Showing 57001 words to 60000 words out of 321579 words

Chapter 20 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

Wago da kanshi, idanunshi sun kaWa jawur hawaye wasu na bin wasu akan kuncinsa.

Cikin shesshekar kuka ya ce, "Babu inda zan tafi, wannan karon, babu wanda ya isa yasa in canza ra'ayina, na riga da na yanke ma kaina hukuncin da na ga ya dace dani, zan mi?a wuya, kuma zan tuba, zan kuma kar6i kowani hukunci da za'a yanke min..."



Gaba Waya Elders din dake a dakin suka hau yi mashi magiya wasu jahilan cikin su har sujjada suke yi mashi duk don ya ji ?an su ya canza ra'ayin shi..



"Dama kun daina wahalar da kanku.." ya faWa yana girgiza kansa.


Cike da sanyin jiki Jan Harshe ya rungumeshi sosai kamar zasu koma mutun Waya, cikin karyayyar murya ya ce, "Koda kowa zai juya maka baya a cikin Elders, ka sani kana da ni, al?awari ne muka daukarwa kanmu tun yarintar mu, duk runtsi duk wuya zamu kasance a tare, a kowane hali na rayuwa, don haka nima na ajiye makaman ya?i na, ra'ayinka shine nawa, ba gudu ba ja da baya, zamu mi?a wuya a tare, kuma zamu kar6i hukuncin da za'a yanke mana, a tare zamu girbi abunda muka shuka." Ya faWa jikinshi na kerma.


"Ka faWa musu ba sai sun sha wahalar nemana ba, zan kawo kaina har abujan, cikin estate dinka, saboda in sau?a?a musu..."


Cikin shesshekar kuka ya ce, "A'a bazai yiwu ba, bazan jure ganinka cikin mawuyacin hali ba, ka bi sauran Elders din ku nemi mafaka, na yi maku alkawarin bazan tona muku asiri ba, koda za'a azabtar dani ne akan in fada, shi kaWai ne gatan da zanyi muku na karshe, kamar yadda kowan nan ku ya sani dokar kurkukun kaddara ne kuma alkawari ne muka daukarwa junanmu wani bazai tona asirin wani ba, don haka ni ma bazan tona asirinku ba, amma ku sani idan har wani daga cikin ku ya yi gigin cin amanata, wallahi! na rantse da izzar mulkina baza ku sha ba, zanyi maku abunda baku ta6a zato ba.." ya faWa da kakkausar muryarsa mai firgitarwa.

Har saida Elders din suka razana da jin maganar shi...

?ara ?an?ame shi Jan Harshe ya yi, "Kaima kasan abu ne da bazai ta6a yiwu ba, ni bazan barka ba, ka so kanka da yawa, idan na barka kai kadai a cikin kuncin rayuwa ban yi maka adalci ba, kamar yadda bazaka sauya ra'ayinka ba, nima bazan ta6a canza nawa ra'ayin ba, ba inda zan je Obinna, ?afarka ?afata, har mutuwarmu..." Ya faWa yana ?ara jaddada mashi...


"Tun da har kun yarda zaku mi?a wuya, me zai hana ku bamu sihirin dake a tare da ku? In ya so sai mu ?ara da namu, in har dagaske kun tuba to kamata yayi ku bar komai da ya shafi tsafi..."


Jan Wuya ne ya yi maganar, sauran Elders Win suka goyi bayansa akan su basu sihirinsu, nan take suka fahimci basu damu da halin da suke a ciki ba, tun da gashi har sun fito da haWamarsu a fili, wato mu?aman su suke so su basu don su samu damar cigaba da aikata fasadi...=ؔ?



Babu wanda ya tanka musu a tsakanin Elder da Jan Harshe sarai sun ji me suka ce a cikin kunnuwansu.

lokaci Waya wani haya?i mai kama da guguwa ya karaWe dakin da suke a ciki, kafin wani lokaci kowannansu ya 6ace, dama ba a guri Waya suke ba, dabarun sihiri ne da suke kira magician's dream, a mafarki suke haWuwa da tsakar dare su yi magana da junansu, kowani Elder dake a kasashen ?etare dana gida Nigeria in har suka yi mafarkin nan to kowannansu zai bayyana ne a cikin sa..=?%?
'?



Dare mahutar bawa, sai dai bakowani rai bane yake samun damar da zai huta a cikin sa, haka ta ke a bangaren Obie family, bayin Allahn nan Yadda suka ga rana haka suka ga dare, babu wanda ya runtsa daga su har ya'yansu, a zaune suka kwana saboda depression din da ya yi musu katutu a zuciya...


_______________________________=?%?
'?


*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE=?%?*


*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*~___________________________________??? &?=ؗ?=?%?
'?~








A washe garin ranar, ba zato ba tsammani Sheikh Imam malik yayi musu zuwan bazata, batare da wani daga cikin su ya gayyace shi ba. Babu wanda yasan da batun zuwanshi saboda bai sanarma kowa ba.


tun jiya da yaje masallaci yin sallar Magrib bai ga kowa na family din Obie ya halarci sallar ba.

kuma a sanin da yayi musu basu da wani masallaci da sukeyin sallah in ba masallacin shi ba, tun nan abun ya fara da mun shi, ya yi ta tunanin anya lafiya, mutanan da duk in lokacin sallah yayi sune zaka gani a sahun farko.

Zuciya da sa?e sa?e har ya fara tunanin ko dai sun canza masallaci ne? lokacin da aka kira sallar isha'i mutane sunata taruwa domin yin sallah yaita baza idanu cike da sa ran ko zai ga gifcin su sai dai har aka ?are sallar babu su babu alamarsu, abun ya dame shi matuka, ba shi kadai ya lura ba, har jama'ar dake yin sallah a masallacin saida sukayi ta tambayar ina ahlin Obie? Meyasa basu zo masallaci ba? kodai ba lafiya ne"?

Wadanda suke zumunci da dattijon arziki har jaraba kiran layin shi sukayi bai daga ba, suka kira layin ya'yansa ba wanda yayi picking, haka shima sheikah imam ba irin kiran da bai yi ma baba Obie ba awaya amma baya shiga kwata kwata.

sai da takaiga ya kira ya'yan shi dukansu babu wanda wayarsa ke shiga, Hakan Ya kara jefa shi a hali na damuwa, daren jiya dakyar ya runtsa saboda tunaninsu da yayi mashi katutu a cikin zuciyar shi.


lokacin sallar asuba nayi bayan ya farka daga bacci, yayi shirin zuwa masallaci cike da sa ran zaiga ahlin Obie sun halarta.

bayan ya isa masallacin ya yi ta sa ran ganinsu har masallata suka kammala hallara ya tada sallah, bayan ya gama sallar, yayi nasihar daya saba yi abayan kowace sallar asuba, anan ne mutane sukai ta tambayarshi meye hana Ahlin Obie halartar masallaci tun jiya? Ko an kira su awaya ba'a samu, ko dai sun canza masallacin da suke yin sallah ne ko sun yi tafiya ne "?


abun daya sa suke tambayarshi Imam saboda sun san yafi su kusancin da baba Obie, cike da damuwa yace musu baida masaniyar akan abunda ya hanasu zuwa masallaci amma in sha Allah zaije Estate din ya dubo a wani hali suke a ciki, gaba daya sunji dadin maganar shi, har suka ce idan ya isa, komai ake ciki kada ya manta ya kira ya sanar da su ko hankalinsu zai kwanta, Yace musu in sha Allah zasu ji daga gare shi.



Ko masaukinsa bai wuce ba, daga masallaci Ya shiga motarshi yana driving yana tunanin su, kaitsaye Ya nufi Obie Estate.. =ؔ?



Tun da Motarshi ta shigo estate din Ya tsinci kanshi da jin matsanancin faduwar gaba da bai taba jin irin ta ba.



Da sunan Allah abakinsa, ya tsayar da motar a parking space yana fitowa securities dake zarka suka dinga gaishe da shi cikin girmamawa, fuskarsa da fara'a yake amsa masu kafin yayi hanzarin wuce hannunsa ruke da cazbaharsa Ya nufi Katafaren falon gidan bai kaiga shiga ba, ya tsaya daga bakin kofar yayi sallama, shiru ba'a amsa mashi ba, kusan sau bakwai yana doka sallama shiru kamar yayi magana da bango, lamarin Ya daure mashi kai, da har zai tafi sai kuma Ya fasa saboda baya jin zai iya tafiya batare dayasan awani hali suke a ciki ba..



Da zuciya Waya ya kutsa kai cikin falon, Yana shiga yaci burki yana kallon abun da yayi matu?ar daure masa kai aransa ya furta dama suna nan, ina tayi musu sallama basu amsa min ba"?

Wlh tun daga yanayin da ya riske su ya fahimci babu lafiya atare da su, akace labarin zuciya a tambayi fuska, karasa shiga ciki yayi, kwata kwata basu san da zaman shi a falon ba, babu alamun sunji motsin tafiyar shi, yadda kasan gangar jikinsu ce kadai zazzaune kan Sofa, ruhinsu baya atare da su, damuwa ta ?ara gusar da hankalin su, saboda rashin baccin da basuyi ba jiya, idanunsu sun kara kumbura, sunyi jawur kamar garwashin wuta, gaba Wayan su babu riguna a jikinsu sai gajerun wandunan da suka bari..

"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un...." Shiekh iman ne Ya furta Yana lekan fuskokinsu, ya razana da ganin Halin da suke a ciki, har yatsunsa ya fifita saitin fuskokin su don yaga ko akwai rai a jikin su amma babu alamun zasu kyafta idanun su, Ya rasa gane suma sukayi ko kuwa wani abunne? Amma fa hankalinsa Ya dungunzuma ainin.

"Hateem! Sharafudeen! " ya fada yana kallon faces dinsu, kamar hotuna, saboda rudu Ya kasa gane suna numfashi ko basayi, juyawa yayi kan sauran"Abdul Razak! Deeni! Wai baku ji ina magana? Meke damunku ne? Meya faru daku? Kuna acikin hayyacin ku kuwa eye"?

Juyawa yayi kan Sir mubarak arude Yace"Mubarak! Wai dan Allah meke damunkune uhum? Mayesa bakwa motsi? Suma ku ka yi ne ko kuwa wani abunne ya faru da ku.." fuskarsa ya mutse da damuwa


bai ?are maganar ba, ya tsinkayi muryar mutun abayansa Yana karanta addu'ar tashi daga bacci.

a hanzarce ya juya dan ganin wanene! Wani faduwar gaba yaji ganin wasu daga cikin matasan familyn kwance akan floor suna bacci, kamar marasa galihu, hankalinsa ya kara tashi matuka.

a hankali Ya mike zaune yana mi?a hadi da yin hamma, Cikin sauri Imam Ya nufe shi cike da sa ran zai samu amsar tambayarsa agurin sa..



Zukunnawa yayi agabansa cikin rawar murya yace"Nadeem, meke damun iyayenku ne? Meke faru wa da ku ne"?

"Gaba daya na rude hankalina ya tashi, kamar babu lafiya atare da ku.." ya kare maganar cike da sa ran zai samu amsoshin tambayoyin shi agurin Justice.


yamutsa fuskarsa yayi cike da damuwa ya fayyace masa halin da suka ris?e su a jiya.

tamkar zai fashe da kuka ya kara da cewa"shiekh ka taimaka mana, mun rasa gane kansu, ba mu san meke damun su ba, babu magana sai kuka, jiya daga mu har su babu wa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?nda ya runtsa, ko ruwa bai gifta makoshin mu ba, bayan haka bamu ga baba ba, Kofar dakinsa a kulle take, ko da muka same su abakin kofar dakinsa, munyi tsammanin ya mutune, saboda mawuyacin halin da muka taras da su yafi kama dana wanda ya rasa abu mafi soyuwa agare shi, amma koda muka tambaye su ya mutune basu tanka mana ba, ko magana basa iyayi..."

araunace ya karasa maganar, ta ko'ina kan shiekh imam ya kulle ya ce"dama sun taba yin irin hakan"? Arude justice ya dubi Uncles din nashi, don kwata kwata bai san abun ya munana har haka ba, har kwara jiya sun motsa lokacin da yan aiki suka fara koken abun daya faru da Saratu...

Girgiza kai Justice yayi"ban taba ganin sunyi ba, amma ina tunanin Zuciya ce, saboda grandpa ya ta6a yi sau biyu daWewa tun kafin na mallaki hankali na, lokacin da Senior mom ta rasu da kuma lokacin da Kanwarsa ta rasu.."

sheikh Imam bai ?arasa sauraran maganar Justice ba, Ya juya jikinshi na 6ari ya samu guri daga tsakiyar Sofas din da suke, afujajen Ya zauna dirshan tare da tankwashe kafafunsa yayin zaman cin tuwo..



"A'uzubillahi minasshaidanirrajim, Bismillahirrahmanirrahim..."

?ira'ar alkur'ani mai girma Ya cigaba da yi musu tun yanayi kasa kasa har ya Waga muryarsa da karfi idan yaja aya saiya dire ta yake jan numfashi kafin ya daura da wata, kankace me tuni ya haWa gumi akan fuskarsa yanayi yana duban su.

justice daya langwa6e kansa, Yayi shiru yana jin yadda kira'ar shiekh ke ratsa zuciyar sa..



Kaitsaye Sautin ?ira'arsa ya ratsa dodon kunnuwansu, har izuwa sassan jikin su, Unexpected zuciyoyin su suka fara bugawa da matsanancin karfi, Numfashin su ya fara fita da sauri da sauri



Gaba daya bai lura ba, saboda ya sadda kan shi ?asa, Yana tsaka da karatun kwatam ba zato ba tsammani suka fara dawowa hayyacinsu, wata irin nannauyar ajiyar zuciya gami da atishawa da tari suka dinga saki a jere a jere.



"Ruwa.. Ruwa.. " cikin disasshiyar murya Hateem Ya firta..



Jikim Justice na bari ya mike garin sauri hada tuntube ya nufi kitchen area, jim kadan Ya dawo da gudu, ya rugume bottle waters masu sanyi a kirjin shi.

bayan ya cire masu murafan robunan ruwan Yabi su daya bayan daya ya mika musu ruwan yatsun hannayensu na kerma suka kakkarba tare da kaiwa baki suka fara sha, makoshin su har sauti ya ke fitarwa kwat kwat!! Kamar zai ballo..



At same time ziyad da captain Yaseer dake kwance kasa suna bacci suka farka sakamakon kira'ar imam data cika kunnan su kamar wadanda suka sha kayan maye a kasalance suka mi?e zaune tare da jingina bayansu jikin Sofas.



Kowan nan su saida ya shanye ruwan dake acikin robar sa, kafin suka jefar da robobin...



Sai lokacin ?wa?walan su su ka dawo bakin aikinsu, sunyi mamakin ganin gari ya waye, ko da suka ga shiekh Imam dake a zaune Yana kira'ar alkur'ani, kusan atare suka sauko daga kan sofas din ko mikewa sun gaza yi saboda rashin kuzarin jikin su, da rarrafe suka ?arasa gaban shi, gaba daya suka kewaye shi kamar zasu lullu6e shi da karajen su, babu wanda bai jigata ba a cikin su, jiya izuwa yau saboda tashin hankali Har faWawa sunyi, kwarin idanunsu sunyi ja musamman masu hasken cikinsu cheeks dinsu sun yi ja.

shesshekar kukan su ce ta cika kunnuwan shiekh imam malik, baisan sa'adda ya dakata dayin karatun alkur'anin ba yabisu da kallo mai cike da ruWani, hankalinsa ya tashi da jin yadda juraman maza kamar su suke kuka da idanunsu..


hankalinsa atashe ya fara tambayarsu meke damunsu? Me yasa suka fita hayyacinsu.

rurru?e hannayen shi sukayi cikin raunanniyar murya su suka soma fadin .

"Baba Imam mun shiga uku, mun bani shiekh, muna a cikin musiba, baba yaja mana bala'e, zuciyoyin mu sunyi rauni, hankalinmu ya tashi, anyi mana bakin tabon da bazai taba goguwa ba..."

gaba daya sun ruWa Imam malik Ya rasa gane ina maganganunsu suka dosa.

Tun da suka fara yin magana su Captain suka shiga rudani, sun rasa gane ina zancen su ya dosa? Shin me baba ya akai ta ne?


"baba ya kunsa mana bakin cikin da har abada bazai taba barin Zuciyoyin mu ba, Ya ha'ince mu, Ya zalunce mu, ya kashe mana rayuwa, kuma ya cuci kan shi, sheikh tun jiya gobara ta kama ci acikin zuciyoyinmu bamu iya kashe wutar dake konata ba sai da kayi mana karatun alkur'ani mai girma tukunna muka samu sassaucin radadin da muke ji" wani irin faWuwar gaba Imam malik yaji adabarbarce yake rarraba idanunsa akan fuskokin su..

"Baba Imam ka tayamu rokon Allah ya dauki ranmu mu huta, watakil hakan ya zama sauki agare mu, saboda bazamu iya cigaba da rayuwa ba, da wani ido zamu dubi duniya? kowa zai juya mana baya, zamu zama abun gudu, baba imam bakin ciki zai kashe mu,...." ya fahimci wani mummunan abune ya faru da su kuma daga maganganunsu ya gane baban su ne ya jefa su a halin da suke a ciki..


Jikinsa ne yayi sanyi tamkar babu laka, tsantsar tausayinsu ne Ya kama shi, tun kafin ma yaji abun da zasu fada masa..

A hankali ya soma Waura tafukan hannayensa asman kawunansu kamar kamun ciwon kai ya ke yi masu, addu'oi ya soma karantowa yana shafe masu kai..


cikin ikon Allah nutsuwa ta fara shigar su, numfashin su dake fita a hargitse ya fara daidaita, wani irin gumi ne ya soma wanke goshinsu alamar zazzabin jikinsu ya fara sauka..



"Ba sai kun fada min abunda ke damun ku ba, na riga dana sani, sai dai karin bayani da zan nema..." arude suke kallon shi da tsantsar al'ajabi .



"Shiekh, taya akai ka sani? Mun shiga uku, shikenan kowa ya riga daya san miyagun ayyukan da baba ya ke aikatawa, kowa ya sani, tamu ta kare, mun bani .."


Senate Lateef ne ya fada tare da daura hannayensa asaman kansa..



Cikin sanyin murya Imam yace"Lateef, babu wanda Ya sani, daga Allah, sai ku sai kuma ni, nima din bakomai na sani ba.."



"Kwana daya da banganku a masallaci ba, Hankalina Ya tashi, bani kadai ba, hatta jama'ar dake halartar masallacin sun damu da rashin ganin ku, kowa muka kira layinsa a cikin ku bama samu, shiyasa na yanke shawarar zuwa nan din dan in duba ku, saboda naji araina ba hakanan ku ka ki zuwa masallaci ba..." ya dan dakata tare da jan numfashi kafin ya kuma cewa" Ba jiya bane ku ka yi family meeting ba? Ina Owais ina kuma sauran ahlin naku"?

Sai lokacin suka tuna da shi, Kowa Yana ta kan shi, cike da rashin ?warin jiki sharafudeen Ya mike tare da juyawa a hanzarce ya nufi cikin gidan ya bazama neman sa, saboda yaji aransa bai fita ba, watakil ya fada wani gurin daban..

"Bakowane Ya samu damar halarta ba..." His excellency deen ne ya fada yana sharce kwallarsa, da yatsan hannunsa Ya nuna su Justice yace "su kadai ne, suka zo, sauran Uzirurrukane suka ru?e su..."

kwata kwata bai nemi su faWa masa ainihin abun da ke faruwa da su ba.


Takun tafiyar su ne Yaja hankulansu ga duban inda sautin ke fitowa, Sharafudden ne ya 6ullo Hannunsa ruke da damtsen Owais dake ta layi kamar wanda yasha kwaya..



Gwanin ban tausayi suke kallon shi, Hankali atashe su justice suka mike tare da nufar shi, kwata kwata basu san yana a gidan ba, sakar musu shi Sharafudeen yayi, cikin sauri suka tallabesa tare da rungumesa suna tambayar shi meke damun shi? Meke faruwa da shi? A ina ya kwana?

"Can na tsinto shi a back room din baba, Ina tunanin tun jiya acan ya kwana..."

Hankalinsu Ya kara tashi basu taba ganin Owais a mawuyacin hali irin wannan ba, ko magana bai iyayi, fuskarsa duk jirwayen hawayen sa..



"Ku miko min shi nan" sheikh Imam ne Ya fada Tare da mika musu hannu, Ruko shi Captain yayi ya taimaka masa Ya karasa ga imam, Jikin nasa ne babu kuzari gaba daya ya durkushe saman gwiwowinsa agaban Imam Malik.

tallabo keyarsa yayi tare da janyoshi Ya fado kan kirjinsa, cikin sigar lallashi Yake dan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login