Showing 315001 words to 318000 words out of 321579 words

Chapter 106 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

motarsa, ya jinginga kansa jikin headrest, sanye yake da riga da wando na voile launin dayafi so, Blue sky, ya lumshe idanunsa sam baiga tafowarta ba, sai dai yaji motsin buWe Cardoor Win..

A hankali ya buWe idanunsa akanta, yayin da take shigowa ciki, zama tayi saman seat tare da sunnar da kanta kasa cike da jin kunyarshi batare data furta kalma ba..

Tayi mashi kyau a cikin atampa ya danyi mamakin yadda ta amsa kiranshi cikin sauri batare da jin shakkar zai iya maimaita abun da yayi mata rannan..

Jin yayi shiru bai motsa ba, yasa ta dago da idanunta da niyar ta dube shi, kaitsaye suka shiga cikin nata, har saida taji gabanta ya faWi saboda kyawun da yayi mata..

"Kin san meyesa na kira ki"? Girgiza kai tayi"a'a"

"Okay, Unguwa nakeso ki rakani, zakije"? da sauri ta jinjina ma shi kai..

Da mamaki ya danyi shiru yana tunanin meyasa ta sake da shi? Kwata kwata bai kawo ma ransa tasan komai game da kasantuwarsa mijinta..

key yayi ma Motar, yayi reverse ya fuce daga gidan, yana driving tana satar kallon shi, komai nashi burgeta ya ke yi, kyawawan idanunsa, dogon hancinsa, karamin bakinsa, uwa uba yalwatacciyar sumar kan shi maikyau da santsi kamar ta jinjiri..

Sarai yana lura da irin kallon da ta ke yi mashi, ya yi kamar baisani ba, don ya bata damar da zata ?arewa mijin nata kallo..

Wani katafaren Bridal boutique su ka je, bayan yayi parking din Motar, suka fito tana ta kallon katafaren store din, duk da batasa dalilin zuwansu ba, amma tanaji aranta siyayyar kayan amarya zaiyi, daga sunan Store din ta fahimci kayan amare suke siyarwa..

Tana tsaka da kalle kalle, batai aune ba, taji ya ru?e hannunta a cikin nashi, wani shock taji, a rude ta saka idanunta cikin nashi har ya sanya mask akan fuskarsa saboda bayason a shaida shi yanzu mutane sun fara taruwa domin kallon shi..

Bayan sun shiga cikin Shop din, Bridal Consultants din dake agurin suka tarbe su tare da yi masu barka da zuwa, Dg ya faWa masu Bridal gown ya ke son gani, daya daga cikin ma'aikatan ce ta kaisu sashen bridal gowns, kala kala masu kyau da tsada gasunan birjik jikin hangers, yana lura da yadda Batool ta ruWe cike da mamaki take kallon rigunan tana Wan zazzare brown eyes Win ta..

"Ki za6i wadda kikeso" ta ji ya furta, aruWe ta nuna kanta da yatsa"Ni"? Jinjina mata kai yayi batasan sa'adda ta saki murmushin farin ciki ba,

"Ki taimaka mata ta za6i wadda zatayi mata daidai" ya fada yana duban ma'aikaciyar wadda keta kallonsu tana ji aranta kamar tasan muryar hamshakin mutumin..

Ru?o hannun Batool tayi a cikin nata, takai ta gaban wasu tsadaddun Bridal gown Limited edition, tana tsaka da kallon su Unexpected ta hango irin Bridal gown din Unaisah banbancinsu kaWanne Hannunta na kerma ta soma shafa rigar.

Ganin kamar tayi matane yasa matar tace"kina sonta"? Jinjina kai tayi"Eh"

"Kin iya za6en riga, tana da kyau da tsada, kuma zata dace da ke.." ta faWa da fara'a akan fuskarta ta curo rigar daga jikin hanger"muje na taimaka maki ki gwada rigar a jikin ki" ta faWa tana nuna mata ke6ataccen gurin dake a kewaye da dogayen labulaye

Amsawa tayi da toh, ta dan juya tana neman yaya Owais, can ta hango shi a zaune kan Arm Chair, ya kara waya a kunnansa..

Bayan sun shiga bayan labulayen, agaban wani katafaren madubi, suka tsaya, Wayan wurin da ake shiga ta nuna mata ciki ta Shiga ta sanyo rigar saidai ko zip ta kasa zugewa, sai sunne kanta qasa takeyi matar ta fahimci kunya gare ta, ita kanta saida ta jinjinama kyawun surarta, da taimakonta ta qarasa gyara mata gown din, Tabarakallahu ahsanul khalikin yadda kasan saboda ita aka ?era rigar, tayi mata daidai, ta ?ara fito da kyawun surarta, tun da ta tsaya gaban madubin bata motsa ba, bakinta yaki rufuwa saboda farin ciki, Matar sai yabo kyanta takeyi tana santin ta.

Har tambayarta tayi wanene mijin da zata aura? Ko mutumin da suka zo a tare ne"? Tace mata Eh.

Ta kuma tambayarta wanene shi? Tana ji kamar tasan shi tun da taji muryarshi, amma dai yana da arzi?i sosai shiru batool tayi batare data tanka mata ba, tun da ta fahimci irin matan nan ne da basu gani su ?yale masu Wan banzan Wumi da son tsegumi..

Duk da ta shareta bata daina yi mata surutu ba, taci gaba da cewa"ai daga gani yana son ta sosai, dama mata irinsu masu kyau maza basa gajiya da kashe masu kuWi, can kuma tace amma dai ita ba jinsin bakar fata bace ko"? ta fada tana jiran amsarta, fashewa da dariya Batool tayi hakan ba karamin mamaki yaba matar ba, juyawa tayi ta nufi curtains din da niyar ta fuce don ta gwado ma yaya Owais rigarta, tana kokarin dage labulen Unexpected ta gan shi yayin da ya ke kokarin shigowa ciki, ya gaji da jiranta yaji shiru basu fito ba.

From head to toe yabita da kallo a hankali sai yaga gaba daya ta sauya mashi, tayi matu?ar yi mashi kyau a cikin bridal gown..

"Masha Allah" taji ya furta, da sauri ta sunkuyar da kanta ?asa,

Unexpected taji ya daura tafinsa asaman waist dinta ya janyota ta fado kan jikin shi, duk tabi ta dabarbarce, sam sun shafa'a sun manta da staff din dake a gurin, sai kallonsu takeyi gwanin ban sha'awa..

Hugging dinta yayi tighly,suka nutsu suna shakar kamshin juna cikin shau?i..

Hannunsa ya daura saman sumar kanta ya soma shafata a hankali, batare da ya iya furta kalma ba, ba karamin kyau tayi mashi ba,

Dakyar suka raba jikinsu daga na juna, bayan ya biya kudin rigar da bank card dinsa, Batool ta cire taba staff din ta sanya masu a cikin shopping bag, ita kuma ta maida atamfarta, ruko hannunta yayi a cikin nashi suka fito, bayan sun shigo mota, yaja suka nufi Estate dinsu..

Bayan motarsu ta karaso cikin estate din, yayi niyar ya mayar da ita gida, amma sai ya tsinci kanshi da juya sitiyarin mota, Ya nufi gidansa, kwata kwata bata tanka masa ba, da taga ya canza hanya, yanzu bata jin fargaban koma ina zai kaita tun da tasan mijinta ne halak malak,

A Wayan duplex din Gidan inda ya kawota a daren auren su, nan ya shigo da ita, ya ruke hannunta a cikin na shi suka nufi ciki still tana jin shakkar shi da fargaba amma ba kamar na ranar ba.

Lokacin da suka shiga falon, yana a gaba tana abiye da bayan shi, zama suka yi saman Sofa daya, ta ajiye shopping bag din akan C-table.

Ta yi shiru tana jira taji me zaice, batare data dube shi ba.

Tsawon mintuna yana daddana wayar sa kamar ya manta da zamanta a falon..

Bacci ta fara ji, ta soma gyangyaWi a karshe ta langwa6e kanta jikin Sofa, tuni bacci yayi awon gaba da ita..

"Batool ina fata sun faWa maki.."

bai ?are maganarba, ganin tana bacci, shiru yayi yana kallon ta, yadda take fitar da numfashi cikin nutsuwa ba karamin jan hankalinsa ya yi ba, lura da takurar da tayine yasa shi yanke shawarar maidata kan gado, mikewa yayi a hankali ya sungumeta kamar jinjira Ya nufi Bedroom Winta, bayan daya shiga Ya kwantar da ita gadon,harya mi?e zai fita yaji wata irin kasala ta baibaye jikin shi, ya dingajin kamar bacci, baisan sa'adda Ya haura kan gadon Ya kwanta daga gefen ta ba,janyota yayi tare da rungumeta a kirjin shi, yana jin tsantsar son kasancewa da ita, sa'ilin data farka taganta a jikin shi a lokacin harya nutsa cikin baccinsa,kasa mikewa tayi, idanunta akan shi, ta nutsu tana kallon kyakkyawar fuskar shi, a hankali ta shafa sajen shi, kafin ta daura hannunta saman sumar kan shi da take marmarin ta6ata, da yake taga yana bacci shiyasa ta saki jiki ta dinga shafa sumar kanshi mai santsin gaske, a hankali ta sauke idanunta akan soft full lips dinsa, sun ciza launin su pink, sun dan bushe, ta kasa yarda Mijin tane yaya Owais! Har yanzu jin abun takeyi kamar a mafarki saboda al'ajabin ta yadda Allah ya juye al'amari ya mallaka mata muradin ranta..

Kallonsa da takeyi ne ya haifar mata da jin matsanancin sha'awar shi, zufa ta soma jike jikin ta, zuciyarta ta dinga azalzalarta akan ta sumbace shi tun da bacci ya ke yi, tsautsayine yakai bakinta saman nashi, ta haWe lips dinta da nashi, ta fara licking dinsu da harshen ta kamar ta samu zuma, tun tanayi a hankali harta koma tana sucking din su sosai, Numfashinsane ya soma sauyawa alamar yanajin dadin abunda takeyi masa, tana kokarin raba bakin ta daga nashi, Unexpected taji Ya dam?i waist dinta da hannunshi, a firgice ta zare idanunta, tayi zaton cikin magagin baccine yayi mata hakan, tana kokarin raba jikinta da naga nashi Unexpected taga ya buWe idanunsa da suka kaWa jawur cike da kasala ya ke kallon ta, cikin rawar Murya ta furta"ya Owais dama idonka biyu? Ko bacci ka ke yi"?

Lumshe idanun shi yayi a hankali ya sake buWe su kan fuskarta, da wata irin kasalalliyar murya taji ya furta"ki cigaba da yi min abun da kikeyi min, inajin daWi sosai" gabantane Ya faWi tana zare ido tace"am sorry.. bansan meke damuna ba, na ruWe.." bata kare maganarba ya katse ta da cewa"karki ji kunyar nuna min soyayya, ni mijin ki ne, muharraminki.." lumshe idanunta tayi taji dadin furucin da yayi, yanzu ta fahimci shima yana jin abun da ta ke ji a game da shi..

Da kanshi ya soma yin undressing Winta, bayan daya kammala Ya tu6e kayan jikin shi, Ya janyo duvet Ya lullu6e su a ciki, gaba daya ta nemi kunyarsa da ta ke ji ta rasa, gaba Waya suka tsunduma cikin faranta ran junan su, almost Hour basu rabu da juna ba.

~______________________________~


A ranar Dinner din auran su anyi gagarumin Shagalin da ba'a ta6a yin makamancin shi a ?asar ba, dangin Amare da dangin angwaye gaba daya suka hallara kwansu da kwarkwatarta su a cikin Event hall din domin tayasu murnar auransu, a dakin Taron Omair yayi abun daya ba kowa mamaki, gaba Waya Ya bi yan uwansa Ex-prisoners Ya basu kyautar key din mota, tare da Gift cards na Hajjin bana, sunyi murnar da bazata misaltu ba, surukan sa ya gwangwaje su da kyautar Motoci tare da Gift cards na hajj, Ummi da Aneelerh da dr shureim harma da Danejo duk saida Ya basu kyautar motoci tare da Albishir din Hajjin bana, saboda Yasan Alkhairin Da Aunty Aneelerh tayiwa Angel dinsa tun da tana ?arama, itama Danejo tun a prison Yasan da ita, lokacin da Unaisah take basu labarin taimakon da tayi mata, ita kuma Ummi mahaifiyar aminiyarsa ta kuruciya ce wato Batool, bazai ta6a manta kyautatawar da tayi masa musamman a lokacin da ya ke fama da lalurarsa ta rashin son haniya.

aikuwa gaba Waya suka dinga yi mashi godiya tare da addu'o'in fatan Alkhairi shida amaryarsa, Sun yi Murnar da bazata misaltu ba, musamman yan uwansa prisoners sun yi mamakin arzi?in Omair din su, ba komai yafi masu dadi ba kamar kasantuwarshi a raye especially matan da sai a lokacin suka ganshi sunji dadi mara misaltuwa, lokacin da yake basu car keys din, fashe wa sukayi da kukan farin ciki saboda ba su zata ba, duk wanda ya ta6a taimakon Unaisah saida Omair Ya bashi kyautar Mota da hajj, kuma babu abun daya ragu na daga arzikin da Allah yayi ma shi, gaba daya kyauttukan daya basu cikin wadanda ya samu ne agurin Partyn da Emir Ya shirya mashi, bayan tarin kyaututtukan daya ba su, saida ya ?ara ma Taj da kyautar Private Villa anan cikin Abuja tare da Diamond cufflinks, na lu'u lu'un gaske, Gaba daya Ya kashe surukin nasa da farin Ciki, Taj har kusan Zubar da ?walla ya yi saboda dadin da yaji na yadda Danish Ya girmama shi fiye da kowa, Unaisah Taji dadin kyautatawar da yayi wa Family dinta, sai taji ta ?ara ?aunarsa fiye da komai a duniyar nan.


Bayan dinner din auransu da sati Waya, su ka fara shirye shiryen tafiya Honeymoon, su biyar suka tafi, Omair da amaryarsa Unaisah, Chief da amaryarsa Batool tare da Uwar gidansa Nazli, tun da suka tafi sai da suka shafe Watanni uku suna zagaye kasashe, daga cikin kasashen da suke je yawon buWe ido ya haWa da Canada, Korea, China, UK, daga bisani suka ziyarci saudi arab, sunyi rayuwar farin ciki da jin daWi, sun more lokacin su, abubuwa da dama sun faru wanda ba zasu ta6a mantawa ba.

kafin dawowar su Nigeria, wasu masoyan sun yi Aure, Arana Waya aka Waura auran, Sajeeda da zaid, dr Jazz da Faryat, Zeenatu da Mahboob, a inda sheikh imam Malik ya auri Hajiya sarah Kowa yayi mamakin yadda har suka fada tarkon son Juna, ikon Allah kenan Musa Ya saka masa da sharri yayin da shi kuma ya saka mashi da alkhairi, Ya aure matar sa, bayan haka Abie Ya auri Ummi mahaifiyar su Zahra, da amincewar Mamie, itace ma ta bashi shawarar ya aureta in dai yana son ta saboda su rufawa juna asiri, ba iya nan ba ma'auratan suka tsaya ba, shima sir mubarak ya auri Hajjaty, a inda Hajiya saratu ta amince da auran dan Uwanta kanin Sarauta dan sarkin Yarbawa wanda yasota tun da daWewa tunma kafin ta auri Praven amma saboda batason shi a lokacin shiyasa bata amince masa ba amma bayan shari'ar Elders ya bayyana mata cewa har yanzu yana son ta, kuma ashirye yake daya aureta, in har ta bashi dama, da farko ta nuna kin amincewarta saboda aure ya fita aranta, tana da ciwon abin da praveen yayi mata, amma daga bisani da yayyanta suka shawarce ta akan ta aure shi tunda yana son, kuma bafa lallai ta samu wanda zai so ta tsakani da Allah ya rufa mata asiri kamar shi ba, dama tunfil azal shine za6in su, shi sukaso ta aura amma ta bijire masu a lokacin ta kawo nata za6in, A yanzu da suka nuna suna son ta auri dan uwan ta bata musa masu ba, ta daina kin bin umarnin su, bayan data amince akayi auren su, ta zama second wife dinsa.

duk a cikin shekarar Ahlin Elders Suka aurar da mafi rinjayen matasan family Win, Kuma auren zumunci su ke yi a tsakanin su, saboda su rufawa kansu asiri don kuma su ?arfafa zumuncin su, Alhamdulillah Allah ya azurta wasu ma'auratan da samun ?aruwa, ta bangaren Chief Owais Uwargidansa Nazli ta haifa masa kyawawan Twins mace da namiji masu bala'in kama da shi, kamar yayi kakin Su, ya yin da Batool ta ke Wauke da cikin sa.

Zaki Ya samu ?aruwa tare da Aneelerh ta Haifa masa kyakkyawar Jinjirarta mace, a inda Zahra Ta haifi kyawawan Twins maza, Zayn da Yan uwansa sunyi farin ciki sosai, Salsabeel da Matar shi Dr Yusrah suma sun ?ara samun ?aruwar ?a mace, Cikin Ikon Allah Danejo da bata ta6a haihuwa ba tsawon shekaru abun na damunta, a lokacin baya har asibiti Taj ya ke kaita in ta matsa mashi akan tana son ta haihu, amma ko sunje likita ya bincika ta kamar kullum sakamakon Wayane bata da matsalar Haihuwa, Taj yasha ya kwantar mata da hankali yace tayi hakuri suci gaba da yin addu'a in Allah ya nufa tana da rabon samun ya'ya, zata haihu ne in da rai da lafiya, a lokacin kwata kwata baya nuna damuwa akan rashin haihuwarta, saboda damuwar rashin ?ar shi Unaisah, Danejo tun tana damuwa har ta cire rai, sai da ga Bisani a ranar da Imam Ya kawo masu ziyara gidan, suna tsaka da yin fira a falon Danejo su biyu Shi da Taj, lokacin da Danejo ta shigo kawo mashi Abinci, Bayan ta gaishe da shi ta ajiye masu kayan abincin, cikin jin kunyar Imam ta nemi daya taya ta da addu'a tana fama da matsalar haihuwa, Kallon Waya sheikh Imam yayi mata ya fahimci tana da evil jins a jikin ta, wanda ita kanta bata sani ba, Taj ma bai ta6a sani ba saboda basu ta6a tashi a jikin ta, Bayan da yayi mata tambayoyi a amsoshin da ta bashi ya fahimci Aljanun sun daWe a jikin ta, tun tana a rigarsu ta daji, kuma sune suka haddasa mata rashin haihuwa, nan take ya yi mata al?awarin in sha Allah zai tayata da addu'a, sannan zai aiko mata da ruwan addu'a da magunguna, ya kuma rubuta mata addu'o'in da zata dinga yi, sannan ya gargaWeta akan ta daina sakaci gurin neman tsarin Allah.

bayan da Sheikh imam malik Ya kawo mata magungunan ta fara amfani da su ta kuma dage da yin addu'o'in daya rubuta mata, Cikin Ikon Allah ta samu warakar lalurarta, salin alin Iskar suka fita daga jikin ta, sai gashi ta samu ciki, har kukan farin ciki sai da ta yi, tsawon wata tara cuff Ta haifi Twins Winta mata masu kyan gaske kamar indiyawa, kamannin su sak da ita kamar tayi kakin su, Taj ya yi farin cikin da bazai misaltu ba, haka Benazir da Unaisah sunfi kowa Wokin ya'yan Danejo, Suna son su sosai.

qarin abin farin ciki! Benazir da ummi suma daga baya ba zato ba tsammani suka samu ?aruwa kusan a lokaci daya Dan har sun fidda rai da qara haihuwa musamman Ummi saboda ita da kanta ta dinga shan kwayoyin da zasu hana ta daukar ciki tun lokacin da take karuwanci, sune suka jaza mata matsalar rashin haihuwa, amma daga bisani sai gashi cikin ikon Allah sun sake samun qaruwa, gaba dayansu ya'ya maza suka haifa, murna a wurin Unaisah da Batool kamar su zuba ruwa qasa susha suma sun samu ?anne sha?i?ai, Cikin yan shekaru albarkar ?a'?a ta yaWu a zuri'ar Elders sun ?ara yawa sun bun?asa, ga arziki ta ko ina.

~__________________________=?%?~

*EVIL FOREST=?%?>?z?*

Wata irin ni'imtacciyar iskace ke kaWawa acikin dajin mai dadin gaske.

baka jin sautin komai saina kukan tsintsaye dana namun dawa dake hargowa daga can cikin dokar dajin.

mata da maza na hango sanye da shiga ta fararen kaya a jikin su, cikin Dajin Evil forest, Suna a zazzaune saman korayen ciyayi, sun kewaye ?abari da ke agaban bishiya, yayin da suka Waga tafukan hannayen su Sama suna


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login