Showing 279001 words to 282000 words out of 321579 words

Chapter 94 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

6ur6ushinta ba zasu iya gani ba balle susan meya faru da ita.

Cikin shesshekar murya ya dinga kiran sunanta yana fadin kada ta mutu ta barshi, Yana bukatarta arayuwarshi... "

babu alamun zata farka, Ya rasa gane suma tayi ne ko mutuwa ta yi ne..

Zuciyarsa ce ta ankarar da shi akan ya mike ya tafi da gawarta kafin Elders su ritsa da shi.

Yunkurawa yayi tare da mikewa tsaye ya goyata akan bayansa ya tallabeta da hannayensa, daga inda yake ya 6ace bai dira a ko'ina ba, sai a wajen kurkukun ta inda suka bar jiragen su da motocin ya?in su yayi zaton zai taras da wasu daga cikin sojojin sai dai baiga kowa ba, babu su babu alamar su.


hawaye ne suka wanke fuskarshi, bai san ina zai sanya ranshi ba, Zuciyar shi ta ?ara karaya, kamar zai fashe da kuka.


Watsawa yayi da gudu Ya bazama cikin dokar dajin goye da khala abayansa, kwata kwata baiji nauyin ta ba saboda jikin tsufa, babu nauyi, Hasken rana ne Ya fara ?walarsa, ga yunwa da kishin ruwa da suka addabesa, ma?oshin shi har ?ai?ayi ya ke yi ma shi, rabon shi da abinci tun jiya da suka baro Sansanin sojoji.

Tsawon awanni takwas Yana tafiya daya gaji ne kafafunsa suka rurruke don dole Ya yada zango a gaban wasu bishiyoyi ya kwantar da khala asaman ciyayi ya tasa ta gaba yana kallonta..

saida ya huta kana ya mike ya kutsa cikin dajin don ya samo abun da zai ci.

Duk inda ya duba babu abun da zai ci, a karshe da yaji bazai iya jure yunwar ba, ganyayyaki ya tasa agaba kamar dabba, da dadi da ba dadi ya dinga cusawa abaki yana ciki, saida ya cika cikin shi ya fara jin kishin ruwa kamar zai zauce, a galabaice ya baza ma neman ruwan da zaisha, tunawa da gawar khala daya baro yasa shi hakura da neman ruwan gudun kada namun dawa su handame ta, Yana akan hanyar dawowarsa wani irin hadari Ya haWu bakikkirin cikin kankanin lokaci ruwa Ya fara safka tamkar da bakin kwarya, da gudu Ya koma gaban bishiyar yana isa ya taras da abun da ya faranta ransa, Khala ya gani ta farfado silar ruwan daya daki fatarta ashe sumane tayi.

cike da farin ciki ya rungumeta a kirjin shi, kafin ya fara tarfa ruwan saman a tafin hannunsa yana bata abaki tana sha, sai kokari ta ke yi tayi masa magana sai dai takasa saboda muryarta tayi rauni

sai dai rungume shi tayi ta dinga sakin gunjun kuka, a lokacin Allah ne kadai yasan farin cikin da tayi na ganin ta rayu kuma Danish ne ya ceto ta, taji dadi mara misaltuwa, Allah ya amsa addu'arta, ba ta ta6a zaton zata rayu ba,..

Tana kuka yana kuka babu mai lallashin wani, Yace mata tayi hakuri baisan meya faru ba, da bazai bari Elders su cutar da ita ba, yama yi zaton ta mutu ashe tana araye, yaji dadin da bazai iya misalta shi ba..."

bai faWa mata abun daya faru da shi ba, bai kuma nemi ta fada masa meya faru da ita ba saboda ganin halin da take a ciki na jinya..

A daren ranar agaban bishiyar suka kwana, ruwa ya jibge su, saboda babu mafaka akusa da su, kafin safiya tayi gaba daya zazza6i ya yi masu mugun kamu, jikin su yaita kerma..

Daya fahimci yunwa take ji, yaje ya tsunko mata ganyayyakin dayasan ba zasu cutar da ita ba, Yabata don taci, bayan ta kammala ci, Ya zukunna agabanta ta hau bayanshi Ya goyata, tare da mikewa Ya cigaba da tafiya batare da tsayawa ba.

Akan hanyar su Ya labarta mata komai daya faru da su Yace baisan meya faru ba bayan ya fada rijiya, baiga gawarwakinsu Chief Ba yana ji aransa kamar basu mutu ba, saboda a cikin gawarwakin daya gani babu na su duk da akwai wadanda gini ya rufe gangar jikin su, shi damuwar shi mahaifin Unaisah baison ta rasa daddynta..."

yayin da yake wadannan maganganun Khala tana agoye bayansa tana sauraron shi, kwata kwata bata iya magana saboda babu koshin lafiya atare da ita, gaba daya ta raunata, har kwara shi da Wan kwarin shi, duk da shima yaji jiki karfin hali kawai ya ke yi, kuma hada karin Evils din da ke a jikin shi shiyasa bai rasa kuzarin shi ba..

Hakika ta tausaya ma rayuwar shi, ta damu da halin da suke a ciki, tayi bakin cikin abun da kakansa ya aikata masa, tasan hada alkawarin da tayi masa na zata fada masa su wanene iyayensa shiyasa ya damu da ita sosai, duk da har i wannan lokacin baisan cewa ita din kakarsa ce ba..


A cikin yan kwanakin da su ka yi a dajin, Sun sha bakar wahala, basu da abincin daya wuce ganyayyaki, Ga miyagun namun dawan da suke kawo masu hari badan Danish Yana atare da Khala ba, da tuni sun jima da kashe ta, Ya bata kulawa, baya bari ko ?waro Ya ta6a fatarta, duk in zata farka tsakar dare zata taras da shi a zaune a gefen ta Yana gadin ta, sai ta tursasa masa sannan take samu ya runtsa shima, bai ta6a bari ta taka da kafafunta ba, duk in zasu cigaba da tafiya abayan shi yake goyata kamar karamar yarinya.

saboda depression din dake damunta kullum da matsanancin ciwon kai take fama, Ga konuwar da kanta yayi tana azabtuwa, don ma Danish Yana kokarin yi mata treatment da yan dabarunsa na sihiri, shima jikin nashi ba lafiya, mararsa tana matsa masa da ciwo, ga gabobin jikinshi da suka raunata, ahaka wata shakuwace mai karfi ta shiga tsakanin su.


A daren wata rana ne, khala ta Wanji saukin jikinta, bakinta ya bude, yaji dadi da yaga ta fara magana, tunkan ya tambayeta wani abu ta fayyace masa abun daya faru da ita sannan tace tasan ya ?araga da yaji su wanene iyayensa cike da zumuWi yace mata eh.

Tayi murmushi tace zata yi mashi wata tambaya daya kacal yace yana jin ta, tace ya fada mata lokacin da Owais yaje da su inda ya ke rayuwa, bai ta6a ganin wani mutum mai kama da shi ba sosai.."

baiyi wani dogon tunani ba yace"Chief yana kama dani amma daddy minister yafi kama dani"

"Wanene shi"? Ta tambaya kamar bata sani ba.

Yace"Uncle din Chief.." tana murmushi tace ya bata labarin farkon haduwarsu, nan ya labarta mata tun ranar farko daya farajin muryarshi a lokacin daya dawo suffarshi ta mutane ashe yaji komai da Prime minister ya ke fada, hatta labarin da yaba Taj na dansa daya rasa, a cikin labarin daya bata hada ranar dinner din hateem da komai daya faru da zuwansu garden tare da shi.

Tunkan Ya karasa bata labarin yaga ta fashe da kuka, hankalinsa Ya tashi ya soma tambayarta meya faru? Meyasa take kuka? Ko Labarin daya bata ne"?

Jinjina mashi kai tayi, cikin shesshekar kuka tace"tayaya baza tayi kuka ba? Ko a tarihi bata ta6a jin soyayyar uba da Wa irin wadda uban shi keyi mashi ba, tunkafin ma yasan shi din dan shi ne"!


lokacin da tayi wannan maganar, ruWewa yayi, muryarsa na rawa yace ta fada masa wanene daddy minister? Tasan shi ne? Ko shi ne daddynsa"!

Cike da zakuwa yayi tambayar kamar zai hadiyi zuciya saboda zumudin ta fada masa, cikin karyayyar murya tace" shine mahaifinka, Prime minister Hateem, jaririn da kaji yana ba da labari bakowa bane face kai, kaine Omair dinsa, ita kuma matar nan data cire maka mask a ranar dinner din da ku ka je, Itace mahaifiyarka, sheikha Mujeedat, aranar da ta haifeka aranar ne munafukai suka hada baki gurin raba ka da ita"

bata kare labarta mashi ba, sakamakon kukan daya fashe da shi, har saida ta razana da ganin yadda yake kuka a lokaci daya kuma yake dariya, ta rasa gane kukan bakin cikine kona farin cikin sanin su wanene iyayensa? Lamarin Ya daure mata kai tamau, saboda bata ta6a ganin Danish yayi irin wannan kukan ba da dai idanun ta

A ruWe ta shiga tambayar shi meya faru da shi? Meke damun shi? Meyasa ya ke kuka? Na bakin ciki ne kona farin ciki"?


A lokacin kasa buWe baki yayi ya bata amsa, tsabar yadda yake kukan jikinshi har jijjiga yakeyi, shatun jiyoyin wuyansa dana goshinsa sun fito ruWu ruWu kan fatarsa.

kifa kansa yayi saman ciyayi, hankalin khala atashe Ta dago da shi tare da rungumeshi a kirjin ta, ta Waura tafukan hannayenta akan bayanshi, Cikin sigar lallashi ta dinga bubbuga bayanshi tace bata san ya zatayi ba don ta kwantar masa da hankalinsa, tasan idan tace yayi hakuri kamar ta cuce shi ne, amma yayi hakuri tasan an cutar da rayuwarshi, an tauye mashi hakkin shi na rayuwa, an kuma raba shi da iyayen shi, wanda tayi imanin da ace a hannun iyayensa ya taso ko chief Owais bazai kai shi samun gatanci ba, saboda arzikin iyayensa bazai misaltu ba, mahaifinsa prime ministern canada ne, mahaifiyarsa kuma diyar Ruler din dubai ce, amma har yanzu bai makaro ba, taji dadi da Allah ya raya shi, in sha Allah zai hadu da iyayen shi, tana da tabbacin a cikin shekara daya zasu sauya mashi rayuwar shi in har ya koma gurinsu, zai manta da duk wani bakin ciki da azabtarwar da ya fuskanta agidan kurkukun ?addara, zai zamanto daya daga cikin matasan da suka fi samun gata agurin iyayen su.."

maganganu masu dadi khala ta dinga fada masa har saida ta samu ya lafa da yin kukan, sai dai Jikin shi yayi zafi rau, da alama zazzabine ya lullube shi, lokacin daya dago da fuskar shi, ta 6aci da hawayensa, idanunsa sun kada jawur, tayi tsammanin zai tambayeta wanene ya sadaukar da shi, sai baiyi hakan ba, muryarshi tayi rauni ta disashe dakyar ta iya gane me ya ke son fada mata..

Cewa yayi yau ce rana ta farko da yayi farin cikin da bai ta6a yin makamancinsa ba arayuwar sa, a halin yanzu baida burin daya wuce yaga iyayensa ido da ido, yana matukar son yagansu koda da numfashin shi na ?arshe ne..."

tsananin tausayinshi ne ya kamata aranar kwana sukayi a zaune yanata yi mata sambatu akan yadda yake zumudin yagan su har tambayarta yayi zasu ji dadi idan suka san shi dan su ne tace mashi fiye da yadda yaji dadin jin cewa sune iyayen shi..."


A washe garin ranar da sukayi firar, bayan ya sama masu abun da zasu ci, suka kama hanya, dayaga bata sauri yace ta hau ya goyata tace aa bata so ya wahala, tun da ta danji sauki zata iya tafiya da kafafunta, ko ta dafa shi tun da babu sanda atare da ita.

Batasan yadda ya matsu su koma gari ba, batai aune ba taji ya sungumeta akan kafadarsa ya 6ace da su..

Cikin sa'a suka faWo wani forest din, A gaban wata bishiya ya sauke khala agajiye suka baje kasa nan bacci yayi awon gaba da su.

Har mafarkin prime minister ya yi acikin baccin sa.

Suna tsaka da yin baccin kwatsam ?arar Mota ta cika kunnuwansu, a firgice suka farka har sun zabura zasu mike saboda sunyi azan wani mugun abunne amma da sukaga ba abun da suka zata bane sai hankalinsu Ya Wan kwanta.

Wata katuwar motar daukar kayace kirar toyota mai budadden baya, ta kunno kai cikin dajin, dattijai ne guda biyu daga gani wani mahimmin aikine ya kawo su cikin dajin..

Kwata kwata basu lura da su ba, har saida sukayi parking din motar, fitowa su ka yi daga ciki.


Waya daga cikin su yana aru?e da bindiga irin ta mafarauta, yayin dayan qugunsa ke a soke da Sheath Knife, daga gani mafarauta ne ko wani abun suka zo nema a cikin dajin, suna ?o?arin wuce wa cikin dajin idanunsa sukayi masu tozali da su, kura masu idanu sukayi kamar sunga wani mugun abu, kamar yadda suke kallonsu haka suma suke kallon su, khala ce ta yi karfin halin yi masu magana tace su taimaka su fitar da su daga dajin, kallon juna sukayi jin tayi magana da yaren da basa jin shi, da ta fahimci basu jin hausa sai ta maimaita maganar cikin harshen turanci.


An ci sa'a suna jin yaren daya daga cikin dattijan yace tayaya zasu taimake su bayan basu san su wanene su ba? Don shi kwata kwata basuyi mashi kama da mutane ba, musamman matashin dake a bayanta" ya fada yana nuna Danish da yatsan shi, dayan dattijon yace"su fada masu gaskiya mutanene su ko aljanu? Me kuma su ke yi a cikin daji"?


Ta lura Danish su ke ji ma tsoro duba da yadda su ke kallon shi ga dukkan alamu kyan shine basu taba cin karo da mai irin shi ba, ga zanan tattoo dinsa dayasa suke zargin dan wata ?ungiya ne ta ?an ta'adda.

Khala tace ba abunda suke tunani bane, suma mutane ne kamar su, matashin da suke gani atare da ita jikanta ne kaddara ce ta ritsa da su suka tsinci kansu a dajin su taimaka su shigar da su cikin gari.."

Karya ta shirga masu ta dinga rokonsu dakyar ta samu suka aminta da su, su ka ce su shiga motar, su jira su su gama abun daya kawo a cikin dajin, bayan sun buWe masu motar suka shiga daga ciki, hankalinsu ba karamin kwanciya yayi ba ganin sun samu taimako, nutsawa dattijan su ka yi cikin dajin tsawon rabin awa, kafin suka dawo hannayensu ru?e da damun ganyayyakin da suka tsinko, abayan motar suka tura ganyayyakin, kafin suka bude motar, suna shiga mazaunin gaba suka yi arba da abun daya daure masu kai, mutanan da suka bari a motar sai bacci su ke yi ga zufa da ta wanke fuskokin su daga yanayin yadda suke fitar da numfashi yasa suka fahimci basu da ?oshin lafiya.


Jan motar su ka yi tare da bata wuta suka kutsa cikin gari sun danyi tafiya mai nisa kafin suka ?araso cikin birnin abomey-calavi da ke a ?asar Benin.

Koda suka shigo cikin gari, sai suka faka motar suka soma kokarin tada su daga bacci don su faWa masu sun karaso cikin gari su sauko su tafi..

Sai dai me? Babu alamun zasu farka, har bubbuga kafadarsu su ka yi amma shiru, hakan ba karamin daga hankalinsu yayi ba, abunda suke ma fargaba kada ace sun mutu a cikin motar su, daga taimako?

Har sun yanke shawarar kaisu wani guri su jefar da gawarwakin su, kwatsam tarin tsohuwa Khala ya katse masu hanzarinsu, da sauri suka shiga tambayarta meke damun su ne?ba su da lafiya ne? Cikin disasshiyar murya tace su taimaka su tafi da su gidan su, idan suka sauke su basu san ina zasu dosa ba, saboda su ba yan nan bane, taji suna wani yare da ba irin na su ba, koda suka tambayeta wani gari take a benin? Tace masu ita ba yar benin bace, Yar nigeria ce,.."

waro idanu waje sukayi, alamar mamaki.

Basu kara tambayarta ba ganin halin da take a ciki, saboda basu yarda da su ba, shiyasa suka ki kaisu gidan da iyalinsu suke, don karsu cutar da su, sai su ka garzaya da su gidan gonar su, su ka basu Waki Waya mai toilet a cikin sa, Ko gado babu sai katifa.


Allah yaso sun fada hannun nagarin, Har abinci suka basu, duk da yunwar da su ke ji sun kasa cin abincin saboda ba irin cimarsu bace, sai dai suka sha kayan marmarin da suka tsinko masu na lambun su.

Bayan sun yi wanka, suka kwanta kan katifar dakin anan bacci yai awon gaba da su..

Dattijan suna le?an duk wani motsinsu a dakin, saboda suna kokwanto akan su.

Saida suka ga bacci yayi awon gaba da su, suka lallaba tare da shigewa cikin dakin suka soma laluba aljihun wandon danish don suji in akwai kudi su sace su, Yana jinsu yayi shiru kamar yana bacci, jira yake su wuce gona da iri su ci uban su.

Da suka ga babu kudi cike da takaici suka bar Wakin, tafiya su ka yi sai dare suka dawo a lokacin suna zaune kan katifar suka shigo masu bayan sun gaida khala tayi masu godiya, su kace su yanzu so suke su san komai game da su, tace suyi hakuri zata sanar da zasu amma kafin nan tana so su fara bata waya zata kira gida..

Dakyar ta samu suka ara mata waya, bayan sunyi deal zata biya su kudin katin da zata ci ma su saboda sunga international call ne tace karsu damu zata biya su konawa su ke so.

Saida ta kar6i wayar, ta fara tunanin wa zata kira cos gaba Waya ta manta phone numbers din ya'yan ta, Danish ne Yace ta bashi wayar zai kira Chief owais ya haddace numbar sa.

da sauri ta bashi wayar ya kar6a Ya soma danna number din Chief bayan ya gama ya danna mashi kira, har sun fara murna ganin kiran ya shiga amma chief bai Waga ba, almost 30 times suna kira baya picking.

har dattijon ya kar6e wayarsa a washe garin ranar da safe, da suka zo kawo masu abinci, ta k
?ara ro?onsu su ara mata wayar, dakyar suka bata, ta dinga kiran Chief baya picking, kamar za su yi hauka, gashi tayi tayi da su su kaisu asibiti don aduba lafiyar su, amma suka kiya saboda gudun kada a caje su kuWi.

A ?arshe Text message ta tura ma Chief owais, tace owais ka taimaka idan ka ga kiran nan ka neme ni, tsohuwa Khala ce ta gidan kurkukun kaddara, Ina a tare da Danish... =?%?



Bayan Sati Waya da ?an kwanaki da kai farmakin farko gidan Kurkukun ?addara

__________CHIEF OWAIS=ؓ?

Around ?arfe sha daya na safe, yana a office dinsa tare da COO Commender Haroon suna dan ta6a fira kan abun daya faru agidan kurkukun ?addara..

"Har yanzu na kasa mantawa da tsohuwar nan, ta tsaya min araina, kuma inaji araina har yanzu Danish Yana araye, amma tayaya zan iya gane hakan? Anya Ba zamu koma kurkukun nan ba"?

Ya fada da damuwa akan fuskarsa, Yayin da idanunsa ke a cikin na Haroon.

"Tunanin mu yazo Waya Sir, Yaron nan yana araina, bazan 6oye maka ba, wallahi ban ta6a jin kaunar shi kamar yadda naji aranar da muka je kai farmaki, yayi kokari sosai, duk da halin dayake a ciki damuwar shi akan mune


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login