Showing 39001 words to 42000 words out of 321579 words

Chapter 14 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

, cike da rudu suke kallon su..


"Dad.. let go of arm" yana huci ya fada sharufudeen Yace"bazan saki ba Owais, kayi duk abun da za ka yi..."


"meke faru ne? Yaya sharafuddeen? Owais! Me ya hada ku ne"?


Hajiya saratu ce ta yi maganar, bai ko kula ta ba, ya nufi baba Obie da ya gaza mi?ewa agaban shi Ya wurgar da chief owais, gaba daya ya tafi zai kife ?asa baba Obie yayi hanzarin ruko kafadunshi Ya janyo shi ya dawo kan laps dinsa.

Yana haki Yace"gayanan baba, ka tambayesa Uban me nayi masa! watakil kai ya iya faWa maka"


ya faWa yana nuna Owais da yatsan sa, Kafin Ya dubi yan uwansa cikin bacin rai yaci gaba da cewa"Owais Ya Waura min karan tsana, yau wata Waya kenan, rabon da in yi bacci cikin kwanciyar hankali saboda shi, gaba ya ke yi da ni! ya juya min baya, yana zargina akan laifin da ban aikata ba, ba yadda banyi da shi ba akan ya fadamin me nayi masa amma yaki ya faWa...."

Daura hannu biyu hajiya saratu tayi akanta..

Uncles dinsa gaba daya sun rude da jin abunda ke faruwa tsakanin Owais da mahaifin sa.

Cikin sanyin murya Baba Yace"meyasa baka fadamin ba tun lokacin daya juya maka baya"?



"Saboda bana so na daga maku hankali, shiyasa nabar abun araina, yau ma dana fada maku naga abun nashi ya fara wuce gona da iri, nema yake ya daura min hawan jini, Baba Hakurina ya kare, Owais Ya kona min rai" ya fada idanunsa cike tab da kwalla.



Gaba daya basu ji dadin abun da Owais ya yi masa ba.


Senate lateef Yace'baka kyauta ba, owais, ka bani mamaki, ina hankalin ka ya ke? Da har ka bari mahaifinka Yana kwana da fushinka acikin zuciyar shi"?

Ya faWa yana kallon chief wanda har lokacin bai Wago ba, tunda Baba Obie ya daura kanshi asaman laps dinsa.



"Owais, ka tashi kayi mana bayani, wani laifi ne kake tuhumar mahaifin ka da shi? " His excellency abdul razak ne yayi maganar..



His excellency deen daya gama fusata da kakkausar murya yace"ba kaji ana magana bane? Ka tashi ka fada mana meya hada ka da shi"!


Cikin sanyin murya Hateem Yace"pls, Kubi shi a hankali, "

ya fada tare da kallon Owais"My son, pls, ka tashi kayi mana bayani, in sha Allah zamu fahimce ka,"



Pravin da ke ?o?arin shigowa falon har zai saci hanya ya nufi dakin hajjaty ganin abunda ke faruwa yasa shi cin burki Ya karya kwana ya nufi gurin su ya tsaya tare da ruke qugun shi da hannu daya ya kasa kunne Yana sauraron maganganun su.


A fusace Owais Ya mi?e tare da juyawa ya nufi daddynsa gadan gadan Kamar zai dokesa, lamarin ya daure masu kai owais bai taba basu mamaki irin na yau ba, har sun fara kokwanton anya ba Aljanu ba ne a jikin shi.



Hannu yasa Ya daki kirjin shi yana faman fitar da hucin bacin rai idanunsa sun kaWa jawur tamkar an watsa barkono a cikin su, wlh a lokacin Sharafuddeen Yasha jinin jikin shi saboda bai taba ganin owais acikin bacin rai irin na yau ba, Batare da jin shakkarshi ba ya fuskance shi gaba da gaba.

Da farko yayi zaton Dukanshi zaiyi, ganin yadda Ya tsaya a gabansa Yana huci.

Gaba daya kawunnansa sun zubawa sarautar Allah ido, suna jira su ga iya gudun ruwan shi.

Dakyar ya haWiyi ?ululun bakin cikin daya tokare Zuciyar shi..



Sautin muryarsa dakyar yake fita"ka za6i in tona maka asiri agaban su"?



Ya jefa mashi tambayar, muryar sharafuddeen tamkar zai fashe da kuka Yace"Sai me owais? Ka fada masu suji, wlh da Allah na dogara, ni nasan ban aikata komai ba..."



GyaWa kai Chief Owais yayi tare da cewa"kana Waya daga Cikin Elders na gidan KURKUKUN ?ADDARAW'...."


AruWe Sharafuddeen yace"bangane me kake nufi ba Owais, su wanene Elders? What Prison of Destiny are you talking about"?


Kallon kallo Uncles dinsa suka fara jefawa Junansu gaba daya sun rude da jin abunda Owais Ya faWa! Su kansu sun kosa suji su wanene Elders? Kuma wani gidan kurkukun kaddara ne ya ke magana akansa?


Hateem har ya buWe baki zaiyi magana baba obie ya dakatar da shi ta hanyar Waga mashi hannu"kabarsu suyi magana atsakanin su, kada wanda ya sa masu baki"! ya umarta, batare daya motsa daga kan kujerar da ya ke ba.



Wani makirin murmushi Pravin ya saki tare da cizon leben shi saboda dadin da yaji.



"ka riga da kasan me nake magana akai, ina da tarin hujjoji akanka, kawai ka amsa min tambayata, Idan har baso kake In fallasa asirinka agaban su ba..."

bawan Allah Sharafudden Ya rasa Ina zai tsoma ranshi yaji dadi, murmushin takaici ya saki, tare da kai hannu Ya dam?i kwalar Chief yana huci yace"ka dade baka tona min asirin ba dan ubanka! ka fada kowa yaji Owais..."

"Haba yaya Sharafudeen pls Owais.."

Hajiya saratu da ta Wauko maganar, bata kaiga dire ta ba, baba obie Ya daka mata tsawa tuni taja baki tayi shiru, da rudu take duban baban nasu ta razana ba kadan ba.



Kasa hakuri Hateem yayi don bazai juri kallon Dan uwansa Da dansa a yanayi irin wannan ba, Nufarsu yayi da niyar ya raba su, bai kai ga isa ba Baba Obie Ya ambaci sunan shi da kakkausar murya"Hateem!"

fuskarshi dauke da damuwa yace"baba pls kada ka hana ni! Bazan iya jure kallon dan uwana ahali irin wannan ba, Wan sa fa ne, wannan ba abune da zamuja baki muyi shiru ba muna kallon uba da Wa suna faWa atsakanin su.."

fuskar baba Obie adaure Ya nuna masa sofa"ka koma ka zauna, Umarni nake baka"! Badan yaso ba ya nufi sofa din daya nuna masa ya zauna ransa abace.


Hajiya saratu data gama hasala juyawa tayi rai abace ta nufi part dinta don bazata juri kallon abunda ke faruwa ba.

"Ba zaka fada ba"? ya fada batare daya saki kwallar rigar shi ba..

Yaso Ya rufa mashi asiri saboda koba komai mahaifinsa ne shi, amma ganin yadda ya matsa ma shi akan ya fada ne yasa shi ya zuciya har baisan sa'adda Ya fara gaya masu irin miyagun ayyukan da Elders suke aikatawa..

Lokaci Waya yanayin fuskokinsu Ya canza zuwa tsantsar tashin hankali da rudani mara maisaltuwa hadi da tsantsar al'ajabi.

bai karasa maganar ba, Sakamakon Tsawar Da Hateem Ya doka masa, tamkar zai fasa dodon kunnansa.

wannan karon bai saurari baba Obie ba ya mike cikin fushi Ya nufi Owais yana fadin

"zaka tabka kuskuren da zakayi danasani arayuwarka! Idan ma zarginsa kakeyi to ka daina, Ka sake bincike akan wadanda kake zargi, amma mahaifinka baya daya daga cikinsu, sai dai idan kazafi aka yi masa...."

girgiza kai Chief yayi hawayen da suka taru acikin idanunsa tuni sun fara sauka kan kuncinsa.

"Uncle Ba zarginsa nakeyi ba, tabbaci nake da shi, Yana daya daga cikin Elders, saboda shine mutumin da ya janye ni daga fagen fama, Ya jefani acikin daki don kada a cutar dani, bayan haka aranar da zamuje kai farmaki, saida ya kira ni a resting home dinsa, Ya gargadeni akan kada inje kai farmakin, ashe ya saka min maganin bacci mai hadarin gaske acikin coffee din da ya bani nasha...." a takaice ya fayyace masu dalilan da sukasa ya ke zarginsa.

Maganganun Owais sun so suyi tasiri a cikin zuciyoyin su, har sun fara jifar sharafudeen da kallon tuhuma.


Dafe kai sharafuddeen yayi da tafin hannunsa, wani irin kululun bakin cikine ya tokare makoshinsa, sam ya kasa magana, dakyar yake iya furta Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..

"Baba dan Allah kasa baki a maganar nan! Kai kadaine zaka iya tsawatar masa..."

His excellency deen ne ya fada yana kallon Baba Obie, wani abun daure kai, kwata kwata fuskarsa babu alamun damuwa.

"Me ku keso ince? Sharafuddeen shi yakamata ya kare kansa agurin Owais, Ni banga laifin Owais ba, kubar yaro yayi aikinsa, ko kun manta cewa shi jami'en bincike ne"?


Cike da rudani suke kallon baba Obie, jin abunda yace, sun fahimci shi ko ajikin shi bai damu ba,



"Ba ku kai shi son mahaifin shi ba, Hakanan dai owais bazai tuhumi mahaifinsa batare da yana da kwakkwarar hujja akan shi ba, kunsan dai ba zai yi maku karya ba....."


Bai kare maganar ba, sharafudeen Ya katse shi, Cikin raunanniyar murya yace"baba, da bakin ka kake fadan hakan? Ka yarda da maganar owais, kaima kana zargina? Baba kaifa mahaifina ne kafi kowa sanin halina, kasan abunda zan iya aikatawa da wanda bazan iya aikatawa ba, wlh banji zafin kazafin da owais yayi min ba, kamar yadda naji zafin maganar ka..."

dakatar dashi baba Obie yayi ta hanyar Waga mashi hannu"Ni bance ina goyon bayan Owais ba, kuma bana goyon bayanka saboda bansan wanene mai gaskiya acikin ku ba, amma in har zaka iya kare kanka agaban yan uwanka nayi alkawarin zan dauki mataki akan Owais, In kuma ka gaza yin hakan hukuma zatayi aiki akanka, donni bazan bari ka zubarmin da mutuncina ba...."

juwace ta kusa dibar Hateem da sauri Ya nemi sofa ya zauna tare da dafe kanshi dake sarah mashi.

Sir mubarak sam Ya kasa magana, saboda yana da fusatacciyar zuciya in har ya bude baki ran kowa zai 6aci ne.

Sun rasa wa zasu goyama baya a cikin su? owais da baba Obie sun haifar masu da kokwanto akan sharafuddeen, aganinsu son owais ne ya rufe mashi idanun shi shiyasa ya goyi bayan shi.

Munafuki Pravin sai ya fakaici idon mutane yake sakin makirin murmushin nan nashi, Ji yake kamar ya zuba ruwa kasa Yasha saboda farin cikin sabanin da owais ya samu da mahaifinsa dama yajima yana jin haushin Owais..

Fuskar Sharafudeen amarairaice ya dubi Yan uwansa..



"Kuma Kuna zargina akan abunda owais ke tuhuma ta"?


Shirun da su ka yi ne yasa shi tunanin suma sun goyi bayan Owais da baba Obie, zubewa yayi kasa kan gwiwowin sa, hawaye suka wanke fuskarsa, ga wani matsanancin ciwon kai da yake ji, zuciyarshi ta karaya.

"ba mu zargin ka, saboda mu shaida ne akan ka, mun san wanene dan uwan mu, amma abun da muke so da kai shi ne ka fada mana, meyasa ka sanya mashi sleeping pill a cikin coffee? After that! Why ka hana sa zuwa kai farmaki bayan baka taba hana shi ba! sai wannan karon? Sannan Yace ka yi fitar sirri a daren ranar da suka je kai farmaki, Sharafuddeen Ina kaje"? his Excellency abdul razak ne ya jefa mashi tambayar.

Shiru yayi batare daya iya kare kanshi daga abunda suke tuhumar shi ba.

A hankali Chief owais Ya sadda kanshi Kasa ko kallonsa baison yi saboda baison tausayin shi ya kama shi, gaba daya komai dake faruwa akan idanun Hajiya saratu dake atsaye bakin kofar shiga part dinta, taji komai daya faru saboda bata kaiga shiga ciki ba..



Hannayen shi dake kerma ya Waga sama cikin karyayyar murya ya ce


_"Ya Allah, bani da mafita daya wuce kai! Kaine shaida ta, kafi kowa sanin wanene bawan nan naka...."

bai kaiga ?arasa maganar ba, sakamakon muryar dattijuwar data karaWe kunnuwan su



*_"NI INA DA JA AKAN MAGANAR KA OWAIS, JINI NA BAZAI TABA AIKATA MIYAGUN LAIFUKAN DA KAKE TUHUMARSA DA SU BA"!*_



~*_________________________________*~



*Daga Al?alamin Boss Bature=?%?
'?*




*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*=?%?=؋?=؞? &?=ؔ?=؞?>???




_ * *_



~___________________________________ '?~





A matu?ar ruWe suka juya tare da kallon mai shigowa...

Sandar hannunta ce ta fara zurowa cikin falon, Kafin ta kunno kai, farar jallabiya ce a jikinta ta lullu6e kanta da head scarf ta rufe fuskarta da takunkumi, haka zalika idanunta suna asanye da shade fari, da?yar t??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a ke dogara sandar hakan ya bayyana rashin kuzari a tattare da jikin ta, daga gani bata da koshin lafiya duba da yadda jikinta ke kerma.

Cike da tsantsar ruWani suke kallon ta daga ?asa har sama, basu san wacece ba, amma maganar da ta furta ta tsaya masu a ?ahon zuciya.


A sukwane Sharafudeen Ya mi?e yana duban ta, Muryarta ta yi masu kama da ta mahaifiyarsu da suka rasa tsawon shekaru wanda basu mance da yanayin sautin muryar tata ba.


Pravin sai faman zazzare Idanunsa ya ke yi burinsa kawai ya ga wacece ita duk da fargabar da ta shige shi saboda muryarta ta yi masa kama da ta wata da ya ta6a sani..



Baba Obie sam ya kasa motsawa, zuciyar shi ta ?i aminta da abunda kunnuwanshi suke juyo mashi, haka kuma ya kasa yarda da abunda idanunsa ke nuna mashi, kokwanto ya ke aransa ya ayyana hakan ma bazai ta6a yiwuwa ba, wanda ya mutu ba ya ta6a dawowa, duk da yanayin fuskarsa ya nuna tsantsar ruWani, sai dai babu alamun fargaba atare da shi saboda ya yi imanin hakan bazai taba yiwuwa ba, sai dai idan fatalwarta ce ta dawo...


"Wace ce ita? Da izinin wa ta shigo estate din nan?" Tambayar da ta cika zuciyoyinsu kenan, gaba Waya sun ?agara da su ji dame ta zo musu.


"Baiwar Allah daga ina ki ke? Wa kike nema ne? Kuma tayaya akai kika shigo estate Win?" His excellency Deen ne ya tambaya fuskarsa a murtuke.


Hajiya saratu dake a tsaye bakin kofar shiga part dinta tayi sototo tana kallon Ikon Allah..

Kusan atare Sir Mubarak Da Hateem suka mi?e daga zaunan da suke akan Sofas suka bi ta da kallo...

"Wacece wannan dattijuwar ne? Me ya kawo ta nan? Da iznin wa ta shigo Estate din nan uhum"! Acewar His excellency Abdul Razaq...

"Dan Allah ku yi wani abu akai, matar nan ba mutun bace, ku duba ku ga yadda jikinta ke kerma," Pravin ne ya faWa yana zare idanun sa..

"Ku kira Security Officers ku tambaye su ta ya akai suka bar bare ya shigo mana estate! Da iznin Uban wa..."

Senate Lateef ne ya Wauko maganar yana huci idanunsa akan tsohuwar, ?o?ari take ta cimmusu sai dai rawar da jikinta ke yi da rashin kuzari ya hanata yin saurin.

Tana gab da zata ?arasa gaban Sofas ta Wan dakata tana mayar da numfashi.

Cikin sauri Chief ya nufe ta, a hankali ya sanya tafin hannunsa ya dafe bayanta ya taimaka mata ta ci gaba da tafiya suka ?araso tsakiyar Sofas Win, rai a 6ace Sir mubarak Ya ce,"Kana acikin hankalinka kuwa? Ko ka san ta ne?...."


Bai ?arasa Maganar ba tsohuwar ta yi kukan kura ta dira agaban Baba Obie ta jefar da sandar hannunta, bai aune ba ta wanka masa zazzafan mari tare da cakumar gaban rigarshi da yatsun hannayenta dake ta kerma.


Tashin Hankalin da ba'a saka masa rana! zazzare idanunsu suka yi cikin tsananin al'ajabin karfin halin dattijuwar nan take ran su ya 6aci, ta tako har cikin estate Winsu ta mari mahaifinsu a gaban idanunsu!!'

Ransu ya yi mugu mugun 6aci har sun harzu?a za su kai mata bugu Sharafuddeen ya yi hanzarin kare ta.

Sir Mubarak yana huci ya ce, "Don Ubanki wacece ke?? Uban me ya kawo ki estate din nan? Da me kike ta?ama ne?"

Senate ya amshe da fadin, "Sharafudeen ka matsa ka bamu guri! Baka ga abunda ta aikata bane? mahaifinmu fa ta mara agaban idanunmu!"

Cikin rawar murya Pravin ya ce, "Wallahi mahaukaciya ce, daga gani irin mahaukatan nanne masu yin hauka tuburan a dawanau ta gudo Allah Ya hankaWo mana ita nan, wlh ku yi gaggawar korarta daga estate din nan idan ba haka ba zata manna maku hauka ne..."


Baba Obie bai motsa ba amma fa ya girgiza sosai, da ruWu yake kallon fuskarta da idanunsa wadanda suka kaWa jawur, sam ya kasa magana saboda rudewar da ya yi ya rasa gane wacece ita meyasa ta mare shi?"

"Ba zaku Wauki mataki ba? Kuna gani a gaban idonku ta mari Baba? Matar nan fa mahaukaciya ce wlh, babu lafiya a tare da ita, da gani tana tattare da ba?a?en aljanu shiyasa har ta yi nasarar shigo mana nan..."

Pravin ne Ya faWa Yana zare idanunshi yadda kasan na kwarton mazuru.

Ran Hajiya Saratu ya 6aci ganin abun da dattijuwar ta yiwa mahaifinsu, cikin fushi ta nufe su tana ?arasowa bata bi takan Sharafudeen ba, ta dam?i mayafin tsohuwar kokawa ta barke a tsakaninsu, tana huci ta ce, "Wlh bazata sa6uba, na rantse sai kin yabawa aya za?inta, ki shigo har estate dinmu ki mari ubanmu a gaban idanunmu? Kina acikin hayyacinki kuwa? Na shiga ukuna! Wai dan Allah uban wanene ya gayyaci tsohuwar najadun nan acikin gidan nan? Da iznin Ubanwa Securities suka bari ki ka shigo.."

Balbaleta da faWa Hajiya Saratu ta yi ta inda take shiga bata nan take fita ba.

Sai da suka gama harzu?a kowa zuciyarshi ta zo a wuya.

Pravin yana ?o?arin zaro waya daga aljihu don ya kira Security Officers din gidan, Kwatsam ba zato ba tsammani Hajiya Saratu ta yakice takunkumin dake akan fuskarta, Ta fusge shade din dake akan idanun tsohuwar ya faWo ?asa ta bi tasa ?afarta ta take shi ya faffashe.

?agowar da za ta yi da niyyar ta wanka mata mari har ta Waga tafin hannunta, idanunta suka sauka akan fuskar tsohuwar cak ta tsaya tana zare idanunta, Gaba Waya suka daura idanunsu akan fuskarta, Wani irin faduwar gaba suka ji ya Warsu acikin zukatansu, Sun ruWe da ganin fuskarta kamar sun so su gane ta sai dai sun kasa gane wacece ita.


Sai lokacin ta yi ?arfin halin buWe baki murya na rawa ta ce, "Saratu, bani bace tsohuwar najadu, kin ga tsohon najadu nan, ubanku Obinna!"


Ta faWa tana nunasa da yatsanta sai lokacin ya shaida fuskarta, Wata irin zabura Baba Obie ya yi jikinsa na 6ari ya mi?e tsaye a kiWime yana zazzare idanunsa! lokaci Waya yabi ya rikice, Hankalinsa yayi mugu mugun tashi, kanshi ya daure, Ya yi matu?ar razana da ganinta, tsantsar al'ajabine ya ru?e shi, ganin abun yake kamar a mafarki sam ya kasa gasgatawa..

Hajiya saratu ta daka mata tsawa tana fadin "Ke! Mahaifin namu ne tsohon Najadu? Baiwar Allah dame kike ta?ama ne, wace ce ke wai..."!

Bata ?are maganar ba Hateem ya daka mata tsawa a ruWe ta ja baki ta yi shiru, matsawa ya yi kusa da Khala ya dafa kafaWunta da tafukan hannayen sa, ya kafe ta da idanunshi yana ?o?arin gano wacece ita..

Cikin sanyin murya ta ce, "Baku gane ni ba? Hateem! Sharafudeen! Ni ce fa, *AURORA EDWARD* Momman ku!"


Ta faWa tana ?o?arin tuna masu ta juya ta dubi su Saratu ta ce, "Saratu! Lateef! Mubarak!


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login