Showing 96001 words to 99000 words out of 321579 words

Chapter 33 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

zuciyar chief zai yi wuya a fadin duniyar nan, he's a true leader, ba karamun mai tsoron Allah bane zai yi hakan=ؘ?=؋?...



Almost one hour suna tattauna yadda zasu kama Elders, kowa yana kawo idea dinsa, a karshe suka yanke shawarar zasu tuntubi Ummi saboda ta hanyar ta ne suke sa ran za su dam?i Musa ta cikin sau?i. Chief ya ce su bar komai a hannunshi ya riga da ya yi mata magana amincewarta ya ke jira, zai ?ara yin magana da ita duk yadda su kai zai sanar da su..=?%?


*PRAVINW'*


Aje Motarsa yayi a haraban wani gida, fitowa yayi jikinsa sanye da suit ya rufe fuskarsa da mask, hatta hannayensa da ?afafunsa ya saka musu safa, sai yan waige waige ya ke yi daga gani yana a cikin fargaba, zagayawa yayi ta baya ya buWe boot din motar, ya janyo ?aton buhun dake a ciki ya aje ?asa, kafin ya bude backseat ya sungumo ba?ar jakarsa ya rataya ta kan kafaWarsa, da sauri ya ja buhun ya shige da shi ciki, kulle door din ya yi da code kafin ya nufi Ciki.

Shigarshi falo keda wuya ya soma jiyo kakarin aman da ta ke yi, hankalinsa a tashe ya zame jakar ya jefar kan sofa ya saki buhun cikin sauri ya nufi bedrom din da take.

Yana shiga ciki bai same ta a saman gadon ba, sai dai bargonta dake a yashe ?asa, cike da fargaba ya bangaje kofar toilet ya shiga yana haki saboda gudun da ya yi, lokacin idanunsa suka sauka akan ta yayin da take a gaban sink tana kwarara amai tamkar yan hanjin cikinta zasu zazzago, ta daddafe bakin sink din da hannayen ta.

?arasawa ya yi da sauri ya dafe kafadarta yana yi mata sannu. Bata ko kula shi ba sai da ta gama amayar da komai da ta ci, ta kunna faucet ruwa ya wanke aman.

Kokarin daukarta ya yi don ya sauwa?e mata tafiyar, cikin bacin rai ta bangaje shi ya yi taga taga zai faWi yai saurin tsayar da kansa yana kallon ta.


Tsantsar bacin rai ne akan fuskarta, idanunta sun kumbura sun kaWa jawur saboda kukan da take sha, gown din dake a jikin ta tayi squeezing kamar an ?watoto daga bakin kura, doguwar sumar kanta ta cukuikuye kamar ta mahaukaciya, mace mai tsafta ta zama ?azamar karfi da yaji saboda rashin lafiya da damuwa..

A hankali zafafan hawaye suka soma zarya kan kuncin ta, labbanta sun bushe ?amas sun Wan faffashe ga jikin nata har yanzu ba sau?i..

Cike da bacin rai ta furta, "Karka kuskura ka ?ara matsowa kusa da ni, i don't want to see you Pravin, ka nisanta kanka dani, idan ba haka ba zan yi ma kaina illa!" Bai ta6a ganin Hajjaty a cikin fushi irin na yau ba..

A hankali ya sanya hannu ya cire mask din dake akan fuskarsa, cikin yan kwanakin nan saboda zullumi da fargaba har rama ya yi, tun ranar da ya gudo da Hajjaty, bai nufi ko'ina ba sai guest house dinsa da ya daWe da mallakarsa, babu wanda yasan yana da gidan.

"Ba halin ki bane, bansan ki da fushi ba, na rasa gane kanki cikin kwanakin nan, duk abun da kika ga ina yi saboda in kare ki ne, amma kin kasa fahimta na.."

Harara ta watsa mashi, cikin bacin rai ta ce, "Idan ba halina bane to kai ne ka sauyani Pravin, ni bazan cigaba da yarda da munafuki ba, na gaji da sauraran ?arairayin ka! ka faWa min gaskiyar abun da ya faru, ka raba ni da mutanan da nake rayuwa da su ka kawo ni wani gida ka boye ni a cikin sa! Kullum na tambaye ka sai ka yi shiru, wai me ka Wauke ni ne? Don ina da hakuri ba hakan yana nufin bani da hankali ba! Zan iya jure komai amma wallahi bazan jure rainin wayon ka ba...."

Tuni ya sha jinin jikinshi jin yadda Hajjaty ke masa faWa kamar uwarsa, tana magana tana ciccije le6enta saboda radadin da take ji..

"Tayaya kake tunanin zan cigaba da zama da kai? Bayan baka Wauki iyalinka da muhimmanci ba sai ni Pravin? Wani laifi ka aikata ne da yasa har ka gudo da ni? A ranar kafin in fita hayyacina na ji muryar Hajiya Saratu a cikin kunnena, ta shigo daki na, duk da ban ji abun da ku ka tattauna ba amma raina ya bani ta gano abun da muke yi shiyasa har ta shigo Wakina, kuma na ji lokacin da ta bangaje mu muka faWi daga nan ban ?ara sanin inda kaina yake ba..."

Dakatawa ta dan yi tana jan numfashi idanunta a cikin na shi, ya yi zuru zuru ya rasa ta ya zai shawo kanta, kwanakin nan basu jituwa saboda ya?i faWa mata laifin da ya aikata, ta ?i kwantar da hankalinta balle har ta ji sau?in abun da ke damunta..

Girgiza kai ta yi idanunta suka cicciko da ?walla...

"Ka kasa kare kanka saboda baka da gaskiya shiyasa ka yi shiru ko? Ni ina ji araina wani laifi ka aikata musu shiyasa ka gudu da ni, saboda hujjar daka bani bata gamsar da ni ba.."

Sunnar da kanshi kasa ya yi, jikin shi ya yi sanyi lakwas, baisan ya zai yi ba, ya jefa rayuwarsu a cikin bala'e da masifa, ya yi danasani tafi sau a ?irga, yana matukar jin kunyar Hajjaty, yana jin nauyin tasan miyagun laifukan da ya aikata wa'iyazubillah!!


Bata ?ara yin magana ba, ta juya ta nufi kofar fita da sauri ya bi bayanta, shigowa cikin dakin ta yi, jikinta na kerma ta nufi bedside drawer ta soma kwashe magungunanta tana jefa su cikin dustbin din dakin, shigowa ya yi da sauri ya dam?i hannayenta, kokoyi suka kama yi..

"Pls ki saurare ni, zanyi maki bayani, ki daina zubar da maganinki, da tsada na siye su saboda lafiyarki..."


Wani kallo ta wurga masa, "Ban damu ba Pravin, bana son lafiyar tawa, nafi son na mutu, saboda wanda na yarda da shi yana neman ya karya min zuciyata..."

Bai san sa'adda hawaye suka wanke fuskar shi ba, duk yadda ya so ya dakatar da ita abun ya ci tura, ?arfi yasa gurin Waukarta Wungurugum ya kwantar da ita kan gadon, ta dinga kuka tana bubbuga mattress da hannayenta, bin ta ya yi saman gadon ya janyota jikinshi tana turjewa, ya rungume ta kan ?irjin shi, duk yadda ta kai ga jin haushin shi da ya yi mata hakan sai da ta ji sassaucin damuwarta.


Cikin sanyin murya ta ce, "Pravin dan Allah ka fadamin meyasa ka gudu da ni? Meyasa ka bar Obie estate? Wani laifi ka aikata? Kada ka yi min karya Pravin, babu sirri atsakanin mu, kasan bani da kowa in ba kai ba, kaine majinginata, ?ashin bayana, bana so ka ci amanar yardar da na yi maka Pravin, dan Allah ka faWamin na yi maka alkawarin zan rufa maka asiri kuma zan taya ka neman mafita.."

wani irin tsantsar sonta da tausayinta ne ya mamaye zuciyar shi, tsoma yatsun hannayensa ya yi a cikin sumar ta yadinga cakuWa gashinta kamar yana mata susa,

Cikin sanyin murya ya ce, "Ki yi hakuri na boye maki ne saboda bana so na Waga maki hankali, amma gaskiyar abun da ya faru, Hajiya Saratu ta gano ina zuwa dakin ki, harma in kwana, bayan mun dawo an fara shirye shiryen family meeting, sai na shiga Wakinta don in canza kayan dake a jikina, ina kokarin cire riga na jiyo muryarta a cikin toilet tana yin waya ?asa ?asa kamar bata so aji, saina lallaba na je bakin ?ofar dakin na yi mata la6e

a nan na ji tana faWin wallahi bazata sa6u ba, dama ta jima tana zargin kin asirce mata miji saboda yadda kike gayu, wallahi ba zata ?yale ki ba, sai ta kashe ki da poison..."

Zare ido Hajjaty ta yi,

Pravin ya sha mur ya ci gaba da zabga mata ?arya, "Da na ji haka gabana na faduwa na fara tunanin me yakamata in yi saboda nasan mugun halinta na kishi wlh tsaf zata kashe ki, ni banma san wani munafukin bane ya kulla maki makirci, na so inji da wa ta ke yin wayar, ina jin alamun ta gama yin wayar na ma fasa canza kayan, jiki na na kerma na baro dakin nata, na nufo Wakin ki don in faWa maki abunda ke faruwa, shigowata keda wuya ina kokarin in tashe ki na ganki a kudundune cikin bargo, kwatsam na jiyo muryar hajiya Saratu daga waje tana tambayar maids ina ne Wakin ki? da sauri na la6e bayan labule ina jira inga me za ta yi maki, tana shigowa Wakin ta nufi gadonki hannunta ru?e da poison..."

Dafe kirji Hajjaty ta yi jikinta ya hau 6ari, daWi ya ji acikin ranshi ganin ta fara yarda da maganarshi..

"Ji nayi bazan iya bari ta cutar dake ba saboda nasan ba imani gare ta ba, saboda tashin hankali banma san lokacin dana yi wuff na fito daga bayan labulen ba tana jin motsi na ta juyo mu ka yi ido biyu, ta ware baki zata fasa ?ara na sha?eta tana ta sambatu tana faWin maciya amana, zarginta ya tabbata akanmu, wlh saita kashe mu, da na ga ta turje ta ?i saurarena kawai saina sumar da ita, na sungumeki na bar estate Win da ke, don nasan muddin ta farka kwanan mu ya ?are..."

Cike da damuwa Hajjaty ta ce, "Banji dadi ba, amma koma wanene ya ?ulla mana makirci Allah ya isa tsakanin mu da shi, mutane basu tsaron Allah. Amma hajiya Saratu bai kamata tana daukar zigar wani ba, ko da ya ke dama ta tsaneni, tasha faWamin saita raba ni da gidan ubanta, amma bansan tsanar da ta yi mini ta kai har haka ba, kuma dama kwanaki ko hanya bata son haWawa da ni, abinci ma indai ni na dafa bata cin shi.."

Pravin ya ce, "Hmmm, Wan adam fa ba abun yarda bane, indai ka biyewa mutane zasu kaika su baro ka, kuma dama bata sonki ta sha saka ki kuka, ta ?untata maki saboda tana jin haushin zaman da kike yi agidansu, ni kaina da nake mijinta bata ?yaleni ba, kullum saita goranta mini saboda ina zaune gidan ubanta. Saratu bata da wayau, sakarya ce, kwata kwata bata da halin kirki, zaman hakuri kawai nake yi da ita, amma ni kaina ba sona ta ke yi ba, wahalar da ni ta ke yi, taita juyani son ranta." Yana magana yana yamutsa fuska,

"Amma pravin meya kamata mu yi yanzu? Ni ina ga kawai mu je mu basu ha?uri mu faWa masu gaskiya, In ba haka ba za su mana kallon mutanan banza kuma maciya amana.."

Waro idanunsa ya yi, "Ke! Kina hauka? Tab lallai, ay wlh muddin muka koma estate din nan sai sun hukunta mu, sai ka ce kin manta irin yadda baba Obie da yayyanta suke ji da ita?

"Pravin, koma me zai faru mu ne masu laifi, mutanan nan sun yi mana hallaci, sun yarda da mu, tsawon shekara da shekaru muna rayuwa acikin su basu ta6a gudun mu ba, amma mu muka ?i fada masu ala?ar dake atsakaninmu, bamu kyauta ba, kuma nasan zasu fahimce mu in har mu ka je muka basu ha?uri muka kuma faWa masu akwai aure a tsakanin mu za su yafe mana, koda hajiya Saratun bata yarda ba nasan za su yi ?o?arin sasanta mu da ita, tun da su din mutanan kirki ne suna da hankali da kuma tausayi...."


Bata ?are maganar ba ya tari numfashinta da cewa, "Hmmm, na lura har yanzu baki san halin hajiya Saratu ba, nasan mutanan kirki ne amma wlh akan Saratu zasu iya komai, kin manta labarin dana baki lokacin da ta zo da ni don inga danginta? ?iri ?iri suka nuna basu sona sun tsaneni saboda ni ba jinsin su bane, kuma bani da asali da arziki irin nasu, a lokacin ba don baba Obie ya goya mini baya ba ai da basu bani auranta ba..."

Dafe kai ta yi da hannu Waya, "Me zai hana mu tuntu6i baban toh? nasan zai taimaka."


"Har yanzu kin ?i fahimtata, nifa bazan ci gaba da zama ?asar nan ba, saboda hajiya Saratu ba zata raga mana ba, ?wara mu tattara yanamu yanamu mu tafi, don yanzu haka nemanmu suke yi ruwa ajallo don su hukunta mu.."

Maganarsa ta Waga hankalinta, da damuwa ta ce, "Pravin meya kawo maganar barin ?asa? Ka san me kake faWa kuwa? Ina zaka kai ?a'?an naka da matarka? kaima kasan wannan bamai yiwu bane, kawai saboda asirinmu ya tonu sai mu gudu kamar waWanda suka aikata wani mugun laifi...?"

dafe kanshi yayi da hannu Waya baisan tayaya zai shawo kanta ba..

"Pravin ka daina wannan maganar, ba zan ta6a baka shawarar ka tafi ka bar iyalinka ba, bamu aikata laifin daya kai har mu gudu ba, kawai kuskuren mu shine ?arya da muka yi masu tun farko muka boye masu gaskiya, in har muka nemi yafiyarsu bayan mun faWa musu komai wlh zasu yafe mana Pravin, mun sha?u da mutanan nan, mun saba da zama cikinsu, sun zama kamar danginmu da muka rasa! Sun Wauki nauyin komai namu Pravin, wlh idan muka gudu baza su ji dadi ba, zasu ga kamar dama da wata manufa muke atare da su shiyasa bayan mun samu abun da muke so muka tafi, kai baka tunanin halin da ?a'?anka da matarka za su shiga? Wai kuwa Pravin anya kana jin kanka amatsayin ubansu..."

bata ?are magabar ba ya toshe mata bakinta da yatsan shi..

Ta rasa meyasa take ji aranta kamar pravin ba gaskiya ya fada mata ba! Saboda yanayinsa da kuma maganganunsa abun tuhuma ne! Kawai saboda ?aramin laifin da bai kai ya kawo ba sai ya gudu ya bar iyalinsa?


Ganin kamar ta fara Wago shi ya sa shi saurin daidaita nutsuwarshi cikin sanyin murya ya ce, "Na gane kuskurena, kawai bana so ta cutar dake ne shiyasa na yi wannan maganar, amma ba har cikin raina ba, ni ba zan iya tafiya na bar iyalina ba, banma san na fada ba, ki yi ha?uri idan na 6ata maki rai.." Ajiyar zuciya ta sauke, "Yanzu da yaushe zamu je estate din mu nemi yafiyarsu?"

"Me zai hana mu bari sai an kwana biyu, lokacin da suka yi kewarmu, koma suka neme mu da kansu don su ji ba'asi sai mu je mu faWa masu gaskiya,..."

ta aminta da maganarsa saboda a halin yanzu tasan jiran su suke yi.

"Na yarda, amma tayaya zasu neme mu? Bayan babu waya gaba Waya mun barsu agidan.."

Yamutsa fuska ya yi, "Kash, sam na manta, amma akwai waya da na siya, nama yi mana hada siyayyar kayan abinci, da duk wani abu da zamu bukata.."

"Pravin basu da layin da zasu tuntubemu a yanzu."


"Karki damu, ki bari da kaina zan je estate din, in faWa masu komai in sun hakura suka yafe mana zan sanar da ke komai." Ta ce, "Toh Pravin, yaushe zaka je ne?" A takure ya yamutsa fuska, kwata kwata bai son tana yi masa maganar Obie estate, da tasan masifar da suke a ciki da bata ?ara marmarin ambaton ko da sunan estate din ba.


"?arshen satin nan." Ajiyar zuciya ta sauke, "Toh Allah ya kai mu, amma dan Allah ka kwantar da hankalinka, bana so in gan ka a cikin damuwa, addu'a yakamata mu yi Allah ya sa abun ya zo da sauki su yafe mana." Jinjina mata kai ya yi batare da ya furta kalma ba. Ta yi tunanin hajiya Saratu ce damuwar shi batasan mugun abun da ya aikata ba.

Ru?o hannunta ya yi, "Mu je in taimaka maki ki yi wanka, yau kwana huWu jikinki baiga ruwa ba." Bata musa mashi ba ya Wauke ta kamar jinjira ya nufi toilet da ita, after mins ya futo dauke da ita, ta yi Waurin ?irji da towel, ya kwantar da ita kan gadon shi.

Juyawa ya yi ya nufi closet tabi bayanshi da kallo tana mai ?ara jin kaunarsa saboda kulawar da ya ke bata.

Dawowa ya yi hannunsa ruke da riga da wando na shan iska, tun ranar da ya kawota nan ya siya masu kaya kala uku uku..

"Za ki iya sakawa ko in taimaka maki?"

Murmushi ta sakar mashi, "Bana so kana wahala, na lura hada damuwar ciwona ke damunka, kada ka damu zan ji sauki in sha Allah..." Murmushin ya?e ya yi mata..

Bayan ta kar6i kayan ya fuce daga Wakin, shiru bai dawo ba, saukowa ta yi daga kan gadon, bayan ta kammala zura kayan a jikin ta, ta je gaban mirror tana kallon kanta.

Zuciyarta cike fal da kewar Ahlin Obie, ita dai ta kamu da ?aunarsu tun farko, kuma ba ta jin zata iya rabuwa da su ko da hajiya Saratu zata hukunta su ne, ta ji zata zu?unna kan gwiwowinta ta ro?eta akan tayi hakuri ta yafe su.

Bakomai tafi ji ba face halin da ?a'?ansu za su shiga idan suka rabu.

Can kuma ta canza akalar tunanin nata, ta fi jin kewar aminiyarta akan komai, ta so ace akwai waya a hannunta da ba abun da zai hana ta kira Turai ta faWa mata halin da suke a ciki tasan zata fahimce su kuma zata taimaka masu..

Body oil ta shafa ma skin dinta ta dauko comb ta sharce gashin kanta dakyar dakyar saboda yawanshi ga tauri da ya yi ga kuma jikinta ba ?wari..

Jin shiru pravin bai le?o ba ya sa tayi tunanin ko ya fita daga gidan ne.


Hakan ya sa ta mi?e daga gaban madubin ta fito ta shiga falo, Wan madaidaici ne ya haWu sosai, Pravin ya daWe yana kokarin jan hankalinta da ta dawo gidansa da zama ta ?iya saboda bata son rabuwa da obie estate...

Idanunta ne suka hango mata bag Winsa da ya ajiye kan sofa, sakamakon jefar da ita da ya yi lokacin da ya shigo har ta buWe abubuwan dake a ciki sun zubo waje..

Buhun ta nufa ta soma buWe shi, ba komai ne a ciki ba face kayan abinci, komai da zasu bu?ata ya siya masu, murmushi ta yi tare da mi?ewa har zata juya idanunta suka sauka akan passports dake ajiye kan hannun kujera.

Zuwa ta yi gaban kujerar, ta kai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login