason bacin ran shi, cikin girmamawa suka amsa mata da toh.

Ta kuma bawa Private chefs dinta Jotter da doc ya rubuta na diet din sa..

Saboda Omair ta dau?i hutun aikin ta, ta dakatar da duk wani business nata, gaba daya ta sadaukar masa da lokacin ta.


She becomes his role model, his mentor, and his influencer, Mommynsa ta siye zuciyar shi da kulawarta, soyayyarta, kyautatawarta agare sa, tayi brainwashing nashi, yanzu halayansa da Wabi'unsa sun sauya, komai nasa natural ne, babu sihiri babu evils gaba daya sun bar jikin shi tun aranar farko da yayi rashin lafiyar nan, Allah ya yaye mashi su, zafin fitarsu ne yasa shi yin jinya.

Halayansa da Wabi'unsa sun sauya sun dawo ainihin yadda Allah ya halicce shi da su, a lokaci yayi loosing memory dinsa baya tuna komai daya faru a baya, ko ta tambaye sa game da rayuwarsa ta baya sai yace mata bazai iya tuna komai ba.


Mommynsa kaWai ya sani da hadiman dake yi masu hidima, sai kuma Chief Owais da kullum Ya ke kiransa awaya suyi video call ko suyi phone call duk da ya manta wanene shi? Wata rayuwa su ka yi atare? A lokacin Yana masa kallon Cousin brother dinsa da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login