Showing 162001 words to 165000 words out of 321579 words

Chapter 55 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

Waya ya razana ya bi ya ruWe ya rasa gane meke shirin faruwa da shi? Wanene ya ci amanarshi ya yaudare shi, tunawa da Mark yasa shi saurin furta sunan shi, "Mark!! Mark..!!!" Gabansa ne ya fadi ganin babu Mark babu alamarsa nan take ya fahimci Mark ne ya ci amanar shi ya bashi zuciyar evil giant a matsayin zuciyar Batool! Bai ta6a zaton hakan daga gare shi ba! Mark Ya shammace shi.

Wata irin kururuwa ya fasa ta ba?in ciki, ya rufe idanunsa gam, baisan sa'adda ya saki Kwalbar ta fadi ?asa ta fashe, sai huci ya ke yi yana gurnani kamar mayunwacin zaki..

Batare da sanin shi ba, Jan ido da jan le6e suka zame jiki da gudu suka bar gurin ya rage saura shi kaWai, saida ya gama haukan nashi ya juyo ya ga babu su..

Cikin fusatacciyar murya ya ce,



"Ka tabka babban kuskure Mark! Har ni zaka ci amanata! Na rantse bazan ?yale ka ba, sai na yi maka azaba, Mark ka gama yawo, dole in kashe ka!!!"



Sai sambatu ya ke yi kamar mahaukacin kare, yana ?o?arin Waga ?afarsa Temple Evils suka yi mashi ?awanya, Tashin hankali! dara ta ci gida!


A dabarbarce ya furta, "Don ubanku ba zaku bani hanya in wuce ba eye! Kar ku kuskura ku bari in buWe idanuna in ganku a gabana!"

Ya ?arashe maganar a tsiwace kamar zai doke su, ya runtse idanun shi yana fitar da numfashi mai huci, niyyar shi ya yi masu sihiri ya kashe su idan su kai masa gaddama.


Bai aune ba ya ji kamar wani abu na fita ta hancin shi, a hanzarce ya buWe jajayen idanunsa kaitsaye suka sauka akan ba?in haya?in dake fita ta kofofin hancin sa, wani irin mummunar faduwar gaba ya ji, Wimuwa ta same shi, a kiWime yake kallon hayakin, ya yi matu?ar razana cikin ruWu ya dinga sanya hannu yana kokarin tattara ba?in haya?in don ya dawo jikin shi.


Da alama dai dubun Jan wuya ta cika, sai sambatu yake yi yana fadin, "Ba zai yiwu ba! Bazai yiwu ba, don ubanku ku dawo jikina! Gidan Ubanwa zaku je! Ya kuke so in yi da raina? Wanene ke son ya haukatar da ni ne! Ya Allah ya zaka yi min haka? Waye ke son ganin bayana! Bazan ?yale shi ba...."


Yana magana zufar tashin hankali tana tsattsafowa kan goshinshi, jikinsa sai 6ari ya ke kamar mazari..


Bai gama sanin yana a cikin musiba ba, saida Temple evils suka yi mashi rubdugu suka Waga shi sama suka nufi cikin temple din da shi, ya dinga hauka yana kokarin kwace kanshi ya kasa, dama ba wani ?arfi ne da shi ba, karfinsa na sihiri ne yanzu kuwa babu shi a jikin shi.


Musa bai ta6a jin yadda radadin azaba ke ratsa jikin mutun ba, sai yau da temple evils suka shigar da shi ?urya, sha tara na azaba suka haWa mashi, saida suka tu6e kayansa suka yi masa zindir haihuwar Uwarsa sannan suka kwantar da shi ta rubda ciki, da za?o za?on ?umbunansu suka yi masa 6alli 6alli a mazaunansa, kafin suka Wauko bulalan su shar6a shar6a da suka tsaface su, Kusan su goma suka shiga zane shi kamar sun samu jaki, sha tara na azaba suka haWa masa, saida suka haWa mashi jini da majina, tun yana kokawar kwace kansa yana kokarin kai musu bugu har saida suka ?arar da duk wani ?arfi na jikinshi ya zamana bashi da kuzari ko kaWan, gaba daya suka wanke jikinshi da jinin shi, wani sa'in in suka shafWa mashi bulalar jini har tsalle Yake yi Ya Wiga a jikin bango, duk suka faffasa bayanshi da bulalansu tun yana jurewa har ta kaiga Ya fara fasa ihu yana shure shuren ?afa, ya aje girman kansa da komai ya dinga ro?onsu akan su barshi da ranshi Ya tuba ba zai ?ara ba, ya bi Allah ya bi manzonSa..."


Wannan maganar da ya furta cikin sambatunshi ce ta ?ara ja mashi bala'e saboda ya furta sunan Allah a temple dinsu, aikuwa ransu ya 6aci, suka aje bulalan suka Webo ruwan dake a cikin tafkin dake agefen temple din a cikin ?warya, suka mayar da shi gishiri a saman bayanshi suka watsa gishirin, Ya fasa wata irin kururuwar azaba kamar ransa zai fita, ya dinga burgima yana fadin ya shiga uku, ya bani, ya lalace, ya mutu! Tun yana iya magana har ta kaiga ko yatsanshi baya iya motsawa daga ?arshe ya sume.

Wauko shi suka yi wasu suka kama ?afafuwansa wasu suka kama hannayensa suka fito da shi daga temple din suka jefar da shi a cikin tafkin ruwan.



*(Jan wuya yau ya sha jar azaba =?? ashe ba daWi shiyasa kafin ka zalunci wani ka fara tunanin idan kai akai mawa ya zaka ji? Bawan Allahn nan ya saba ya kashe rai, ko ya ?ona rai yau ya WanWani kwatankwacin radadin a jikin shi)*


A bangare su ?an iya da suka arta a guje, suna ?o?arin saukowa down daga kan bene, ba zato ba tsammani sojoji suka ritsa da su, ?ofar raggo suka yi masu, burki suka ci a matu?ar ruWe, wato sun yi gudun gara sun faWa gidan zago.


A tsawace Sojoji suka ce karsu kuskura su motsa, su mi?a wuya kawai su zo su tafi..



Ja da baya da baya suka yi gaba daya sun ruWe kansu ya daure da ganin yadda aka farmake su batare da saninsu ba, wannan wata irin ba?ar rana ce? Gaba Waya sun fahimci makirci aka ?ulla masu ta bayan fage tun akan zuciyar bogin da aka ba Musa.


Wata irin zufa ce ta wanke fuskokin su, fargaba da tsoro ya cika su.


"Ya zamu yi? Mu gudu kawai ko mu 6ace, idan ba haka ba kama mu zasu yi.." Jan le6e ne ya faWa, sojojin suna a tsaitsaye suna kallonsu sun saita su da bindigu, Chief Owais ne a gaba tare da Commender James sun zubawa sarautar Allah Ido.


Zu?unnawa suka yi ?asa kamar zasu mi?a wuya, cikin sauri suka buga ?asa da tafukan su don su 6ace..


Saboda shafewar basira da ruWu yasa su sakin dariya a tunaninsu sun 6ace sojojin basu ganinsu su kaWai suke ganin su..



Cike da tun?aho suke taka matakalar benen suna tunkarar sojojin da suka yi kasa?e suna jira su ga iya gudun ruwansu don su fahimci rashin wayon su..


Saida suka shiga tsakiyar sojojin da niyyar su ra6a su wuce..

Sai kallon su kawai suke yi, ganin sun ?i motsawa kuma sun ?i tafiya kuma kallonsu suke yi yasa suka shiga ruWu a ransu suka ayyana tsayuwar me suke yi basu tafi ba bayan basu ganin su? (=??)


"Gidan Ubanwa za ku je??" Da kakkausar murya Chief Owais ya furta, wata irin firgita suka yi a razane suka kalle shi...

Cikin rawar murya Jan ido yake tambayar shi wai da wa yake magana? Da sojojin da yake a tare da su ko kuwa da su yake...?"

Bai ?are maganar ba, Chief Owais ya sakar mashi zazzafan naushi akan kuncinsa..


"Da ku nake magana don Ubanku, Marasa hankali..."

Zazzare idanunsu suka yi ganin da gaske fa babu garkuwar sihiri a jikinsu, abun da basu sani ba lokacin da suka gudo daga gurin Jan wuya suna tsaka da yin gudun ba?in haya?in ya dinga fita ta hancinsu ba tare da sun ankara ba..

?aura hannu biyu Jan ido ya yi asaman kanshi alamar ya shiga Uku.


A kiWime ya shiga ambaton, "la'ila ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin, Allahumma innee a'uzu bika minal khubthi wal-khaba-ith..."

?iris ya rage musulman da ke a cikin sojojin su fashe da dariya,

Chief Owais ya ce, "Ka ji jakki, tayaya kaida kake azzulumi zaka nemi tsari daga azzalumai? Bayan Allah baya a tare da azzulamai, bayan haka saboda da?i?anci addu'ar shiga banda?i ce zata taimake ka?" Ya tambaya yana jifarsu da kallo mai cike da tsana.

Jan le6e da ya gama rikicewa nan take ya saki fitsari a wandon shi...

"Wa'inna hu min Sulaimanu Wa'innahu Bismillah, ?an iya mu gudu mu bar gurin nan...!" Jan Le6e ne ya faWa a dabarbarce.

"Tayaya wanda yake rayuwa da aljanu a jikinsa zai nemi tsarin su?" Chief Owais ne ya fada..


Ganin basu da wata mafita, yasa Jan ido ya dam?i rigar Jan le6e suka watsa a guje kamar zasu tashi sama, basu san ma a ina suka jefar da takalmansu ba, sai da suka gama gudun ceton ran nasu suna kokarin shan kwana suka yi kici6us da wasu gungun sojojin, aikuwa a firgice suka juya suka nufi wata hanyar daban, duk inda suka shiga sojoji ne a ciki, no way out, ?arasowa bakin kofar wani hall suka yi, a guje suka shige tare da saka sakata suka kulle kansu a ciki.

A wahalce suka ran?wafa tare da dafe gwiwowinsu da tafukansu suna ta haki kamar jakuna.

"Ganin komai nake kamar a mafarki! Tayaya hakan zai yiwu? Wanene Ya ?ulla mana makircin da aka farmake mu? Ina ji a raina dole na jikin mu, tun da shi kanshi Musan sun shammace shi, hakan na nufin bashi bane ya ci amanarmu ba..."

Jan le6e ne ya yi maganar da?yar saboda haki...

Cike da takaici Jan ido ya ce, "Nima kamar a mafarki nake ganin komai, na kasa yarda dagaske komai ke faruwa? Benjamin rayuwar mu tana a cikin musiba, nifa tun da jami'ai suka zo gida nemana nasan cewa tawa ta ?are, wlh dana san da zuwan wannan ranar da ban jefa kaina cikin bala'e ba, yanzu wa gari ya waya? Sai da Elder Obinna ya ce mu aje mukaman ya?in mu mu gudu mu yi nesa da kowa amma muka yi kunnan uwar shegu da maganar shi yanzu ai ga irinta nan..."

Benjamin ya ce, "?an iya, kai baka tunanin su Jan ?eya ne suka tona mana asiri? Saboda mun juya masu baya, watakil shiyasa suka yi mana cinne, in ba su ba wanene zai iya yi mana haka?"

Jan ido ya ce, "Bana tunanin ko su sunsan da zuwan sojojin nan, ka yi tunani mana wanene ya kwance sihirin jikinmu? Ko shi Musa da ya fi mu shaiWanci yaudararsa aka yi, an bashi zuciyar bogi a matsayin zuciyar yarinyar...."


Zurfin tunani suka shiga kowa da abun da ya ke sa?awa a ranshi, kusan a lokaci Waya suka furta, "Elder Obinna!" Tare da kallon juna idanunsu a zazzare.


"Shi kaWai ne zai iya yi mana haka? Amma meyasa ya ci amanar mu?" Cike da 6acin rai Jan le6e ya faWa..

Jan ido ya ce, "Ja mana akai, Elder bazai ta6a iya cin amanar mu ba, in har ba wani daga cikin mu bane ya ci amanarsa, yana da ru?on amana amma kuma shi baya yafe ma wanda ya ci amanarsa ....."

Tsoki Jan le6e ya yi fuskokinsu sai naso suke yi ga idanuwannan nasu a zare kamar na kwartayen mazurai sun yi jawur.


"Musa nake zargin shine ya ja mana, in ba zaka manta ba, shine ya kawo shawarar mu tura evil giants su farmaki Estate dinsa, Musa da?i?ine, baida wayou, gashi nan ya ja mana gaba Wayan mu. Wayyo Allah mun shiga uku! ..." Cike da ba?in ciki Jan ido ya faWa..

Jan le6e ya ce, "HaWamamman banza, dama haushinshi nake ji, ya cika izza da ji da kai, gani yake kamar ya fi kowa a cikinmu, komai shine kan gaba, in har bashi ya bada shawara ba babu wanda ya isa ya faWi ra'ayinsa a bi.."

Jan ido ya ce, "Inda na gode ma Allah bamu kaWai abun ya shafa ba, shi da ya ja mana yafi mu shiga cikin bala'e nasan i warhaka yana can hannun evils yana kar6ar tsumagiya...." Duk da halin da suke a ciki hakan bai hana su ?yalkyacewa da dariya ba.

"Dukkan mu mun yi asarar iyalanmu, dukiyoyinmu da kuma mutuncinmu, yanzu me ya kamata mu yi kafin su ritsa da mu?" Jan le6e ne ya tambaya tare da zu?unnawa ?asa ya dafe goshin shi dake sara mashi..


*"Babu wata mafita da ya wuce mu ha?a ?asa mu binne kanmu, idan ba haka ba tayaya zamu fita, bayan sojoji sun yiwa kurkukun ?awanya!"*



"Wannan wace irin banzar shawara ce muna da makamin da zamu ha?a ?asar ne? Ko kamanta bamu da sihiri a yanzu...?" Ya faWa tare da juyowa ya dubi Jan ido dake ta zazzare idanunsa...

Cikin rawar murya ya ce, "Don ubanka bani ne na yi magana ba!"

Gabansu ne ya yanke ya fadi, zuciyarsu ta shiga harbawa fat fat kamar zata tsaga kirjinsu, tsoro ya hana su juya su ga wanene a cikin hall din bayan sun kulle ?ofa kafin su shigo.


Kuskuren da suka yi shine kwata kwata basu lura da inda suka shigo ba, kawai sun ja kofa sun datse sun juya baya suna ta sambatunsu...


"Congratulations, You're Under arrest!" Muryar Chief Owais ce ta ratsa kunnuwansu, A razane suka juya suna kallonsu, su biyu ne shi da Commender James, abun da ya faru lokacin da suka shiga hall Win sun gan su saboda sun biyo su, sai dai basu bi ta ?ofar da su suka shiga ba, saboda sun ga akwai wata kofar ta bayan hall din.

Su biyu suka yi masu rubdugu, wani irin bugun mutuwa suka yi masu, idan Chief ya jibga sai ya tilla ma Commender James shi kuma ya jefa masa na hannunshi, haka suka dinga musayar su, saida suka haWa musu jini da majina akan fuskokin su, Chief bai iya bugu cikin fushi ba, lahanta sassan jikin mutun yake yi, sai da suka faffasa fatar jikinsu, wani naushi da Chief ya sakarma ?an Iya a bakinsa nan take ha?oransa biyu na gaba suka babbako jaga jaga da jini suka faWo ?asa, ya dinga buga kanshi jikin bango, Wan iya ya dinga fasa ihu da azaba ta ishe shi, ya rasa meke masa daWi gaba Waya ya fita hayyacinsa .


James da ya lura Chief ya kusa kashe shi..


Cikin sauri ya jefar da Jan ido gefe Waya ya nufe shi ya na kokarin raba shi da shi..

Cikin fushi yake fadin ka barni james! Ka ?yale ni! ka barni in kashe fasi?in mutumin nan..."

yana magana muryarsa na rawa saboda 6acin rai, shatun jijiyoyinsa sun fito ruWu ruWu.


"Owais, ka dawo hayyacinka mana, kashe shi ya sa6a ma doka!"


Da ?yar ya 6am6are Chief Owais daga jikin ?an iya, aikuwa ya koma kan Jan le6e abokin kakansa ya sha?i wuyansa kamar zai tsinka shi, cikin harshen turanci yake fadin, "Owais ka sakar min wuyana ni fa ne Benjamin abokin kakanka, ka yi mini rai, kada ka kashe ni, na tuba Owais ka ?yale ni..." Yana fitar da huci ya ce, "In ?yaleka ka ce! To ai ko shi kakanka nawa ba ?yalesa na yi ba balle kai da ban haWa ala?ar komai da kai ba, banza da?i?i.."

Ya faWa tare da watsa masa yawu akan fuskarsa, kafin ya shiga kai mashi naushi a tsakiyar cikinsa, jini har ta baki yake amansa, ya dinga kurma ihu yana ambaton Jesus,
Commender james ya ce, "Baka da hankali! ai ko shi jesus din bai ce a aikata zalunci ba, banza dakiki..."

Sai da suka raunata duk wata ga6a ta jikin su, suka haWa masu jini da majina akan fuskokinsu, Jan le6e tuni ya sume, ?an iya da ya kasa tsayuwa akan ?afafunsa aikuwa ya yi taga taga cikin rashin sa'a da rashin sani ya faWa cikin kaskon wutar da ke a bayan shi ya yi zaman yan bori a kanshi, wutar dake ci balala ta kama mazaunansa ya shiga kwarma ihu, raWaWi ta ko'ina a jikin shi, da sauri Owais ya dam?o gaban rigarshi ya fusgo shi daga kan kaskon wutar ya maka shi da ?asa, ya yi saurin janyo wani madaidaicin carpet dake a ?asan hall din ya shiga kakka6e masa wutar da ta kama rigarsa.

Saboda bai son ya mutu yanzu batare da ya gir6i abun da ya shuka ba, tsabar radadi yasa har zawo Wan iya ya saki a cikin gajeran wondon shi, da?yar ya samu ya kashe mashi wutar, nama dai ya soyu (=??)


Fito Owais ya yi,


Nan take sojojin da suka kewaye hall Win suka shigo da igiyoyi a hannunsu, biyu daga cikin su suka WaWWaure su kamar mushen dabbobi gaba Waya sun sume, a haka suka cuccu6esu tare da fucewa da su.


Yanzu mutun Waya ne ya rage su kama wato Jan Wuya da basu san inda ya boye kanshi ba...



Bakomai ne yafi damun Owais ba fa ce rashin ganin su Unaisah da bai yi ba, har sojoji ya tura su dudduba ko'ina na kurkukun su gano su amma har yanzu ba labari, Ya Salam! Daurewa kawai ya ke yi.



Fucewa suka yi da sauri suka nufi Cikin kurkukun, bayan sun raba kansu kaso uku, wasu suka bi straight, wasu sukai dama wasu suka bi hagu..




*JAN WUYA, Alhaji Musa, ?aramin su babban su, Big boss, duk shi kaWai=?%?*



Tun lokacin da Evils suka wurgo shi cikin tafki ya nutse can ciki, kuma nan take ya farfaWo saboda taurin rai irin nasa bayan azabar da ya sha, da yake dai lokacin mutuwarsa bai yi ba shiyasa ya rayu, zuciyar nan tasa ta yi ba?i??irin saboda 6acin rai da fusata, ya ji ba?in cikin da bazai iya misalta shi ba, duk irin izzar dake gare shi wai shine yau Evils suka tu6e ma kaya, suka zane shi da bulala kamar jaki? kamar ba su san shi ba? Ya Ilahi! Ya gaza yarda da komai da ya faru, kamar a mafarki yake jin kan shi, bai ta6a muzanta irin na yau ba, duk da mawuyacin halin da yake a ciki hakan bai saka ya saduda ba, shaiWaniyar zuciyar nan tashi sai tunzura shi take yi akan ya nemo wadanda suka ci amanarshi ya kashe su don ba zai ?yale su ba. Abun ya matukar ?ona masa rai, wutar ba?in cikin dake ci a cikin zuciyarshi sai ?ara ruruwa take yi.



Bakomai ne ya fi karya masa zuciya ba face cin amanarsa da Mark ya yi, duk irin yardar da ya yi da shi, Ko p.a Winsa bai yarda da shi kamar yadda ya yarda da Mark ba, ya yi danasanin sanin shi a rayuwar shi, kuma ya ci alwashin sai ya azabtar da shi, kuma ba zai fasa mummunan kudirin nan nasa ba.


Bai damu da raunatar da jikinsa ya yi ba, cin amanar da aka yi masa yafi radadin raunukan da ke a jikinsa..

Yayin da yake wannan zancen zucin yana a bakin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login