Showing 231001 words to 234000 words out of 321579 words

Chapter 78 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

Owais ya bata kyautar shi a estate Win su tun da wannan gidan da suke a ciki na Alhaji Musa gwammanti ta kar6e shi, da zarar wa'adin da aka basu ya cika zasu kar6e ginin ne..

Sun ji daWin yadda ta nuna bata son su tafi, dama ba son tafiya suke yi ba, kawai don ba yadda zasu yi ne tunda ba gida gare su a Abuja ba. A ?arshe gaba Wayan su suka koma gidan Hajiya Sarah na Imam Estate, yana da girma da faWi, side by side duplex ne, bangare Waya na Hajiya Sarah da ?a'yanta, Wayan bangaren na su Hajiya Layla ne, babu abun da suka nema suka rasa a gidan, sun ji daWi sosai tsakanin su da ahalin Obie sai godiya da addu'a.

Alhaji Ubaid gaba Waya ya siyar da kadarorinsa na Jos, da kuWaWen yake amfani gurin tafiyar da iyalinsa da na Alhaji Musa, yanzu shi ke Wawainiya da su, don ma Hajiya Sarah tana da arzi?inta, dama can mace ce mai zafin nema babbar ?ar kasuwa ce, daga baya ne ma da gwamnati ta ?wace kadarorin Alhaji Musa itama ta rasa aikin da take yi a companyn sa.


Amma Alhamdulillah yanzu gaba Waya waWanda suka rasa ayyukan su cikin family Win Elders sakamakon abun da ya faru Sharafudeen ya Wauke su aiki a babban companynsa, babu mai zaman banza, Kowa ya na ?o?arin neman na kansa.


Gaba Waya dai Ahlin Elders sun zama tsintsiya Waya maWaurinta Waya, wata irin sha?uwa da zumunci mai ?arfi ne atsakanin su.


Shin ya labarin Zeenatu? tun bayan da tayi doguwar suma sai da ta shafe makonni bata dawo hayyacinta ba, tana a ?ar?ashin kulawar docs, bayan shari'ar Elders da sati Waya, Zeenatu ta farfaWo cikin hayyacinta, mommynta da ?an uwanta sun yi murna sosai, har kukan farin ciki suka yi duk da a lokacin bata magana sai dai idanunta da ke tsiyayar da hawaye, sun fahimci har yanzu da damuwar abun a ranta, bayan doc ya sallame ta suka dawo gida da ita, tsantsar kulawa suke bata, kwata kwata bata tambayi ina daddynta ba, saboda tsanar da ta yi mashi ko sunan shi bata son ji, kuma wani iko na Allah Zeenatu ta daina son Yaya Shureim da aure, b??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????abu soyayya a ranta, da suna ta zullumin tayaya zasu faWa mata game da soyayyar Shureim da Aisha amma da suka lura babu son shi a ranta, yanzu kallon Wan uwa kuma Yaya take yi masa sai suka godewa Allah da ya kawo masu mafita, bakomai ne ya faranta ran Zeenatu ba, face ganin tagwayen da mommynta ke ru?o, har tambayarta ta yi su wanene? Nan Hajiya Sarah ta labarta mata komai game da su, ta tausaya ma rayuwarsu, ta kuma ji daWi da ya kasance mommynta ne zata ci gaba da ru?on su, da kallo Waya ta ji ta kamu da ?aunar su, suma haka suka ji, yanzu ta samu tsararrakinta a gidan duk da sun girme ta da shekara Waya.


Batare da 6ata lokaci ba, Alhaji Ubaid ya mayar da su school, daga jami'a suka fara shi ya yi masu ?o?ari gurin sama masu takardun secondary da kuma admission na shiga jami'a da taimakon Owais.

A baya kafin zuwan su twins kurkukun ?addara sun yi karatu harma sun kammala secondary, shiyasa karatun su ya zo musu da sau?i, gaba Wayan su yanzu suna a jami'a, sajeed Yana karantar Cybersecurity, yayin da Zeenatu da Sajeeda suke karantar Human Rights, su suka za6a da kansu saboda suna da burin su bada gudummuwa gurin kare hakkin Wan adam.


bayan haka kuma suna zuwa islamiya wadda ke a cikin estate Win neman ilimin addini sun bada himma sosai.

Hajiya Sarah ta yi namijin ?o?ari gurin tafiyar da rayuwar su, babu abun da suka nema suka rasa da arzi?inta ta ke kula da su, ba zaka ta6a gane ba ita ta haifi twins ba sai in an faWa maka, haka zalika Alhaji Ubaid da Hajiya Layla suna bada gudummuwa gurin tallafa mata akan kula da yaran, Shureim da Benazir da Omar ma ba abar su a baya ba, suna ?o?ari gurin koya masu abun da basu iya ba, sun zama yayye nagari a gare su.


A zahirin gaskiya rayuwar Prisoners a gurin iyayen su sai son barka, wata irin soyayya suke nuna masu, tsantsar gatanci, kulawa da tarairaya kamar jinjirai, sai abun da suke so iyayen su suke yi masu, gaba Waya sun sanya su a school Win cikin estate Win su bayan private teachers Win da ke zuwa yi masu lessons na boko dana islamiya a cikin home classroom din su.


Yara fa sun zama ?a'yan mommy da daddy, hutu ya zauna masu, babu tashin hankali babu damuwa, sai zallar farin ciki da jin daWin rayuwa, in ka gansu ba zaka ta6a yarda sun yi rayuwar ?unci a gidan kurkukun ?addara ba, su kan su mantawa suke yi da sun ta6a shan wahala a rayuwar su, Yanzu sun waye, ilimin boko da na addini ya shiga kan su, halayan su da Wabi'un su sun sauya, lamarin Ubangiji kenan, gwanin hikima, mai yin yadda ya so, mai jujjuya al'amurra, godiya ta tabbata ga Allah maWaukakin Sarki =?Q?

Bayan da ?ura ta lafa, kwanciyar hankali da farin ciki suka wanzu a zukatansu, bayan shekara Waya da rabi Dr Shureim ya auri Aisha, yayin da Taj ya mayar da Benazir Wakinta, Owais ya auri Nazli, A canada aka yi shagalin bikin su na gani na faWa, ya so ya haWa da Unaisah ya aure su a rana Waya amma ta nuna bata shirya ba, tafi so ta kammala karatunta, bai musa mata ba, shima ya goyi bayan ta yi karatu, da taimakonsa ya yi mata hanya ta zana jarabawar ssce batare da ta shiga ss one ba, dama a baya kafin ?addara ta kaita kurkukun ?addara ta kammala junior secondary, shiyasa karatun nata ya zo mata da sau?i, tana a jami'ar da su Sajeed suke, anan take karantar Computer Science, Owais ya yi masu al?awarin in har suka kammala karatunsu zasu Wauke su aiki a hukumar su ta Isod saboda suna bu?atar irin su.


Tun farko abun da ya sa Unaisah ta ?i yarda ya aure su a rana Waya ita da Nazli saboda tana jin shakkar ta zama kishiyar Nazli wayayyar ?ar gayu, tafi son ta ?ara wayewa ta yi zurfi a ilimi sannan ta koyi abubuwan da bata iya ba don kada Nazli ta raina ta, a yanzu ta dage damtse gurin koyon girki a wurin mommynta, kuma ta bada himma sosai gurin karatunta, bata wasa da yake Allah ya yi ta da brain she's gifted, tana da baiwar haddace karatu da saurin koyo shiyasa bata jin wahalar komai.


Bayan da ya auri Nazli sai da ya yi hutun wata biyu a gidansa na Canada tare da amaryarsa Nazli, gaba Waya suka sauke girman kai da izzar su suka nuna ma juna soyayya, tun a first night Winsu suka raya daren su, daga bisani suka tafi honeymoon.


Owais bai tashi dawowa Nigeria ba, sai lokacin bikin Omar da Salsabeel, kuma shi ya haWa Omar da matar da zai aura, bakowa bace face ?anwarsa Hindu, yayin da Momma ta haWa Auran Salsabeel da Yusra ?ar gidan his excellency Abdul razak, kuma cikin sa'a jinin su ya haWu, duk da a lokacin da momma ta zo mashi da maganar Yusra, ya ji shakkar haWa shi da ita saboda yasan tafi ?arfin shi, gata dai Wiyar gwamna, wayayya, kyakkyawar budurwa, jinin shuwa, a da kafin yanzu tana da girman kai da izza, amma tun bayan faruwar lamarin nan ta sauya hali, ta zama mutuniyar kirki, koda momma ta faWa mata game da Salsabeel ta kuma nuna mata hoton shi a waya, nan take ta ce ta amince in har yana sonta, zata aure shi, amma tana son bayan sun yi aure ya koma makaranta ya nemi ilimi, itama zata taimaka mashi, Salsabeel ya yi farin ciki mara misaltuwa a lokacin da momma ta faWa mashi yadda suka yi da Yusra, har sujjada ya yi don nuna godiyar sa ga Allah, Auran gata Momma ta yi ma Salsabeel, ko sisin shi bai kashe ba, tun daga lefensa har sadaki ita ta bayar, har kuka saida ya yi mata saboda farin ciki, A ranar bikin su anyi gagarumin shagali a Imam Estate, amare sun tare a gidajen mazajen su, abun sai son barka.


Idan muka koma bangaren Faryat, reshe ne ya juye da mujiya, yanzu ita ke son Jazz shi kuma yana ja mata aji, ta sauya hali ta nutsu ta koma tagari, ta daina duk wani abu mara kyau da take yi, amma Jazz ya ?i sauraron ta, wahalar da ita yake yi, kusan kullum sai ta yi kuka saboda azabtuwar da ta ke yi da son shi, idan ta kira wayarsa baya picking, ko sa?o ta tura mashi baya mata reply, a ?arshe ma ya yi blocking duk wata hanya da zata haWa su, har gidansu ta zo gaban mommynsa ta zu?unna kan gwiwowinta tana kuka sha6e sha6e ta dinga ro?onta akan ta sasanta tsakaninta da Jazz in har bata aure sa ba mutuwa zata yi, shi kaWai take so, ta yi danasanin komai da ta yi masa, ta tuba.

Turai ta tausaya mata musamman da ta ga ta gyara rayuwarta, ko shigar banza ta dai na yi, kullum cikin hijabi da jan cazbaha take, ta ce mata ta yi ha?uri zata yi magana da shi, amma ta Wan Waga ?afa saboda a yanzu jazz fushi ya ke yi da ita, ta bari sai lokacin da ya huce in sha Allah zata ci gaba da lallashin shi, da ?yar ta shawo kan Faryat har ta samu ta koma gida, sai da ta kai ga kullum da zazza6i take kwana duk don saboda Jazz, Hajiya Saratu tasan komai da ke faruwa tsakanin Jazz da Faryat, amma bata sanya baki ba, saboda tana jin kunyar Jazz da Mahaifiyarsa, tsakaninta da Faryat addu'a ne da ta ke yi mata da kuma lallashinta.

Shi kan shi Jazz Win ba don ya daina sonta ba yake share ta, sai don yana son ta ji irin raWaWin da shima ya ji a lokacin da ta ke yi masa wula?anci saboda ta ga ya mutu akan ?aunar ta, amma har lokacin bai daina sonta ba, yana da burin auranta.... =ؔ?


A bangaren Zayn ya yi nadama tun bayan afkuwar lamarin, ya shiryu ya sauya halayensa daga munana zuwa kyawawa, ya zama mutumin kirki, ya daina biyewa matan banza daga shi har Zaid yanzu basu wasa da ibadar su ko a masallaci sune a sahun gaba, sa6anin da ko masallacin basu zuwa sai an tasa ?eyar su suke zuwa yin sallah.

Soyayyar Zahra kullum ?ara nunkuwa take yi a cikin zuciyarsa, sai dai ya kasa tunkararta da maganar saboda kunyar wula?ancin da ya yi mata a baya, duk da itama yasan hada mahaifinta a cikin elders, ?addarar su iri Waya, amma yana jin shakkun ya je gareta, gudun kada ta juya masa baya ko ta kore shi, da damuwa ta ishe shi ya kasa dannewa ya faWa ma Zaid halin da yake a ciki, Zaid ya shawarce shi da ya shirya su je gidan su Zahran ya nemi yafiyarta yasan zata yafe mashi saboda yasan Zahra tana son shi.

A ranar da su ka je gidan su Zahra, bayan sun yi parking suka kasa fitowa su shiga ciki saboda zullumi, har sai da Abie ya fito daga gidan zai tafi Office ya hango ba?uwar mota a harabar gidan, suna ganin shi suka fito tare da nufar shi cikin girmamawa suka gaishe shi ya amsa masu da fara'a ya ce baigane su wanene ba kamar ?an'uwan Owais, har suna haWa baki gurin cewa eh ?an uwansa ne su, ?a'yan Hajiya Saratu sun zo ne suna son ganin Zahra, murmushi Abie ya yi ya ce su shiga daga ciki, godiya suka yi mashi tare da wucewa cikin gidan.

Sallamar su ce ta katse karatun ?ur'anin da Mahboob ya ke yi, sai da ya kai ?arshen ayar da ya janyo, tukunna ya dube su yayin da yake akan kujera ru?e da kur'ani, da murmushi ya amsa masu sallamar, sun ji daWin sakin fuskar da ya yi musu.

Mahboob kenan bawan Allah tun bayan mutuwar Ana ya canza, yanzu gudun abun duniya ya ke yi, baya son kuWi tun da ya ga yadda suke kai mutun ga halaka ya ji sun fita a ran shi.

A yanzu daka bashi kyautar kuWi tsurar su ?wara ka siya masa wani abu ka bashi saboda baya kar6ar kuWi, har kawo wannan lokacin bai daina yiwa Ana addu'a ba, tana a ran shi, a duk lokacin da ya tuna zaluncin da mahaifinsu ya yi mata sai ya ji Waci a ran shi.

Bayan sun shiga cikin falon ya nuna masu sofas suka zauna, ya mi?a masu hannu suka yi musabaha, daga bisani Zaid Ya tambayesa ina mutanan gidan? ya ce su Umminsu basa nan sun tafi anguwa, amma Zahra tana a Waki tana bacci.

Sun ji daWin jin tana nan, Zaid ya ce ya kira masu ita in ba damuwa, mi?ewa ya yi ya nufi Wakin Zahra ya yi sallama daga ciki ta amsa mashi, farkawar ta kenan daga bacci, bayan da ya faWa mata ba?in da ke neman ta, ta yi mamakin jin zuwan Zayn, mutumin da ta sani da girman kai, tana kokwanton in shine! Me ma ya kawo shi gidansu nemanta bayan baya son ta? A ranta ta faWa, har tambayar Mahboob ta yi ta ce ya kuwa tabbatar shi Winne ya zo? Yana murmushi ya ce mata da gaske shine ya zo tare da twin brother Winsa Zaid.

Cikin sauri ta sauko daga kan gadon ta shiga toilet, kafin fitowarta Mahboob ya wuce bedroom Winsa don ya basu guri su zanta.

Bayan ta fito daga toilet shaf shaf ta shirya kanta cikin abaya, ta fito ta nufi falon, tunkan ta ?arasa ta hango su, har saida gabanta ya Wan faWi ganin abun da bata zata ba..

Zama ta yi kan sofa Win dake fuskantar su, ta yi masu barka da zuwa, bayan sun gaisa kowannansu ya yi shiru, sam Zayn ya kasa haWa idanunshi da nata saboda nauyinta da yake ji amma ganinta da ya yi ya sanyaya zuciyar sa sosai, yana jin in har ya mallaketa zata sama masa farin cikin da ya rasa a rayuwarsa.

Jin sunyi shiru sun kasa magana yasa Zaid yanke shawarar fara gabatar mata da abun da ya kawo su..

Cikin nutsuwa ya fayyace mata komai ya ce yasan Wan uwansa bai kyauta mata ba, ya yi mata wula?anci a baya, amma a yanzu ya yi nadama tun bayan fallasuwar sirrin grandpa Winsu da daddyn su sun sauya halinsu, koda can Zayn yana sonta, shi shaida ne saboda baida hira da ta wuce tata, amma a lokacin girman kai ne yasa bai nuna mata so ba.

Tun da ya fara yin maganar Zahra ta zare idanunta cike da mamaki take sauraron Zaid..

Bai ?are maganar ba, Zayn ya kar6e da cewa, "Wallahi na shiryu Zahra, na gyara halayena, Ki tausaya ma rayuwana, nasan kin daina sona a yanzu amma ki yi ha?uri ki yafe min abun da na yi maki a baya, na yi danasani kuma wallahi ina son ki, in har kika bani dama zan nuna maki irin ?aunar da na ke maki.

Tsantsar farin ciki ne ya lullu6e zuciyarta tsabar murna kamar ta zuba ruwa ?asa ta sha amma kwata kwata bata bari ya gane ba, baiwar Allah tun bayan abun kunyar da ubansu ya aikata bata ?ara samun farin ciki irin na yau ba.

Da suka ga ta yi shiru babu fara'a akan fuskarta sai suka yi tunanin bata ji daWin zuwan su bane, Zaid ya ce ta yi ha?uri idan kalamansu sun 6ata mata rai, za su tafi amma ta zauna tayi tunani idan ta yanke shawara ta sanar da su..

Ya ?arashe maganar cikin sanyin murya tare da ru?o hannun Zayn da ya tsareta da idanunshi, shi kaWai yasan me yake ji a game da ita, baya jin zai iya ha?ura su koma gida batare da Zahra ta faWa masa ra'ayinta akan shi ba.

Zame hannunsa ya yi daga na Zaid ya mi?e daga kan kujerar ya je gaban sofa din da take a zaune ya yi kneeling a gaban ta, wani yanayi ta ji mara misaltuwa, ta kasa haWa idanunta da nashi, cikin karyayyar murya ya ce, "Bazan iya tafiya batare da kin yafe min ba, nasan har yanzu kina fushi da ni, amma ki yi ha?uri Zahra! ki taimaki rayuwana, ki rufa min asiri, a halin yanzu zan iya ha?ura da komai amma banda ke! Wallahi ban zo don na 6ata maki lokaci ba, Auren ki nake so na yi.. "

idanunsa cike tab da ?walla ya ?arashe maganar, ji tayi kamar ta fashe da kuka saboda tausayin shi, cikin sauri ta ce ya tashi ya zauna, ya girgiza mata kai tare da cewa in har tana son ya mi?e toh ta faWa masa me ta yanke akan shi.

Shiru ta yi tana tunani, a ranta ta ayyana Allah ne ya kar6i addu'arta, ta daWe tana ro?on Allah ya karkato da hankalin Zayn akanta in alkhairi ne shi a rayuwarta, saboda tana son shi tana son ya zama mijin ta, sai gashi ya zo mata a lokacin da take bu?atar wanda zai rufa mata asiri, saboda samarin da take da su duk sun juya mata baya saboda abun kunyar da ubansu ya aikata amma yanzu ta yi farin ciki da zuwan Zayn saboda tasan ?addararsu Waya ce idan suka yi aure zasu rufawa kansu asiri, babu wanda zai goranta ma wani..

Numfasawa ta yi da Wan murmushi akan fuskarta ta ce, "Ni ban fara son ka don in daina ba, har yanzu ina son ka, zan iya cewa na fi kowa farin ciki da ka gyara halayen ka, kuma na yi murnar ganin ka, sannan shawarar da na yanke na amince zan aure ka Zayn.. "

Bata ?arashe maganar ba, ta ga ya yi sujjada yana kukan farin ciki, batasan sa'adda ta ji hawaye sun wanke fuskarta ba saboda daWin da ta ji..

Hatta Zaid dake kallon su saida ya ji ?walla ta cika idanunshi, ya tausaya musu ya kuma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login