Showing 33001 words to 36000 words out of 321579 words

Chapter 12 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

da gumi kamar babu A.c a dakin.

Lokaci daya ta fashe da kuka tana fadin wayyo Allah na, na shiga uku, ina son naga momnyna, Ina son in nemi ya fiyarta, Inaso na bata hakuri! i love her, i really wanna see her..."

ganin yadda ta daga hankalinta yasa Chief Ya mi?e tare da kar6ar phone din gudun kada ta kayar da ita kasa, Cikin boxer pocket dinsa Ya zura phone din, kafin ya tallabo fuskarta da tafukansa.

"Kalli cikin idanuna Unaisah" dakyar ta iya buWe idanunta da suka cika da hawaye, cheeks dinta sunyi jawur da su.

"Ki daina kuka, Ba laifin ki bane Unaisah, rashin sanine yajawo hakan, nasan yanzu kinyi danasani, saboda kin gane gaskiya" Jinjina mashi kai tayi alamar Eh.

"Ki gode ma Allah Unaisah, mommyn ki jaruma ce, I've wondered who gave birth to this remarkable child, cos you're different, with a sharp mind and loving, Ina alfahari da mommynki, saboda tayi bajinta, tayi abunda ya cancanta a jinjina mata..."

tun daya fara magana ta Wan sassauta da kukan sai shessheka da ta ke yi, Kalaman Chief Sun ?ara sa ta jin wani irin masifaffan son mahaifiyarta fiye da komai na duniyar nan.


"Uncle din mommynki Shine silar komai daya faru, shine munafukin dake ?ulla makirci atsakanin su, bayan haka muna zargin yana da sa hannu a kungiyar matsafan kurkukun kaddara, yanzu haka mun fara bin diddiginsa nan bada jimawa ba zai shigo Hannu"

In a low voice tace" I think he's the one who sacrificed me, kuma ina zargin yarinyar Aunty Ummi daya dauka in dai basu kashe ta ba, zai iya yiwuwa tana a cikin fursinonin kurkukun kaddara, watakil ma tana atare da mu"



"Tunanin mu yazo Waya Unaisah ..."



"Amma, Ina jin fargaban mommy na ta?i kula ni"



"Zata kula ki Unaisah, a yanzu haka jiran ki ta ke yi, na fada mata zaki neme ta da kanki, ki kira ta awaya ki bata hakuri sannan ki nemi yafiyarta hakan zaisa taji dadi acikin zuciyarta"

cike da zumudi ta juya zata tafi yai saurin dakatar da ita"ina zaki je"

Fuskarta a yamutse tace"i wanna call her"

kayataccen murmushi Chief ya dan saki"Okay, ga kayanan ki tafi da su"

ya fada tare da nuna mata suitcases din dake ajiye gaban Couch, arude take kallon su a lokacin harya juya ya nufi ?ofar da zata kai shi gym room dinsa Ya shige ciki.

Kasancewar akagare take da ta kira mommynta, bata tsaya yin wani dogon tunani akan akwatinan ba, cikin sauri ta nufe su, taja handle din daya ta fuce da shi.



______________________________ '?



Tana shiga Bedroom dinsu, ta Waura akwatin saman gadon su, Ta dauko wayarta dake ajiye kan bedside drawer ta danna ma layin da tayi saving da Aunty Benazir kira, saboda zumuWi sam ta kasa zama sai zarya ta ke yi a tsakar dakin, almost 3 times tana kira ba'a picking, jikinta ne yayi sanyi saboda ta yi zaton fushi take yi da ita shiyasa bata daga ba.



_Message ta tura mata mommy, dan Allah ki daga kirana akwai abun da nakeso In fada maki_



Ba'afi minti biyu data tura sakon ba, sai ga kiran Aunty Pretty ya shigo wayar ta, kwata kwata batayi farin ciki da ganin kiran ba, saboda a halin yanzu bata son ganin kiran kowa in ba na Aunty Benazir ba, har ya katse batayi picking ba, sai da aka ?ara kira, ta haWe rai ba annuri ta Waga kiran tayi shiru batayi mata sallama ba.

On the Other hand jin tayi Shiru yasa Benazir tace"daughter, kin bukaci kina son yin magana dani, kuma na kira kinyi shiru"?


Waro idanu waje ta yi saboda rudanin da ta shiga, sai da ta fara janye wayar daga kunnanta ta duba number Win da kyau taga ta aunty pretty ce da sauri ta shiga messages ta duba number Win data tura ma sa?on, taga ba kuskure tayi ba Aunty Benazir ne ta turamawa amma ya akai Aunty Pretty ta kira ta sannan tace taga sakon ta?

Nan take zuciyarta ta bata amsa da cewa zai iya yiwuwa mutun Wayane ke amfani da layi biyu, Ras taji gabanta Ya dan faWi, labban na kerma ta furta"Aun.. Aunty pretty, dama kece Mommyna Aunty Benazir"?

Sautin Dariyar Benazir ce ta ratsa kunnanta, cike da nishadi tace"ni ce mana, layin da kika turama sako na Uncle din ki ne da nake amfani da shi, bayan na kar6i contact dinki agurin Aneelerh, ina saka number din Unexpected naga sunan da nayi maki saving ya bayyana akan screen din wayata nayita mamaki nace ashe da daughter dina nake waya batare da sanina ba, daga nan na yanke shawarar kiran ki da layin ya shureim saboda bana so ki gane ni ce...."


wata irin kunyace ta kama Unaisah, tayi shiru tana zare idanun ta.

"Kin daina fushi dani..."? Benazir ce ta tambaya akagare da son jin amsar ta.



Kwatsam taji ta fashe mata da kuka kamar ranta zai fita, Hankalin ta ba karamin ta shi yayi ba, muryarta na rawa tace"Unaisah lafiya kike kuka? Meke damunki ne? Waya taba min ke"?



Cikin shesshekar Kuka tace"Forgive me, Mommy I realize my mistake I apologize for hurting you, I love you more than anything in this world, I want Daddy to remarry you and bring you back to me, cos I need you in my life...."

tana jiyo muryar Benazir dake ambaton Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah daya nuna mini ranar da nake ta jiran zuwanta Unaisah dagaske Kina sona yanzu? Kina son mommynki ta dawo kusa dake"?

Jinjina kai tayi kamar tana agabanta tace"seriously, I love you so much, i want you to take care of me, I thought since Daddy had done everything for me, bazan bukace ki ba amma ayanzu na gane ke ce cika makon farin cikin rayuwata, bani da tamkar ki har abada..."

Bata karasa maganar ba sautin kukan Benazir ya cika kunnan ta, hankalinta ne ya tashi da rawar murya tace"dan Allah ki daina kuka, bana son ji, pls, Allah zaiyi fushi dani idan kina kuka akaina..."

cikin shesshekar murya Benazir tace"ba kukan bakin ciki bane Unaisah, kukan Farin Ciki ne, kin faranta raina, Kin sani jin kamar nafi kowa farin ciki a duniyar nan, yanzu bani da sauran damuwa, Mijina ya daina fushi dani, yata ma ta daina guduna, Alhamdulillah..."



"Ba ki ce kin yafe min ba"?



Benazir bata bata amsar tambayarta ba, sai taga ta canza call din zuwa Video Call, picking tayi lokacin da idanunta suka sauka akan fuskar Benazir wata irin kunyace ta lullube ta, fadawa tayi kan gado wayar na a hannunta tayi saurin janyo pillow da dayan hannun ta lullu6e fuskarta tana dariya, itama Benazir din dariya take ma yi.

Cike da zolaya tace"rasa kunyan 6eran taka, Lemme see your face, kin tuna karyar da kikai min, Kina zuwa school sannan a kano kike da zama uhum"? ?yal?yalewa tayi da dariya ba tare data furta kalma ba.

"Oh ni Benazir, mamaki nake wai ni ce na haifi zankaWeWiyar balarabiyar nan tubarkalla kamar hurul ain"

fashewa ta kumayi da dariya, Hakan ba karamin faranta ran Benazir ya yi ba, dama tayi ne donta saka ta farin ciki ganin ta damu sosai.

"Aneelerh ta bani labarin kuruciyarki, yadda kasan ni agari, nima haka nayi kuruciyata amma fa ban kaiki rashin ji ba, gaskiya ni ban taba sa an kai daddyna cell ba" ta fada tana kallon Unaisah data kare fuskarta da pillow sai dariya ta ke yi.

"Taya zamuyi magana bayan kinki bari inga fuskarki uhm? Pls let me see your face, " A hankali ta zame pillow din, ta matso da screen din wayar saitin fuskarta suka zubawa juna ido gwanin ban sha'awa.

"Wow, ?ata tafi ta kowa kyau, launin idanunki irin na Ammin mu ne ta eygpt, kinsan me har yanzu tana araye ta tsufa tukuf..."murmushi Unaisah ta yi tana faman sauke ajiyar Zuciya.

"Fadamin waya sa ki kirani awaya"?

"Chief ne, shine ya fada min komai daya faru da ke"

"Mutumin kirki, ya taimake ni, Allah ya saka sa masa da mafificin Alkhairin sa"

Ta amsa mata da ameen..

"Kina da saurayi" cike da jin kunyarta tace"shine ai"


"Wa"?


"Zan fada maki ba yanzu ba"



"Okay, abun da nakeso dake, Ki manta da komai daya faru, na yafe maki Unaisah, kuma ba laifin ki bane, rashin sanina yasa kika ?ulla ce ni aranki, amma ni ban ruke ki a cikin zuciyana ba, in ma akwai mai laifi to ni ce Unaisah, duk da nima bada son raina na tafi nabarki ba, amma naji dadi da ban tafi dake ba, watakil da yanzu baki araye tunda bana acikin hayyacina zan iya jefar dake akan titi...."

kasa karasa maganar tayi saboda kukan dake kokarin balle mata, cikin karyayyar murya Unaisah tace"pls kada kiyi kuka mommy, bana son ganin hawayen ki,..."

jinjina mata kai tayi"bazan yi ba tun da bakya so....." sun dade sunayin waya akalla sun shafe awa daya da rabi a hakan ma basu gaji da yin wayarba, sai da Benazir tayi mata alkawarin zata zo gidan tukunna ta hakura su ka yi sallama da junansu.

mi?ewa tayi tsaye kan gadon, ta dinga tsalle kan matress din fuskarta dauke da murmushin Farin ciki.



Shigowa dakin Batool tayi, jikinta asanye da kayan bacci riga da wando ko mayafi babu akanta.

burki ta ci ta tsaya tana kallon ikon Allah ganin yadda Unaisah ke daka Tsalle tana dariya kamar karamar yarinya.



Baki asake da mamaki tace"Sis Meke damunki ne? Meyasa kike yin tsalle akan katifa sai kace karamar yarinya"?



Bata amsa mata ba, ta duro daga kan gadon ta nufe ta, tare da rungume sosai, Batool duk ta rude ta rasa gane kanta fatanta Allah yasa ba tabin hankali ta samu ba.



"Sis meyasa ki farin ciki ne uhm"? Ta fada tare da raba jikinta daga na Unaisah



Fuskarta dauke da annurin farin ciki tace"Batool ki tayani farin ciki, na gano wacece mommyna wadda ta haife ni" waro idanu Batool tayi"are you serious? Ta ina? Wacece"?

Murmushi tayi"Aunty Benazir, mai kama dake, Itace Mommyna, kuma itace Aunty pretty da mukeyin waya da ita.."

farin ciki ne ya lullu6e Batool"ina tayaki murna sis, Kinji dadin rayuwarki, Mommynki da daddynki suna nan, Baki rasa kowa naki ba..."

maganar Batool ta taba zuciyarta, jikin ta ne ya yi sanyi sosai, tsananin tausayinta ne ya kama ta, su da basu taba sanin dangin su ba.

"Sis amma kin yafe mata laifin da tayi maki ne? Kuma taya akai kika gane itace mommynki uhum"? Ta fada akagare da son amsar ta.

"Shekaran jiya bana baki labarin Aunty Benazir da Aunty Aneeleeh sunzo ba"?



"Eh na tuna, ay time din na fada maki aunty ummi bata jin dadi, atare ma bacci ya dauke mu adakin ta.." Wan girgiza kai Unaisah tayi"baiwar Allah, Aunty Ummi, ta bani tausayi, naji labarin rayuwarta ashe kawaye ne su, da ita da mommyna da Aunty Anila, kaddara ce tayi silar raba su, nima mommyna bada son ranta ta gudu tabar ni ba" ta fada fuskarta. amarairaice.



"Waya fada miki pls, nima ina son ji"?



"Zan baki labarin komai daya faru amma ba yanzu ba, saboda nasha kuka wlh har zazzabi nake ji a jikina, amma da nayi waya da mommyna sai naji sauki acikin zuciyana.."

badan taso ba tace"Toh sis zan jira ki, wlh har na kagara naji, kuma ina ?ara tayaki murna Unaisah"



"Nagode my own sis,"



"Lah! Akwatin wanene wannan"? Ta faWa tana nuna suitcase din da Unaisah ta aje, bata jira amsarta ba ta nufi akwatin dake ajiye, ta zauna daga gefen gadon ta soma kokarin bude shi tana fadin"wallahi yayi kyau sosai..." sai da tayi maganar Unaisah ta tuna da akwatin, da sauri ta dawo gaba gadon ta zauna, suka saka akwatin a tsakiyar su..

Kasa bude akwatin tayi, dakyar Unaisah ta buWe shi waro Idanu waje su kayi ganin jigunanun Laces dinkakku tare da Materials da atampopi hada shaddoji, WaWWaga kayan suka somayi bakunansu sun ki rufuwa saboda mamaki.

"Dan Allah waya baki su"

"?azu da chief ya kirani naje dakinsa shine yace min in dauka, dama ya kar6i awona ran nan, amma naji dadi wlh dama bamu da kayan hausawa acikin kayan mu..."

sai murna ta ke yi tana yaba kayan, Batool dai jikinta yayi sanyi ganin kamar kayan na Unaisah ne kadai banda nata a ciki.



"Bai ce hadani ba"?

Da budar bakin Unaisah sai cewa tayi"Anya, kamar nawa ne ni kadai, amma kada ki damu zamu dinga sanyawa atare, ai abuna naki ne"

mood din fuskarta kamar bataji dadi ba, in a cool voice tace"a'a ni bazanyi amfani da su ba, naki ne saboda ke ya siye su, kada ki damu..."

ta fada tare da saukowa daga kan gadon, ruko hannun ta Unaisah tayi"meya faru ne naga kamar bakya farin ciki"?

Murmushi ta kakalo kan fuskarta"don't mind your self, Am ok, inaso zan je dakin Aunty Ummi"

tana ?arasa maganar ta juya ta fuce daga Wakin, Unaisah bata kawo komai aranta ba, ta maida kayan cikin akwatin kafin ta datse shi tare da ruko handle dinsa, ta sauko ta fito daga dakin ta nufi dakin Aunty Ummi.



_=ؘ?UMMIN AMERICA=ؘ?_



Fitowa tayi daga Toilet jikinta sanye da bathrobe, wayar ta dake akan gado sai ringing takeyi, da zarar kiran ya katse wani ke shigowa.

Hararar wayar tayi bata da niyar daukarta.

Sai da ta gama shirya kanta cikin Jallabiya, kafin ta dauki wayar tare da yin picking ta kara a kunne.



Kakkausar muryarsa ce ta ratsa kunnanta " Ummi, why haven't you been answering my calls for two days? I've even sent you ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?messages, but you didn't respond."


Batasan ya akai ta tsanci kanta da jin haushin shi ba.



"Bana jin dadi ne, wayar ma ban san inda na jefa ta ba, sai yau na dauko ta"



"Okay, ya jikin naki"



"Da sauki"



"Inason ganin ki, zanzo da anjima.."

bai ?are maganar ba ta katse shi da cewa"Sorry, basai ka zo ba, ka bari idan na samu time zanzo gidan ka"

muryarsa da mamaki yace"Ummi kin canza min, wani abu ya faru ne"?



"A'a ba abunda ya faru, kawai bana so kazo nan dinne,"



"Okay.." ya na faWa yai rejecting call Win.

nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, har zata aje wayar saiga kiran dr shureim ya shigo wayar, tun shekaran jiya da suka zo yake ta kiran ta, sau daya ta taba picking tana jin muryar shi ta katse kiran amma tayi saving contact dinsa.

A kalla tana da missed calls dinsa kusan dari da hamsin, daga shekaran jiya izuwa yau, ga messages da ya ta turo mata na ban hakuri da rarrashin ta akan rashin da su ka yi na yar su.



Wi-pi din wayar ta kunna kafin ta shiga whatsapp, ta bude chat din shi, A hankali ta zauna daga gefen gadon ta soma karanta last message da ya tura mata.



_Aisha ba zaki yafe ma yayanki ba? Pls bani baki tausayi, tsawon shekara sha takwas ina dakon soyayyarki a cikin zuciyata, dan Allah ki taimaki bawan Allahn nan, gani da ?o?on barata agare ki, ko bacci bana iyayi saboda tunanin ki, nasan da babynmu tana araye watakil inci albarkacin ta, saboda kina son ta, amma baki son mu sake samun wata atare? Kiyi tunani Aisha ni kadai ne zan iya baki irin ta_



A hankali ta furta"nasani ya shureim, kai kadai ne zaka iya bani irin ta, tabbas ina so na sake haihuwar mai kama da ita, but I can't marry you! I've already told you I won't marry the man who raped me, I can forgive you, but I can't marry you, even though I still love you amma meyasa kayi mini haka?

jefar da wayar tayi kan gado kafin ta kifa kanta jikin pillow, kuka take ji sai dai hawayen sun?i zubowa, sai dai takama yin kukan zuci.



"Aunty Ummi" cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Unaisah, Da sauri ta shanye damuwarta ta mike zaune tana kallon Unaisah dake shigowa ciki hannunta ruke da akwatin ta.


"Ina Batool din? Tace min zatazo gurin ki, "



"Batool bata shigo nan ba, akwatin wanene wannan"? Ta fada tana nuna akwatin hannun ta



"Kayan da Chief ya siya minne"

ta fada tana murmushi, Ummi tace"Masha Allah, amma na taya ki murna, gaskiya Chief yana ji dake.."

ta fada yayin da take buWe akwatin data kar6a a hannun ta, tayi mamakin kayan masu kyau da tsada.



______________________________
'?



bayan ya kammala motsa jikin shi, ya fito daga Gym room din ya nufo dakin sa, hannun shi ruke da bottle water me sanyi, ya rataya farin towal akan shoulder dinsa, kwata kwata babu riga a jikin shi sai Boxer short dinsa, gaba daya jikin shi gumi yake fitarwa..



Harya bude murfin robar zai kai baki da niyar yasha ruwan, wayarsa ta doka alert, dan dakatawa yayi ya nufi wayar dake akan couch, ya danna unclock button, bai jira yaga wanene zai shigo ba ya juya baya ya kanga bottle din abakinsa ya fara shan ruwa.

can cikin kunnansa yajiyo takun tafiyar mutun, abun ya daure kansa aransa ya ayyana wanene ya shigo masa daki batare da sallama ba? A sukwane ya juyo don yaga wani isasshen ne, da dan mamaki akan face din sa ya ke kallon ta, tayi tsaye idanunta na kallon floor, kamar mara gaskiya sai wasa takeyi da yatsun hannunta..

*~_____________________________////////////////////=?%?

*Daga Alkalamin Boss Bature=?%?>???*


*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*=?%?=؋?=؞? &?=ؔ?=؞?>???




_ *The Unexpected Guest *_



~___________________________________ '?~






Da ace wani ne ya shigo masa daki haka zai tuhumesa ne amma da yake yasan wacece ita, da irin rayuwar da tayi sai bai damu ba.



"Me ke damun ki"? Ya fada ganin kayan baccin jikinta sunyi squeezing, ga sumar kan nan nata a haukace ba gyara.



Sam ta kasa bashi amsa, wani irin shakkarshi take ji, batasan ma ta shigo dakin ba, saboda bata a hayyacin ta,



Nufo ta yayi jikinta na bari ta juya zata fuce, tana ruke handle din kofar taji ta adatse, wani irin faduwar gaba taji, ta dinga jan handle din amma taki buWewa kamar zata saka kuka.



Mamakine ya kama shi, ya rasa gane kan ta, aransa ya ayyana ko dai tana da tabin hankali? If not why zata shigo dakinsa ba sallama kuma yayi magana tayi shiru, sannan ya nufo ta tana kokarin guduwa"?



Daga bayanta ya tsaya yana kallon yalwatacciyar suman kanta data cika bayanta.



"Fada min meke damun ki? Baki da lafiya ne? Ai ko ki akayi guri na? Ko kinzo ne don ki gaishe dani'?



Cikin rawar murya tace"am sorry, bansan na shigo


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login