Showing 81001 words to 84000 words out of 321579 words

Chapter 28 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

fashe da kuka na dinga rokonsa akan ya taimaka min da abun da zamu ci, Iyalina bata da lafiya ga ciki a jikinta, tun safe nake bin gidajen masu hali don su taimaka mini amma babu wanda ya kula ni don Allah ya taimake ni kamar yadda Allah ya taimake sa..."

DaWin baki na shiga yi masa, da farko ya Waure min fuska kamar bazai taimaka min ba, sai kuma ya zaro kudi bendir Waya ya bani ya ce ya taimake nine saboda Allah saboda kuma shima ya taba shiga irin halin da nake a ciki.

?in kar6ar kudin na yi nace masa idan ya bani yau wa zai bani gobe? Na nuna masa bawai don na raina abin da ya bani bane sai don bana so zuciyata ta mutu in koma ina bara da maula, nafi son ya taimaka mini da jari mai ?arfi, ko ya sama mini aikin da zan dinga yi har in samu wadatar da zan iya Waukar nauyin iyalina.

Bai kawo komai aransa ba ya ce nayi tunani mai kyau, In bashi number ta zai neme ni idan ya sama min aikin."

Jikina na kerma na curo ?ar karamar wayata da ta ji jiki na mi?a masa, da ya kar6i wayar har jujjuyata yayi ganin yadda ta rakwarkwa6e, bayan ya saka min number ya ce in tafi, na yi masa godiya na nufi gidana.

Bayan kwanaki uku ina ta jiran kiransa shiru shiru har na fara fidda ran zai neme ni, kwatsam a cikin kwana na huWu saiga kiran tsohon ya ce min yana taya ni murna ya sama min hanyar da zan samu jari, na ce Alhamdulillah ya tambayi ina da kudin abun hawa ko kuwa ya zo ya Wauke ni? Na ce mashi zan ranci kudi in zo, ya ce mini a'a yafi so ya zo da kanshi saboda ya ga iyalina"

Da jin hakan sai gabana ya fadi na fara tunanin tayaya zan samu iyalin ?arya wadanda suka jigata? A gurguje nabar gidana na nufi bakin titi, da akwai wasu almajirai da suke bara agurin, mata ce mai jiki tare da ?a'ya guda biyu, da matar na haWa baki bayan na yi mata al?awarin zan biya ta kudi masu yawa in har tayi abun da nake so ta ce mini ta amince.

Bayan nayi shigar basajan da nike yi, na kwashe su a abun hawa ita da yaran nata muka nufi wani kango na ginin da na fara yi.

Anan muka zauna ni da su, kafin ?arasowar shi nabi mutanan dake rayuwa a layin na basu cin hanci saboda koda ya tambaye su dangane damu su faWa mashi sun san mu da kuma halin talaucin da muke a ciki. Haka kuwa aka yi bayan ya ?araso bai kira ni a waya ba saboda wayau sai ya fara tambayar matasan unguwar ina ne gidan Barau matalauci, suka nuna masa kangon suka ce anan muke da zama, kuma kongon ma ba namu bane, wani bawan Allah ne ya bamu shi don mu zauna ganin yadda muke ta garari muna neman matsugunni.

Da jin wannan maganar sai ya ji tausayinmu ya mamaye zuciyarsa, kusan duk wanda ya tambaya amsa Waya ya ke bashi hakan yasa ya yarda da ni.

Bayan ya shigo cikin kangon ya taras damu a zaune kan tabarma, yaran matar suna ta kuka suna fadin baba yunwa muke ji, ita kuma almajirar sai faWa take min tana faWin, "wai ba zaka tashi ka nema mana abun da zamu ci ba? Jiya haka muka wuni ba ci ba sha, ko so kake mu mutu ne?"

Sallamar mutumin ce ta katse mu, dama mun san da zuwanshi da gangan muka nuna kamar bamu lura da ya shigo ba, jiki na 6ari na mi?e na je gaban shi ina kuka na ru?e kafafunsa na yi masa magiya akan ya taimake mu ya dubi halin da muke a ciki, tun jiya rabon mu da abinci, na yi fafutuka amma ban samu komai ba.

Cike da tausayawa ya ke duba na, bayan ya gaisa da iyalin nawa yace in same shi a mota.

Yana fita nabi bayan shi, bayan mun zauna ya ce da ni kamar yadda ya faWamin na samu jari sai dai baisan ko zan iya bin sharuWdan ba, saboda sai an kauce hanya..." na ce mashi koma wani irin aiki ne zan yi, in dai bai sa6a ma mahaliccina ba,

Ya ce min, "baka ji me na ce bane? Dole sai an kauce hanya, in har kana son ka zama attajirin mai kudi cikin kankanin lokaci.." Na ce masa toh ya faWamin inji in zan iya.

Yana murmushi ya ce, "Sadaukarwa ce, in har kana so zaka bada ya'yanka ko jaririn dake a cikin matarka, idan har ka yi hakan ta zaka samu abun da kake so." Hankali a tashe na ce Alhaji bangane me kake nufi ba? Ya'yana fa ka ce, wace irin sadaukarwa ce wannan? me kuma za'a yi da ?a'ya na?"

Kwantar min da hankali yayi tare da cewa ba wani abu za'ayi masu ba, Uban gidansa ne Allah bai basu haihuwa ba, shine yake neman yaran da zai raina a matsayin nasa, In har na bashi ?a'yana zan samu abunda nake so kuma yaran nawa zasu taso cikin wadatar arziki, amma fa in har na bada su, ya zama dole in manta da su kwata kwata, don ba za su taba dawowa gurina ba.

Nuna mashi na yi ban amince ba, ya dinga tausata yana kokarin shawo kaina har dai na ce mashi na amince zan bada jaririn dake a cikin matana in ta sauka.

Nan ya ce min toh zai haWani da ubangidansa don mu yi magana, anan ya kira sa har ya bani muka yi magana, tun daga kan muryarsa na shiga ruWu saboda sai na ji kamar na ta6a jin ta.

Bayan wasu kwanaki ubangidan nasa ya kira ni a waya ya ce in same shi a gidan gonar shi yayi min kwatance.

Kafin in tafi saida na sallami almajiran nan da ?a'yanta na ce su nisanta kansu da garin saboda bana so in jefa rayuwarsu cikin haWari, sai da na haWa musu sha tara na arzi?i kafin tafiyar su.


Bayan dana zo gidan gonar da yayi mini kwatance, cikin shigar basajan da na saba yi, A garden na iske shi zaune kan kujera, ya rufe fuskarsa da takunkumi ya kuma sanya ba?in tabarau a idanunshi.


Hakan ya hana in gane wanene, bayan mun yi musabaha ya ce in zauna, na samu guri na zauna kan kujerar dake fuskantar shi, wani kallo na ga yana bina da shi tun daga ?afafuna har izuwa hular dake a kaina, duk saina sha jinin jikina..

Yace min kada in damu da kallon da yake yi min, na ce masa toh.

"Saura wata nawa matar taka ta sau?a?" ya tambaya, cikin faWuwar gaba na ce masa biyar.

Ya ce, "Toh yanzu kamar nawa kake bu?ata mu fara baka bashi kafin zuwa lokacin da zata sauka.. ?"

Na ce Miliyan Waya..

Mi?a hannu ya yi tare da buWe jakar dake akan table Win gabansa ya zaro bandir bandir na ?an dubu dubu ya ajiye min a gabana, ya ce in Wauka in tafi zasu neme ni.

Na yi masa godiya da fara'ata ta ?arfin hali, bayan ya gargaWeni akan kar in kuskura wani ya ji maganar na ce masa toh kafin na tafi.

Bayan na koma gida, na fara tunanin komawa gidan gonar saboda in yi masu le?en asiri tun da na ga h???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?anya..

A cikin kwanakin matata ta rasa gane kaina, hatta ?a'yana basu samun kulawata, saboda hankalina ba zai kwanta ba in har ban ?arasa aikin dana Waukarwa kaina ba. In ta fara min korafi, sai in ce suyi hakuri su taya ni da addu'a Allah ya bani sa'a akan abun da nasa a gaba, da yake tana da hakuri sai ta ce min toh in sha Allah zasu cigaba da tayani addu'a..

Tsautsayi ne da ?addara ya maida ni gidan gonar nan, Allahne ma ya nufa zan iya gane hanyar komawa saboda ruWun dake akwai ina tafiya ina karanta addu'o'i a cikin zuciyata..

Ban taras da kowa a ?ofar shiga ba hakan ba ?aramin dadi yayi min ba, cikin sanWa na shige ciki kaitsaye, koda na shiga falo ban iske kowa ba, na fara bin Wakunan dake a cikinsa ina le?e ta window nan ma banga kowa ba, ni ne har hawa na ukun gidan gonar still nan ma babu mutane kwata kwata, raina ya bani ko dai babu kowa ne? Wata?il kuma dalili ne ke kawo su gidan gonar, wata kofa na gani kamar wadda zata fitar da mutun bayan gidan, banyi ?asa a gwiwa ba na bi kofar, ina le?awa idona ya sauka akan dattawan dake a zaune kan kujerun shan iska...., Sheikh na shiga rudu sosai saboda ganin fuskokin mutanan dana sani, na ga Wan iya, na ga dattijon arziki da surukinsa ba'indiyan nan, na kuma ga Musa, a raina na ayyana me ya kawo mutumin kirki dattijon arzi?i a gidan gonar nan? Ko dai nayi makuwa ne? Kasa kunne na yi ina sauraron firar da suke yi,

"Kai saura sadaukarwa Waya ta rage maka, kai kuma sadaukarwa biyu ya rage maka, idan har kuka yi zan ?ara maku mu?ami, ta yadda zaku samu ?arfin sihiri a jikin ku da kuma Waukaka ta har abada.." dattijon arzi?ine ya faWa yana nuna surikinsa ba'indiyan nan da Musa.

RuWewa na yi jin abun da ya girgiza tunani na, ganin abun nake kamar a mafarki.

Ban gama dawowa hayyaci na ba na ji ?an Iya ya ce, "Bansan me kuke jira ba, yin ciki ne naku, muna da karuwan da zasu haifa maku ?a'ya ba dole sai ?a'yanku na sunna zaku sadaukar ba, amma idan kuka bada na sunna Win sai kun fi samun ?arfin sihiri..."

Dattijon arziki ya ce, "Na yi magana da abokan huldarmu na kasashen waje, karshen shekarar nan zasu kawo mana yaran mutanan da suka sadaukar, gaba Waya a gidan kurkuku zamu zuba su domin biyan bu?atar kanmu...."

Dafe kai na yi da hannayena, a ruWe na shiga ambaton Inna lillahi Wa'inna Ilaihirraji'un..!

Kwatsam na ji muryar Wan iya ya na fadin, "Na ji ?amshin mutun a kusa damu, ina ji araina akwai wanda ya shigo gidan gonar nan..."

Da jin wannan maganar, na arta aguje na nufi hanyar barin gidan gonar, cikin tashin hankali da fargaba. Sheikh Allah ne ya taimake ni harna samu na ?araso gida..

Ban iya bacci ba saboda zullumi da fargaban kada asirina ya tonu agurinsu su gano ni saboda nasan irin mutanan nan basu da imani indai akan sirrinsu ne zasu iya yin komai koda kuwa kashe mutunne.

Amma fa dattijon arziki ya karya min zuciyata, kwana na yi ina kukan zuci, duk in na tuna yadda mutane suka yarda da shi, kowa nayi masa kallon jagora nagari ashe mutumin banza ne mai fuska biyu..."

Chief Owais da ke sauraron sheikh Imam Malik, damuwa ce ?arara akan fuskarsa, bai san sa'adda ya saukko daga kan sofa ya dawo kan carpet ya zauna tare da dafe kansa dake sara masa.

Dakatawa sheikh Imam yayi idanunsa cike da ?walla ya ce, "Owais, tun bayan da muka yi waya da shi ya sanar dani komai ban ?ara jin Wuriyar shi ba, sa?o na karshe da ya tura min shine. "Sheikh nifa tawa ta ?are asirina ya tonu, sun gane nine nake yi masu le?en asiri, nasan bazasu ?yale ni ba. Don Allah ko bayan ba raina kada ku kyale su, kuyi kokarin dam?a su ga hukuma in ba haka ba zasu cigaba da aikata fasadi ne, nasan abu ne mai wuya saboda manyan mutana ne masu faWa aji a ?asar nan, bakowa ne zai yarda da labarin nan ba, dole sai kun yi takatsantsan gurin tona masu asiri, in ba haka ba zasu iya salwantar da rayuwarku."

Numfasawa sheikh Imam ya yi kafin ya Waura da cewa, "Owais, da na ji shiru bai ?ara tuntu6a naba, kona kira wayarsa baya Wagawa sai hankalina ya tashi, duk wani abokinmu da na tuntuba sai ya ce mini shima ya kwana biyu bai ji daga gare sa ba. Na damu sosai, a karshe na baro Sudan na shigo Nigeria ban nufi ko'ina ba sai gidansa ina zuwa na iske gidan a gar?ame da kwaWo, na tura yaro ya kira min makwabcinsa, bayan ya fito muka gaisa na tambaye shi ina malam Jazuli kwana biyu ban ji duriyarsa ba.."

Makwabcin nasa ya ce, "Ai yau wata Waya kenan babu shi babu ?a'yan shi an neme su an rasa, matarsa ma tuni ta tattara kayanta ta koma gidan iyayenta..." Hankalina ya tashi da jin maganar, ban 6ata lokaci ba na nemo address din gidansu matar tashi na je, bayan nasa anyi min sallama da ita, ta fito muka gaisa na ce mata na ji abin da ya faru meyasa bata sanar damu ba, kuma ina son in san ha?i?anin abun da ya faru. Tana kuka ta ce min wallahi batasan komai da ya faru ba, a daren ranar da abun ya faru bata a gidan, tana a gidan ?anwarta da ta haihu acan ta kwana saida safe ta dawo gidan, ta taras babu kowa daga shi har yaransu biyu, sun mi?a case din gurin ?an sanda amma har yanzu ba wani labari.

Lallashin ta na yi na ce ta yi ha?uri in sha Allah mu ma zamu bada gudummuwar mu gurin nemo su, ta yi min godiya bayan mun yi sallama na baro gidan nasu cike da damuwa.

Owais ban iya ta6uka komai ba saboda bana so nima in jefa rayuwata cikin haWari batare dana cika burin malam Jazuli ba na ganin na tona masu asiri, saboda raina ya bani su ne suka Wauke shi watakil ma sun kashe su, saboda ba irin neman da ba'a yi masu ba amma ba'a gansu ba, har tsawon shekara jami'ai suna bibiyar case Winsu, daga baya ma suka watsar da batunsu.

Ni da yan kungiyar mu, mun yi neman har mun gaji, ban ta6a gigin tunkarar mutanan da ya faWamin sunayensu ba, saboda duniyar nan ta 6aci da marasa gaskiya Owais, kuma suna da karfin da ni bazan iya ja da su ba, babu wanda zai goyi bayana don ko abokanmu dana faWa masu basu yarda da maganar ba nan take suka ?aryata labarin da malam Jazuli ya bani, tun daga nan gwuiwata ta sage amma ban sare ba, sai na fara tunanin ta wace hanya zan shiga jikin waWannan bayin Allahn don in samu hujjojin da zan maka su ga hukuma..

A ?arshe na yanke shawarar dawowa Abuja da zama don in samu kusanci da su, saboda nasan dukansu mazauna Abuja ne, a lokacin bani da iyali. Da taimakon wani abokina mazaunin nan dana tuntu6a na faWa masa zan dawo nan da zama, shi ya taimaka min gurin sama min apartment din nan da nake haya,
bayan na saida wasu kadarorina na tattara yanawa yanawa na baro Jos na dawo Abuja. Ban jima da dawowa ba na fara tunanin ta wace hanya zan samu kusanci da Obinna? saina fara bibiyar mutane ina neman sani akan halayanshi anan nake jin mutane suna yabon shi suna cewa mutunne shi na jama'a, yana da mutunci, ga tausayi da jin ?ai kuma yana da yawan kyauta da sadaka.

Dana bincika saina gano babu masallacin dake a kusa da Obie estate, sai kun baro arean ku ku ke zuwa masallaci, ni kuma dana tashi sena nemi dillallin wani fili dake a kusa da Obie estate, bayan mun yi ciniki da tsada da komai na siye shi, saida kuWina suka ?are gurin gina masallacin. Bayan da ya kammalu na gayyaci yan uwa da abokan arziki don su tayani murnar masallacin da zan buWe, daga cikin wadanda na gayyata harda family Winku, da manyan mutanan da muke ma hidima da ta shafi bangaren addini da sauransu, araina inata zumudin zuwan ranar walimar saboda inga ko wani daga cikin family dinku zai halarta ko kuwa ba zaku zo ba, don nasan mawuyacin abu ne saboda an faWa min ba kowani taro kuke halarta ba.

Da ranar walimar ta zo, dubban jama'a suka hallara a masallacin domin taya ni murna tare da yi min fatan alkhairi, har na fidda rai da zan ga wani daga ahalin ku, sai da aka kusa gama walimar, ba zato ba tsammani sai ga motocin escorts na obie estate suna shigowa cikin masallacin, nan fa mutane suka fara zancen su, wani irin farin ciki ne ya lullu6e ni, dama abokina ya faWa min in har aka gayyace shi taro da wuya yayi fashin zuwa.

Lokacin da escorts suka bubbuWe masu motar, jiki na rawa na ga mutane suna kewaye su, nayi ta mamaki na ce wannan wani irin farin jini ne da Waukaka? Mutane kamar zasu dur?usa ?asa saboda tsabar girmamawar da suke yi mashi kuma daga cikin mutanan harda manyan ?an siyasa na gomnatin dake ci a lokacin da hamshakan yan kasuwa, nima saina bi bayan mutanan, da ?yar na samu aka bani hanya na mi?a masa hannu muka yi musabaha ina ta faman washe baki na gaishe da shi cikin girmamawa, da fara'arsa yake amsa min. Wlh Owais a lokacin ban ta6a ganinsa ido da ido ba, a tv nake ganinsa in ana labarai sai kuma a social media saboda kullum labarin family dinku trending ya ke yi, tun anan zuciyata ta karaya ban san ya akai na ji ya kwanta min arai ba, komai nasan cikin dattako ya ke yin sa, mutum ne wayayye baya ?yamar kowa, ko ma?iyansa burgesu yake yi, wlh har kokwanto na yi a raina na ce anya malam Jazuli ya gano dakyau hada mutumin nan? Ko dai bai gani da kyau ba ne? saboda na ruWe da ganin yadda yake kyautatawa mutane, ban zaci mutun mai daraja irinsa zai iya aikata abun da aka faWa min ba.

A ranar muka haWu kuma duk a ranar muka fara sha?uwa, tare da shi muka ci abincin walimar har muka ta6a fira da shi, shi kanshi saida ya faWa min yayi mamakin yadda ya saki jiki da ni.

Lokacin da aka kira sallah bayan kammala walimar ni na jamu sallar muka yi, bayan mun kammala mutane suka fara watsewa kamar karmu rabu da shi kafin tafiyarsa saida mukayi musayar numbers...

Dakatawa ya Wan yi yana mayar da numfashi, Chief


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login