Showing 51001 words to 54000 words out of 321579 words

Chapter 18 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

ba, ko magana basa iya yi sai dai suka dinga bin su da raunatattun idanunsu da suka galabaita.



gaba daya gumi ya wanke jikin su kamar babu iska a wurin.



Magiya suka dinga yi masu akan suyi masu magana su fada musu meke faruwa amma babu alamun zasu tanka musu.


Labbansu duk sun faffashe sakamakon cizon su da suka dinga yi cikin fitar hayyaci, sunyi zugudum kamar hotuna, daga wanda ya zabga tagumi da hannayensa biyu, sai wanda ya langwa6e kansa jikin door room din baba Obie, Sir Mubarak ya dage sai tauna farcensa ya ke yi da hakoransa baima san yana yi ba, tsabar damuwa ne da fusatar zuciya ke addabarsa..



"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Na shiga uku! Daddy! Uncles! Meke damunku? Meya saka ku zubar da hawayenku? Baba Ya mutu ne?" Ziyad ne ya faWa arude tare da tallabo fuskar Senate da tafukansa yana kokarin tursasa masa don yayi maganar.



"Dan Allah ku faWa mana abunda ke faruwa? Hankalinmu ya tashi da ganin halin da kuke aciki, pls daddy ka faWa min! Me ya jefa ku a halin da kuke aciki ? Ina baba Ya ke? Me kuke yi a kofar dakin sa, ko dai ya mutu ne?"



Cikin shesshekar murya Captain Yaseer Ya fada tare da dafa kafadun daddynsa da tafukan hannayensa.


"Uncles pls, kuyi mana magana, dan Allah kuce wani abu! Gaba Waya bakwa acikin hayyacin ku, yanayin ku ya nuna kuna acikin mawuyacin hali na damuwa, idanunku sun kumbura alamar kunsha kuka, wai meya faru ne??" Zayn ne ya fada yana rarraba idanunsa akan fuskar Hateem da Sharafudden, kusan atare suka sadda kawunansu ?asa batare da sun tanka ma shi ba!


Zaid Ya ru?o hannayen mai girma Sharafudden acikin nashi cikin raunanniyar murya ya furta, "Mun shiga uku, pls Uncle ku yi mana magana ko hankalinmu ya kwanta, wai meke damunku ne? Gaba Waya kun raunata babu wani mai walwala acikin ku? Idan baba Ya mutu ne ku fada mana..."



Cikin sanyin jiki Justice Ya tallabo fuskar mahaifinsa, "Dad ka yi min bayani pls, meke damunku ne huh? Meya faru? Ni ban taba ganin ku a mawuyacin hali irin na yau ba, dan Allah daddy ka fadamin kada zuciyata ta buga don bazan juri ganinku acikin wannan halin ba.."



ba irin magiyar da basuyi musu ba amma shiru basu tanka musu ba."



hakan ya ?ara jefasu cikin damuwa har ta kaiga sun fashe da kuka, suma ubannin nasu wani sabon kukan ne ya 6alle musu, aka rasa me lallashin wani, suna kuka suma suna kuka yayin da suke fuskantar junansu, Hakika zuciya ta karaya, tayaya zasu yi ma ?a'?anasu bayanin abun da kakan su yake aikatawa? Wani hali zasu shiga idan suka ji? Ya zasuyi da rayuwar su? Yaran da basu san wani abu wai shi tashin hankali a rayuwarsu ba, tun da suka taso nasara da gatanci suka sani basu taba neman wani abu sun rasa ba, wannan ne karo na farko da zasu fara fuskantar mummunar jarabawar rayuwa mai wuyar gaske, amma duk bama wannan ba tunanin da yafi tsaya musu a ?ahon zuciya ya'yansu da suka rayu tsawon shekara da shekaru cikin u?ubar rayuwa har suka mutu basu san su wanene iyayen su ba? Ba don addu'o'in da suke ta nanatawa a cikin zukatansu ba, da tuni zuciyarsu ta daina bugawa saboda depresssion din dake barazanar yi musu illah.


A lokacin baba Obie Ya daWe da yin shiru, shiyasa suka ?ara rikicewa basu san awani hali ya ke a ciki ba yana a raye ko ya kashe kan shi!


_______________________________
'?


"Jazz meke damun ta? Ko ta suma ne uhm? Mom Turai ce ta faWa tana duban shi, yayin da ya ke tsoma mayafin khala da ya cire a cikin bucket mai Wauke da ruwan sanyin daya Webo, A hankali ya ke matsa mata shi a saman kanta da wuyanta har izuwa kafafun ta.



Girgiza mata kai ya yi, "Bata suma ba, but she needs medical attention, da bukatar a yi gaggawar kai ta asibiti..."


Har ta buWe baki zata yi magana kenan, Unexpected suka jiyo sautin koke koke da sallallamin da ake yi..


A sukwane suka mi?e tsaye suna duban hanyar da suke tsammanin daga nan koke koken ke fitowa kafin suyi wani motsi, ?an aikin gidan suka shigo agurguje cike da tashin hankali suke ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Sai faman yarfa hannayensu su ke yi sautin muryoyin su ma da?yar su ke fita saboda tashin hankalin da suke a ciki..


Har suna haWa baki ita da Jazz gurin tambayar su meya faru?



"Wayyo Allah! Inna lillahi! Aunty Saratu! Tana a Wakin Hajjaty rai hannun Allah kwance cikin jini, dan Allah ataimaka kada ta rasa ranta, wlh bamu san meya faru da ita ba, fuskarta duk ta 6aci da raunuka.." Kaitsaye maganganun ?an aikin suka dira acikin kunnuwan kowa dake a bangaren kasantuwar da ?araji suke yin maganar.


Lokaci Waya hankulansu da ya gushe suka dawo jikin su, arude suke nanata sunan Saratu da suka jiyo a cikin kunnuwan su.

Especially twins wadanda tuni sun jima da barin gurin, duk da rashin kuzarin Jikinsu hakan bai hanasu mi?ewa ba gaba dayansu suka baro part din baba Obie tsabar saurin su ?arasa har suna bangaje junan su, kafin su iso falon tuni Jazz da Turai da yan aikin sun nufi Wakin Hajjaty aguje.

Tunkan su karasa ga dakin suka soma jiyo koke kokensu,

Lokacin da suka shiga dakin kusan suman tsaye suka yi, sa'ilin da idanun su suka sauka akan fuskar hajiya Saratu, Turai ce ta kwantar da kanta saman cinyoyinta sai kuka ta ke yi kamar ranta zai fita twins ma kukanne ya balle musu..



Cikin raunanniyar murya Hateem ya furta. "Who's she?" Ya fadi hakanne saboda bai gane fuskar wacece ba, sakamakon jinin da ya wanke fuskarta.

Cikin shesshekar kuka abla tace"Aunty Saratu ce, bamusan me ya faru da ita ba, ni ce Wazu na zo duba jikin hajjaty da bata da lafiya, ina shigowa na taras da mutun kwance a ?asa cikin jini ga glass ya sossoke fuskar ta, wlh na yi zaton hajjaty ce amma dana duba ta dakyau sai nagane aunty Saratu ce saboda launin fatarsu ba Waya ba, na yi mamakin ganinta adakin hajjaty saboda bata ta6a takowa sashen yan aiki ba...."


Ta karasa maganar tana matse kwallar ta, hankalinsu idan ya yi dubu toh ya tashi, abin da ya ruWar dasu shine meya kawota dakin yar aiki? Meya faru da ita?" Wa kuma yayi mata wannan Wanyan aikin? Saboda sun gane buga kanta aka yi a jikin mirror tun da gayanan sunga madubin ya zube ?asa..

"Ina ita wadda ke Wakin??" Zayn ne ya tambaya a fusace fuskarshi sharkaf da hawaye, amsa mashi suka yi da basu ganta ba.

Sharafuddeen bai tsaya bata lokaci ba, ya yi hanzarin matsawa ya sanya hannayenshi biyu ya ciccibi hajiya saratu ya daura akan kafadarsa ya juya a gaggauce ya fuce daga dakin su twins dake ta kuka kamar ransu zai fita gani suke kamar hajjaty ce ta yi mata haka, dama sun tsaneta basu kaunarta, bayin Allah sai bin bayan sharafuddeen suke yi kamar jela.



Sune har bakin Entry Hall, Yana fitowa da ita ya nufi Escorts dinsa dake sintiri agaban motocinsu, tunkan ya karasa ya daka musu tsawa a rude suka dube shi da hannu ya yi masu alamar su buWe mashi mota, a hanzarce suke bude backseat na daya daga cikin motocin su, jiki na bari zayn ya fara shiga ya zauna yana ta kuka, bayan daddy Sharafudden ya shigar da ita cikin motar, zaid ya shiga suka saka ta atsakiyar su.



gaba daya suka kankameta suna cigaba da kuka.'


In weak Voice Prime minister Ya ce, "Twins ku daina kuka, baku ga halin da take a ciki bane? Addu'arku take bukata, kuyi hakuri In sha Allah zata ji sau?i, kuma koma wanene yayi mata aika aikar nan zamu kama sa ne sannan ya karbi hukuncin abun da ya aikata" ya fada yayin da yake datse murfin motar, kalaman shi sun Wan tausasa zuciyar su..


Umarni yaba escort din da zaiyi driving dinsu da ya kai su Asibitin Villa, batare da 6ata lokaci ba escort din ya shiga driver's seat ya zauna tare da yiwa motar key ya ja ta da matsakaicin gudu ya bi titin da zai fitar da shi daga estate din..


Motar su bata kaiga fita daga estate Win ba, sai ga Jazz ya fito kafadarsa dauke da Khala, gaba daya hankulansu suka ?ara tashi ganin ta, sam sun manta da ita saboda gushewar da hankalinsu ya yi, umarni Sharafudeen yaba wani Escort din da ya buWe wata motar, bayan Escort din ya buWe, Sharafudeen ya kar6i khala daga hannun Jazz, a mazaunin baya na motar ya shigar da ita cikin kulawa ya zaunar da ita tare da jingine kanta jikin seat, basu barta ita kadai ba jazz ne ya shiga cikin motar ya zauna daga gefen ta Hajiya Turai ma ta shige ta zauna cike da fargaba, Jazz ya daddafe ta a jikin shi duk da baisanta ba ya ji ajikin shi tana da alaka da baba Obie..'


Akan Idonsu Motar ta fuce daga eatate din tabi bayan motar da aka dauki hajiya Saratu tare da wasu motocin na securities..


Acikin Mota Twins sai magiya suke yi ma mommynsu, akan kada ta mutu ta barsu ta taimaki rayuwarsu, Idan suka rasa ta basu san ina zasu sa ransu ba, kwata kwata bata acikin hayyacin ta, bata san ma wake akanta ba..


Kafin su karasa Villa, Mai girma Sharafudeen ya kira gimbiya malika a waya bayan tayi picking ya sanar da ita game da zuwan su Hajiya Saratu ta ce ai su har sun shirya zasu dawo nan saboda ba?in da suka yi sun tafi.

Ya ce mata ba wannan ba yanzu, Su aje maganar dawowa Estate, so yake ashirya medical team din da zasu duba lafiyarsu kafin su ?araso, Jin wannan maganar ya Waga hankalin ta dama tunda suka fara wayar ta ji muryarsa kamar babu walwala, a ruWe ta ce, "Meke damun ta ne? Ko bata lafiya ne? Amma ba Wazu muka rabu da ita lafiya agurin celebration ba?"



Bata kare maganar ba yace"Eh amma ba ita kadai bace, tana atare da yar'uwar mu, ki yi abunda na ce pls, a tabbatar an duba su yadda ya dace su, zamu yi magana anjima." badan ta so ba, muryarta da damuwa tace, "Toh shikebnan, Allah ya kawo su lafiya, ka kula min da ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????kanka." da ga haka su ka yi sallama.


Gaba dayan su suka koma falo, anan suka zauna kan carpet din da ke atsakiyar kujerun falon, bayin Allah daga wannan sai wannan, kuma ransu ya 6aci da abunda aka yiwa Saratu, sunyi mamaki suna a mawuyacin halin nan a haka aka samu wani mara imanin ya zagaya ta baya yaje ya cutar da ita, damuwarsu ta ?ara ninkuwa.



Har lokacin sun?i sanar da ya'yan nasu meya faru! Sunyi magiyar har sun gaji sunyi shiru sun zubawa sarautar Allah ido.



Yan aikin gidan kuwa bayan da aka tafi da hajiya Saratu, jiki asanyaye suka koma part dinsu, suna taya juna alhinin abun da ya faru da ita, su abunda da ya daure musu kai me ya kawo hajiya Saratu dakin Hajjaty? Bayan basu jituwa ko kaWan! Ina kuma hajjatyn take? Tayaya akai madubin dakinta ya fashe har ya sossoke fuskar Aunty saratu?

Sun rasa wa zasu zarga akan lamarin nan! Sun san da wuya in Hajjaty zata iya yin hakan, Gaba Waya suna zargin wani mummunan abun ne ke faruwa da ahalin gidan cos sun lura ma gaba daya mutanan dake gidan babu kwanciyar hankali atare da su.


Shin Ya labarin Chief Owais? Bawan Allah Tun lokacin da suka daina jiyo kururuwar da baba Obie ke yi jikin shi na 6ari ya zame jiki daga cikin su ya kewaya ta bayan part dinsa koda ya ga Wayar kofar a kulle take, sai ya matsa daga gaban katafariyar glass window din dakin baba Obin dake a bayan, nan ma ya taras da ita a gar?ame ya yi ta kokarin balle glass din cikin shesshekar kuka yake kwala masa kira yana fadin baba ka buWe min kofa, kada ka kashe kanka baba, idan ma kana tunanin mutuwa ce mafita agare ka, to kadaina, kada ka mutu ka bar ni, in ka yi min haka baka yi min adalci ba baba..."



Shiru bai amsa mashi ba, dunkule hannayensa ya yi yasa karfi yai ta dukan glass din duk ya raunata yatsunsa amma windown bata buWe ba saboda quality dinta, dole sai idan ta ciki aka buWe ta, ko aka yi amfani da remote control din ta, da takaici Ya ishe shi ya dinga bubbuga goshinsa jikin glass din dama akwai tsohon rauni a gurin nan take ya fama sa wani azababben ciwon 6arin kai ne ya fara addabarsa, lokaci Waya ya fara ganin biji-biji juwa ta Webesa nan take ya yanke jiki ya faWi ?asa, bai ?ara sanin inda kan shi ya ke ba, bai mutu ba kuma bai suma ba, sai dai bai san inda kan shi ya ke ba, komai dake faruwa a cikin gidan bai sani ba haka zalika babu wanda ya yi tunanin ina ya ke saboda hankalinsu ba a kwance ya ke ba... (>?z?)



___________________________________



Damuwa ce ?arara akan fuskar Unaisah, ta rasa ina zata sa ranta taji dadi, tayi jiran dawowarshi har ta fara gajiya da jiran shi, tana ta kiran layin sa baya picking.



Bayin Allah har sun kammala shiryawa tun da rana da ya ce su shirya zasu yi celebration na birthday dinsa a gida, bayan tafiyar sa Aunty Ummi ta shiga da su home beauty saloon dinsu tayi masu hadadden gyaran gashi da gyaran jiki, after sallar la'asar suka yi wanka, kowaccensu ta Wauki wanka na mutunci, Shi kadai suke jiran dawowarshi, Chefs har sun kawo masu ?aton Cake mai hawa bakwai komai ya kammalu sai dai babu Chief babu alamarsa.


Hakan ya jefa su acikin damuwa, fitowa tayi daga bedroom dinsu jikinta a sanye da fitted gown ta swiss cord lace, gown din tabi shape din jikinta kayan sunyi mata kyau sun fito da kyakkyawar surarta, tana tafiya jikinta na girgiza sautin chunky heels din kafafuwanta ya cika kunnuwansu, kwas! kwas!!


Hannunta Waya ruke da head din kayan yayin da dayan hannun yake a ru?e da wayar ta, idanunta na akan screen din wayar, da take pressing, light make up ne akan fuskarta.


Gyaran gashin da ummi tayi mata fishtail braids ne ya ?ara fito da kyawunta, kitsone masu gwa6i guda biyu wutsiyarsu ta sauko ta gaban kirjinta har kan stomach dinta, ga wani daddan fragrance dake busowa ta jikin ta, fuskarta a yamutse ta nufi cikin falon.


"Unaisah har yanzu bai Waga kiran ba?"


?agowa tayi tare da kallon ummi da tayi maganar, suna a tsaye gaban table din da aka Waura Cake.

Ummi tana sanye da atampa Chiganvy gold riga da skirt sun kama jikin ta, tudun hips dinta ko cup aka Waura sai ya zauna, ta kashe daurin kallabi, Batool kuma kalar kayan Unaisah ne a jikin ta, hatta takalmansu iri Waya, Ummi taso ta bambanta musu hair style din amma ta nace ta ce itama irin na Unaisah take so saboda bata son Unaisah tafi ta kyau, amma fa sunyi kyau su dukan su, sun wanku kamar ya'yan Minister of finance..


Girgiza kai ta yi da damuwa ta ce, "Har yanzu bai Waga kiran ba, ni dai hankalina bai kwanta ba, ina ji araina kamar ba lafiya, saboda bai saba min haka ba, har message na tura mashi bai mayar min da reply ba.." tana magana tana yamutsa fuska..


Ummi ta ce, "Anya lafiya kuwa? a sanina da chief bai sa6a alkawari, amma ko ya akai shiru bai dawo ba, har an kusa fara kiran sallar magrib?"

Ta tambaya da damuwa akan fuskarta, Batool duk tafi su shiga damuwa duk ta yi sukuku da ita..


"Har daddy na yiwa magana yace shima ya kira shi ba sau Waya ba ba sau biyu ba amma bai daga ba, wlh ji nake kamar in bi shi cikin estate din.." ta faWa tana zum6ura ?aramin bakin ta..


Murmushi Ummi ta yi, "Allah ya huci zuciyarki gimbiyar Chief Owais, da girman kujerar ki, mu yi hakuri mu jira shi, may be kafin mu kammala sallar magrib ki ga ya dawo gidan..."



Bubbuga kafafunta ta yi akan floor da dan murmushi akan fuskar ta, alamar ta ji dadin kalaman Ummi, "Haba Aunty Ummi, in har sai lokacin zai dawo ni dai bai kyauta min ba Allah.." Ta faWa tare da goya hannayenta akan kirjin ta.


"Calm down your mind his princess, nasan me kike yi mawa, wato kada kije yin alwala make up Winki ya goge, toh kada ki damu kina da ni, zan canza maki wani make up din ne.."


ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon Batool da ta yi shiru idanunta sun ciko da ?walla, kwata kwata hankalinta ba ya akan su.


"Sis are you okay?" In a cool voice ta ce, "bana jin dadin zuciyata, ji nake kamar wani abu na faruwa da Chief din mu.."

Dafa kafadarta Ummi ta yi, "Na fahimci kun damu sosai, nima na damu da shi, but pls ku kwantar da hankulanku, in sha Allah ba abunda ya faru da shi, zai dawo gida lafiya har ma mu yanka cake atare da shi, wata?il wani uzurin ne ya ruke shi."

murmushi suka Wan saki badan hankalinsu ya kwanta ba..


A fakaice Ummi take satar kallonsu daga ?asa har sama, ta daWe bata ga kyawawan matasan ?an mata irin su ba, tana yaba kyawun su sosai, Allah yayi halitta masha Allah tabarakallahu ahsanul khalikin, A ranta take fada, kamar yadda take mamakin kyawunsu suke burgeta suma haka take burgesu, burinsu suma suyi irin body dinta, especially Unaisah in dai zata kalli Aunty Ummi sai tayi fatan dama ita ke da dirinta.


"Ku matso mu yi hotuna kafin ya karaso" Matsawa su ka yi gefe da gefenta suka tsaya, yayin da cake table din ke agabansu ta saita su da camera wayarta ta fara Waukar su zafafan hotuna style kala kala ta dinga nuna masu yadda za su yi, bayan sun gama ta nuna masu hotunan, koda suka gani ihu suka sanya suna santin su saboda kyawun da su ka yi a pics din..


"Aunty Ummi ki turamin hotunan In turama Mommy da Aunty Aneeleeh su gani.."


Ta faWa tana kallon fuskar Ummi, walwalarta ce ta dauke kamar bata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login