Showing 30001 words to 33000 words out of 321579 words

Chapter 11 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

ya kama shi ya yi danasanin zarginta da ya dinga yi, ashe bayin kanta bane, makircine aka shirya mata.

Numfasawa ta yi, cikin shesshekar kuka ta ci gaba da cewa, "Bayan wani lokaci, ban ?ara jin Wuriyar Uncle musa ba, har lokacin da cikin Unaisah Ya cika wata tara cuf, nima kuma ban ?ara tuntubarsa ba ko in yi tunanin sanar da wani game da sirrin, a tunanina saboda bana son in jefa rayuwar ahalina Cikin hadari ne, a daren ranar da na?uda ta kama ni, da ni da kai muna a kwance kan gadonmu mun yi nisa a cikin baccinmu, kwatsam ba zato ba tsammani, na fara jin na?uda na taso mun, a firgice na farka daga baccin hannayena daddafe da cikina, ina ta faman cizon le6e saboda radadin da nake ji a jikina.

Zufa duk ta wanke jikina, naita kokarin kai hannu don in tashe ka daga bacci amma nakasa, na yi kokarin in yi koda addu'a ne nan ma abun ya ci tura saboda ha?orana sun game gam, Taj ban ?ara sanin me ya faru dani ba, nadaisan bana a cikin hayyacina na sauko daga kan gado ina jan ?afa na tura ?ofar toilet na shiga. Wlh Taj haihuwar Unaisah ikon Allah ne, kwata kwata bana a cikin hayyacina a haka na kar6i haihuwana da kaina amma bansan na yi ba, bansan dame na yi amfani gurin yanke cibin ba, a lokacin dana haifeta saida na kalleta cikin jini, na rungume abuna ina kuka tana kuka, abun da nake ta gudun in haifa sai gashi na haifeta, kuma sai na ji na kamu da ?aunarta fiye da komai na duniyar nan, ina tsaka da kallonta, Kwatsam na fara jin ana ambaton sunana da wata iriyar murya mai matu?ar tsoratarwa, kuma nan take na dinga jin bakin ciki a cikin zuciyata, na ji na tsani komai in har ban je na amsa kiran da bakuwar muryar ke yi mini ba zan iya rasa raina ne, saboda yadda tsigar jikina ke tashi kamar ana tunzurani, yadda kasan ana zare raina ban ma san sa'adda na kwantar da Unaisah cikin bathtube ba, cikin hanzari duk da rashin ?warin jiki na fuce daga cikin toilet din, ko waiwaye ban yi ba na nufi gate, baba mai gadi yana adakinsa yana bacci baisan na fita ba, saboda wani ?arfine ya zo mini bangaza Waya na yi wa kofar jikin gate din mu dake a kulle nan take ta buWe nasa kai na fuce da gudu na bi santar mu. Ban ?ara sanin meya faru ba, sai dai na wayi gari na ganni a kwance kan gadon asibiti magashiyan rai a hannun Allah, bayan dana dawo hayyacina na tambayi nurses din dake kula dani akan meya faru da ni? anan suke faWamin wani matashi ne ya bankaWe ni da motarsa akan titi shine ya kawo ni asibitin, abun da ya Waure mini kai, ni da na ke a Jos meya kawo ni Abuja? Ban sanya damuwa araina ba saboda lokacin burina kawai in yi nesa da dangina saboda bana son su a kusa da ni.=ؔ?

Tun kan ta ?arasa bashi labarin ya soma ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! cikin karyayyar Murya ya ce, "Benazir! Dama haka komai ya faru baki ta6a sanar da ni ba? Kika sa nayi ta zargin ki, Ya Salam!! Pls ki yafe mini"!

In a cool voice ta ce, "Ba laifin ka bane, rashin sanine ya jawo hakan, Nima ka yafe mini 6ata maka rai da na yi a zaman mu na aure.."

"Ki manta da komai ya wuce, saboda ke ma bayin kanki bane, Ina tunanin Uncle dinki shine Ummul aba'isin komai da ya faru, yanzu ina so ki faWa mini kece kika tura min sakon In sake ki!"

"Bani bace Taj, saboda ni ban tafi da waya ba, ni bansan wanene yayi mini hakan ba amma ina zargin Uncle Musa, saboda bayan na dawo gida Daddy da Mami sun faWa min ana tura masu sakonni ta layin wayata, wai hada sakon da nace ni na gudu da son raina kuma na shiga duniya kada suyi tunanin zan dawo gare su kuma kada su sha wahalar nema na..." Dafe kai Taj ya yi da tafin hannunsa, Idanunsa sun kaWa jawur da su.

"Benazir, Ni kuma sa?on da aka tura mini da bakuwar number ne, Idan bazan manta ba, abun da aka rubuta a cikin sakon shi ne ka sake ni Taj, kuma kada ka yi tunanin zan dawo na tafi kenan har abada, har kiran layin na yi amma saina ji shi a kashe kuma daga ranar ba'a ?ara tura min sa?o ba, tun ina sa ran dawowarki har dai na fidda rai"


Fashewa ta yi da kuka tana fadin, "Shiyasa kowa ya ?ullace ni aranshi saboda ana zargin da son raina na tafi, Koma wanene ya yi min hakan bazan ta6a yafe masa ba, Allah ya isa wlh sai Allah ya yi min sakayya, lallashinta ya shiga ya har ya samu ta yi shiru, shima ya yi shiru na Wan wani lokaci, sai sautin Numfashin junan su da suke ji ta cikin wayar, so yake ya bata labarin rayuwar Unaisah a gidan Kurkukun ?addara saboda Yana zargin dasa hannun Uncle dinta sai dai ya kasa saboda baya son ya ?ara Waga hankalinta, ganin halin damuwar da ta shiga, gaba daya ya fahimci bibiyar rayuwar su ake yi, tun daga kan Benazir, da Aisha da Dr Shureim, da kuma Iyayensu suma ba'a ?yale su hakanan ba.

Jin shirun ya yi yawa ne yasa shi tunanin ko ta yi bacci ne .

"Benazir?"

In a low voice ta ce, "Na'am'

"Pls, Ki kwantar da hankalinki, nasan ba zaki rasa ciwon kai ba saboda kukan da kika sha, dan Allah kada ki sanya damuwa a ranki, maganar Uncle din ki zan faWa ma Chief in sha Allah, duk yadda mu ka yi da shi zamu tuntu6e ku, yanzu ki kwanta ki yi bacci..."

Bai ?are maganar ba ta katse shi da cewa, "Don Allah Taj, ku taimaka mana, har yanzu ina ji araina Babyn Shureim tana a raye, kuma tana a gurin Uncle, shi kadai yasan inda ya aje ta, amma nasan in har kuka yi bincike akan shi zaku gano komai..."

Kwantar mata da hankali ya cigaba da yi saida suka raba dare suna yin waya kafin suka yi sallama, A daren ranar Taj bai iya runtsawa ba, saboda maganganun da suka tattauna da Benazir sun hana shi sukuni, har dai ya gaza jurewa ya kira layin Chief saboda yasan ba lallai bane idan ya yi bacci ba saboda a irin lokacin yana yawan tashi yin nafila, Cikin sa'a Chief ya yi picking call dinsa, a nan ya sanar da shi sun yi waya da Benazir, ya ce ya duba whatsapp dinsa ya tura mashi recording din da ya Wauka na tattaunawar da suka yi, Chief ya amsa mashi da toh.

Bayan Chief ya kammala sauraron audio din da Taj ya tura masa, har sujjada saida yayi saboda nuna godiyarsa ga Allah da ya fara kawo masa sau?i a cikin lamuransa ya kuma ?ara yin addu'ar neman nasara akan abun da suka sa a gaba.

After Two days, ana gobe za'a yi family meeting, kiran sallar asubahin farko Private jet din Prime minister ya yi landing a Airport, Mai girma Sharafuddeen tare da Security details dinsa ne suka je dauko su acikin dankara dankaran motocin su, wannan karon daga shi sai Escorts dinsa suka zo Nigeria batare da iyalinsa ba, kuma bakowa ne yasan da zuwan nashi ba sai family dinsa, ko yan jarida ba a bari sun san da zancen zuwan na shi ba.

Kaitsaye suka wuce Vila da shi, Sai da ya fara huce gajiyar da ya kwaso, Har bacci ya yi a dakin Wan uwansa Sharafudden kafin zuwa marece suka shigo Estate.

Gaba daya yan'uwansa suka hallara a main falo din baba Obie don su tarbe shi, Yana shigowa falon suka nufe shi cike da tsantsar farin cikin ganin shi, Waya bayan daya suka dinga yin hugging dinsa, burinsa ya ?arasa ga mahaifinsa sun hana shi motsawa kowa Wokin ganinsa yake yi. Da?yar ya samu suka kyale shi ya nufi Baba Obie dake ta sakar mashi murmushi ya rungume shi kamar zai maida shi cikin jikin shi, su Hajiya Saratu baki ya?i rufuwa saboda murnar ganin Yaya Hateem, kowa ya buWe baki sai ya tambaye shi ina iyalinsa? Meyasa bai zo da su ba? Ya ce masu su kwantar da hankalinsu suma zasu zo ne, amma a halin yanzu gimbiya da su Yazrin sun tafi Dubai gurin danginta hidima ce gare su, ita kuma Faryat bata samu hutun makaranta ba, shiyasa bata samu damar zuwa ba.

Lokacin da marece ya nutsa, sai ga kiran his excellency Abdul razak ya shigo wayar Baba Obie ya sanar da shi sun ?araso Abuja yana a aiport, Batare da 6ata lokaci ba Baba Obie ya tura da motocin Escorts suka dauko shi, bai jima da ?arasowa ba sai ga motocin His excellency Deen na Kaduna sun iso cikin Estate din. Sun yi farin cikin sake haduwa da yan uwansu saboda sun yi kewar juna, Baba Obie sai haba haba yake da su, saboda murna bakinsa ya ?i rufuwa. A daren ranar saida suka raba dare suna hira da mahaifinsu kamar ba zasu yi bacci ba har saida Baba Obie ya ce suje su kwanta su huta tukunna suka yi sallama da shi, Hateem dai ru?e shi ya yi a Wakinsa yace tare zasu kwana saboda ya yi kewarsa, hakan ba ?aramin dadi ya yi ma Prime minister ba, a kan gadon Baba Obie suka kwanta, zai kwana da tunanin mutumin da ya kwallafa rai da son ganinshi, Wazu da Chief ya zo gaishe da shi har tambayar shi ya yi ina baby boy dinsa? Yana lafiya? A lokacin hankalin Chief ba karamin tashi ya yi ba, amma saboda baya son ya Waga masa hankali yasa shi cewa yana nan cikin ?oshin lafiya, amma baya a gidansa yanzu, yana a camp din su na isod, yana kar6ar training.

Dakyar ya samu ya shawo kan Hateem har ya ha?ura da maganar Danish amma fa yace duk yadda za'a yi kafin ya koma yana son ganin sa.


~________________________________


*_=?%?=?%?=?%?The Chief Owais Birthday Celebration and Family Gathering=?%?=?%?=?%?_*



*Daga Al?alamin Boss Bature=?%?
'?*



*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*=?%?=؋?=؞? &?=ؔ?=؞?>???

_*~....................................................................~*_


~___________________________________ '?~





Around ?arfe 10 na safe, Kiran Chief Ya shigo wayar ta, a lokacin tana a zaune kan prayer mat ta nutsu tana yin karatun alkur'anin da ta buWe akan qur'anic stand, bayan da ta kai aya mi?ewa tayi daga kan Prayer mat din, ta Wauko wayarta da Waura kan Pillow ta yi picking Call din tare da kara wayar a kunnanta.



"My babe, how're you? i hope you slept well "?



Sa'ilin da muryarsa ta ratsa kunnanta wani sanyi taji ya ratsa zuciyarta.



"I'm doing well, thanks hubby,



"Okay, Idan baki komai ki same Ni a part Wina"



"Okay Sir" rejecting call din ta yi.


da sauri taje gaban prayer mat din ta rufe qur'anin, Bayan ta saka High heels dinta ta fuce ta nufi part dinsa.



yana a kishingiWe kan bedmattress dinsa, single da short ne a jikin shi Ya mike kafafunsa yayin da idanunsa ke a lumshe kamar na mai jin bacci, yau tun da ya farka daga bacci Omar ke ta faWo masa arai, saboda a duk ranar birthday dinsa Omar ne mutun na farko da ya ke fara turo ma shi happy Birthday greetings tare da Birthday gift, Omar baya so wani ya riga shi taya Chief murnar birthday dinsa, wannan karan Allah bai nufa za'ayi da shi ba.




Lokacin da ta karaso bakin Door room din, sau Waya tayi knocking kofar ta buWe, sallama tayi mashi daga ciki tajiyo voice dinsa ya furta"Come In babe"



Walking slowly ta nufe shi ta dan tsaya daga gaban Gadon, idanunta akan fuskar shi still bai buWe eyes dinsa ba suna a lumshe.


sumar kan shi tabi da kallo ganin hadadden ducktail haircut din da akayi masa, ya ?ara ?awata kyawun fuskar shi, ya yi mata kyau daga gani yau akayi masa shi.



Sau uku tana gaida shi bai amsa mata ba, tayi azan bacci yakeyi amma sai ta tuna before ta shigo saida ya bata izni.



"My Chief, ko ka yi bacci ne? Nayi magana naji ka yi shiru, pls kayi min magana"



bata ?arashe maganar ba, taji ya furta"kin bata min rai Unaisah, fushi nake da ke" Ya faWa tare da buWe idanunsa akan fuskarta.



Gabanta ne ya fadi adabarbace tace"I'm sorry ban fahimce ka ba, Meyasa ka ke fushi da ni? Laifin me nayi maka"?



Saukowa yayi daga kan gadon, hannun sa ruke da wayar sa, ya juya ya nufi tattausan rug din dakin sa, a ruWe tabi bayan shi da kallo, gently ya zauna akan rug din tare da nuna mata gabansa da yatsan shi"sit here Babe"

jiki asanyaye ta zauna tana fuskantar shi, jikinta duk yayi sanyi ganin mood dinsa ba walwala.



Kasa jure kallon da ya ke yi mata tayi, slowly ta kawar da idanun ta gefe daya..



"Meyasa kika tsani mahaifiyar ki? Laifin me ta yi maki?

nan take bacin rai ya wanzu akan fuskar ta, her voice barely above a whisper tace"Because she doesn't love me, she hates me, That's why lokacin da ta haife ni ta jefa ni a cikin bathtub, sannan ta gudu ta tafi batare da ta sake waiwaye na ba...."

tun da ta fara magana ya nutsu yana kallon smooth pinkin lips dinta har saida ta kai aya tayi shiru tana jiran amsar shi..

"You were rude to her, banji dadin maganganun da kika gaggayawa mahaifiyar ki ba!" ya fada yana mai nuna bacin ran shi

"uwa uwa ce koda ta banza ce It's not acceptable to disrespect her!"

"Amma bata sona meyasa tayi watsi da ni"?

"Ki daina cewa bata sonki Unaisah"!

Da yar tsawa ya fada, har saida ta zare mashi gray eyes dinta hakan yasa shi sassauta muryarsa saboda baison ya daga mata hankali



"I know you're intelligent and thoughtful, Don't you think there's a reason your mother ran away from you? pls kiyi tunani ta haife ki a tsakar dare a cikin toilet ta kar6i haihuwarta da kanta, ta saka ki a cikin bathtub ta gudu daga gidan ba tare da sanin mahaifin ki ba..."

arude ta dube shi gabanta na faWuwa



"Nasan bakomai kika sani dangane da tafiyarta ba, kamar yadda shima mahaifinki bakomai ya sani ba, rashin sani ne yasa kuke fushi da ita saboda kunyi tunani ta gudu ne saboda bata son zama da ku bayan ba haka bane....." gaba daya Unaisah ta rude da jin maganar shi.



Audio Recording din da ya Wauka na Labarin Ummi da Benazir ya kunna mata a wayarsa, ashe ya yi recording batare da sanin su ba.



Tun da ta fara sauraran shi yanayin fuskarta ya canza zuwa rudani da tashin hankali, aranta ta ayyana dama Aunty Ummin su Malama ce? Bata taba jin mace mai tausayi da kamun kai da tsantsar ilmin addinin islama irin ta ba, baiwar Allah ashe kaddara ce ta yi silar canza rayuwar ta.

Hawaye ne suka cika idanunta tab, tsananin tausayin Aunty ummin su ya kamata, ga wani kaunarta daya shiga zuciyarta, abun daya yafi ta6a zuciyarta a cikin labarin Hukuncin da sheikh Imam ya yanke ma ta, da kuma binne yarinyar da wan mahaifiyar yayi, Abun ya ta6a Zuciyarta sosai, muryarta na rawa tace"ban ta6a jin labarin daya taba zuciyata ba, irin wannan, kuma banyi zaton sheikh Imam zai iya yin hakan ba, a matsayin shi na malami, Aunty ummi ta bani tausayi ita da ya ya shureim, amma banji dadin binne yarinyar da yayi ba" muryarta na rawa ta ?arashe maganar.

"Yanzu inaso ki fadamin, Kafin ki saurari wannan labarin Wani irin kallo ki ke yi ma Aunty Ummin ku"?

tamkar zata fashe da kuka tace"tun kafin na santa, Dr. Laura ta america ce ta fara bani labarin ta, tace min karuwace ita, bata da kamun kai, kuma tayi kaurin suna a america, kawai dai ba mutuniyar kirki bace, amma da zama ya hada mu da ita sai na gane tana da sau?in kai, ba kamar yadda na zata ba, a ranar da ta fara yin karatun al'qur'ani agabana, na razana sosai, har nayi tunanin meya sa bata amfani da saninta take aikata sabon Allah ashe ba halin ta bane, kaddara ce ta afka mata...." ta karasa maganar cikin sanyin murya.



"Yanzu fada min meyasa ki ke yi mata kallon mutuniyar banza"!



"Rashin sani ne,"



GyaWa kai Chief yayi"haka zalika, itama mahaifiyarki rashin sanine yasa ki ke tunanin ta gudu ta bar ki saboda bata sonki, bayan ba haka bane, itama bada son ranta ba"

waro idanu waje tayi, jinjina mata kai yayi"kwarai kuwa, ni na hana mahaifinki yayi maki magana, saboda na daukarwa mommynki alkawarin zan sasanta tsakanin ki da ita, tun shekaran jiya da su ka zo bayan sun tafi, a daren ranar mommyn ki ta kira dad din ki, ta fada masa komai da ya faru da ita, har ma sunsasanta tsakanin su saboda ya gane ba laifin ta bane, may be bai fada maki ba, saboda nace yabar komai a hannu na"

ya ?arasa maganar tare da kunna mata audio din da Taj ya tura masa ya mika mata wayar

"Calm down and listen, zaki samu amsoshin tambayoyin da kike nema a gurin mommyn ki..."


yatsun hannunta na kerma ta kar6i wayar daga hannunsa tare da kangata saitin kunnanta don ta samu damar ji da kyau.



A hankali Chief ke kallon fuskarta yadda take zazzare gray eye balls dinta tare da moving lips dinta ba ?aramin tafiya yake da shi ba.



Bai aune ba Yaga ta zabura ta mi?e, Jikinta na kerma yadda kasan wadda Electric shock Ya kama, wayarsa dake a hannunta sai kerma take saboda jikinta dake kakarwa, Dafe kanta tayi da tafin hannunta, Labbanta na rawa ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un"!


Ganin ta juya arude yasa shi sauri kiran sunanta"Unaisah Ina zaki je ne"?

Yarfa hannun ta Waya tayi, ta kamo gaban hijab din jikinta ta soma fifita da shi saboda zafin daya taso mata gaba daya ta rude.

"Calm down babe, dawo ki zauna muyi magana mana"

Calmly ya faWa idanunsa akan fuskarta dake fitar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login