Showing 42001 words to 45000 words out of 321579 words

Chapter 15 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

Deeni? Razak! Baku gane ni ba ku ma?" Ta fada idanunta cike tab da ?walla.

Cikin shesshekar kuka ta ce, "Ba laifinku bane, laifin ubanku ne, Mugu azzalumi, Kun ganshi nan..., Shine ya Wauke ni tsawon shekara ashirin ya raba ni da ku, ya yi maku ?aryar na mutu bayan ina a raye...."

Waro idanunsu waje su ka yi suna kallon fuskarta yayin da ?wa?walwarsu ke ?o?arin tariyo masu wacece ita saboda ta canza musu sosai, tayi tsufan da bazasu iya gane ta ba cikin sauki.

Saboda tsabar tashin hankali, duk da sanyin A.c din dake a falon hakan bai hana baba Obie fitar da gumi ba, jikinshi Ya ji?e sharkaf kamar wanda aka tsamo daga teku, Firgici da tsoro sun mamaye zuciyar shi, duk yabi yasha jinin jikin shi.

Pretending ya yi duk don ya ?ara dagula masu lissafin ?wa?walwar su ya ce, "This can't be Aurora Edward, bazai ta6a yiwuwa ba, matata ta mutu kuma mun shaida mutuwarta, wanda ya mutu baya dawowa sai dai idan Aljana ce ke!"

Ya faWa a tsawace kamar zai doke ta, bata ko kula shi ba ta mayar da dubanta akan ya'yan ta burinta su gane ta saboda hankalinta ya tashi ganin sun kasa yarda cewa ita ce.

"Hateem, Sharafudden nasan ko kowa bai gane ni ba, Ku zaku gane ni..."

Ta faWa tare da tallabo fuskar Hateem da tafukan ta, wata matsananciyar damuwa ce mai tattare da ruWani ta mamaye zuciyar Hateem da Sharufudeen, kokwanto su ke yi akanta, abu Waya da ya yi masu kama dana mahaifiyarsu ajikin ta, shine launin ?wayar idanun ta.

In a broken voice, Hateem yace "Momma... Is that really you I'm seeing? But how is that possible after you died? Ni dai a iya sanina wanda ya mutu baya dawowa ..." Ya faWa yana girgiza kansa.

Bai ?are maganar ba Sharafuddeen ya ce, "Don Allah ki fahimtar damu, kin jefa mu a ruWani! gaba daya mun ruWe, tabbas ba zamu manta da mahaifiyarmu ba, amma taya kika rayu bayan kin mutu? Dan Allah ki fada mana! Mafarkine wannan ko gaske..." Ya faWa fuskarsa sharkaf da hawaye.

Murmushin takaici ta saki tare da juyawa ta dubi baba Obie da ya yi tsaye sototo kamar mutun mutumi.

"Ku tambayesa ina ya kai maku mahaifiyarku tsawon shekaru ashirin bayan ya yi maku ?aryar na mutu, shine ummul aba'isin komai, shine ya azabtar da mahaifiyarku, wuya ce ta sa na yi tsufan da basu kai na shekaru na ba..."

La66ansa na kerma ya ce, "Kada ku yarda da ita! ?arya take gaya maku, Fatalwa ce ba mutun ba ce, dan Allah ku kawar da ita daga cikin gidan nan, ku kira Security officers su fitar da ita, Ku kore ta bana son ganinta" Ya faWa yana nunata da yatsansa dake kerma..

"Don't believe her! I don't want to see her, Crazy ghost, hypocrite, get her out ba mutun bace Aljana ce ku kira sheikh Imam ya yi mata ru?iya zaku tabbatar da abunda nake faWa maku..."

Kamar zararre sai sambatu ya ke yi, duk yabi ya dabarbarce ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.


Murmushin takaici ta sakar mashi, ga wani ?ululun bakin ciki da ya tokare ma?ogwaronta, "Haba Obinna, idan har ni aljana ce to kai kuma bakin shaiWani ne, wannan bawan Allah da kuke gani ba mutumin kirki bane, fasi?i ne mara imani, daga shaidan sai shi, daga shi kuma sai fir'auna a wurin aikata zalunci...."

bata ?are maganar ba suka daka mata tsawar da ta razanar da ita, gaba daya sun ruWar dasu, da ita da baba Obie sun rasa maganar wa zasu Wauka sai dai sun yarda da mahaifinsu fiye da yadda suka yarda da kansu.

Komai dake faruwa akan idanun Chief Owais da ya ?ame a tsaye kamar gunki sam ya kasa motsawa, tsantsar rudanine da fargaba akan fuskarsa.

Dam?ar hannunta baba Obie ya yi ya dinga janta yana faWin, "Zo ki fice ki bar mana Estate, wuce ki tafi, mahaukaciya, makira annamimiya mai son haWa uba da yayansa, ni nasan ma?iya ne suka turo ki don ki yi mini ?azafi..."

Fashewa ta yi da kuka tana kiran sunan Hateem dana Sharafudeen don su kawo mata Wauki.

"A'uzu billahi minasshaiWanir rajim tuf tuf, wa innahu min sulaimanu wa'innahu bismillah! Aniyarki ta biki makira algunguma ba?ar munahika"

Ya faWa yana tottofa mata yawu akan ta, sam sun kasa tsayar da shi, al'amarin ya rikita zukatansu.


Tana kuka haWi da waiwayonsu cikin shesshekar murya tana magana tana mi?a masu hannu,

"Hateem kada ku bari ya fitar dani, Sharafudeen ka taimaka mini, kada ku bari ya ?ara raba ni daku! Na yi kewarku, Wlh ni ce mahaifiyarku Aurora Edward! Your momma, ban mutu ba, ba fatalwa bace ni, Owais Kada ka bari ya kore ni, Ni kaWai ce zan iya fayyace maku komai akan shi, Owais kaima ba ka tuna ni ba kakarka momma? ...." Ta faWa idanunta cike tab da ?walla, tana ta ?o?arin ?wace hannunta daga mugun ru?on da baba Obie ya yi mata sai dai ta kasa saboda babu karfi atare da ita.

Hankalin Pravin Idan yayi dubu toh ya tashi, murnar da yake yi tuni ta koma ciki, ya murtuke fuska, hannayenshi biyu ya Waura a saman kanshi alamar ya shiga uku, ?irjin shi kamar ana luguden ta6are, kafin ka ce me tuni ya haWa uban gumi, jikinshi ya kama makyarkyata kamar wanda farfaWiya ta kama.


Har ya kusa fucewa da ita daga falon Sharafudeen ya yi kukan kura ya watsa da gudu ya nufe su, yana ?arasowa ya bangaje baba Obie gaba daya ya kife ?asa kafin ya Wago Sharafudeen ya dam?o hannun Khala ya juyo da ita suka dawo Falon.

Da sauri Hateem ya nufe su ya kar6e hannun Khala dake acikin na Sharafuddeen ya yi hugging Win ta akan broad chest dinsa, ya ?an?ameta sosai kamar zai mayar da ita cikin cikin shi, wani irin sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta kamar yadda shima ya ji sanyi a ranshi, rungumar da ya yi mata tasa ya ?ara yarda mahaifiyarsu ce saboda wani yanayi da ya tsinci kan shi wanda uwa da Wa kadai ke jin irin shi idan jikinsu ya haWu da na juna.

"Yaya kun yarda da ita? Kun yarda cewa momma ce?" Hajiya saratu ce ta faWa a ruWe

"Ta yaya bazamu yarda da ita ba, koda kowa bazai yarda ba mu mun yarda mahaifiyarmu ce, ni tun lokacin da idanuna suka shiga cikin nata, raina ya bani momma ce..." A cewar Sharafuddeen.

"In hakane taya akai ta rayu bayan ta mutu? kuma mun ga gawarta da idanunmu?" Ta jefa ma su tambayar .

Sharafuddeen ya ce, "Shi yakamata ku tuhuma.." Ya faWa tare da nuna baba Obie

"Saboda na fara kokwanto akan shi! kuma dama shi borin kunya da hauka ake naWe shi, in ba haka ba meyasa zai Waga hankalinshi don kawai ya ganta? Bayan haka a gabanku baba ya juyamin baya ya hana kowa ya yi magana akan tuhumar da Owais ke yi mi ni, wai har ni zai ce in kare kaina agurin Owais!....." Ya faWa yana jifar shi da kallon tuhuma.

Bai ?arasa maganar ba Baba Obie Ya nufo su cike da rashin kuzari, yana fitar da huci kamar mayunwacin zaki ya nufi Khala da Hateem ya rungume, har ya mi?a hannu da niyyar ya dam?o ta, Sharafuddeen ya yi saurin dam?o hannunsa ya jefar da shi gefe Waya baima san sa'adda ya daka mashi tsawa ba, dama da haushinshi a cikin zuciyar shi.


Gabansa ne ya yanke ya faWi jin yadda Sharafudeen Wan cikinsa ya daka masa tsawa kuma ya jefar da hannunsa, hankali a tashe ya furta, "Na shiga uku..!!!"

"Baba, don't dare touch our momma! Don't touch her! Let her talk, Idan har kana da gaskiya meyasa zaka Waga hankali akanta huh? Ka barta ta yi magana mana!" rai abace Sharaudeen ya faWa yana kallon cikin idanun shi.

Zare idanu baba Obie ya yi with pure confusion on his face,

Tsantsar mamaki ya hana su Sir mubarak furta magana sai binsu da idanu su ke yi.

nuna kanshi ya yi da yatsan shi, "Sharafuddeen ni kake yi ma tsawa? Ka na cikin hayyacinka kuwa? Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un.." ya faWa yana dafe kanshi da tafukan hannayensa..

"Baka ga komai ba Obinna...."

Tsohuwar ce ta faWa tare da raba jikinta daga na Hateem ta dubi baba Obie da wani ?as?antaccen kallo mai cike da tsana..

"Dama bana faWa maka ba akwai ranar ?in dillanci? Shin ban fada maka duk min daran daWewa asirinka zai tonu ba? Dama hausawa sun ce rana dubu ta 6arawo rana Waya ta me kaya, yau dubun taka zata cika...."

Girgiza mata kai ya dinga yi idanunsa sun kaWa jawur tamkar ya fasa ihu haka ya ke ji, ya rasa ya zai yi ya dakatar da ita.."

Cikin raunanniyar murya ya furta, "Kada ki yi min haka! Na ro?e ki, kada ki tona mini asiri, Kada ki raba ni da ?a?a na, kada ki raba ni da mutuncina, Ki rufe mini asiri ki agazama rayuwata, ki taimake ni kodan saboda darajar ya'yan mu, In kika fallasa asirina kamar kin fallasa asirin ahalinmu ne, zaki ja mana tozarci a idon duniya...."

Zubewa ya yi akan gwiwowinsa yana ci gaba da girgiza mata kai hadi da marairaice mata fuska don ta tausaya mashi.

Kallo Ya koma sama, kalaman Baba Obie sun Waga hankulansu, sun jefa zuciyoyinsu acikin rudani tunma kafin su ji wani asiri ne nashi da baya son ta tona.

"Lokacin da na dinga ro?onka akan kada ka kashe ni ka barni da raina baka yi hakan ba saboda zuciyarka ta ?e?ashe babu Wigon imani a ranka, zalunci kadai kasa a gaba, ba irin magiyar da ban yi maka ba amma ka toshe kunnuwanka kuma ahaka kake tunanin ni zan rufa maka asiri bayan Allah ya tseratar da ni uhm?"

Ta faWa tana kallonshi da raunatattun idanunta. Ru?e ?afafunta ya yi da hannayenshi ,"Dan Allah ki rufa mun asiri, kiyi min rai, kada ki kashe min rayuwata, na yi maki al?awarin zan shiryu..."

cikin jin ?unar rai ta haWiyi yawu mai Waci tare da kawar da idanunta daga barin kallon shi ta dubi sama hawaye na cigaba da zarya kan kuncinta, ranar da ta daWe tana gargadinsa akan zuwanta, ba irin jan hankalin da bata yi mashi ba amma ya?i ji yanzu wa gari ya waya?


"Dan Allah ki faWa mana dagaske momma ce ke? Dama baki mutu ba kina a raye? Kuma me ya faru dake? Me babanmu ya akaita? Dan Allah ki faWa mana, kun Waga mana hankali, Kun ruWar damu..." Hajiya Saratu ce ta fada fuskarta a yamutse, Sir Mubarak ya ce,"Momma ki faWa mana gaskiya, muna son mu ji taya akai kika rayu bayan kin mutu? Kuma me mahaifinmu ya akaita maki? Sannan wani asiri ne nashi da baya son ki faWa?"

Tsantsar tausayinsu ne ya kamata, saboda tasan in ta faWa su da farin ciki har abada, watakil ma ba?in cikin mahaifin nasu zai yi silar rasa ran wasu daga cikin su.

Amma ya zata yi bata da mafita da ya wuce wannan, saboda alwashine ta daukarwa kanta, Allah ne ya amsa addu'arta shiyasa har ta rayu don ta tona masa asiri don haka bazata butulce ba, mutun azzalumi irin sa bai cancanci a rufa masa asiri ba.

Cikin karyayyar murya tana kuka ta ce, "Ku yi ha?uri! ku yi ha?uri!! ku yi hakuri!!! da abun da zan faWa, nasan abun da ciwo amma ya zaku yi ubanku ne ya ja maku, shine silar komai...."

Ta faWa da tsawa tana kuka jikinta har jijjiga ya ke yi, Chief Owais ya kasa furta kalma, sai rarraba idanunsa ya ke yi akan fuskar Obie da Khala ha?ika sun jefa shi a ruWani.

"MAHAIFINKU OBINNA SHINE ELDER NA GIDAN KURKUKUN ?ADDARA, SHI DIN MUGUN MATSAFI NE, BAIDA IMANI, MUGUNTA DA ZALUNCI YASA A GABA, TUN FIL AZAL, DUKIYARSA BATA HALAL BACE, KUMA SHI BA MUSULMI BANE, ARNE NE, IDAN BAKU SAN KURKUKUN KADDARA BA, ZAN FAYYACE MAKU KOMAI, GIDAN KURKUKUN KADDARA GIDAN MATSAFA NE, YA KAFA SHI TSAWON SHEKARU TALATIN DA DAURIYA, ME AKE AIKATAWA A GIDAN KURKUKUN ?ADDARA? ?ANANUN YARAN DA BASU JI BA BASU GANI BA SUKE KULLEWA A CIKINSHI, BA FUCE BA SHIGE, TUN SUNA JARIRAI SUKE RAINONSU HAR SU GIRMA, ZASU TASO BATARE da addini ba, ba salla ba sallati, sai tsantsagwaran jahilci cike da kansu, basu san wanene mahaliccinsu ba, gaba daya sun tauye masu hakkinsu na rayuwa, abu mafi muni suna azabtar dasu azaba mai radadi, su yi lalata da su, su sha jininsu, su kwanta da gawa, su cire sassan jikin su, kai har jarirai basu bari ba da mata masu ciki suna kwanciya dasu, matasan yan mata da suke tsaka da shan azabar Jinin al'ada a haka suke saduwa dasu duk watan Allah idan ya kama, Ni kaina bazan iya misalta rayukan da suka salwantar ba, Nima ina Waya daga cikin fursinonin kurkukun kaddara, saboda tsautsayi yasa na yi masu le?en asiri nasan sirrinsu shiyasa ya shirya makirci ya dauke ni daga gare ku,....."

Bata ?arasa maganar ba Sir mubarak ya doka mata tsawar da ta yi silar firgicewarta, Yana huci ya ce, "?aryane! Bazai ta6a zama gaskiya ba, kazafi ki ke yi masa, mahaifinmu bazai ta6a iya aikata munanan zunubban nan ba, mahaifinmu mutumin kirki ne, Mai jin tsoron Allah, mutun ne mai zuciyar imani da tausayi, bazai taba aikata abunda kike zarginsa da shi ba...."

Bai ?are maganar ba senate Lateef da ya gama harzuka zuciyarshi a wuya yai kukan kura zai sha?e wuyanta, Sharafuddeen ya yi saurin dakatar da shi ta hanyar dam?e wuyan hannunsa, yana huci ya ce, "Ka sake ni Sharafudeen!! Wannan mahaukaciyar matar ta rasa wa zata yi ma ?azafi sai mahaifinmu? Baka ji munanan kalaman da ta jefe shi da su ba? Wai mahaifinmu ne matsafi? ?an kungiyar asiri???" Ya faWa yana zare idanunsa da suka kaWa jawur.

Cikin jin ?unar rai His excellency Abdul Razak ya girgiza kai yana fitar da numfashi mai Wumi ya ce, "Wlh kodai ku fitar da tsohuwar nan ko kuma in kashe ta a gurin nan, ta ya zaku bar mahaukaciya tana cin zarafin mahaifinmu a gaban idanunmu, wannan ai zancen banza ne, wlh sai munyi shari'a dake dole ki fuskanci hukunci mai tsanani...."

Deen ya amshe, "Ai ga irinta nan! tun farkon shugowarta yakamata a kore ta, ni bansan uban waye ya bata iznin shigowa ciki ba! Ku kuma kun yi tsaye kamar wasu sakarkaru a gabanku ake yi wa mahaifinmu ?azafi, daga gani abokan adawarmu ne suka turota don ta tarwatsa zaman lafiyar mu...." Ya faWa yana nuna su Hateem.

Kalamansu sun cika kunnan baba Obie, wata irin karaya mai haWe da faWuwar gaba ce ta Warsu acikin zuciyarshi dake yi mashi wani irin mahaukacin bugun barazana, wani kallo yake binsu da shi mai wuyar fassaruwa ganin yadda suka ha?ikance akan kazafi ne ake yi masa saboda yardar da su ka yi da shi.

Cikin raunanniyar murya Khala ta ce, "Koda zaku kashe ni bazan fasa faWar gaskiya ba, na yi maku uzuri saboda nasan irin yardar da ku ka yi wa mahaifinku, hakika ya cutar da rayuwarku, ya zalunce ku, tsawon shekaru kuna tare da mugun iri acikin ku batare da kun sani ba, Ya daWe yana munafurtarku...."

Ta Wan dakata tana jan numfashi, sai ?o?arin kai mata bugu suke yi amma Hateem da Sharafudeen sun hana, sai ma suka katangeta ta yadda bazasu iya ta6ata ba, hakan ba ?aramin daWi ya yi mata ba, tana a tsakiyar su taci gaba da magana.

"Dukiyarsa bata halal bace, Haramun ce tsantsa, ya ciyar daku da haram! Ya tufatar daku da haram!! Ya gina ku da haram!!! Mahaifinku mutunne mai neman duniya ido rufe, baidamu da lahirarsa ba, koda ya ke baiyi imani da Allah ba, burinshi ya shahara, darajarsa ta Waukaka duniya tasan da zaman shi, shiyasa ya jefa kanshi cikin halaka da ku kanku saboda kuma bai barku hakanan ba, duk wata nasara da kuka samu, da duk wata Waukaka da kuka samu, sun samo asali ne daga abunda mahaifinku ya ke yi maku, shiyasa baku ta6a faWuwa ba a rayuwarku, ya sanya maku farin jinin da in har kuka shiga mutane sai kun shahara acikin su, haka zalika in kuka ta6a abu zai yi albarka......"

Wannan karon bakinsu ya mutu bawai don sun yarda da maganar ba, sun dai fara wasiwasi acikin zuciyoyin su.

Yanayin fuskokinsu ya nuna tsantsar tashin hankali da damuwa haWi da rudanin al'ajabin maganarta.

Baba Obie dake a zu?unne kan gwiwowinsa ya kasa motsawa ji yake kamar an rufa masa bargon azaba a bayanshi saboda tashin hankalin da ya shiga, da wani ido zai dubesu a wannan ba?ar ranar, gaba daya ya Wimauce ji yake kamar ya ha?a rami ya binne kansa, babban abun takaicin sihirinsa ya ?i tasiri a kanta, ya so tun farko ya dakatar da ita sai dai Allah bai yarda ba, this time around jikinta akwai kariyar ubangiji.

Tsohuwa Khala bata dakata da yin magana ba taci gaba da cewa, "Sau nawa matayenku suna haihuwar ya'ya su zo babu rai a jikinsu ko bayan sun haihu jariran su mutu?" Ta faWa tamkar tana yi masu tambaya,

Ta Waura da cewa, "To waWannan yaran ba mutuwa su ka yi ba, ku tambayi ubanku Obinna ina yaran ku suke! Ta faWa a tsawace tare da nuna shi da yatsan ta.

Tashin hankalin da ba'a saka mashi date!, Wlh al?alamina bazai iya misalta tashin hankalin da suka shiga ba, zuciyarsu ta karaya da ganin yadda ya yi shiru ya kasa kare kanshi daga abunda tsohuwar ke tuhumarsa."

Cikin shesshekar kuka Hajiya Saratu take fadin, "Nashiga Uku! Na bani na lalace! Baba dan Allah ka yi magana! Baba ka ?aryata tsohuwar nan! Baba ka agazamana zuciyarmu ta raunata! al'amarin nan ya fi karfin zukatanmu! Baba mu mun yarda da kai munsan bazaka iya aikata abunda take jefanka da shi ba, wlh kazafi ta ke yi maka, Mahaifinmu ba fasi?i bane, mahaifinmu ba matsafi bane, mahaifinmu bazai taba iya aikata rashin imanin da kike tuhumarsa da shi ba, dan Allah baba ka tashi ka ?aryata tsohuwar nan....!"

Tana cigaba da kuka ta nufe shi ta dafa kafaWunsa tana kokarin mikar da shi tsaye don ya yi magana sai dai ya ?i bata haWin kai, wasu irin narka narkan shatun jijiyoyine suka fito saman fatar goshinsa..

"Baba ka taimaka min, Ka agazama rayuwarmu,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login