Showing 21001 words to 24000 words out of 321579 words

Chapter 8 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

ta dauki waya ta kira dr shureim a lokacin duk yana a egypt, cikin sa'a ya daga kiran bayan tayi ma shi ta'aziyar babaynsu da suka rasa ta bashi hakuri tare da lallashin shi, har ya tambaye ta agurin wa taji nan ta labarta ma shi komai, har tace yaya shureim meyasa baka sanar dani ba? bayan haka meyasa da suka matsa maka baka dauki yarinyar ka kaima Aneelerh don ta ruke maka ita ba? Yace mata baiyi tunanin hakan ba, saboda a lokacin baya acikin hayyacin shi komai ya faru, ta kuma tambayar shi meyasa me kira uncle musa ya nemi taimakonsa ba, yace mata ya kira amma baya samun shi, a karshe tace mashi kada ya damu, in sha Allah zata dawo mashi da farin cikin shi, a lokacin bai gane maganar ta ba, har dai su ka yi sallama da juna Sauran bayani game da abun da ya faru zamu ji ne abakin wanda ya dace muji=?M?)_

Gaba Waya suka bita da kallo yayin da take ?arasa saukowa daga kan stairs Win ta nufe su Jikinta na 6ari yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarta.


cikin raunanniyar murya dr shureim ya furta"Aisha dama Kina nan"!

Muryar mutumin da yai silar tarwatsa rayuwarta, tun kallo daya da tayi ma shi tayi saurin kawar da idanunta akan su Benazir.


Anila data gama rudewa tace"Aisha kece dagaske Nake Gani? Aisha dama Kina nan da ranki da lafiyarki baki ta6a tunanin ki waiwaye mu ba? ko awaya baki taba kiran mu ba, ko mun kira bama samunki! kullum layinki a kashe! aisha Kinsan Irin radadin danaji saboda tafiyarki? Laifin me mukayi maki Aisha dayaja har Kika manta damu arayuwarki, kika zabi kiyi nesa damu bayan alkawarin da mukayi ma juna duk runtsi duk wuya zamu kasance atare, Why Aisha? Kinbar mu da zullumin ina kika tafi? Kina araye ko kin mutu? Awani hali kike Ciki...."?

Kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya kwace mata kamar ranta zai fita.

Idanunta akan na Aisha wadda gaba daya ilahirin jikinta rawa ya ke yi kamar mazari, ga hawayen dake yar tseral kan kuncin ta.


Cikin shesshekar Kuka Benazir tace"baki kyauta mana ba Aisha! Kinci amanar amintakar mu, a zatona In matsala ta same ki nice mutun ta farko daya kamata ki fara tuntuba sai bakiyi hakan ba, tsawon shekara goma sha takwas baki waiwaye mu ba, ban ta6a tsammanin akwai wata rana wadda zatazo ki juya mana baya ba, sai gashi tazo Aisha.."!

Kasa karasa maganar tayi saboda zafin da zuciyarta tayi mata ta fashe da kuka, Taj dake ta kallon su duk da baisan me ya faru da su ba, jikin shi yayi sanyi kawas, zuciyarshi ta kwaWaita da son jin labarin Alakar dake a tsakanin su, Ummi tana ?arasowa gaban su Benazir da Anila suka rungumeta kamar zasu mayar da ita cikin su, Jikinta ne yayi sanyi lakwas tausayin junansu ya kamata, they had deeply missed each other, more than words could express cike da sanyin jiki a hankali ta daura hannayenta akan bayansu, suka haWa kawunansu Jikin na juna suna ta kuka babu mai lallashin wani, idanunsu arurrufe sai ruwan hawayen da ke shararowa ta cikin su.


"Aisha, ashe da rabon zan sake ganin ki a rayuwata"? Ya faWa yana kallonta har time din bata raba jikinta daga nasu Benazir ba, tsawon mintuna kafin a hankali suka raba jikinsu daga na Juna.


Komai daya faru arayuwarta take tunawa, gani take kamar a yanzu komai ke faruwa, Kallon kallo suke jefawa Junansu tsakaninta da Anila da Benazir, sunyi mamakin haduwar bazatan da sukayi.

Taj dai Ya rasa gane takan maganganunsu, duk yabi ya rude sai binsu da kallo yakeyi ..


Dr shureim duk ya Sha jinin jikin shi ganin kamar bata son kallon shi, fargabansa kada ace har yanzu bata yafe masa ba.

Lokacin da Idanunsu suka shiga cikin na juna, wani irin yanayi suka shiga mai wuyar fassaruwa, tayi mamakin manyantakarsa, ba kamar yadda ta tafi ta barshi ba, Ya ?ara girma ya kuma ?ara kyau, su ma sunyi mamakin Sauyawar da Aisha tayi, ta zama babbar mace, dirin jikin nan nata yana nan ya ma kara ninka na da.

Dakyar ya iya furta"Aisha, na gaza yarda cewa kece nake gani, dan Allah ki yi min magana ko na gasgata kaina" Ya faWa idanunsa cike tab da kwalla.


"Nice ya Shureim..." bai jira ta karasa maganar ba, ya furta "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! ya ambaci hakan Yafi sau a kirga kafin ya zube kan gwiwowinsa tare da daura goshinsa kasa yayi sujudusshukur cikin harshen larabci yake yiwa Allah kirari tare da hamdala saboda bayyana masa Aisha da yayi,.Lamarinsu Ya daurewa Taj kai Ya rasa gane meke faruwa, sun bar shi a duhu.

Mikewa yayi ya mayar da duban sa agare ta, Cikin karyayyar murya dr shureim Yace"ba irin neman da banyi maki ba, Allah bai nufa zan ganki ba, har yau bandaina kallon hutunanki ba, kuma har yau bandaina jaraba kiran layin wayarki ba don inji ko zai shiga amma ban ta6a samun ki ba Aisha, Kin manta damu, amma ni ban manta dake ba, You're always in my nightly prayers"

Lumshe Idanunta tayi tare da bude su A hankali kan fuskar shi, Ji yake kamar yayi hugging din ta ko ya samun sassauci nadaga abunda Zuciyarshi ke ji a game da ita, Sam sun kasa Daina kallon juna, ita kadai tasan me take ji

"Dan Allah Aisha ki bude baki kiyi magana ko munji sanyi a cikin ranmu" Aneelarh ce ta fada tana share kwalla.

Numfasawa tayi kafin ta furta"Ya shureim Where's my baby, ina Fatima Batool dina? Has she grown up? Is she attending school? Have you told her about me? Does she know about me?"

Gabansu ne Ya faWi rass! gaba daya suka sha jinin jikinsu, Da jin abunda tace sun fahimci bata su take ba, Yar da ta bari itace aranta.

Sunkuyar da kanshi yai kasa sam Ya kasa bude baki Ya furta kalma saboda fargaban halin da zata shiga! Hankalinta ne Ya tashi jin yayi shiru bai furta mata kalma ba.

"Ya shureim kayi shiru bakace komai ba? Inason ganin ta fiye da komai na duniyar nan! Nasan yanzu ta girma, a lissafina zata kai shekara goma sha takwas...."

bata ?are maganar ba, ganin hawaye na shararowa kan kuncinsa, aruWe ta dubi su Benazir daga yanayin fuskarsu ta fahimci wani abu ya faru.

"Benazir, Ina fatima na? Nasan kin kula min da ita, saboda na yarda dake, nasan ba zaki taba bari jinina ya wulakanta ba, dan Allah ki fada min ina take? Inason naganta! Ku kai ni gurin ta! Sunkuyar dakai kasa Benazir tayi, idanunta cike tab da kwalla.


Hankalin Ummi ba karamun tashi yai ba, hannayen Anila ta ruko a cikin nata..


"Anila, nasan ba zakiyi min karya ba, pls ina babyna dana barma ya shureim? Keda Benazir wanene Ya shayar min da ita uhm? Waye ya raine ta har ta girma? Na yarda daku nasan ?ata tana samun kulawa a gurin ku, Dan Allah ku fada min tana ina"?

Kamar mai faman da tabin hankali, sam babu nutsuwa atare da ita, Yar ta kawai take son gani.

Gaba daya maganganun Aisha sun ruWa Taj, sai binsu yakeyi da kallo daya bayan Waya, ya rasa gane inda suka dosa.

Dakyar ya iya furta"pls ku zauna, sai kuyi magana atsanake! Kukan Ya isa Haka, bana so inganku a cikin damuwa, duk da bansan meya hada ku ba"


"Daddyn Angel, kace suyi min magana Ina babyna take? Sunyi banza sun kyale ni suna ji ina magana"!

Tausayin ta ne ya kama Taj, yace"dan Allah ku fada mata Ina babynta ta ke"!

In a cool voice shureim yace"kiyi hakuri Aisha, fatima ta koma ga mahaliccinta tun bayan da kika bani ita, badajimawa ba ta rasu....."

kasa ?arasa maganar yayi ganin yadda ta dafe kanta da tafukan hannayenta labbanta na kerma take ambaton Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un..


"Kiyi hakuri Aisha, wlh Yaya shureim yayi iyakar bakin kokarinsa gurin ganin ya ruke amanar da kika bashi, amma Allah bai nufa Batool zatai zawaicin kwana ba..."

Benazir bata ?arasa maganar ba, Aisha ta soma ja da baya tana girgiza kanta, wani irin kuncine Ya mamaye zuciyarta, Taji zafin mutuwar yarinyar data kwalla fa rai akai, tayi azan ta girma har ta zama budurwa ashe ma ta rasu.

"Pls Aisha, Ki tsaya zamuyi maki bayani, pls, kiyi hakuri ki jure, mu ma munji zafin mutuwar ta, ba yadda zamuyi ne Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan.."

Aneelerh da ta dauko maganar, bata kaiga dire ta ba, Aisha ta juya da gudu tana kuka kamar zatayi tuntube yayin da take taka stairs, cikin sauri suka bi bayanta sai dai kafin su karasa tuni ta shige daki ta kuma datse ?ofar.


*Daga Al?alamin Boss Bature=?%?
'?*





*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*=?%?=؋?=؞? &?=ؔ?=؞?>???





~___________________________________~



A bakin door room dinta suka tsaya, fuskokinsu Wauke da damuwa.

"Aisha meyasa baki tuntube ni ba a lokacin da abun ya faru? saboda laifin ya shureim ya shafe ni? mun yi zaton kina a Sudan ashe kina a gida, da ace kin sanar dani ke kinsani ni me iya tsaya maki ce, wlh zan tayaki faWa ne don ganin na kwatar maki hakkin ki, amma bansan komai ba, sai dai na ji labari bayan na dawo gida, abun da yafi ?ona min rai tafiyar da ki ka yi batare da kin neme ni ba, kuma baki yi tunanin kije gidan su Anila ba......"

da?yar Benazir ta ?are maganar tana jan numfashi saboda Zuciyarta dake tafarfasa.

Idanunta na akan door room din Aisha, suna jiyo shesshekar kukan ta daga cikin dakin.


"Lokacin da naji abun da ya faru tsakanin ki da ya shureim da kuma kazafin da akayi maki, Har jinya nayi gadon asibiti saboda ba?in cikin da na ji, wallahi Allah shine shaida ta, nayi bakin cikin da bazai misaltu ba, Na ji zafin hukuncin da baba Imam ya yanke maki cikin fushi batare da ya yi bincike ba, mu shaida ne akan ki Aisha sannan mu shaida ne akan Yaya Shureim abun da ya faru a tsakanin ku sharrin shaidan"


Aneelerh ta Waura da cewa,"Ni kaina sai dai naga sakon ki, har kiran ki na yi ba ki yi picking ba, har messages na tura maki akan ki faWa min ina kike ko ki zo gidanmu amma babu amsa, Aisha meyasa ki ka zabi ki tafi ki bar mu? Bayan kinsan irin kaunar da muke yi maki, ko bayan tafiyarki bamu manta dake ba, a Kullum muna cikin damuwar rashin ki, tunanin mu ina kike? Kina raye ko kin mutu? Meke faruwa a cikin rayuwar ki.... "

Aneelerh bata ?arasa maganarta ba, Dr Shureim ya katse ta, cikin sanyayyar muryarsa mai tattare da rauni ya ce,"Pls Aisha, mu manta da abunda ya wuce, ki yafe mini, Ki yi hakuri Aisha, dan Allah ki fito mu yi magana, gaba Waya Wokin ganinki mu ke yi"

Babu alamun zata tanka masu.

"Pls Ku dawo ku zauna mana, indai Ummi ce tana a gidan nan, duk da bansan meya faru a tsakaninku ba amma na tausaya maku, in har kuka bamu hadin kai in sha Allah zamu yi kokarin sasanta ku da ita"

Taj ne ya yi maganar daga inda yake a zaune, Jikin su asanyaye suka baro kofar dakin Ummi ba don sun so ba, suka koma falo kowannan su ya zauna kan Sofa, kwata kwata babu walwala akan fuskokinsu, Idanunsu sun kaWa jawur saboda kukan da suka sha, babu mai magana a cikinsu kowa da abunda yake sa?awa a cikin Zuciyar shi.

Taj dake fuskantarsu, A tsanake ya ke nazarin yanayin su sam ya kasa dauke ido daga kallon su.

"Pls ina son insan meye ala?arku da Aisha ne? A nan take zaune?"

Murmushi Taj ya Wan yi tare da kallon Dr Shureim da ya yi maganar.


A tsanake Taj ya zayyana masu alakar dake a tsakanin su da Aisha, tun daga kan aikin da U.s armies suka saka ta, ya ?ara da cewa,"Tamkar uwa take a gurinsu, tana kula da su sosai..."

Ajiyar zuciya suka sauke gaba daya hankalin su ya kwanta da jin a nan take da zama don basu son su kara rabuwa da ita.

A bangaren Ummi bayan data shige daki ta yi locking door din, tana kuka ta fada kan gadon ta, Batool dake a cikin toilet tana jiyo shesshekar kukanta ta fito hankalinta atashe ta haye kan gadon tana tattaba bayanta, "Aunty Ummina! Meke damunki? Meyasa ki ke kuka? Waya 6ata maki rai!"

Kwata kwata Ummi bata saurare ta ba, hakan yasa ta fashe da kuka itama tana fadin, "Dan Allah aunty Ummi ki daina kuka, bana so! Ki faWa min meke damun ki?"

dakyar ta iya furta,"Bana jin dadin Zuciyata, zafi take yi mini! Babe na rasa Fatima na, I've lost my Batool ta mutu, na yi babban rashi! Baki ji radadin da nake ji ba..."

sambatu ta dinga yi mata, Batool data gama ruWewa ta kasa gane inda maganganun ta suka dosa.

"Aunty Ummi, ban mutu ba, Ina a raye, ba ga ni a kusa dake ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ba?" ta faWi hakanne saboda ta yi zaton ita Batool din take nufi.

Tana kokarin tallabo fuskar Ummi da tafukanta don ta mi?ar da ita zaune saboda karfin hali irin nata..

Ba ta yi aune ba, Ummi ta janyota kan chest Winta ta rungumeta sosai, duk don ta samu relief na radadin da take ji, damuwace ta mamaye zuciyar Batool lokacin da fatar jikinta ta haWu data Aunty Umminsu, saboda zafin da jikinta ya Wauka har a jikinta tana jin shi.

RuWewa ta yi cike da tashin hankali take fadin,"Baki da lafiya Aunty Ummi, you're burning up, in wani abu ke damunki ki fada min zan taimaka maki har ki samu sauki.. "

ta faWa tana ?o?arin ?wace kanta daga rukon da Ummi ta yi mata don ta samu damar zuwa ta faWa ma daddy Taj da Unaisah halin da take aciki sai dai sam Ummi ta?i bari ta motsa.

Tunawa tayi da addu'a, cikin sauri ta fara karanta yan addu'o'in da ta iya a cikin zuciyarta ta tottafa mata saman wuyanta.


Kafin Ta Waura hannayenta biyu akan bayanta cikin sigar lallashi ta ke Wan bubbuga bayanta kamar ta samu karamar yarinya.


Ji ta yi inama ace Batool ce Wiyarta, Murnar da za ta yi ba zata misaltu ba, tana son Batool sai dai ita bata fito daga mahaifarta ba, tasan duk mun daran daWewa, wata rana Batool zata ga iyayenta ne.

Cusa yatsun hannayen ta ta yi acikin sumar kan Batool, yayin da zuciyarta ke tariyo mata fuskar babynta, bazata taba mantawa da suffarta ba, tana ji aranta tabbas da ace tana a raye kuma ta girma, ba abun da zai hana su yi kama da Batool saboda kamanninta da Dr Shureim, ta dade tana ganin kamanceceniyar su sai yau ta ?ara tabbatar da hasashen ta.

"Aunty Ummi da sauki?"
Cikin disasshiyar murya ta furta,"Ki cigaba da yi min addu'a, Allah yaye min abunda ke damuna" Da sauri ta amsa mata da toh .


Time da aka fara kiran sallar la'asar, Taj yace ma su Anila su shiga daki su yi sallah, bayan ya nuna masu Waya daga cikin bedroom dinsu Sajeed suka tashi suka shiga, Dr Shureim ya ce ya tashi su tafi masallaci, sam ya ma manta da ?afarsa dake ciwo har ya yunkura zai mike kafar ta fara yi masa zogi ba arzi?i ya koma yana nishi, anan Dr shureim ya fahimci baida lafiyar ?afa har ya tambayi meke damunshi ne? ya ce mashi ya samu rauni ne a cinyar sa ta dama amma da sau?i, cikin nuna tausayawa Dr shureim ya yi masa sannu da jiki, har ya ce in bazai iya zuwa masallacin ba ya yi zaman shi tun da lalurace, Taj yace ma shi kar ya damu, zai iya zuwa ai yana da wheelchair, ya faWa tare da kai hannu Ya janyo kan kujerar sa da ya 6oye tsakankanin Sofas, ya janyota ta dawo ta gaban shi, ya yi ta ?o?arin mi?ewa yana kasawa har saida Dr. Shureim Ya taimaka mashi ya zauna a akanta, tukunna suka tafi.


__________________________________
'?

Tana a kwance tsakiyar gadonsu, ta ?urawa ceilling idanunta da suka kaWa jawur, hawayen da suka cika idanunta a hankali suke gangarowa kan kuncinta, bakomai take tariyowa ba face fuskar Benazir, wai dama itace mahaifiyarta da ta yi watsi da ita? Tana yi mata kallon mutuniyar kirki ashe ba haka bane ta yaudari kanta, abin da yafi ?ona mata rai, jinyar ta da ta yi, ta bata abinci a baki, ta yi hugging dinta har ma ta sumbace ta saboda kaunar da ta ke yi mata bisa rashin sanin wacece ita, but now that she knew the truth, she hated her more than anything in the world, abun da yafi tsaya mata a rai meyasa ta gudu tabarta bayan ta jefar da ita cikin kwamin wanka? In bata sonta meyasa bata kashe ta ba tun lokacin da ta haife ta, Laifin me ta yi mata da yaja har ta tsane ta?

Tabbas tana son ta tunkareta gaba da gaba don taji amsar tambayoyin ta.. ranta yakai ma?ura a gurin 6aci, sai faman yin juyi ta ke yi akan gadon kamar mai fama da ciwon mara.

_______________________________ '?


Around ?arfe biyar na marece, motar Chief ta kunno kai cikin main gate, bayan driver dinsa ya tsayar da motar a parking space cikin hanzari Waya daga cikin security Officers din da ke sintiri yai hanzarin zuwa gaban car door ya bude masa motar, fitowa ya yi daga ciki jikinshi sanye da Suit.

With respect Security Officers din suka sara mashi, har zai juya muryar driver dinsa ya katse shi

"Sir, should I bring in the suitcases?" He nodded, then turned away, ya nufi falo.

Cikin sauri SA Win ya buWe tan?ameman boot din motar Chief, ya soma fiddo wasu hadaddun akwatina, guda biyu bayan ya gama ya rufe boot din, ya ru?o handles dinsu ya bi bayan Chief da su.

Chief bai taras da kowa a falon ba, Kaitsaye Ya nufi Upstairs saboda a gajiye ya dawo he needs some rest, duk da yafi bukatar ya gana da su.

Bayan shigar shi dakin, SA din Ya shigo mashi da akwatinnan ya ajiye su kafin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login