Showing 63001 words to 66000 words out of 321579 words

Chapter 22 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

yau, ko ruwan gidan ba zasu ?ara sha ba..."

sauran ma suka goyi bayan maganarsa, sheikh imam bai musa masu ba, sai dai yace shi bazai barsu da yunwa ba, yana ji kamar Allah ne ya kaddara zuwansa gare su don ya taimaka musu don haka suyi hakuri su bar shi yayi aikin shi Yana kwadayin ladar da zai samu ta silar taimakon su da zaiyi.



Badan sunso ba, suka amince masa amma fa bisa sharadin ba zasu ci abincin gidan ba.



A karshe shi ya basu shawarar tunda matayensu suna da restaurant na hadin gwiwa kuma bada dukiyar mahaifinsu suka gina shi ba, halal din su ne, me zai hana su kira manager ayi musu order na kayan abinci da duk wani abu da zasu bukata naci..


Shawarar shi suka Wauka, batare da bata lokaci ba, Mai girma sharafuddeen ya dauko wayarsa bayan ya kunnata ya kira hajiya laura, lokacin data daga kiran nashi kuka yaji tanayi tare da tambayarsa meke faruwa ne? Jiya taga an kawo hajiya saratu asibitin su rai hannun Allah, fuskarta duk ta baci da raunuka garin ya ya hakan ta faru da ita? har su twins ta tambaya suka ce mata hajjaty suke zargin tayi mata haka! Shin dagaske ne? Kuma wacece dattijuwar da aka kawo su a tare? Sannan suna ta kiran layinsa basa samu tun jiya bai dawo villa ba" kamar yar jarida ta tsare shi da tambayoyi ga kukanta daya cika kunnansa.

bai bata amsar tambayarta ba, sai dai ya kwantar mata da hankalinta, yace tayi hakuri su jira shi idan ya dawo villa zaiyi masu bayanin komai, dakyar ya samu ya shawo kanta kafin daga bisani ya bata umarnin tayi musu order na kayan abincin dana sha daga restauranta dinsu akawo masu anan estate dinsu..." maganarsa ta jefa ta a rudani tana kokarin ?ara tambayar shi ya katse kiran..



Cikin abunda baifi mintuna ba, Delivery Vans (motocin daukar kaya) biyu suka fara shigowa estate din, masu dauke da tambarin Royal Courtyard Restaurant.


bayan sun tsayar da motocin a parking space, Delivery staffs suka fara fitowa daga cikin motocin kafin suka fara jigilar Wauko Containers na kayan abinci da kayan sha daga cikin motar suna kaiwa Cikin Store din gidan..



Lokacin da suke shigowa, Maids din gidan dake lekensu daga sashen su, Sunyi mamakin ganin restaurant staffs suna shigowa ciki da kayan abinci, bayin Allah har sun fara tunanin ko dai wa'adin aikin su ne Ya kare, nan fa hankalin su Ya tashi, dama jiya sun kwana da fargaban abun daya faru da hajiya saratu, zuciya da sake sake sai ta dinga ayyana musu Hajjaty ce ta yi silar abun daya faru da ita, shiyasa ta gudu daga gidan, gayanan zata ja musu ba'la'e idan laifin ta ya shafe su basu san ina zasu sa kansu ba, har saida ma'aikatan gidan suka kammala aikinsu, tukunna maids din suka koma cikin part dinsu cike da zullumi.



Dakyar Sheikh Imam ya samu suka ci abincin kadan badan suna jin dadin shi ba.



Kasa tafiya yayi, saboda ya damu da su, gani yake idan ya haura kafa ya bar gidan zasu kara shiga mawuyacin hali ne, Hakan yasa bai je ko'ina ba, afalon gidan ya zauna atare da su Yana ?ara kwantar musu da hankali..



Su ka ce su yanzu damuwarsu suna son su san awani hali baban nasu Yake a ciki? Yana araye koya mutu, don tun daya gama kururuwarsa adaki basu kara jin koda tarin sa ba, ganin yadda suka nuna damuwarsu Yasa shi ce musu su taso su tafi part dinsa, gaba daya suka mimmike tsaye Yace Ma Chief ya Wauko mashi abincin da zai ci, store Ya shiga ya hado masa lunch a madaidaicin tray, Ya fito suka dunguma Izuwa Part din baba Obie.

kwankwasa kofar dakin Sheikh Imam yayi tare da ambaton sunansa kusan sau biyar bai amsa ba, cike da damuwa Chief yace bazai bude ba, amma su zagaya ta bayan dakinsa, akwai glass windown da ya fara kokarin fasawa jiya ya kasa, yasan zuwa yanzu quality din glass din Ya ragu zai kara jaraba fasa shi..

In a weak voice Justice Yace nima zan taimaka abude tagar, captain da ziyad ma sukace zasu taimaka gurin balle tagar...



Batare da bata lokaci ba, suka zagaya ta bayan dakinsa cike da sa ran zasu iya balle kofar..



Bayan sun Isa gaban Window din, suka fara kokarin fasa glass din, abunka ga majiya karfi sun haWu, Naushi suka dinga sakar ma glass din har saida Ya fara barazanar fashewa.

Kubi a hankali kada ku raunata kanku, shiekh Imam ne yayi maganar..

Dakyar da sidin goshi suka samu faskeken glass din Ya fara Tsastsagewa, naushi daya Hateem Ya sakar mashi gaba daya ya zube kasa har saida suka dan ja da baya..

Lokacin da suka dago da idanunsu ba zato ba tsammani suka hango sa a zaune Tsakiyar gadonsa sanye cikin doguwar riga baka mai hula, basu iya ganin fuskarsa ba saboda ya basu baya.

duk da haushin shi da suke ji hakan bai hana sunji sanyi aransu ba, ganin shi araye ba kamar yadda suka zata ba..

labbansu na kerma suka hada baki gurin ambaton sunan shi Baba.

Shiru bai amsa musu ba, kuma da alama yana jin muryoyin su acikin kunnanshi.

Ba irin magiyar da basu yi mashi ba, akan Ya juyo ya fuskance su amma yayi shiru ba alamun zai yi abunda suke so kuma bai tanka musu ba, hakan yayi matu?ar taba zuciyarsu, su ziyad da basu gasgata abunda owais ya labarta musu ba ayanzu sun fara kokwanto akan kakan nasu l.

wani sabon kukan suka kuma fashewa da shi ganin yadda lokaci daya mahaifinsu ya jefa kanshi a mawuyacin hali ya kuma jefa su suma...

Shiekh Imam Yayi kokarin sanya shi yayi magana kodan saboda ya'yanshi da suka damu da shi, amma yayi shiru bai tanka masa ba..

badan sun so ba suka hakura dayi mashi magana, Jikin asanyaye suka fara zame jiki suna barin bayan dakin nasa saboda ganin sa da su ke yi yana kara fama raunin da ke a cikin zuciyar su.

Imam malik yaso yayi magana da shi saboda akwai wani abu dayake so ya fada masa sai dai ya ?yalesa zuwa lokacin da zasu ke6a saboda idon ya'yansa dake a gurin.

Chief ne kadai Ya rage a bakin tagar yanata kallon bayansa, ba dan akwai makarin daya toshe tagar da dakin ba, da ba abunda zai hana ya dira.

tray din abincin daya zo masa da shi ya fara kokarin turawa ta cikin tagar yaki shiga, dakyar yayi dibarar aje tray din kasa ya dauki warmers din ya dinga jefa su ta tagar ta yadda abincin ciki bazai 6are ba, saboda ya datse murfinsu sosai, hada drinks din Ya jejjefa cikin dakin bayan ya kammala ya sauke ajiyar zuciya..


Cikin raunanniyar muryar shi Ya furta"baba kana jina, jiya ina ta kiran sunanka baka amsa min ba, anan na kwana, wai meyasa kayi min haka baba? Kaga halin da ka jefa kanka damu kanmu ko? Muna zaman mu lafiya, gaba daya ka lalata farin cikin mu, Jiya babu wanda ya runtsa saboda tashin hankali baba, ka kuntata kanka muma ka kuntata mu, ina kaunar da mukeyiwa juna baba? Yanzu ka sanya katanga atsakanina dakai..."


kasa karasa maganar yayi, kumburarrun idanunsa sun cicciko tab da kwalla, Sai kallon bayan shi yakeyi yayi tunanin zai motsa sai dai ko gizau baiyi ba, kamar gunki.



In a broken Voice Ya furta"shikenan, ni zan tafi, ga abinci nan na kawo maka, dan Allah, ka taimake ni kaci, kada ka zauna da yunwa, kuma bana so kaje wani wuri, dan Allah kada ka tafi kabar mu, nasan zaka iya 6acewa idan ka so, amma pls kada ka tafi pls.."



Harya juya zai bar bakin tagar, kwatsam Ya tsinkayi muryarsa wlh bai taba jin muryar data daga hankalinsa irin tashi ba, kamar ba muryar kakansa ba muryar tayi rauni ta kuma disashe..



"Owais, nasan meyasa ka roke ni akan kada in tafi, ba dan kana sona bane, sai dai baka son in gudu batare da ka mika ni ga hukuma an yanke min hukunci ba ko"?

Kamar ba shi yayi maganar ba, dan ko kadan bai motsa daga yadda yake ba.

Shiru owais yayi batare daya iya furta kalma ba, tabbas babu karya a maganarsa,



"Hakane, Inaso ka tsaya ka kar6i hukuncin da za'ayi maka, ta hakane zaka samu yafiyarmu, kuma ta hakane zaka samu sassauci, In har ka mika wuya batare daka bamu wahala ba, amma maganar nadaina sonka, ka daina, tabbas na tsaneka baba, ka karya min zuciyata, ka ci amanar yardar da nayi maka, amma ya zanyi? Inason ka wlh, har yanzu ina kaunar ka, amma ba kamar da da nake ma kallon dattijon arziki mutumin mai mutunci, kuma wlh kaunar da nakeyi mak??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a bazata hana in hukuntaka ba, dole hukuma tayi aiki akanka baba, dole ka girbi abunda ka shuka baba, tabbas idan nabiyewa son zuciyata, zance ka gudu ne saboda kaunar da nake maka, amma in na tuna hakkin rayukan dake akanka, da zaluncin da ka aikata, sai inji bazan iya kyale ka ba, saboda koda na kyaleka wlh Allah bazai barka ba, dole ka ga sakayya tun agidan duniya, nima kuma in ban dauki mataki akanka ba, Allah zai kamani ne wlh..." cikin shesshekar kuka ya kare maganar..



"Jikallena, kada ka damu, kakanka ba inda zaije, nayi maka alkawarin ina nan, kuma zan mika wuya saboda inason ku dauki fansar abunda nayi maku, in har hakan zaisa ku yafe min, duk da nasan ban cancanci ayafe min ba, Owais bazan iya misalta maka halin da nake a ciki ba, danasani bata da dadi ko kadan, gayanan naja ma kaina..."

a hankali ya kifa kansa saman bedmatress din sa, duk akan idon Chief owais, baisan ya akai ya ke jin kamar tausayinsa na shigar shi ba..



"Kai kenan, Inaga wadanda suka yarda dakai, wadanda sukeyi maka kallon jagoran rayuwarsu, kasan kuwa halin da muka shiga jiya izuwa yau? Bai amsa mashi ba yayi shiru kamar ma kuka yakeyi..



"Ka taimaka ka bude min kofar dakinka, Inaji ajikina baka da koshin lafiya, zan kira doctor ya dubaka"



In a low voice ya furta"wata irin zuciyar imani gare ka Owais uhum? Meyasa zaka damu dani? Ko da yake nasan kanayi ne don kada inyi rashin lafiyar da zatayi silar mutuwana batare daka hukuntani ba...."

katse shi yayi"ba haka bane baba, na damu dakai .." bai kare maganar ba ya katse shi"bana bukatar likita Owais, Azzalumin mutun irina bai cancanta aduba lafiyarsa ba, Yaran da muka azabtar agidan kurkukun kaddara, da yawansu idan suka fara ciwo, likitocin mu basa duba lafiyarsu, illa iyaka idan muka ga zasu gaza sai musa Surgeons su farke cikin su su debi sassan jikin su, shine ni zaka ce ka kira doctor ya dubani? Na cancanci hakan Owais..."

bai kare maganarba, Zuciya ta debi Chief Ya daki karfen jikin tagar, Yana faman cizon lips dinsa Ya furta"Ya isa haka baba! Bana son ji! Kabarni inji da abunda ke damuna..." ya fada yana jan numfashi..



Dakyar ya tausasa zuciyarsa, Yai karfin halin Furta"Ina so ka fada min, su wanene sauran Elders..."



"Kaje ka tambayi Aurora ta fada maka"!



"Tace bakowa ta sani a cikin su ba, kuma a halin yanzu tana a kwance gadon asitibi batasan inda kanta yake ba, Kai kadaine zaka Iya fada min su.."

cikin karyayyar murya ya furta"aurora bata da lafiya? Meke damun ta"? Bai amsa masa ba Yace"ba wannan na tambayeka ba, baka cancanki ka sani ba, kaida kaso ka kashe ta Allah bai nufa ba, kawai ka fadamin su wanene sauran Elders saboda tace min kun kai ku goma sha biyu, shida suna jagorantar gidan kurkukun kaddara, sauran shiddan kuma ba'a kasar nan suke ba, sune suke safarar yara daga kasashen waje suna shugo maku da su gidan kurkukun ?addara.."



"Owais, naso ace zan iya fada maka su wanene su amman ba zan iya ba, dokar aikin mu ce, amana ne kuma alkawari ne a tsakanin mu, wani bazai tona asirin wani ba, don haka kayi hakuri ba zaka taba ji abakina ba, nidai na mika wuya, Aminina basai kun sha wahalar kama shi ba, shima ya mika wuya zai kawo kan shi, su kuma sauran ba zasu taba canza ra'ayin su ba, tun da har kun ceci rayuwar sauran yaran da suka rage, kuyi ?o?ari ku sanya musu tsaro, sannan taimakon da zanyi maku shine ku yi gaggawar gano su wanene sauran Elders din ku kama su, idan ba haka ba, kama ni da kukayi kamar kun kashe maciji ne baku sare kan shi ba, ko dai ku kamo sauran Elders din, ko kuma ran kurkukun kaddara ya dawo fiye dana da..."


wani irin faduwar gaba Chief yaji, Cikin rawar murya ya fara yi masa magiya akan ya fada masa su wanene in ba haka ba taya zai iya gano su? su da suke matsafa kama su zaiyi masa wuya.

Baba Obie yace"Owais, Kai fa musulmi ne, meyasa zaka nemi taimakon matsafi uhum? Shiru yayi bai tanka masa ba.

"Ka nemi taimakon Allah Owais, shi kadaine zai kawo maka mafita, duk da banyi Imani da Allah ba, amma bayan da asirina ya tonu na zauna nayi nazari na gane cewa Allah yana da karfin ikon da babu wani mahalukin da yake da shi, zai iya mayar da abu mara yiwuwa ya zama mai yiwuwa tabbas naga ishara akaina Owais, Dan Haka inaso ka mika lamuranka gare sa, kuma bana so damuwar abun da na aikata yasa kayi rauni Owais, bana so kayi sanya, bana so ka karaya, jarumtakar nan taka da kwazon ka, da kaifin basirarka su nake so ka farfado da su gurin bada himma akan aikin ka..."

hakika yayi mamakin kalaman baba Obie, Har cikin ransa yaji dadi daya fara gane Allah daya ne, kuma Yaji dadin karfafa masa gwiwa da yayi duk da bai samu abunda yakeso agurin sa ba..



"Danish Yana araye ko ya mutu"? Kamar daga sama yaji ya tambaya..



"Bani da masaniya akan hakan, tun ranar da muka je kai farmaki ya fada cikin rijiya tare da sabon garkuwar ku amma meyasa ka tambaye ni bayan nasan kasan komai"?



"Hmmm, kawai Ina mamakin wani abu ne, amma ina kokwanto owais.."



"Zan iya sani"?


"Kawai kayi abun da nace maka owais, shi kadaine taimakon da zan iya yi maka ayanzu, sannan idan har aka kawo maku farmakin bazata, Kayi gaggawar sanar dani Owais..."




yaso ya kara yi mashi wasu tambayoyin amma saiya hakura ya bari zuwa wani lokacin yanzu hankalinsa ya karkata akan gano su wanene sauran Elders din..

_"kaddara da bugun zuciyar kurkuku, Ku sanya musu tsaro, rayuwarsu tana a cikin hatsari, da su ka Waine za'a iya dawo da ran kurkukun kaddara a halin Yanzu"_

Lokacin da Obie ya furta maganar shi ta karshe, Chief owais bai jiyo shi ba.


baisan Ya tafi ba saida yaji shiru babu motsin mutun tukunna ya sauko daga kan gadon Ya nufi kayan abincin da Owais ya jefo masa ya zukunna yana tattara warmers din guri guda..



*Daga Al?alamin Boss Bature=?%?
'?*




*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*~___________________________________??? &?=ؗ?=?%?
'?~







Lokacin da sheikh Imam zai tafi rokonsa suka dinga akan kada ya tafi yabarsu, ya zauna atare da su, ya fahimci kamar suna jin tsoron ya tafi yabar su, gani suke kamar idan ya tafi zasu kara shiga cikin damuwa ne, lallashinsu yayi tare da basu hakuri yace in sha Allah kullum zai dinga kawo masu ziraya sannan su jure su danne damuwarsu kada su bari tun yanzu agane halin da suke a ciki, yakamata su cigaba da zuwa masallaci yin sallah saboda mutane sun damu da rashin zuwansu, su cigaba da gudanar da komai kamar yadda sukeyi ada, cike da ladabi suka amsa mashi da toh har bakin motarsa suka rako shi, har zai shiga ciki ya juyo ya fuskance su, idanunsa cike tab da kwalla, suma idanun nasu kwallarce ta cika su, bayin Allah sun koma abun ban tausayi, kafin tafiyarsa yace ma Owais ya jira kiransa, sannan yace ma sharafuddeen next zuwan da zaiyi zasu raka shi asibiti ya dubo jikin Hajiya saratu da momma daga bisani ya yi musu sallama ya tafi har saida sukaga motar shi ta bace ma ganin su tukunna suka koma ciki jikinsu asanyaye... >?z?

Sheikh Imam yana driving yana share kwallar dake kokarin gangaro masa kan kuncin sa, bakomai ya ke tunawa ba face labarin rayuwar prisoners daya ta6a Zuciyar shi, ga tausayin Ahlin Obie daya mamaye zuciyar shi, shiyasa ya za6i ya tafi yabar su saboda ya samu damar da zai huce radadin da ya ke ji a zuciyar shi..

_____________________________=?%?
'?
Da marece=ؔ?

a lokacin gaba Wayan su suna a falo zazzaune kan Sofas zun zabga tagumi kamar masu zaman makoki, damuwar rashin dawowar chief ne ya hana su sukuni, Unexpected suka jiyo motsin shigowar mutun falon, ransu ne ya basu shi ne ya dawo, Kusan atare suka mike cike da zumudin ganin shi, kwata kwata basu lura da halin da ya ke a ciki ba, jikin su na bari suka nufe shi don suyi mashi sannu da zuwa, sai dai ko kallo basu ishe shi ba, bai kula kowannansu ba hatta Taj Da Unaisah, kaitsaye ya juya ya nufi part dinsa batare daya waiwaye su ba, Ya Ilahi, jikinsu ba karamin sanyi yayi ba, ganin yadda Chief ya sauya babu annuri ko walwala akan fuskarsa, abun dayafi daga hankulansu share sun da yayi, Batool har kuka saida ta yi..

Kasa jurewa su ka yi hakan yasa suka wanki kafa suka nufi part dinsa, a bakin kofar dakin suka tsaya gaba dayansu, suka soma yin knocking din kofar hadi dayi mashi magiya akan ya taimaka ya bude musu kofar amma yayi shiru bai tanka musu ba, babu alamun zai bude masu kofar.

Lamarin Ya Waure musu kai, sunyi matu?ar damuwa da shi, Yadda ya wuni a cikin Waki ba ci ba sha, haka suma suka wuni abakin kofar dakinsa baci ba sha, lokacin salla ne kadai ke tayar da su, haka zasuje suyi sallar ko sun dawo bakin kofar a datse suke taras da ita, da suka matsa da rokonsa akan ya fada musu mai ke damunsa dakyar yace su taya shi da addu'a Allah ya yaye mashi abunda ke damun shi, Ya kuma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login