Showing 201001 words to 204000 words out of 321579 words

Chapter 68 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

kuma abun da zaka taras a cikin kabarinka na sakamakon zunubin da ka aikata. Na tsaneka, kai ba abun a tausayamawa bane, mahaifin mu bashi ya jefa ka a halin da kake a ciki ba, saboda shi ba Allah ba ne da in ya ce ka yi abu ya zama dole ka yi, bayan haka, meyasa lokacin da ya yi maka ta yi baka fallasa asirinsa ba, ko da zai kashe ka ne ka ?i amince masa, yanzu bala'en da kake a ciki ko mutuwa ba zata zama hutu a gare ka ba wlh. Praveen ka shiga uku! kana cikin musiba dumu dumu, ina taya ka murna sai mun haWu a kotu.

Ta ?arashe maganar idanunta cike tab da ?walla tare da murmushin takaici akan fuskarta.

Bai ta6a jin karayar zuciya da danasani irin na wannan lokacin ba, baisan sa'adda ya fashe da kuka ba kamar ransa zai fita


"Praveen yanzu ba lokacin kuka bane, lokaci ne da zaka fara tunanin menene makomarka! Ai ba ka ga komai ba, shawarar da zan baka shine, ka daure ka tanadi hawayenka, zuwa lokacin da al?ali zai yanke maku hukunci..."

Yana kuka hadda majina ya ce, "Ki taimaka min Saratu! Ki taimaki rayuwana, in har da gaske kin yafe min ki sa baki, su yafe min su fitar da ni daga ciki, ko don albarkacin ?a'?an mu, wlh na tuba, na bi Allah, na yi danasani zan sauya rayuwata, zan ma nisanta kaina da kowa..."



Girgiza kai hajiya Saratu ta yi, "Praveen babu mafita, babu taimakon da zan iya yi maka, ka riga da ka jagula komai, kai koda zan iya fitar da kai Allah ba zai ?yale ka ba, dole ka ga sakayyar rayukan da kuka zalunta, don haka ka yi ha?uri kawai ka girbi abun da ka shuka. Taimako Waya da zan iya yi maka shine zan ro?i yayyena, su bar Hajjaty ta ci gaba da zama cikin mu, saboda na tausaya mata bayan da na ji tarihin rayuwar ku, in sha Allah Hajjaty ba zata wula?anta ba, zamu zama danginta daga nan har ?arshen rayuwarta, ba zata yi maraicin rashin wani nata ba.."

ta Wan dakata da yin maganar tana Wan girgiza kan ta kafin ta Waura da cewa,

"?a'?an mu zasu kasance ?ar?ashin kulawar yayyena da kuma ni! Ba za su yi maraici ba, bayan da suka san komai da ka aikata sun tsaneka fiye da yadda suka tsani mutuwarsu, wlh da zasu ganka ido da ido da sai sun kashe ka har lahira, amma karka da mu, zan sama musu uba na gari wanda zasu yi alfahari da shi!"

tana ?arashe maganar ta katse video call din.


Komai da suke tattaunawa, observers suna kallon su ta Computer Win su.


Wata irin ?ara mai cike da ba?inci ya fasa, ya kama kuka kamar ransa zai fita, ya dinga yi ma Owais magiya akan su yafe masa kar su hukunta shi, ba laifinsa bane, baba Obie ne ya ja ma shi.



Owais bai saurare shi ba, ya mi?e ya fuce daga cell Win,

Har ya fita yana jiyo ihun da Praveen ke yi kamar zai fasa dodon kunnan sa.




*On the previous days (kwanakin baya)*




*HAJIYA ADAMA=ؔ?*



Tana a zaune kan darduma jikinta sanye da hijab, wayarta dake ajiye kan gado ta fara ringing, saida ta kammala addu'o'in da ta ke yi ta mi?e cike da sa ran surukanta ne ke kira saboda ta yi kewar su.

?aukar wayar ta yi tare da duba sunan me kiranta, ?anwarta ce Fatima, picking call Win ta yi, tana kara wayar a kunne ko sallama ba ta yi ba, muryar fatima ta katse ta da tashin hankali ta ce, "Aunty kin ji abun da ke faruwa?"

"Wani abu ne kike magana akai fatima?"

"Wai kina nufin bakisan bada?alar da ake yi a cikin ?asar nan ba?" Yamutsa fuska ta yi, "Look, kada ki Waga min hankali, kawai ki faWa min menene?"



"Hmmm, Aunty labari da Wumi Wuminsa, baya faWuwa da baki, ki yi maza maza ki shiga social media ki gane wa idonki."


Cikin sauri ta katse kiran, tana kunna wi-fi ta fara cin karo da labarai iri iri na Kurkukun ?addara, tun tana daga tsaye har ta fara ganin jiri jiri jikinta na 6ari ta zauna tana ci gaba da bibiyar labaran.


Tiryan tiryan ta karance shi tsaf, hankalinta ya tashi matu?a, ta razana ta kuma kiWima, hotunan fursinonin ta buWo tana duddubawa unexpected ta fara cin karo da video din Angel da Batool, zumbur ta mi?e tana zare idanunta, muryarta na rawa ta furta, "Bab...baby Angel! Angel!! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un.. !"



RuWu ne yasa ta saki wayar ?asa ta futo a guje ta nufi falo don ta faWa ma Abdalla, tana shigowa ta iske shi zaune kan kujera sai kuka yake yi kamar ?aramin yaro, zufa duk ta wanke jikin shi, ya tasa plasma tv a gaba yana ta kallon tattaunawar su Dg da manema labarai.



Yama fita shiga tashin hankali, nufar shi ta yi, cikin rawar murya ta ce, "Mijina kaima ka gani ko? Yanzu nake ganin labarin da ya tada hankalina! Ka ga Unaisah da Taj suna a raye, kuma ka ji mummunar ?addarar da ta faWa masu..?" Idanunta suka cicciko tab da ?walla ta zauna gefen shi, tare da dafa kafaWar shi, sai kuka yake yana kallon labaran, jikin shi har wani jijjiga ya ke yi.


Cikin shesshekar kuka ta ce, "Tun da har Taj da Unaisah suna a raye, wata?il shima Uzair yana a raye, ya kamata mu tashi mu tafi gurin su..." Girgiza mata kai ya yi hawaye na sauka kan kuncin shi ya dubeta da idanunshi waWanda suka kaWa jawur, "Akwai abun da na daWe ina 6oye maki, amma yanzu tun da asirin su ya tonu gaskiya ta yi halinta, nima zan bayyana maki komai..."


Wani irin faWuwar gaba ta ji, a dabarbarce ta furta, "Bana son ji, pls kada ka faWamin in dai kasan ba alkhairi bane, ka barni kawai in ji da abun da ke damuna"

Mi?ewa ya yi tsaye. "Ya zama dole ki sani Adama.." mi?ewa ta yi tsaye itama tana zare idanunta cike da fargaban abun da zai sanar da ita.

"Kada kace min kana Waya daga cikin su!"


Wani irin kallo ya ke yi mata



"Bana Waya daga cikin su, amma akwai wani abu da ya ta6a haWa ni da Waya daga cikin su, wanda ya yi silar samuwar arzi?i na!"


Da tsawa ta katse shi, "Are you out of your mind! Abdallah me ka aikata? Waye ka sani a cikin su? Tayaya ya zama silar samuwar arzi?in ka ? Ko hakan na nufin kaima ka ta6a sadaukar da wani naka??" Sam ya kasa cigaba da magana saboda fargaban yadda zata Wauki abun.


"Kada ka ce min kaine ka yi silar 6acewar su Uzair!" Ta faWa tare da kama kwalar rigar shi da hannayen ta dake ta kerma..



"Assalamu Alaikum." A kunnansu suka tsinkayi muyarsa, hakan yasa suka dakata da maganar da suke yi,

Kusan atare suka dubi kofar falon jin muryar mutumin da suka daWe basu ji ta ba, wani irin annurin farin ciki ne ya cika su duk da halin da suke ciki, har suna haWa baki gurin furta "TAJUDDEEN."


Yana a tsaye bakin kofar falo fuskarsa Wauke da murmushin farin ciki ya amsa da na'am mommy Adama and My Only Uncle.


Cikin sauri ta nufe shi, suka yi hugging din juna, ta Wago tana shafa fuskarshi ta ce, "Taj, dama kuna a raye baku ta6a neman mu ba Taj?" Tsawon shekara bakwai! kasan irin neman da muka yi maku kuwa? Meyasa baka tuntu6e mu ba?" Ta faWa fuskarta a yamutse, hawaye sai sintiri suke kan kuncinta, daga yanayin su ya fahimci sun ji komai.


Matsowa kusa da Uncle Abdallah ya yi, da sauri ya rungume Taj kamar zai mayar da shi cikin shi..


Sai ya ji kamar ya haWa jikin shi dana mahaifin shi Zaheer, saboda Uncle Abdallah madadinsa ne, shi kaWaibne shakikin mahaifinsa kuma Wan uwansa na kusa da ya rage masa a duniya.



Haka Uncle Abdallah shima ya ji kamar ya rungume mahaifinsa Zaheer, sun yi kewar juna.


"Alhamdulillah! Taj, ashe da rabon zamu gana da juna? bayan tsawon lokaci da muka neme ku muka rasa? Taj ka ga yarda ka manyanta? Ka ?ara girma ka yi kyau.."


Ya faWa bayan ya raba jikinshi daga na Taj ya dafe kafaWunsa da tafukansa, idanunsu a cikin na juna, kamar yadda yake mamakin sauyawarshi shima haka yake mamakin tsufan da Uncle Win nasa ya fara.


"Na yi kewarka Taj. Na ji komai da ya faru da ku, yanzu muka gama kallo a news."


"Taj Ina Uzair? Ina Angel? Nasan suna a tare da kai." Hajiya Adama ce ta faWa cike da ?aguwa.

Numfasawa ya yi tare da cewa, "Ku yi ha?uri na yi laifi da ban faWa maku ba, amma nima bada son raina na ba, ya zama wajibi mu 6oye kanmu idan ba haka ba masu farautar rayuwar mu za su kashe mu ne, amma bamu manta da ku ba, kuna aran mu ko yaushe, mu ma mun yi kewar ku sosai."

"Amma Taj, ko a waya ai ka kira ka sanar da mu kuna nan, kasan halin damuwar dana shiga na rashin ku?"

"Uncle, Dg shine ya hana kowa yasan muna a raye, kuma shi ne ya taimaki rayuwar mu.."


Jinjina kai Abdallah ya yi, "Allah ya saka masa da alkhairi, na ji dadin ganinka Taj, mu shiga ciki mu zauna, amma tayaya akai kasan inda muke?" Ya faWa tare da ru?e hannunsa ya nufi Sofa da shi, hajiya Adama tabi bayansu baiwar Allah duk ta ?agu da ta ji ina Uzair Win ta..

Bayan sun zauna, Hajiya Adama ta shiga kitchen don ta hada mashi abun da zai ci, sai zumudi take yi..

Duk in ya kalli Uncle Win nasa sai ya ga kamar Uzair saboda kamannin shi dake a kan fuskarsa.

"Taj, ka yi ha?uri ban baka kulawar da ya dace ba, gani nake kamar komai da ya faru laifina ne Taj, zamana Korea bai amfanar da ni komai ba, da a ce ina kusa da ku wata?il da hakan bai faru ba.." Ya faWa tamkar zai fashe da kuka.

A hankali Taj ya Waura tafin hannunsa kan kuncinsa ya soma share masa ?wallarsa.

"Pls Uncle mu manta da komai da ya faru, tunawar baida amfani.."


"Taj, ba zaka gane ba, akwai damuwa a tare da ni, ina jin ciwon abun a raina.." Ru?o hannayensa Taj ya yi, "Uncle, nima na fahimci halin da ka ke a ciki, nasan bai wuci akan Wan uwana uzair bane ko?" Maimakon ya amsa mashi tambayar shi sai cewa ya yi.


"Baka bani amsa ta ba, tayaya kasan inda muke da zama?" Ya kuma tambaya.

Murmushi Taj ya yi, "Anila ce ta tura min da address naku."


"Masha Allah, ashe kun haWu da ita" Jinjina kai ya yi, "Eh..." Bai ?are maganar ba, Hajiya Adama ta shigo falon hannayenta ru?e da tray na kayan abinci ta Waura akan c-table.


"Nagode mommy, har yanzu kina nan yadda na sanki."


Murmushi ta yi kawai.

"Bari na WanWana girkin mommyna na yi missing na shi." Murmushi suka saki suna kallon shi yayin da ya soma cin abincin sai santi yake yi masu, in ya yi wani abun sai ya dinga tuna masu da Uzair, Wabi'unsu iri Waya sak..

Bayan da ya kammala ci, ya maida hankalinshi akan su.

"Taj, har yanzu baka amsa min tambayana ba? Ina Uzair?"

HaWa ido suka yi da Abdallah, da kai ya yi masa alamar kar ya faWa mata, dubanta ya yi in a cool voice ya ce,


"Mommy, lokacin da abun ya faru ba a tare da Uzair muka bar gida ba..." A ta?aice ya labarta mata komai da ya faru bai dai faWa mata game da irin mutuwar da uzair ya yi ba.


Tashin hankali ne tsantsa akan fuskokinsu, sun shiga damuwa sosai, kwantar masu da hankali ya shiga yi.

"Yanzu haka Angel tana a tare da mommynta a gidan dg.."

"Taj, komai da muka ji game da kurkukun kaddara da gaske ne? Don ni wlh ji na yi kamar shirin film ne ko irin hausa novel, saboda yadda kaina ya Waure, ko a tarihi ban ta6a jin labarin da ya ta6a zuciyata irin shi ba." hajiya Adama ce ta tambaya tana kallon shi,

Jinjina masu kai ya yi cike da tabbaci ya ce, "da gaske ne komai da kuka ji"

"Meyasa ba ka zo mana da Unaisah ba?"

"Zuwa nan gaba in sha Allah zan zo maku da ita har ma da mommynta"


Tun da suka fara magana Uncle Abdalla bai sanya baki ba, gaba Wayansa babu walwala a tattare da shi, Taj ya lura da yanayin shi.



Firar yaushe rabo suka yi cikin raha da annushuwa..

Kiran sallar azhar da aka fara yi ne ya katse masu firar ta su..

A tare da Uncle Abdallah suka tafi Masallaci..

Hajiya Adama ta zauna tana ta jiran su dawo, burinta ta ji menene Abdallah yake son sanar da ita? duk da tana jin zullumi da fargaban abun da zata ji.

Bayan da suka dawo daga masallaci, Uncle Abdallah ya ru?e hannun Taj ya ja shi suka zagaya daga bayan gidan, kan kujerun sha?atawa suka zauna suna fuskantar juna..

"Taj, na ji dadi da Allah ya bayyana mun kai da ranka da lafiyarka, tsawon lokaci ina addu'a akan Allah ya bayyana min ku cikin ?oshin lafiya.."

Murmushi taj ya yi, ya ji daWin maganarsa.

"Nima haka Uncle, na ji dadi dana same ku da ranku da lafiyarku, na yi farin ciki mara misaltuwa.."

Shuru suka Wan yi na wani lokaci Taj ya lura da yanayin fuskar Uncle din nasa..

"Uncle, na fahimci akwai abun da ke damunka, kuma akwai abun da ka ke son faWamin tun zuwa na na lura da hakan, don Allah ka sanar dani.."

Shuru ya Wan yi jimm kamar yana jin shakkun ya faWa


"Tajo, ina so ka fara fadamin gaskiyar meya faru da ku! Uzair yana a raye ko ya mutu? Pls kada ka 6oye min, ni ba yaro bane, kafin wannan anyi min rasuwa, na rasa iyayena da yayana mafi soyuwa a gare ni, a yanzu babu abun da bazan iya jurewa ba, saboda na yi imani da ?addara"


Jinjina kai Taj ya yi, kalamansa sun sa shi jin zai iya faWa masa..

A tsanake ya labarta masa komai da ya faru lokacin da Uzair ya kira sa a waya cikin tashin hankali ya sanar da shi abun da ke faruwa da shi, bai dai ce sun ?ona Uzair ba, amma ya ce mishi su yi ha?uri su fidda rai da Uzair saboda babu shi a raye, shekara bakwai da rasuwarsa yanzu."


Girgiza kai Uncle Abdallah ya yi idanunsa sun ciko tab da ?walla, ya ji zafin mutuwar Uzair dama saida ran shi ya bashi baya a raye, wani ba?in ciki ne ya mamaye zuciyarsa, dafe kansa ya yi da tafin hannunsa yana tariyo rayuwar sa da Wansa mafi soyuwa agare sa, yanzu shike nan ya rasa Uzair babu shi a doron duniya? Uzair ya mutu? Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un! Ya faWa a cikin ran shi.

Taj da ke kallonsa jikinsa ya yi sanyi da ganin halin da Uncle din nasa ya shiga.

"Ka yi ha?uri Uncle, nasan dole ka ji zafin mutuwar Uzair.." Bai ?are maganar ba, Uncle abdallah ya katse shi cikin raunanniyar murya ya furta, "Bakomai Taj, dukkan mai rai mamaci ne, nagode daka faWa min. Allah Ya ji?an Uzair, Allah ya gafarta masa, Allah ya kai rahama ?abarinsa." Amsa masa ya yi da ameen ameen,


"Su kuma waWanda suka yi silar mutuwar shi Ubangiji Allah Ya wula?anta rayuwar su, in sha Allah zasu ga sakayyar abun da suka yi masa.." Shiru suka yi jigum kowa da damuwa a cikin ran shi.


Har na tsawon mintuna babu wanda ya tanka a cikin su.


"Taj, dagaske kun kama Elders kamar yadda na ji a labarai?"


Jinjina mashi kai ya yi, "Hakane Uncle, mun kama su, yanzu haka suna a cikin cell na headquarter Win mu."


"Alhamdulillah, na ji daWi da Allah ya fallasa asirin su. Don Allah Taj kada ku raga musu, ku azabtar da su har sai sun tsani rayuwar su..."


Murmushi Taj ya yi, "kar ka damu Uncle, yanzu haka idan ka gansu saika tausaya musu saboda raunukan dake a jikin su.." Ya faWa da zolaya, wani kallo Uncle Abdallah ya yi masa. "Allah Ya kiyaye inji tausayin su, ai sai dai ma inyi masu Allah shi ?ara.." ?ar dariya Taj ya yi.


"Idan muna fira da kai, sai in ji kamar yayana ne Zahir saboda komai naku iri Waya, na yi rashi Taj, Allah ya ji?an shi da rahama." Zuciyar Taj ce ta karaya tunawa da mahaifin nasa, "Ameen" ya amsa..


"Allah Ya ji?an Yahanasu da mama, Allah Ya kyautata makwancinsu."

hawaye ne ya ji sun ciko idanunsa.


Amsawa ya yi da, "Ameen don son Annabi."


Shiru suka yi na wani lokaci, still ya lura da akwai abun da Uncle Win nasa yake son sanar da shi, kamar yana jin shakkar fitarwa ne.


"Uncle, idan akwai abun da kake son faWa min pls kada ka ji komai ka sanar da ni, a yanzu bani da tamkarka kaima haka."


jinjina kai Uncle Abdallah ya yi, "Ka faWi gaskiya Taj, da akwai abun da nake son sanar da kai, duk da ina jin fargaban yadda zaka ji abun a ranka, amma zan sanar da kai saboda inaso ka taimaka min, ita kaWai ce damar da nake da ita."


ya Wan numfashi kafin ya Waura da cewa,


"Shekarun baya da suka gabata, Hajiya Adama ta ta6a yin matsananciyar rashin lafiya kamar bazata rayu ba, bayan da likitoci suka duba ta sai suka gano ta samu matsalar da sai anyi mata tiyata zata samu lafiya, kuma in har ba ayi saurin yi mata ba zata iya rasa ranta, ni kuma a lokacin bani da halin da zan iya biyan kuWin da suka bu?ata, bani da wani wanda zai tallafa min saboda iyayen mu ba hali gare su ba, yayana ma baida kudin da zai iya taimaka mun da su, shima fama yake yi da iyalin sa, ita ma haka iyayenta ba masu ?arfi bane, hasalima talakawa ne sosai, ko kafin in aureta nasha wahala saboda basa bama talaka auren ya'yan su sai masu arzi?i, sun mayar da su kamar jarin su saboda Allah ya yi su da kyau. Taj ba irin wahalar da ban sha ba gurin fafutukar neman kuWin da zan biya a yi mata aiki, amma na kasa tara adadin kuWin da suke bu?ata, ranar da na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login