Showing 234001 words to 237000 words out of 321579 words

Chapter 79 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

ji daWin nasarar da Wan uwansa ya yi akan Zahra..


Tun a wannan lokacin sha?uwa ta shiga tsakanin su, daga bisani da kanta ta kawo masu abinci da abun sha ta ce suyi ha?uri mamakin ganinsu ne ya mantar da ita bata kawo masu komai ba.

Duk da ba abincin ya kawo su ba, amma saida suka ci saboda ta matsa lamba akan su ci girkinta, aikuwa Zaid ya yi ta santi yana faWin Zayn ya yi dacen mata saboda ta iya girki zai dinga zuwa gidan su cin abinci, Zayn ya ce karma ya soma, don shi kawai zata dinga yin girki shima in yanaso to ya nemi mata ya aura, Zahra duk tana jin su, murmushin farin ciki ya ?i barin fuskarta, Zaid ya ce gashi farin sunansu duk iri Waya, dama can Allah ya ?addara Zahra ta Zayn ce shima zai nemo mai irin farin sunan sa ya aura.

Cikin nishaWi da annushuwa suka yi firar su, da zasu tafi har bakin mota ta raka su suka yi sallama kamar kar su rabu da juna, su kansu sun ji daWin karramawar da Zahra ta yi ma su.

bayan tafiyar su ta watsa da gudu ta nufi Waki tana taka rawar murna.


Benazir ce ta haWa soyayyar Aneelerh da Zaki Mubarak Obinna, cikin sa'a jininsu ya haWu, soyayya mai ?arfi ta shiga a tsakanin su, da farko Benazir ta yi zaton zai ?i amincewa da Aneelerh a lokacin ma baya a Nigeria yana a Canada, a waya ta kira shi ta yi mashi tayin aminiyarta, harta faWa mashi abun da ya faru da mijinta, ya ce ya gode da tayin da ta yi mashi amma baya jin zai iya son wata ?a mace a halin yanzu, ta ce ya jira ta tura mashi hotonta tana da tabbacin in ya ganta zai so ta, saboda Aneelerh tamkar madadinta ce, bayan da suka kammala wayar, ta tura mashi hoton Aneelerh da baby Junaid a wayarsa, ko minti biyar ba a yi ba, sai ga kiran shi tana yin picking ya ce ta tura mashi contact Winta, amma baya son ta faWa mata ita ce ta haWa su, yana son ya nemi soyayyarta da amincewarta, ba tare da ta yi tunanin haWa su aka yi ba, zata iya amincewa don ta yi mata kara ba don tana son shi ba.

Benazir ta ji daWin maganarsa, nan take ta tura mashi contact din Aneelerh via chats din su..


Lokaci na farko da Aneelerh ta ga kira da ba?uwar number kuma daga ?asar Canada sai da gabanta ya faWi saboda ruWewar da ta yi, kamar bazata Waga kiran ba, amma ta yi shahada ta Waga, tun daga kan muryarsa ta fahimci mutunne mai nutsuwa da kamala, bayan sun gaisa ta tambayesa wanene shi? Kuma a ina ya samu contact Win ta? Da zolaya ya ce a mafarki aka nuna masa ita tare da contact Winta, da ta ji hakan sai ta yi dariya ta ce ita dai ya faWa mata wanene shi? Tana ji aranta ya santa shiyasa ya kirata.

Ya ce haka ne ya santa, amma ta yi ha?uri ya kar6i contact dinta batare da saninta ba, kuma ya kira batare da izininta ba, amma kar ta ga laifin sa, sonta ne ya ja hakan tun da ya ga hotonta ya ruWe..

Tambayarsa ta kuma yi wanene ya basa contact Winta? Kuma a ina ya ga hotonta?"

Still bai sanar da ita ba, sai dai ya ce ta duba whatsApp ya tura mata sa?o..

Bayan sun gama wayar, ta shiga whatsapp ta duba sa?on da ya tura mata..

Hotonsa ne tare da bayaninsa.

Farat Waya ta gane Wan uwan Chief Owais ne saboda kamanninsu, da kuma sunan shi da ta gani Zaki Mubarak Obinna..

Zurfin tunani ta shiga tana ?o?arin gano wanene ya bashi contact Win ta! Don ta ji aranta wani ne yake son haWa su..

Da ?yar ta tuna da labarin da Benazir ta basu na abun da ya faru da ita bayan ta bar gidanta da kuma hannun mutumin da ta faWa! Nan ta fahimci haWin Benazir ne...


A ranta ta ayyana in kuwa hasashen ta ya zamana gaskiya zata yi farin ciki sosai, a lokacin ta yi mamakin yadda har ya kira ta a waya, gani take ya fi ?arfin ta, gashi babban mutum mai arzi?i ga kyawun sura, ita kuwa har aure ta ta6a yi ga Wa tana da shi, har kokwanto ta yi anya Benazir ta faWa masa komai game da ita? Tayaya yana saurayi zai nemi soyayya da bazawara mai Wa!

Bayan da ya sake kiran ta, ta ce mashi ta gano komai, Benazir ce ta bashi contact Winta, kuma shine mutumin da ya taimaki Benazir bayan da ta bar gidan mijin ta..

Baiyi mamakin jin ta gano ba, nan take ya fayyace mata abun da ke tafe da shi, ya ?ara da cewa yana sonta ba don Benazir ta haWa shi da ita ba, a karo na farko da ya kalli hotonta ya ji ya kamu da ?aunarta, kuma da aure ya ke sonta..

Zare idanu ta yi, cike da mamaki ta ce dagaske ya ke ko wasa? Kuma Benazir ta faWa masa ta ta6a aure tana da Wa?"

sautin muryarsa da annuri ya ce ta faWa masa komai, har hotonta dana Wanta ta tura mashi ya gani, kuma yana son yaronta, zai kula da rayuwar su gaba Waya, kar ta ji komai.

Bazan iya bayyana maku farin cikin da Aneelerh ta yi ba, a daren ranar da suka fara soyayya, kusan kwana su ka yi suna waya..

A washe garin ranar, tun da sassafe ta je gidan Benazir don ta yi mata godiya, Taj da ya ji labarin a gurin Benazir ya nuna farin cikinsa duk da ya so ya auri Aneelerh saboda akwai sonta a zuciyarshi kuma yana son ya ru?e Junaid a gurinsa amma sai ya ha?ura saboda ya ji labarin kyawawan halayan Zaki sai ya ji ya kwanta masa arai, ita ma Aneelerh ta so Taj a baya, amma saboda bazata iya auran mijin aminiyarta ba shiyasa ta ha?ura da shi, dama can Allah bai ?addara za su auri juna ba. Duk a shekarar bayan dawowar Zaki daga Canada, ya turo magabantansa gidan su Aneeleerh, abun Allah! daga zuwa sanya biki suka ji daWi nan take suka zarce da Waura aure bayan sallar azahar, duk da Abie ya faWa masu yana bu?atar lokaci da zai yi ma Aneelerh kayan Waki, Sir Mubarak ya ce basu bu?atar komai daga gare su, Zaki yana da gida da komai na bu?ata a estate Win su, ba su son a kawo ta da komai. Alhamdulillah, bayan shagalin bikin Aneelerh a ?arshe ta tare a gidan mijin ta..


A gurin bikin Aneelerh, Allah ya haWa wasu masoyan, Zaid da Sajeeda! Da kallo Waya Allah ya jarabce shi da sonta, kuma cikin sa'a ta amince da soyayyar shi.


Yayin da Mahboob namu ya faWa tarkon son Zeenatu dama ya santa tun lokacin baya da Benazir ta ta6a zuwa da ita gidan su, amma bai so ta a lokacin ba saboda yana tare da Ana, bayan haka ko babu Ana ba zai so ta ba a lokacin saboda yana jin tashen ma?on shi baison auren mace mai kyau wadda zai yi wahalar kashe mata kuWin zuwa saloon balle ita da ta ke baturiya=??


To a ranar walimar bikin Aneelerh suka haWu, yaita kallonta yana bibiyarta batare da sanin ta ba, duk wani motsin ta akan idanunshi, kwata kwata bata lura ba, har saida Sajeeda ta ankarar da ita tukunna ta lura da bawan Allan dake ta bibiyarta, tarko ta Wana masa ta fuce daga event hall Win walimar ta la6e baya gurin furanni, yana fitowa ta sha gabanshi, ta haWe rai ta ce ya faWa mata meyasa ya ke ta kallonta yana bibiyar ta duk ya hanata sukuni.!

Baisan sa'adda jarumta ta zo ma shi ba, ya gyara tsayuwar shi cikin nutsuwa ya faWa mata abun da ke a ransa.

Abun ka ga rainon turai, da ta ji ya kwanta mata arai nan take ta kar6i tayin soyayyar shi, tun kafin a tashi daga walimar suka ke6e a garden su biyu suka sha soyayyar su, har bayan da suka koma gidajen su basu rabu da juna ba, chatting suka ci gaba da yi, tun daga wannan ranar ne sha?uwa mai ?arfi ta shiga tsakanin su, sai da ta kai ga Mahboob ne ke zuwa gidansu ya Wauke ta ya kaita school idan an tada su ya je ya Wauko ta, Hajiya Sarah tasan da komai, kuma ta ji daWin kulawar da yake ba Zeenatu, saboda shi yasa yanzu bata zama da damuwa a ranta.

Daga bisani Zayn Ya auri Zahra bayan kammaluwar bikin su, Anan gidan sa na cikin Imam Estate suke da zama, yayin da Zaid ya ke jiran Sajeeda ta kammala karatu kamar yadda ta nemi alfarma a gurinsa na cewa ya bari ta gama karatu sai su yi aure, Shi ma Mahboob Zeenatu ya ke jira ta kammala karatu kafin su yi aure.

___________________________________=ؗ?=?%?


Taj bai manta da alkawarin da yayi akan Zai raka Danejo takai ziyara gurin yan uwanta fulanin Daji, bayan da suka samu kwanciyar hankali, a rana Waya suka shirya da shi da Unaisah da mommyn ta, tare da Danejo da kuma rakiyar Isod Soldiers wanda Owais ne ya Umarce su da su basu kariya saboda yaji Daji ne in da zasu je, bayan sun isa Dajin danejo bata manta da inda rigarsu take ba, ita ta jagorance su can cikin dajin har inda rigar ta ke, Ba zato ba tsammani Yan uwanta suka ganta tare da mijin ta da iyalinsa, tsantsar Al'ajabi ne ya kama su, nan take suka fashe da kukan farin ciki, itama ta kama kukan murnar ganin yan uwanta, bayin Allah basu ta6a tsammanin za su sa ke haWuwa da Danejo ba, tun bayan da suka ba Taj amanarta ya tafi da ita, damuwa da zullumin awani hali take a ciki ya cika zukatansu, basu ta6a mantawa da ita ba, a lokacin har sun fidda rai da ita, duk in su ka tuna da ita sai sun yi danasanin Waukar ?ar su marainiya su ka ba bare, amma zuwan da Taj ya yi da Danejo Ya faranta ran su, sunyi farin ciki mara misaltuwa, sun ?ara jin kaunarsa ganin yadda ya ruke amanar ?ar su, sun kuma yi mamakin ganin Angel, ?ar yarinyar da suka sani tun tana da shekara sha Waya sai gata sun ganta ta girma ta zama budurwa, itama Unaisah tayi farin cikin ganin su, musamman Hasiya Yar uwar Danejo.

Benazir ta yi masu godiya sosai akan taimakon da Sukayi ma Yar ta Unaisah, gaba daya sunji dadin karramawar da sukayi masu, sati ?aya sukayi A rugar, Lokacin da zasu dawo Taj Ya ro?i alfarmar da su biyo su su dawo birni cikin mutane da zama, har ya yi masu al?awarin zai taimaka masu da muhallin da zasu zauna, da farko sun nuna ?in amincewar su saboda sun saba da rayuwar daji tun kaka da kakanni, amma da Danejo ta lallashe su ta kuma basu labarin rayuwar birni da kuma ababen more rayuwa sai suka amince da zasu biyo su, dama kuma suna cikin matsin talauci tun bayan da su ka rasa shanayensu da 6arayi su ka sace.

Taj da Benazir sunji dadin amincewar su saboda suna son su saka masu da halaccin da su ka yi wa Unaisah, bayan da suka baro rigar, kaitsaye suka nufi Jihar Joss, already Ya gyara gidansa na Joss da niyar duk in zasu kawo ziyara sai su sauka anan, Gaba daya Ya mallaka ma Dangin Danejo gidan, da ya ke basu da yawa ya ishe su har ya yi masu yawa, Unaisah ta basu kyautar Kaso mafi tsoka a cikin kudin da kotu ta raba masu na Elders, yayin da Benazir ta ?ara masu da kyautar KuWin da zasuja jarin sana'a, ga kuma kudin da Owais ya bada abasu kimanin miliyan goma.

suka dinga yin kukan farin ciki suna yi masu godiya, kafin tafiyar Taj da iyalinsa sai da suka rakasu kasuwa suka yi siyayyar dabbobin da zasu kiwata, a bayan gidan suka hada garken Dabbobin su, inda zasu cigaba da kiwon su, ga kuma sana'ar siyar da fura da nono da za su farayi, Taj ne Ya haWa su da abokinsa Muhsin bayan daya nemi taimakonsa Akan ya dinga taimaka masu har su samu wayewa tun da shi anan joss ya ke da zama tare da family dinsa, Muhsin yaji dadin alfarmar da Taj ya nema agurinsa saboda shima yana Neman hanyar da zai saka mashi alkhairin da yayi masa.
bayan Taj da iyalinsa sun koma Abuja, Muhsin da danginsa ne suka cigaba da kula da dangin Danejo, suna taimaka masu ta fannin wayar masu da kai game da rayuwar birni da kuma mu'amala da jama'a, sun kuma taimaka masu gurin neman ilmin addini dana zamani.

*FLASH BACK=ؗ?=ؔ?*


bari mu koma baya muji shin wanene Mahaifin Prisoner Chinonso wanda muka fi sani da Majnoon, Unaisah ce ta gano wanda ya sadaukar da shi saboda ta ?wallafa rai akan son sanin wani mugunne ya sadaukar da ?aramin yaro mai ta6in hankali har yayi silar mutuwar shi? saboda bata manta da shi ba, yana aranta, har Yau har gobe bata daina yi masu addu'a ba shi da Unaizah, da sauran yan uwansu prisoners wadanda suka rigamu gidan gaskiya, tun kafin ayi shari'ar Elders, ta ta6a jin labarin kundin rijistar fursinoni a gurin Owais shi ne ya fada mata yadda suka samu kundin ya kuma fayyace mata abun daya ?unsa, ko da taji haka nan ta ro?e shi daya taimaka Ya dubo mata wanene ya sadaukar da Majnoon dinsu a cikin littafin rijistar fursinoni, bai tambayeta dalili ba, bayan daya kawo mata littafin, a gaban ta Ya buWe shafin prisoners din da aka sadaukar Na sashen su a kurkukun, suna tsaka da dubawa nan take suka gano sunan Chinonso, da wanda Ya sadaukar dashi, bakowa bane face aminin baba Obie, Jan kunne, Chinonso yana daya daga cikin ya'yan sa daya sadaukar a gidan kurkukun kaddara, gaba daya ma ya'yan da yake sadaukarwa bata hanyar aure yake samun su ba, Majority dinsu tsohuwa zafreen ce ta ke haifa mashi su, a tare suke sadaukar da jinin su gidan kurkukun, Unaisah batayi mamakin jin sunan wadanda suka sadaukar da shi ba saboda tasan Tsohuwa Zafreen takuma san kafurar zuciyarta, daga bisani tayima Chief Owais godiya daya taimaka mata gurin gano abun da ta ke nema =ؔ?

__________=ؖ?TURAI_____,


Shin wacece Harriet (khadija) Mahifiyar Dr Jazz ? Menene asalin su? Me kuma yasa ta baro ?asarta England da danta tazo Nigeria? Tayaya kuma akai ta samu aikatau a obie estate?

Harriet Baturiya ce ta usili, Yar asalin London ce babban birnin kasar England , ta taso a hannun Mari?inta, kawunta kanin mahaifin ta, wanda tun bayan rasuwar iyayenta ya Wauke ta ya dawo da ita gidan shi, Yana da mata daya tare da Wansa Abraham wanda ya haifa tare da mariganya matar shi ta farko, kawunta ne ya rike ta tun daga ?uriciya har ta girma ta zama budurwa, bayan data mallaki hankalinta, ta kammala karatunta, ya haWa ta aure da Wan su, wanda sun daWe suna son Juna tun da kuruciya, bayan data samu cikin shi wata tara cuf ta haifi danta mai suna Eric wanda muka fi sani da Jazz, daddynsa Yana mutuwar son shi kamar ranshi, arayuwar Turai bata da matsalar daya wuce Matar Uncle dinta wato step mother din mijin ta Beatrice, Beatrice bata da mutunci ko kaWan, ta Waura mata karan tsana tun lokacin da Mijinta Ya kawota gidan, bata son ta, bata kula da ita, kullum cikin ?yarar ta ta ke yi, idan ya kasance su biyu ne a gida har wankin bango take sanyata, ta dinga yi mata barazana akan zata kashe ta.

haka lokacin da Uncle dinta ya hadata aure da dan uwanta, Beatrice ta nuna ?in amincewarta, saboda bata son idan Abraham Ya mutu ta gaji dukiyar shi, shiyasa tun farko taso ta hada shi aure da diyar kanwarta, amma ya bijire akan baison ta turai yake so, bada son ranta ba Abraham Ya auri harriet sai don saboda Ubansa Ya matsa akan saiya hada Yar dan uwansa da dansa aure saboda baya son bare Ya aureta, kuma ya fahimci son juna su ke yi, bayan auransu Ta ?ara tsanar turai babban bakin cikinta, Arzi?in Abraham da yake yana da dukiyar daya gada agurin mommynsa, tasan muddin Ya mutu turai ce zata gaje shi tare da danta, ita kuma batason hakan ya faru, gani take kamar ma Turai badan Allah ta aure shi ba, sai don saboda dukiyar shi, gaba daya ta hana rayuwarta sukuni, gashi ta kasa faWama kowa game da ?untatawar da ta ke yi mata da ya ke a gida daya suke rayuwa kowa da part din sa, ta hana ta sukuni agidan Mijinta, karshe ma ta fara shiga tsakaninta da mijinta, ta dinga kulla mata makirci duk don ta rabasu amma Allah bai nufa ba, saboda daddyn Jazz yana yi mata son da baya ganin laifinta akan komai, a wata rana Allah yayiwa Uncle dinta rasuwa sunji mutuwarshi, musamman ita daya zama gatanta, hankalinta Ya tashi saboda tasan Beatrice ba zata raga mata ba tun da mai goya mata baya baya araye yanzu zata samu damar rabata da mijinta, ko ta kashe ta kamar yadda ta saba fadin itace zatayi ajalin ta.

Kamar kuwa ta sani, bayan rasuwar Uncle dinta, ta canza salon cuzguna mata, har maza take dauka haya ta biya su kuWi don su farmaketa saboda kawai ta shiga tsakaninta da mijin ta, amma Allah bai nufa ba, kullum batayin nasara akanta, kuma takasa tankwara zuciyar Abraham akan ya rabu da turai saboda a lokacin ya kara sonta fiye da da saboda kafin mutuwar daddynsa lokacin dayake jinya agadon asibiti saida ya roke shi akan ya kula da rayuwar yar uwarsa, ya bar mashi amana, Yasan step mom din sa bata sonta, zata iyayin komai donta rabashi da ita, don haka ya kula da rayuwarta, duk runtsi duk wuya karya rabu da ita, wannan wasiyar da babansa yabar masa ce tasa baya sauraron maganar Beatrice, akan Turai sun sha samun sa6ani da ita, saboda ya bijire mata akan Umarninta.

a lokacin da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login