Showing 249001 words to 252000 words out of 321579 words

Chapter 84 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

da ameen Aunty tare dayi mata godiya.

"Deejatun harisu! Azeeza matsoraciya, naja'at Sojanya foodie Rai ba aburi, kuzo ku kar6i naku.."

Unaisah ce ta kira sunayensu tana jin dadin tsokanar su, gaba daya mutanan dake falon suka tuntsire da dariya jin sunayen data kirasu, Benazir sai kallonta takeyi kamar zata hadiyar yar tata, wani irin alfahari ta ke yi da ita.

Bayan ta mimmika masu bags din su, ta Waga murya ta furta"UKHTY will You be My babbar kawar amarya? Ta fada tare da daga jakar dake a hannunta sama mai dauke da sunan Batool.

Farin cikine Ya lullu6e Batool da sauri ta nufeta suka rungume juna.

kallon juna Ummi da Benazir su kayi wani dadine ya lullu6esu ganin yadda ya'yan nasu suka hada kansu, suma sun zama aminnan juna kamar dai su Win.

Bayan Sun gama rarraba masu jakunkunan, tun anan wasu suka fara budewa suna duba kayan dake a ciki..


A hankali Batool ta zaro outfit din da ke a ciki, fitted gown ce dinkakkiya, ta code lace maroon da ashoke, asaman sofa ta daura kayan, ta fiddo
invitation card mai Wauke da event programmes, hada phone case with wedding logo harafin sunan amarya dana Ango ne a jiki O&U ga wani karamin kit, bayan data buWe cikin shi, tissues ta gani tare da breath mints and pain relievers.


Murtuke fuska tayi wani irin 6acin raine Ya turnuke zuciyarta, babu wanda ya lura da yanayinta sai Unaisah dake ta satar kallonta, aranta ta ayyana meke damun Batool? Kishi take dani? Ko bakin ciki takeyi! Ya Allah kasa zargina karya zamana gaskiya.


Batool in wani abu kikeso ni me iya bar maki ce ta fada a ranta.

?awayen amarya sun rude da ganin zunzurutun kyaututtukan da aka basu, ango ya gama masu komai, sun fahimci Yana ji da su, sai santin kayayyakin sukeyi suna yabawa banda babbar kawar amarya.

"Yeehh hohoho Wayyo Allahna Nima ga nawa kayan"

Jemimah ce ta furta da karfi, gaba daya hankali ya dawo kanta, tana akan kujera ta zazzage kayan dake a cikin jakarta sai washe baki takeyi farin ciki Ya cika ta..


?yal?yacewa su ka yi da dariya suna kallon ta.


"Amma ni abin daya Waure mun kai? Tayaya akai wadanda suka dinka mana kayan sukasan size din mu, ku dube ni ku gani? Nayi kyau"? Parveen ce tayi tambayar yayin da take nufo su daga wani daki ta fito, jikinta sanye da kayan data gwada.

Sakin baki su ka yi suna kallon ta, Kayan sunyi mata kyau sunbi shape din jikin ta.

Benazir tace"masha Allah, autar minister, you look gorgeous, nafi tunanin angone ya bada awonku may be yana da shi, Ko kar6a ya yi agurin parents din ku"

har suna haWa baki gurin yi masu godiya.

Ummi tace"bamu yakamata ku godemawa ba, Unaisah da angonta.." sunnar da kai Kasa Unaisah tayi, gaba daya suka nufeta sunayi mata godiya"thank you sis, pls ki fadama hubbynki muna godiya, Allah ya kaimu lokacin da rai da Lafiya, Allah ya cika maku burinku" kasa kasa da murya take amsawa da ameen.

Tana lura da Batool data haWe rai, sai ci ka takeyi tana batsewa, kowa yana yi mata godiya ban da ita, ta rasa gane laifin me tayi mata S'

"banga na yan uwanmu maza ba, Ko su banda su ne"?

Deeja ce ta tambaya taji shiru ba abata na yayanta ba..

Benazir tace"hada su, amma nasu ba gurin mu aka kawo ba, ai su ta bangaren ango suke ko"?

ta fada tare da Wage mata gira..

Dariya Deeja tayi"nagode auntyn mu.."


Cikin kwanakin da suka rage, bothside dangin ango da dangin amarya sun dage damtse suna ta shirye shiryen Bikin ya'yan na su, haka zalika Amarya da ango suma shiri su ke yi na musamman domin tarbar ranar auran su.


*ANEELERH

Fitowa tayi daga Bedroom din ta dake a downstairs ta nufi main falo, sanye take da bubu gown ta material, tayi rolling mayafi akanta, Masha Allah ta zama babbar mace, fatarta tayi haske irin na wadanda hutu ya samu mazauni a jikin su, daga gani tana samun kulawa agidan mijin ta.

A cikin kunnanta ta tsinkayi muryar mijin nata "idan ina yi maka Assignment ka dinga maida hankali akan bayanin da nake yi maka, kana ji na ko"?

?agowa tayi a hankali ta Waura idanunta akan shi, Su biyu ne zaune kan rug, ya tasa baby junaid agaba yana yi masa Assignment da textbook dinsa, daga gefen sa Laptop dinsa ce da ya ke aiki da ita..

Baby Junaid an girma yanzu sai dai har yanzu bai daina shagwa6a ba saboda step father dinsa ya sangartashi da gatanci, idan kagansu a tare ba zaka ta6a cewa bashi ne ya haife shi ba, hatta kayan jikin su kala Waya ne.

"Assalamu alaikum.. " sallamartace ta katse su, a tare suke dube ta, Murmushi ta sakar masu Junaid ya ambaci sunanta Mommy
"Na'am daddys Boy..." ta fada tare da kallon Zaki dake bin ta da kallon kauna.

"Sannu da kokori honey, Halan shine ya hana ka yin aiki, kullum baya gajiya da kawo maka assignment, har cewa nayi ya dinga bani inayi masa amma yafi son wahalar min da kai" ta karashe maganar tana zama daga gefen shi.

murmushin gefen fuska yayi mata"ai ni nace ya dinga kawo min inayi masa, saboda banaso ya takura min ke"

Taji dadin maganarsa

"kana ji da mommyn babynka, yanzu dai ya maganar zuwa gidan biki, please ka barni inje, gaba daya satin nan ban leka ma su ba, nasan me kake mawa, wlh zan kula maka da kaina.." ta faWa tana marairaice masa fuska.

"Ki fahimce ni wifey, bawai banso ki motsa jikin ki bane No, fita ayanzu bazaiyiwu gare ki ba, tayaya zakije gidan biki kina fama da laulayin ciki"? zumbura masa baki tayi.

Hankalin baby junaid ba akansu yake ba, ya mayar da idanunsa akan plasma tv yana kallon cartoon.

"Ai na daina laulayin, Jikin da sau?i yanzu... " bata kare magabar ba, taji tashin zuciya, nan take ta soma yun?urin amai kafin tayi wani yun?uri aman ya kubce mata kaitsaye ta kwarara shi asaman lap dinsa, zare idanu tayi tana faman jan numfashi, babu alamun yaji kyankyami ko haushin ta sai ma murmushin daya sakar mata"kinji sau?i ko? Kuma kin daina laulayi"? Ya faWa da zolaya, cike da jin kunyarshi ta sunnar da kanta ?asa.

"A haka zakije gidan biki, kina yi masu amai, su kansu zasuji ba dadi" idanunta ne suka ciko da kwalla"na hakura da zuwa, amma pls ranar biki, kabarni inje"

Jinjina kai ya yi"In sha Allah zan barki kije, yanzu tashi muje toilet ki wanke min wandona da kika 6ata da amai"

atare suka mike, tare da barin falon, kwata kwata Junaid bai lura sun fita ba,

"Junaid... " muryar khadija mai aikin su ce ta katse shi, dagowa yayi tare da dubanta yayin da take nufo shi "Aunty Khady, yunwa nake ji, har yanzu baki gama mana girkin bane"? Ya fada yana yamutsa mata fuska.

Murmushi tayi sai naga tayi min kamanceceniya da tsohuwar mai aikin Anila.

"kwantar da hankalin ka, na kammala shirya mana Dinner, Ina aunty Aneelerh da daddyn naka ne"? adan rude ya juya yana duban gurin da suke ganin babu su yasa shi cewa"nan suke zaune fa, ?ila sun shiga Waki"

"Okay, kaje ka faWa masu dinner is ready amma ka fara knocking room door din kafin ka shiga kamar yadda na koya maka"

Amsawa yayi da toh ya mike da sauri ya nufi bedroom din mommynsa..

Shin wacece Khadija mai aikin Anila? ko zaku iya tunawa da Yan uwan mariganya Aisha wadda kuka fi sani da (ANA) >?z??

_Janet da Esther, wadanda bayan da suka musulunta Ana ta sauya masu suna, Janet khadija, Esther (Zainab) tun lokacin da al'amarin Mutuwar Ana Ya fasu sunji tashin hankali da bakin cikin abin daya faru da yar uwarsu a lokacin da labarin ya ris?e su, wanda silar hakan yasa gaba dayansu suka kamu da depression har jinya sukayi gadon asibiti, sunji mutuwar Aisha, saboda suna son ta fiye da komai, tamkar uwa take a gare su, da ya ke Anila tasan basu da kowa a arewa kuma marayu ne tasan idan suka koma ?auyensu na kudu a matsayin musulmai danginsu ba zasu kar6e su ba, wannan dalilinne yasa ta kai kukan ta gurin abie a lokacin da sukazo cikin mawuyacin hali, ta rokesa akan ya taimaka ya bar su su cigaba da zama tare da su, abie yace ko bata fada ba shima bazai bari su koma ba, zai ruke su a hannun shi, kuma zai dauki nauyin komai na rayuwarsu, tun daga lokacin zainab da Khadija suka kasance karkashin kulawar Abie da iyalin sa, a yanzu haka Zainab tana zaune agidan abie yayin da khadija ta ke aiki agidan Anila, Yanzu haka sun kusa yin aure har an sanya bikin auran su_

~_______________________ =ؓ?=؞?~


*THE DAY BEFORE WEDDING DAY=?%?*



Tana a kwance cikin bathtube wanda ke a cike da ruwan Wumi daidai kirjinta ruwan ya tsaya ta kishingide kanta, idanunta suna a lumshe tayi zurfi a cikin tunanin ta.


"burina zai cika na ganin nayi aure sai dai farin cikina ragagge ne..."



Bata ?are zancen zucin nata ba, tajiyo sautin ?wan?wasa kofa daga waje, Kwan! Kwan!!

"Unaisah! My baby Girl! Kina ina! Daddynki Ya dawo, Yana son ganin ki" Benazir ce ke kwaWa mata kira..

waro idanu tayi cike da farin ciki ta yi saurin Wauraye jikinta da ruwa, ta fito daga kwamin ta warci towel dake rataye jikin hanger ta yi daurin gaba da shi.

Sai rawar jiki ta ke yi jin daddynta ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa joss, shigowa bedroom dinta ta yi adaidai lokacin Benazir ta shigo dakin.

Unfortunately, garin rawar jiki, sul6i ya kwashi kafar Unaisah gaba daya ta tafi zata kifa, a gigice Benazir ta nufeta kafin ta karasa tuni ta kife ?asa nan take daurin towel din da tayi ya warware ya dawo kan qugunta sumar kanta ta baje kasa.

"Subhanallah, daughter, tashi baki ji ciwo ba! " kasa amsa mata tayi saboda zafin dataji sakamakon dakar tiles da kirjinta yayi.

Cikin sauri Benazir ta nufe ta, tana kokarin kai hannu don ta mi?ar da ita, kwatsam ba zato ba tsammani ta yi arba da waist tattoo dinta ya zanu raWau.

"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..."

Ta faWa da tashin hankali tsantsa akan fuskarta.

sallallamin da tayine yasa Unaisah ta tattara sauran karfin daya rage mata a jikinta tayi saurin mi?ewa tare da jan towel din ta daure kirjinta.

Ta yi zaton faWuwar da ta yi ne yasa Benazir ta Waga hankalinta hakan yasa tayi saurin furta"mommy, banji ciwo ba, lafiyana lou,"

daura hannu biyu Benazir tayi asaman kanta tana fadin"nashiga Uku! Unaisah Uban wa ya zana maki tattoo a waist din ki! Yaushe akai! A ina"?

gabanta ne ya faWi aruWe ta zabura ta mike Tsaye jikinta ya kama kerma kamar mazari duk tabi tasha jinin jikinta..

"Bakiji ina magana bane? Uban wa ya zana maki tattoo? Da yaushe akayi maki shi ."

ta faWa rai a6ace ta fusgota ta juyar da ita tare da tum6uke towel din ta ?ura idanunta akan tattoo din, zanan giant snake ne nannaWe da sunan Garkuwa da wani irin salo akayi tattoo din launin black and red ya yi bala'en yin kyau a fatarta.


Unaisah duk tabi ta rude tsabar kaWuwa cikin sauri ta mayar da towel din da benazir ta cire mata ta mayar kan kirjinta ta daure shi.


"banza shashasha!, kina a cikin hayyacin ki kuwa? Ba zaki amsa min tambayana ba? Sunan uban waye garkuwan?


Ta fada kamar zata rufeta da bugu, ta tsorata sosai, bata ta6a ganin mommynta cikin fushi irin na yau ba.

Cikin rawar murya ta furta"nick..nick.. Nickname dinsa ne"_

"Shi ubanwa"! Ta katse ta da tsawa.

"Dad.. danish..." zare idanu Benazir tayi"na shiga Uku Unaisah, baki da hankaline? tayaya zaki yi zanan tattoo da sunan wani kato a waist din ki, Kin manta gobe za'a daura maki aure? Wani irin abun kunyane kikeso kija mana Unaisah? Idan mijinki yaga wannan me kike tunanin zai biyo baya..."

ta faWa idanunta cike tab da kwalla, ji ta ke kamar ta kikkifa mata mari kota huce takaicin da ta ke ji.

Cikin shakakkar murya ta furta"ki yi hakuri mommy, nayi kuskure.. "

"Sorry for your self Unaisah, wlh ba zaki kwana da tattoo din nan a jikin ki ba ! Wai meke damunki ne? Bayan kinsan haramunne yin tattoo a jiki? Ina hankalinki ne? Girgiza kai tayi batare data iya furta kalma ba..

"dole ki goge shi a yau din nan kafin gobe, ki rasa sunan wa zakisa sai sunan matacce mutumin da babu shi araye, Ina laifin ma sunan wanda zaki aura"! Ta faWa cikin bacin rai...

Zafafan hawaye ne suka wanke fuskarta masu dumi

In a weak voice ta furta"bazai gogu ba, in har ba fatar jikina za'a gurje ba.."

"Kina nufin permanent tattoo ne"?

Girgiza kai tayi"temporary tottoo ne, amma zai dauki lokaci kafin ya goge"

"Hmmm, nasan maganinki, Idan na faWa ma dadynki, kin yi bayani kuma Allah ba zaki kwana da shi ba, lalle zansa in dame shi, wallahi kin ban kunya, har kika iya zuwa wani ?ato ya zana maki tattoo a waist Winki don hauka"

tana fada ta juya zata fuce, da gudu tabi bayanta tayi saurin shan gabanta tana kuka tace'dan Allah ki rufa min asiri kada daddy yaji, wlh ransa zai baci, zai yi fushi dani, bana so na rabu daku kuna fushi dani, zan iya samun matsala agidan aurena.."

ta fada tana jan magina, hawaye wasu nabin wasu akan fuskarta.

"nayi danasani mommy banyi zaton zai zamarmin matsala ba sai da kika ankarar dani, ki yarda dani wallahi ba namiji ya zana min shi ba, babu wanda yaga tsiraici na, tsautsayi ne yasa naje akayi min a tattoo studio kuma artist din da tayi min macace, wallahi bata ga jikina ba, iya fatar gurin da tayi zanan tagani kadai ban kware jikina ba, kuma wallahi a private room dinsu ne babu wanda ya gani"!

cikin shesshekar kuka ta faWa.

"Mommy ki taimaka min mu nemi mafita kafin gobe..."

kalaman Unaisah sun karya mata zuciya, wani irin tausayinta ne ya kamata.

"Unaisah meyasa kika yi tattoo da sunan garkuwa"? Ta kuma tambayarta!

"Zan fada maki amma kada ki fadamawa kowa, ki rufa min asiri, nasan zakiji haushina watakilma kiyi min kallon mara hankali amma wlh ba haka bane, soyayyarshi jarabtace daga Allah, in ba haka ba tayaya zuciyata zata dinga azabtar dani da son matacce? Ba irin addu'ar da banyi ba akan Allah ya yaye min son shi, ya mantar dani tunaninsa amma har yanzu babu abun daya sauya mommy..."

kasa ?arasa maganar tayi saboda kukan daya kwace mata.

Da sauri Benazir ta rungumota a jikinta, taja ta suka zauna kan couch, ta ?an?amate cike da tausayin ta, take jin kukanta a cikin kunnanta.

"Meyasa baki fadamin ba tuntuni? tayaya zaki zauna da damuwa aranki baki sanar dani ba? Kina da tamkatane Unaisah"?

Cikin shesshekar kuka tace"saboda inajin tsoron abun da zai biyo baya, kuma banaso daddy yaji, saboda tunkafin rabuwa na da Danish ya nuna baya sona da shi, yaya owais ne zabinshi, shiyasa nake kokarin inga na cika mashi burin shi amma abun yaci tura.. "

"La'haula wala'quwata Illah billah"

ta fada tana shafa sumar kanta, batasan ya zatayi da ita ba! ta razana da jin abun da ke damunta, al'amarine mai girman gaske son wanda baya araye.

"akwai wanda ya san da maganar nan"?

"Batool kaWai na taba fadamawa"

"Kashh,! baki kyautamun ba Unaisah, Idan matsala ta same ki irin wannan ni ya kama ta, ki fara sanarmawa, ni na haifeki, ni nasan ciwon kanki, duk duniya babu wanda zai fahimceki kamar yadda ni zan fahimce ki, zanfi kowa rufa maki asiri"!

"Nagane kuskurena mommy, zan dinga fada maki..."

hankalin Benazir ya tashi sosai jin yadda jikinta yaWau zafi, ko a tarihi bata taba jin soyayya makamanciyar wannan ba, tayaya wanda ke araye zai dinga dakon soyayyar mamaci?

Lamarin akwai Waure kai duk da ba abin mamaki bane tunawa da halin data ta6a shiga lokacin da taji abun da ya faru da taj kusan hauka ta yi ita.

"Kina kallon hotunansa ne ko akwai wani abu dake tuna maki da shi"?

"Babu, saboda azabtuwar da nakeyi yasa na goge komai nashi daga kan wayata, Amma na kasa goge momeries dinshi dake a cikin brain dina, mommy, in zai yiwu, ki kaini asibiti su goge min memory dinshi ta yadda zan manta da komai nashi, Idan ba haka ba bazan iya zaman aure da waninsa ba, zanjama kaina zunubi ne.."

Ta razana da jin abun da tace, aruWe take kallon fuskarta da ta 6aci da hawayen ta, cheeks dinta sunyi jawur..

Benazir ta rasa ya zatayi da ita? Da me zata iya taimaka mata?lamarin yafi karfin tunaninta, bata taba ganin hoton Danish ba amma daga labarin da Unaisah ta taba bata na irin rayuwar da sukayi a tare yasa taji inama ace har yanzu yana araye, saboda taji dadin kyautatawar da yayima Unaisah... "


Numfasawa tayi a hankali ta ce

"Unaisah, na tausaya maki, i feel your pain, wlh da inada halin da zan iya cire maki son shi daga cikin zuciyarki da nayi, sai dai bazan iya ba, sannan bazaiyiwu muje asibiti don acire maki tunaninsa ba, kinsan bame yiyuwa bane amma tun da har kin fahimce son shi jarabtarkice to kiyi hakuri Unaisah kiyi hakuri, ki cinye jarabawarnan da hakuri da addu'a."


Nasiha mai ratsa zuciya Benazir tayi mata sosai har saida taji tayi shiru ta daina shesshekar kuka, tukunna ta samu kwanciyar hankali..

"Zan tayaki da addu'a Allah ya yaye maki abunda ke damunki Unaisah.."

"Ameen mommy, nagode da kulawarki a gare ni.." bata kare maganarba, Muryar Taj ta katse su"Ummu Unaisah naji shiru bata fito ba? Ko bacci takeyi ne"?
Daga murya tayi"a'a na iske ta ta shiga wanke ne, Yanzu zamu fito.."

"Tashi ki shirya, pls kada ki bari ya gane akwai abunda ke damunki kafin nasan yadda zamuyi da tattoo din nan"

in a cool voice ta amsa da toh, dakyar ta mi?e ta nufi wardrobe dinta, ta dauko kaya ta sanya.



Lokacin da suka sauko down a saman Sofa suka iske taj yana kallo a plasma tv Ya daura kafarsa daya kan daya.

Takun tafiyarsu ne yaja hankalin shi ga kallon su, murmushi yayi tare da mika mata hannu.

Da sauri ta nufeshi ta kwantar da kanta saman kafadarshi"sannu da dawowa daddy, nayi missing dinka, ya gajiyar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login