Showing 156001 words to 159000 words out of 321579 words

Chapter 53 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel



"Tayaya Allah zai taimake ta? Kefa da kanki ki ka ce Allah baya taimakon mutun kaitsaye sai dai yayi masa hanyar da taimakonsa zai iso gare shi? tayaya Allah da ya ke jinkirta amsa addu'ar bayinsa zai iya taimakon ku cikin sauri a irin wannan lokacin? Ki daina saka rai, saboda babu wanda zai taimake ku, babu wanda yasan a inda ku ke, babu network din da ma za'a iya bin diddigin ku, babu wanda zai iya tunkarar kurkukun nan a halin yanzu, saboda a kewaye yake da Evil Giants, sun ci nasara a karo na farko amma wannan karon babu wanda zai ?ara farmakar mu ya zauna lafiya.."


girgiza kai ta yi, "In sha Allah zaka ga yadda addu'ar wanda aka zalunta take tasiri akan wanda ya zalunce shi, zan kuma gwada maka yadda addu'ar mai imani wanda ya dogara da Allah take tasiri, ka jira ka gani, ni da kai wa zai yi nasara"


Ido cikin ido suke kallon juna, fuskarsa a murtuke ya ce, "Mafarkinki ba zai ta6a zama gaskiya ba, baki isa inyi jayayya dake ba, nasara tawa ce, ke da zaki mutu ...." Ya faWa tare da mi?ewa tsaye yana kallonta..


"Waliyiya Unaisah, zan jira in gani idan addu'ar taki zata yi tasiri, sannan ki taimaki kanki da kuma yar uwarki." Ya faWa tare da nuna mata ?warin dake daddabe jikin nama.

"Ba irin ?warin da kika saba gani bane, wadannan na gidan kurkukun ?addara ne, mun tsaface su, jinin jikin mutun suke tsotsewa, su sanya mashi dafin da zai lalata yan hanjin jikin shi, ya ru6e." Wani irin tsoro ne ya mamaye ta.

"Da zarar sun gama tsotse jinin da ke a jikin naman zasu dawo kanki ne."


Hankalinta a tashe ta zazzare idanunta cike da fargaba ta wurga idanunta kan su, yawu ta haWiya ilahirin jikinta ya kama kerma.


"Na barki lafiya.." Juyawa ya yi taku Waya biyu ya 6ace ma ganin ta..


Fitar sa ke da wuya, ta lura ?warin sun kusa gama tsotse jinin naman, kafin kyaftawar ido har sun gama tsotse gaba Waya jinin dake a Wakin sun fara bin bango suna tunkarota da saurin su, ga kukansu mai tsiwar gaske..


Cike da tashin hankali ta zazzare idanunta akan su, gwanin ban ?yama, cikin rawar murya ta shiga furta duk wata addu'a da ta zo bakinta, batasan ya zata yi ba, ga hannayenta a WaWWaure kafafuwanta ma, kuma ba halin ta motsa saboda inda suka Waure ta jikin taga, lokacin da ?warin suka fara gangarowa kan floor gungu guda suka nufo ta sai sauri suke yi, ?ararsu ta cika kunnanta..

Tana ta tunanin wata dubara zata yi me yakamata ta yi? Saboda bata son ta mutu batare da ta ceci rayuwar Batool ba..

Juyawa ta yi da sauri ta dubi tagar da suka Waure sar?ar hannayenta a jikin iron bars Winta (sandunan ba?in ?arfe) mai gida gida, yun?urawa ta yi a tsorace tana nishi ta soma ?o?arin tura kanta a tsakankanin ?arfen, da?yar ta samu ya shiga ta dinga ingiza jikinta ya ?i wucewa, fashewa ta yi da kuka jin kukan ?warin dab da ita, bata yi aune ba, ta ji sun fara hawa kan kafafunta suka soma caccaka mata tsinin bakinsu suna tsotsar jinin ta,Ya salam! wani maganaWisun raWaWi ne ya ziyarce ta, ta fasa ?ara kamar ana zare ranta, ta dinga kuka tana bubbuga kafafunta har ta samu ta kakka6e su.

Karkata jikinta ta yi ta fuskanci hannun damanta, a haka ta ci gaba da tura jikinta, da?yar da siWin goshi ta samu qugunta ya wuce, gaba Waya ta kundumo ta bayan tagar ta fado cikin wani Waki, still bata tsira ba saboda sar?ar da aka Waure hannayenta da su tana a jikin tagar, kuma a buWe take zasu iya faWowa ciki, kwata kwata bata lura da inda ta faWo ba, Saboda hankalinta ba a kwance ya ke ba, karfen jikin tagar ta lura da tsatsa a jikin shi alamun ya daWe ba a musanya shi ba, daddagewa ta yi da iya karfinta na karshe ta dinga jan hannunta tana nishi, gumi ya wanke jikinta, kukan ?warinne ya cika kunnanta kamar zai fasa dodon kunnanta.

Saida ta galabaita, wuyan hannunta ya yi jawur kamar zai fashe saboda sarkar da ta takure gurin ga kuma jan gurin da take yi, dai dai lokacin da ?warin suka fara hawa jikin ?arafunan tagar, a gigice ta fasa wata irin ?ara mai sauti tare da rufe idanunta, buWe idanun da zata yi keda wuya, ta ga abun da bata yi zato ba, ?arfen da aka daure sar?ar hannunta da shi ya 6alle biyu sakamakon jan da ta dinga yi, jikinta na 6ari ta buga murfin tagar da hannunta, ta danne da bayanta, tana jiyo kwarin dake ta bugun tagar kamar zasu fasa ta yadda kasan wata ?atuwar halitta, lumshe idanunta ta yi gabanta na ci gaba da faWuwa.


BuWe idanun da zata yi keda wuya, ta yi arba da tarin kawunan ?warangwal cike da dakin da ta faWo, kwata kwata bata tsorata ba, saboda mawuyacin halin da take a ciki.


Shiru ta ji ?warin sun daina fitar da sautin su, mi?ewa ta yi tsaye kan kafafunta da ke a Waure, ta Wan buWe tagar kaWan ta le?a kanta, ruWewa ta yi ganin ?warin kwakkwance a ?asa basa motsi kamar sun mutu, lamarin ya daure mata kai, har ?ara zare idanunta take yi don ta tabbatar da sun mutun ko lambo ne suka yi mata, dabara ce ta faWo mata a rai, da sauri ta tsotsi jinin dake akan le6anta, ta watsa shi cikin Wakin don ta ga idan za su tsotse shi, still ba su motsa ba, shiru ta yi jim tana yanke shawara da zuciyarta, so take ta koma cikin Wakin don ta kwance leg irons Win ?afarta, shahada ta yi duk da shakkar da take ji, ta daddake ta ruke sandunan kofar da hannayenta ta kutsa kanta ciki, wannan karan bata sha wahala ba, ta burma cikin Wakin gaba Waya ta faWo kan ?warin dake yashe a ?asa, anan ta ?ara tabbatarwa kanta sun mutu.

da?yar ta iya mi?ewa, kamar yar tsana ta dinga yin tsalle tana tunkarar teburin Wakin dama shi take hari, har kifewa ta yi ?asa ta kuma mi?ewa da?yar ta ?araso gaban shi, ta zube kan gwiwowinta, jikin ?arfen table din ta dinga buga sar?ar hannayenta da ?arfi, duk ta hada gumi akan fuskarta, sai nishi take tana jan numfashi, dakyar da sidin goshi ta samu sarkar ta saki daga tamkewar da ta yi, 6an6areta ta yi daga hannayenta ta jefar da ita ?asa, ta kai hannunta da ke kerma ta Wauki zarto ta kunna shi tare da saita shi daidai saitin leg irons din kafafunta, duk da fargaban kada ta datse ?afar saboda jikinta dake kerma a haka ta daddage ta dadara zarton da ?arfi kamar ranta zai fita har fitsari saida tayi a cikin wandonta saboda wahala, dakyar ta yi nasarar 6alle irons din ta zame ?afafunta daga cikin shi ta mi?e tana haki, tsayuwarma da?yar ta yi ta saboda raunin da legs dinta suka yi, saida ta dan sarara tukunna ta mi?a hannu ta sungumi zarton ta rataya shi akan kafaWarta, hakan bai isheta ba saida ta ?ara da tsinken ?arfe ta soke shi a cikin aljihu, duk don ta kare kanta kamar wata mai ?arfi, duk da ta zuciya, jinin ta akan akaifa ya ke, ?wara ayi ta ta ?are, ko a mutu ko ai rai.


Gaba Waya ta sauya kamar ba Unaisah ba, ta zama kamar ?ar daba, Overroll Win jikinta duk ta 6aci da jininta, haka fuskarta ma a 6ace take da jini, sumar kanta kuwa bata da maraba da ta mahaukaciya, tana Wangyasa ?afarta ta nufi tagar nan ganin babu ?ofar da zata bi ta fita daga dakin duk a kulle suke, bayan da ta dira cikin Wayan Wakin ta shiga rarraba idanunta tana neman ta wace hanya zata fita daga Wakin, ganin shima duka tagoginsa a kulle suke haka ?ofofin Wakin ma. Da zarton ta soma kokarin 6alle ?ofa Waya, sai dai ta kasa saboda rashin kuzarin dake a tare da ita, gaba Wayanta a raunace take...

Langwa6e kanta ta yi jikin kofar, tana nishi yayin da zuciyarta ke tariyo mata wasu abubuwa da suka faru atsakaninta da Batool, nan take ta ji karfi ya zo mata, tunawa da kalamansa..


Bugu Waya ta kara yi ma kofar nan ta ke ta buWe.


Cike da fargaban me zata taras ta le?o waje, bata ga kowa ba, wasu hanyoyi ne da babu kowa.


Sama ta kalla don taga ko akwai cctv can kuma ta tuna da inma suna ganinta bai wuci ta madubin zafin su ba, komai zai faru sai dai ya faru amma fa ta ci alwashin ko zata rasa ranta saita ku6utar da Batool, cikin sanWa take tafiya, duk dakin da ta gani sai ta le?a tagar shi don ta ga idan nan suka kulle Batool.


Cikin zullumi da fargaba, tana ?o?arin karya kwana kwatsam ta hango gungun Giants sun nufo gurin da take, ruWewa ta yi cikin sauri ta koma da gudu batasan sa'adda ta dura wata windown Waya daga cikin Wakunan dake a gurin ba, sai haki ta ke yi, ajiyar zuciya ta sauke jin alamun sun wuce, bin Wakin ta yi da kallo, tsofaffin metal bed ne aka jibge Waya kan Waya a cikinsa, wata dabara ce ta faWo mata, lokacin da ta dubi ceilling Win Wakin da akwai access panel a jikin shi, duk da a kulle yake amma ta na jin zata iya tsaga shi, kama jikin gadajen tayi ta dinga bin jikinsu tanayin sama dakyar ta haura ta saman su, ta zauna tana mayar da numfashi.


Tunawa da tarin ?alubalen da ke agabanta yasa ta zaro tsinken karfen da ta soke, ta shiga caccaka ma panel din, kasantuwar yana da quality, ta ci wahala kafin ta 6alle murfin, ta le?a kanta cikin ceilling din, ba laifi yana da space din da bawa zai iya ratsa cikinsa, tura kanta ta yi, a hankali ta shige dukanta, zafi ya doka mata sallama, ta fara zubda gumi, kwata kwata babu tsoro ko fargaba atattare da ita, jan ciki ta dinga yi tana yin gaba, har wata kwana kwana gare shi, bata tashi sanin ta yi wauta ba sai da ta rasa hanyar da zata 6ula, nan fa ta fara rarraba idanu, kwata kwata ba ta yi tunanin ta kalli ?asa ba, kawai jan jiki ta ke yi tana yin gaba, sai daga baya tunanin hakan ya zo mata, cikin sauri ta soma bin celling din tana ?are masa kallo cikin tsantsar ruWu..



~_____________________JAN WUYA=?%?~



A tsaye ya ke gaban dakin fiWa, zuciyar sa fari fat yau zai cika burin da ya daWe yana mafarkinsa.


BuWe kofar Wakin aka yi, babban yaronsa Dr. Mark ne ya fito, sanye da uniform din tiyata.


"Mark, ka gama tiyatar ne? Ko har yanzu ba ka cire zuciyar ba ne?"


Jinjina mashi kai ya yi, "Ban kaiga farawa ba, ina jira allurar kashe zafin da na yi mata ta fara aiki a jikin ta"


Bai ?arasa ba ya dakatar da shi. "Ba wannan na ke son ji ba, bana bukatar ka bi ta lalama, ka saka ?umbunanka ka faffarke kirjin ta, bafa ta da wani amfani zuciyarta kaWai nake so, in ba zaka iya ba ni ka bani guri in yi!"


"Allah ya huci zuciyarka sir, in har mu ka ce zamu bi ta tsiya zamu iya lalata shirin mu, dole mu bi a sannu don mu cire zuciyar batare da an samu matsala ba."


Tsoki ya ja, "Na baka nan da mintuna biyar ka cire ta kota halin ?a?a, don mu yi saurin lun?umata a bakin dodon tsafi, bana bukatar bata lokaci." Cike da ladabi ya amsa mashi da toh ya juya ya koma dakin..

Bai motsa daga inda ya ke ba, jira kawai yake yi ya gama tiyatar, abun da ya faru tun jiya da daddare da suka zo kurkukun da su, ya so yayi amfani da sihirinsa gurin farke kirjin Batool don ya cire zuciyarta, sai dai matsalar, da aka samu, sihirin sa ya yi ma jikinta ?arfi, in har ya kuskura yasa ?arfi don ya cire zuciyar toh gaba Waya zata dagargaje, shiyasa dole su bi tsarin tiyatar asibiti.



Gajiya ya yi da tsayuwa, ya fito daga sashen da tiyata room din ya ke, ya koma cikin wani katafaren falo mai kyan gaske komai na cikinsa launin ja ne, zama ya yi kan wata doguwar kujera ya Waura ?afar sa daya kan Waya kamar wani basarake, kwata kwata baya tunanin a wani hali iyalinsa suke a ciki, ta kansa ya ke, already an riga da an fada masa sojojin isod sun kewaye gidansa da gidan Wan iya, hakan bai dame sa ba.


"Musa ya za kai mana haka? Wasa tare ci bambam? Me hakan Ke nufi?"


Unexpected ya tsinkayi muryar Jan Ido a cikin kunnan sa, a sukwane ya mi?e yana duban su.


Waya bayan Waya suke ratsa bango suna shigowa falon, cikin shigarsu ta dogayen riguna ba?a?e masu huluna, hannayensu ru?e da sandunan su, rabin fuskokinsu rufe da mask, idanunsu ne kaWai a bayyane.


Kansa ya Waure da ganinsu saboda bai sanar da kowa shirin shi ba, saboda baya son su sani, shi kadai ya ke so yayi.


"Don me zaka yi komai a sirrin ce batare daka faWa mana ba? me hakan ke nufi?

Wani daga cikin Elders dinne ya faWa..


Banza yayi da su bai tanka masu ba, sai ma wani shu'umin murmushin sha?iyanci da yake saki.


"Ka yi shiru baka ce komai ba? Ko hakan na nufin dagaske ne abun da aka fada mana? Kana so ka ci amanar mu ko? Shiyasa ka shirya komai a boye batare daka fada mana ba bayan mu yakamata a ce ka fara sanarmawa.." A cewar wani elder, wani kallon tuhuma suke jifarshi da su.


Tafa hannayensa ya yi tare da bushewa da dariya cikin takun izza ya nufe su yana fadin, "Sannunku da zuwa! Tayaya akai kuka san ina anan? Wanene ya fada maku um?" Ya fada yana Wage masu gira.


Wani tsoho daga cikinsu cikin fushi ya ce, "Jan wuya baka isa ka ci amanar mu ba, mune a gaba da kai, baka isa ka yi gaban kanka ba, dama ni ban yarda da kai ba, saboda nasan halin ka ba ?aramin shaiWani bane kai, ka ?ware gurin iya haWama da kulla makirci, wato shine yanzu da ka ga Elder ya yi murabus kuma asirinka ya tonu shine ka kware mana baya, ka sato yaran da kowan nan mu ya ke burin ya Wauko su, don ka riga mu cika sharuddan allon tsafi saboda ka samu karfin ikon da za ka juya mu..."


?yal?yacewa ya yi da dariya, tare da nuna su da yatsan shi da izgilanci ya ce, "har kuna da bakin faWin ban isa in ci amanar ku ba? Dama akwai amana a tsakanin mugu da mugu? To ni ban yarda da kowannan ku ba, babu wani mai iko da ni a cikinku, saboda na fi karfinku nesa ba kusa ba,
.." Ya fada yana huci.


"Buri ne da na daWe da shi a zuciyata tun farkon dana fara yi ma Elder bauta, duk wani ci gaba da aka samu a gidan kurkukun kaddara nine sila, don haka yanzu lokaci ya yi da zan fanshe wahalata, ni na cancanta in hau karagar Elder Obinna..."


Ransu ya 6aci, yanzu sun gasgata abun da aka faWa masu game da ma?ar?ashiyar da ya ke shirin ?ulla masu.


"You son of a bitch, Musa, you'll never become an Elder over my dead body, You're not worthy, If anyone deserves it, it's one of us, who've been with the Elder for a long time before he even knew you existed."


(ba zaka ta6a zama Elder ba, baka cancanka ka zama ba, idan ma akwai wanda ya cancanta to daya daga cikin mu ne, mu da muka daWe tare da Elder tunkafin yasan da zamanka a duniya,..." )

jan le6e ne ya faWa rai a 6ace.


Wani Elder din ya ce, "Ba zamu ta6a lamunta ka zama shugaban mu ba, saboda mun ji ma?ar?ashiyan da kake son kulla mana, kana so ka samu ?arfin sihirin Elder don ka ?wace sihirinmu sannan ka kashe mu ko?"


tun da suka fara magana hankalinsa kwance babu damuwa a ransa, amma da wannan Elder Win ya yi magana sai ya fahimci kamar wani ne ya yi brainwashing Win su.



"Na fahimci wani ne ya zugo ku ya faWa maku karya da gaskiya akaina don ya shiga tsakanin mu! nasan ban kyauta ba da ban sanar da ku ba amma banyi hakan don bana so ku sani ba, kuma ni bani da mummunan nufi akan ku, sai don nafi so in sawwa?e maku wahala, amma maganar nan ba gaskiya bane, ni bana nufin kowannanku da sharri, burina dukanmu mu gudu tare mu tsira tare, saboda mun riga mun zama Waya, yakamata ku fahimce ni..."


Ya faWa cikin lalama, wani kallo suke yi mashi na rashin yarda duk da kokwanton da zuciyarsu ke yi sai dai ba zasu iya ?aryata abun da aka faWa musu akan shi ba, saboda daga majiya mai ?arfi suka ji.



"Koda zamu yarda da maganarka, ba zamu ta6a bari ka zama Elder ba, saboda baka cancanta ba..." Elder din da ya Wauko maganar bai kaiga direta ba, Jan wuya ya daka masa tsawa yana huci ya furta, "Saboda me ba zaku bari in zama shugaban ku ba? Ko ina da wani aibu ne? Ko baku yarda da ni bane? Ko kuwa shi Elder Obinnan yana da wani magaji ne ehe? Meyasa ni ban cancanci in hau karagar mulkinsa ba?"


"Bamu yarda da kai ba Musa, saboda ka yi abun da yasa mana zargin ka a cikin zukatan mu, kwata kwata babu gaskiya a tare da kai, kuma kai in ban da abun ka, ka yi tunanin hawa kujerar Elder abu ne mai sau?i? To bari ka ji in faWa maka gaskiyar zance, bare baya hawa kan karagar Elder, dole sai idan jinin Elder ne kadai zai iya hawa kan karagarsa, su da suka gaji abun ba kai da ka ke bare ba"

Jan dasashi ne ya furta, ran Musa ya 6aci zuciyar shi ta zo wuya, sun fara harzu?a shi.

Sauran Elders din da suke haWamar samun kujerar Elder


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login