Showing 300001 words to 303000 words out of 321579 words

Chapter 101 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

daya gano alakar dake a tsakaninta da Omair, amma ba hakan na nufin ita kaWai zai aura ba, a yanzu haka Ya samu wadda zata maye masa gurbin Unaisah daya rasa.

Daya faWa mata hakan taji kishi har tayi danasanin kiran shi cikin 6acin rai tace meyasa bazai aureta ita kaWai ba? me Allah ya rage ta da shi? ya fada mata ko tana da makusa ne"?

Cikin lallashi yace tayi ha?uri daga zuciyar shi ne, bazai iya hana kanshi son wata ?a mace ba, amma ta sani har abada itace mace ta farko daya fara yi ma son da bai ta6a yi ma wata ?a mace ba, kuma har a wannan lokacin babu abun daya sauya na daga son da ya ke yi mata, shiyasa ma zai fara auranta, ita kuma Yarinyar da ya ke so ya aura Allah ne ya jarabce shi da sonta bayan daya rasa yar uwarta Unaisah.


kalamansa sun tausasa zuciyarta, cikin sanyin murya ta tambayesa wacece yarinyar? tana so ta san ta.


A takaice Ya bata labarin Batool, nan take Taji tausayinta ya kamata, har taji zata iya amincewa Ya aure ta, duk izzar Nazli tana da zuciyar imani.


Nan take tace mashi ta amince saboda ta yarda da shi, ta yarda da son da ya ke yi mata kuma tasan shi din adaline zai kula da su.

ya yi farin ciki da jin hakan daga gare ta cikin ruwan sanyi ba tare da yasha wahala ba.


Bayan auran Owais da Nazli, a lokacin da suka dawo daga honey moon, da zai dawo Nigeria Prime minister Hateem ya biyo shi donsu zo nema ma Omair auran Unaisah, bayan da suka zo nigeria, Chief Owais Ya fada ma Iyayensa game da fasa auran Unaisah da yayi da kuma wanda ya bama ita, sun dan nuna rashin jin dadinsu saboda sunsan irin kaunar da yakeyi mata tun da daWewa tunkan Yasan wacece ita, amma daya fada masu dalilansa da kuma alakar dake atsakanin Unaisah da Danish sai sukaji dadi aransu, suka kuma goyi bayan bar mashi ita din tun da har yaji zai iya jurewa kuma su ba zasu hana shi yin aikin alheri ba kuma kamar yayi ma zumunci ne.



Ranar da suka shirya zuwa Neman auran Unaisah, kafin zuwan su saida Chief ya saisaici lokacin da Benazir da Unaisah basa agidan, Unaisah ta tafi School, Benazir ta tafi gurin aikin ta, sannan ya kira Taj ya faWa masa game da batun zuwan magabatansa, yayi farin ciki sosai yace Allah ya kawo su lafiya.


Kafin su ?araso gidan, Taj ya kira Danejo ya fada mata game da zuwan magabatan Owais, yace ta shirya masu abun da zasu ci, cike da farin ciki ta amsa mashi da toh, ya kuma kira dr shureim da Uncle abdallah, Hada Alhaji Ubaid duk ya sanar da su za'a zo neman auran Yar su Unaisah, kafin su ?araso gaba Wayansu su ka hallara agidan.


Hateem da ?an uwansa ne su ka zo neman auranta tare da Owais da Omar, a main falo suka zazzauna kan sofas, gaba dayan su, sunyi masu kyakkyawar tarba cikin girmamawa suka gaggaysa da su.

Danejo ta kawo masu abincin da ta girka masu tare da soft drinks, bayan ta gaishesu daga bisani ta fuce ta basu wuri, kafin suka fara tattauna batun daya kawo su.


daga bisani bayan sun gama gaisawa, Owais ya soma magana cikin nutsuwa yace ma Taj ya yi hakuri da abinda zai ji daga gare shi, yasan burinshi ne Ya kyautata masa shiyasa ya bashi auran Unaisah, amma Allah bai kaddara shine zai zama mijin Unaisah ba, shima Yaso Ya auri Unaisah amma bazai Iya raba soyayyar Unaisah da Danish ba, In yayi hakan baiyi masu adalci ba, sannan Idan harya ba Omair auran Unaisah to kamar ya bashi ne, zai yi farin ciki fiye da shi ne zai aureta, still zai zama surukin su, don haka yana rokon alfarma agurinsa ya maida auran shi da Unaisah akan Omair, kar ya ji komai, tun da shi yaba ita shi kuma ya hakura yabarwa dan uwansa kar yaji ba daWi, da shi da Omair abu Waya ne.."


zuciyar Taj ta karaya da jin maganar Owais, Hawaye suka cika idanun shi, kwata kwata baiji ba?in cikin abun da ya faWa ba saboda shima yana son Omair yana kuma son abun da yar sa take so, duk da ba haka yaso ba, yaso Ya cika burinsa na ganin Owais Ya auri Unaisah saboda halaccin da yayi musu arayuwa, Yana son Owais Yana son ya auri Yarsa amma Allah bai nufa shine zai zama mijinta ba, dama can rubutacciyar kaddarace! Wadda babu wanda Ya isa Ya sauyata! In har mutun ba kaddararka bane bazai taba zama kaddararka ba, Owais shiya fara sanin Unaisah, Amma Allah bai kaddara Unaisah zata san da zamanshi ba har saida ta fada kurkukun ?addara ta haWu da Omair, gaba daya dai rayuwarmu abisa mizanin ?addara take, kana naka Allah na nashi, duk abun da kaga baka samu ba dama can ba rabon ka bane =ؔ? Ubangiji Allah Ya zaba mana mafi alkhairi arayuwar mu.

Kowa da ke agurin saida ya lura da halin daya shiga, cikin sanyin murya yace tun da har shi da kan shi ya nemi alfarmar ya bar masa, shima ya amince ma auran su.

Sunyi murnar da bazata misaltu ba, suka dinga yi masa godiya yace su daina sunfi karfin komai agurin sa, sune sukayi masa halacci da har suka nuna suna son yarsa ta auri dan su.


daga bisani su ka ce basu san bikin ya Wauki lokaci, Sati uku kacal Ya ishe su, Uncle Abdallah Yace su Wan ?ara lokaci saboda suna son su shirya ma bikin.


Su ka ce karya damu, sun san me su ke jimawa, Su kawai Unaisah suke so Abasu, basu bukatar komai daga gare su, ko tsinke basu son akawo ta da shi gidan Wan su.


Gaba Waya sunyi murna da jin hakan daga gare su.


Duk a zaman Chief Ya bayyana masu game da son da ya ke yi ma Batool, harya nemi da su nema masa auranta tun da ga Mahaifinta akusa, kowa dake a gurin yayi mamaki, Musamman Dr shureim tsantsar rudu da farin ciki ne ya cika zuciyar shi, sai yaji ma kamar kunnansa ne suke jiye masa ba dai dai ba, Alhaji Ubaid yace shikenan faWuwa tazo daidai da zama, wannan ai yar gida ce, sai ayi tuwo na maina, gaba Waya suka sanya dariya.


Omar yace dama yana son Batool bai ta6a fada masu ba, yana murmushi yace ''itama batool din batasan yana son ta ba, amma shi yasan tana son shi, tsabar farin ciki yasa Dr shureim jin kwalla ta cika idanun shi, gani yake kamar Owais yafi karfin Batool, bayan yasan ta hanyar da suka same ta, amma ya za6i daya aure ta saboda Yana son ta, Allah abun godiya, kowa dake agurin saida ya fahimci farin cikin da ya ke a ciki, bawan Allah, dama yana ta zullumin wanene zai auri Batool ya zauna da ita lafiya batare daya goranta mata ba? Kullum in yayi sallah sai yayi addu'a akan Allah ya bata miji na gari wanda zai so ta, batare daya goranta mata ba, sai gashi Allah ya kar6i addu'arsa a lokacin da bai zata ba.

Sa'ilin da hawayen da ya ke dannewa suka soma kokarin gangarowa daga cikin idanunsa, taj daya lura cikin sauri ya zaro hanky daga aljihu Ya mika masa ya kar6a tare da rufe idanunsa da shi, gaba Waya sun fahimci dalilin shigar shi halin da ya ke a ciki, haWuwa su ka yi gurin lallashin shi don ya daina zubar da hawayen sa, Chief yafi kowa farin ciki da ganin yadda Dr. Shureim ya nuna jin dadin sa.



Bayan da suka shawo kan dr shurem, Prime minister yace"yana neman?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? alfarma agurin su da su bar komai a sirrin ce, baya son Unaisah tasan Omair yana araye koshi zata aura, kuma baya san kowa ya sani har sai ranar Waurin auran saboda mommynsa tana son ta bata mamaki" basu musa ba suka amince masa..


Chief Owais yace"shima yana neman alfarmar kada abari Batool tasan zatayi aure har sai bayan Waurin auren nasu, saboda yana son ya bata mamaki"

Gaba Waya sun goyi bayan maganar sa saboda suma suna son su faranta masu.



~_____=؞?______=ؗ?_____=ؘ?_____???___~




Bayan komawar prime minister Canada, Ya labarta ma sheikha game da sanya auran Omair, taji dadi sosai, aranar da zasu faWa masa bazata sukayi masa saida suka saisaici ranar daya gama degree dinsa na farko kuma duk aranar ya gama haddar alqur'ani mai girma.

A gurin walimar safkar alqur'anin sa, suka bashi gift box daya buWe akwatin Unexpected Ya tsinci Invitation card na auransa da Unaisah a ciki, tsabar farin ciki bakinsa kasa rufuwa ya yi.

yadinga yi masu godiya kamar zai yi musu kuka, farin cikin da suka gani akan fuskarsa ba ?aramin biyansu yayi ba sunji daWin faranta masa da su kayi.

Cikin shesshakar kuka yace ashe haka iyaye suke da daWi? burin su su farantawa dansu rai da iyakar iyawarsu koda su zasu rasa jin daWin su ne, ba abun da zai ce sai dai yayi godiya ga Allah da irin ni'imomin da yayi masa arayuwa, daga jahili zuwa mai ilmi daga mara asali zuwa mai cikakken asali, daga talaka zuwa hamshakin mai kudi, Allah Ya dawo masa da dukkan Hakkinsa da Elders suka tauye masa, a lokacin fa kwata kwata baya son tunawa da kurkukun kaddara, tun daya hadu da mommynsa Ya shafe babin su a memory din sa, a ranar da Yaji labarin farmaki na biyu da su Owais sukai da kuma nasarar da sukayi harma da shari'ar da akayi Ya ji komai abakin Owais ya kuma gani a labarai, Ya yi farin cikin kawo ?arshen Gidan Kurkukun ?addara da Elders.


A ranar Waurin aurenshi, sukazo Nigeria a privet jet din daddyn sa, a gidan su na estate din suka sauka, Yana ta zumudin ganin yan uwansa da yayi kewa tsawon shekaru, musamman babban amininsa Haris na amana.


Bai tashi haWuwa da su ba, sai a wurin Waurin aure, a masallacin imam malik, kwatsam ba zato ba tsammani sukaga Danish kamar a mafarki Ya zo, suka kasa tunkararshi saboda ruWun da suka shiga, zullumin su kar ace bashi bane wanine mai bala'en kama da shi sai suka dinga satar kallon shi, Dayaga kamar suna kokwanto akansa Saiya nufe su da fara'a ya fada musu cewa shine Danish dinsu bai mutu ba, suka ki yarda har saida Ya labarta musu tukunna suka fashe da kukan farin ciki, Haris Ya rufe shi da fada akan don me ya nisanta kanshi dasu? Meyasa ya tafi yabarsu? Meyasa zai boye musu yana araye? Yasan kuwa halin da suka shiga lokacin da sukaji baya araye"?


Murmushi yadinga sakar musu yana lallashin su dakyar ya shawo kan su suka daina kuka. Kafin ya soma bin su daya bayan daya ya rungume su sunata santin shi badan anyi rayuwar wahala atare ba da ba abunda zai hana su ji shakkar sake mashi saboda da kallo daya suka fahimci Danish din yanzu yafi ?arfin su, yana magana zaka fahimci ilmi ya shige shi ga hutu daya zauna a fatar sa, kamar yadda suke mamakin sauyawar da yayi shima haka yake mamakin sauyawarsu, yaji daWin canjin da kowan nansu ya samu, har yanzu yana son yan uwansa, musamman da suka kara samun kusanci na yan uwantaka ta jini da wasu daga cikin su.


Abun da yafi faranta ran su jin cewa shi ne zai auri Unaisah, yaya Owais kuma zai auri Batool sunyi murna kamar kamar me amma yace masu bayason ta sani su yi shiru karsu fada mata har sai bayan an kaita gidan shi sannan zai bayyana mata kan shi, suma sun goyi bayan ya ba ta mamaki saboda suna son farin cikin ta.

zan iya cewa Salsabeel yafi kowa murnar ganin Danish a lokacin da su ka haWu a masallaci, yaji daWin sauyin rayuwar daya samu, ya kuma ji dadin jin cewa shine zai auri Unaisah, burin sa ya cika, bakinsa ya ?i rufuwa saboda farin ciki, daya rungume shi har saida ?walla ta cika idanun shi, shima Danish din duk sai yaji ba daWi daya nisanta kan shi da su, sun yi kewar juna, hakuri ya dinga bashi yana lallashin shi har saida ya shawo kan shi.

Sheikh imam already yasan shine zai Auri Unaisah tun a ranar da Taj ya kirasa ya sanar da shi komai, amma bai samu halartar gidan ba saboda baya agari, gaba daga a masallaci suka haWu da shi kafin daurin auren.

Bayan kammala Waurin auren, al'ummar Annabi suka dinga taya angwaye murna tare da yi masu fatan Alkhairi.


Daga masallacin gaba daya suka wuce Reception, cikin farin ciki da Wokinsa su ke ta bashi labarin abubuwan da suka faru bayan da babu shi, Yaji dadi sosai harya taya Sajeed murnar ganin yar uwarsa Sajeeda, daya tambayi haris Ya labarin deejan sa? Har yanzu suna son juna? Zai aureta? dariya yayi tare da girgiza kai yace hmmm ai zance Ya 6aci, aurensa da Deeja haramun, saboda uwar su Waya ubansu Waya".


Danish ya yi mamakin jin cewa sha?i?ai ne, duk agurinsu Yaji labarin Unaizah yar gidan daddy da Unaisah yan uwane da kuma alakar su, haka sajeed ma ya'yan kawunta ne jan wuya, ga kuma Cousin dinsa, Yaji daWin kasantuwarsu Ya'yan wa da ?ani,dayake duk bai bibiyi wadannan labaran ba yasan dai kowa an mikashi ga iyayensa, a yadda ya samu labari but baisan su waye iyayensu ba,sai Yan zu ya gane dalilin dayasa su ke bala'en son juna ashe soyayyar su ta jini ce.


Bayan da suka gama shagalin su Tare da Yan uwansa daga Reception suka tafi gidan daddynsa na estate din sunki rabuwa da juna, an dade ba'a haWu ba, wuni yayi tare da su har saida lokacin daukar amarya yayi tukunna sukayi masa sallama kamar karsu rabu suka tafi dauko masa amaryarsa kamar yadda suka tsara.

Kamar Yadda Iyayen Unaisah sukayi mata nasiha akan zamantakewar aure shima haka Iyayen sa su ka yi masa, a ?arshe suka sanya mashi albarka tare da fatan alkhairi arayuwar auran sa.

Daga baya ne Sheikha mujeedat ta shiga gidansu Owais donsu tarbi amarya idan danginta sun kawo ta, dama anan suka nemi alfarmar suna son su fara kawo ta, in yaso daga bisani sai ta kaita gidan angonta da kanta, sunyi hakanne saboda sunfi son Unaisah ta fara ganin sa a matsayin angon ta don su bata mamaki, kafin sauran su san yana araye kuma shi ta aura, haka Batool ma sun boye duk wani abu da zaisa tasan cewa anyi auranta da Owais.



Daddynta bai sanar da su ba, saboda Sun tsara sai daga baya zasu sanar da ita.


Shiyasa suka Wage date din Dinnern Auran su zuwa bayan biki da sati.




*Gaba Waya komai daya faru a cikin shekarun da suka gabata ne zuwa yanzu*



~__________________________________ '?~



Safa da marya ta ke yi a tsakar falo, cikin fushi da bacin rai take doka tsoki, dr shureim Yana a zaune kan sofa, gaba daya babu annuri akan fuskokin su.

damuwa da zullumin Ina Batool Ta shiga Ya hanasu sukuni, fin awa suna neman ta shiru babu ita babu alamarta, kowa suka kira wayarsa sai yace masu baya a tare da ita ko bai ganta ba.

"Pls ummu batool, ki dawo ki zauna mana, In sha Allah ba abun da zai same ta, Ni nasan duk inda taje bazai wuce cikin Houses din da ke a kewaye da mu ba"

Tana huci Tace"ai wallahi idan kaga na zauna to Batool ta dawo gidan nan ne! Zatasan da wa take, kawai don taga ana ji da ita kamar jinjira shine take nema ta manna min hauka! Tare da ita fa mukaje gidansu Owais amma saboda ta raina mana wayou sai ta zame jiki batare da saninmu ba ta kara gaba, awa daya da rabi bata dawo gida ba!da daren nan yarinya budurwa tana garari awaje, Na rasa gane me Batool take so ta zama ne! Ta sauya gaba daya, Ni bazan iya daukar rashin wayon ta ba wlh, dole in dauki mataki akan ta"

akan Batool ta ke yin faWa amma sai yaga kamar da shi take magana saboda yadda take zare mashi idanu tana watsa hannayenta, Tsabar yadda take zazzaga masifa jikinta na girgiza har saida daurin kallabin ta ya karkace.

"Allah Ya huci zuciyarki Ummu Batool, kiyi hakuri, muyi mata uziri bamusan meya tsayar da ita ba tunda ba halin ta bane fita yawon dare ba.. " bata tanka mashi ba, ta ruke qugu tana huci kamar zakanya..

Mikewa yayi"ki shiga ciki ki kwanta, zan koma in ?ara neman ta watakil adace"

"Sai dai kai ka shiga ka kwanta, amma ni banga ta zama ba, Allah ba wanda ya isa ya hanani in bugi batool Yau, da wayar wuta zan zane mata jikin ta.. "

zare ido dr shureim yayi kamar zaiyi dariya yace"amma dai wasa kikeyi ko, Ina ma laifin kiyi mata nasiha, amma Batool ta wuce shekarun bugu, bafa yarinya bace, ta mallakin hankalin ta"

bata kula shi ba, ta juya da niyar ta bar falon, Unexpected su ka jiyo sallamar Batool da ke ?o?arin shigowa falon cikin tafiyar sanWa, ta rungume kayan data cire a kirjinta.

jikinta sai kerma yakeyi saboda zullumin hukuncin da zasu yanke mata, yadda suka dubeta a lokaci daya yasa tasha jinin jikinta, musamman da taga kallon hadarin kajin da Ummi ke watsa mata.

"Daga gidan ubanwa kike"? Kasa yin magana tayi, wata tsawa ta ta daka mata"ba zaki bani amsar tambayana ba? Ina kikaje tsawon lokacin nan?.."


bata ?are maganarba ta lura da kayan jikinta da wadanda ta rungume a hannunta"na shiga ukuna, Batool meya faru da har kika sauya kayanki? Ina kika samu jallabiyar jikinki"? Ta fada cikin fushi ta nufeta kamar damusa.

Dr shureim yabi bayanta yana kokarin dakatar da ita, Batool data rikice arazane Ta juya zata fuce bata kaiga karasawa ba, Ummi tayi saurin sha?o kwalarta kamar zata doke ta ta janyota.

Cikin rawar murya tace"zan yi maki bayani ummi wlh zan fada maki komai, ina atare da Unaisah, Ni na rakata dakinta tare da yan uwan mijinta, abin dayasa na musanya kayana, 6acewa sukayi da Miyar abincin da mukaci a gidan ta.. "


Dakyar ta ?are maganar, Da yake bata saba yi mata karya ba, daga yanayin yadda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login