Showing 45001 words to 48000 words out of 321579 words

Chapter 16 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

baba ka yi magana, na ro?e ka, dan Allah dan soyayyarka da manzon Allah SAW......"

Murmushin takaici khala ta yi, "Hmmmm Saratu dama kin daina wahalar da yawun bakin ki, saboda a halin yanzu mahaifinku baida bakin magana, wannan kaWai ya isa yasa ku gasgata magana ta..."

Ta faWa tana kallon fuskar baba Obie dake fitar da gumin zufa, shatun jijiyoyin wuyansa sun fito ruWu ruWu, jikinshi ya Wauki wani irin mahaukacin zafi.

"Duk wani jariri da matayenku suka haifa ya zo ba a raye ba sune suke Wauke shi daga gare ku, da haWin bakin munafukan likitocin asibitinsa, Ku tambayi munafuki MD Dr Jidanna, da Dr Adam da kuma Dr chisom, da sa hannunsu ake yi maku wannan aika aikar...."

"Zaku haifi Wa ku ganshi a mace alhalin ba shi bane rufa ido su ke yi maku su yi musayar shi da aljani su Wauke na gaskiyar su tafi da shi gidan kurkukun kaddara, ku kuma ku dauki aljanin ku yi jana'izarsa ku rufe a ?abari da sunan jinjirinku ku ka rufe...." ta faWa cike da takaici,

"Ha?i?a Obie ya zalunce ku wlh wata shari'ar sai dai a lahira, amma fasi?in mutumin nan ya daWe yana aikata luwaWi da zina da jikokinsa da ya sadaukar a gidan kurkukun kaddara, ya sha jininsu, ya kashe su saboda neman duniya, bashi kaWai ba harda sauran fasi?an da suke aikata fasadi a bayan ?asa, Elders din suna da yawa sune miyagun dake sadaukar da jininsu matsayin fursinoni, da yawa ma ?a'?an naku azaba ce ke kashe su, cikin ka so Wari baifi ka so goma ne ya rage daga cikin su ba...."

Numfashinta ne ya fara tsaitsayawa, jini ya fara bleeding daga cikin hancinta hakan ba ?aramin Waga hankalin Sharafudeen da Hateem ya yi ba..

Daurewa ta yi duk da azabar da ta ke ji a jikinta a haka ta cije ta ci gaba da cewa, "Na rantse da wanda raina ya ke a hannunshi duk abunda na faWa maku ba ?arya bane, idan baku yarda ba, gayanan agabanku ku turkeshi ya fada maku gaskiya...."

Tsayawa ta yi tana haki fuskarta ta ji?e sharkaf da gumi, ta dafe saitin zuciyarta da tafin hannunta...

"Kamar yadda na faWa maku, bashi kaWai bane Elder, akwai mu?arrabansa da suke take masa baya, Amininsa Ifeanyichukwu inkiya Jan kunne amma a gidan kurkukun kaddara jan harshe shine nickname dinsa, shine Mataimakinsa a tare suke aikata fasadi, abun takaici sun auri junansu tun da daWewa saboda tsantsagwaran jahilci da tumasanci...."

Kutumar U! Zaro idanu suka yi kamar ?wayar zasu faWo ?asa, sun shiga matsanancin tashin hankali, maganarta ta ?ara dagula masu lissafi, jin abun suke kamar wasan kwaikwayo.

"Bayan haka, surukinku mijin Saratu, shine Jan kunne na gidan kurkukun ?addara..." Tunkan ta ?arasa maganar hajiya Saratu ta daddafe kanta da tafukan hannayenta, ta dinga girgiza kanta, tsabar kiWimar da ta yi ne yasa ta dinga sambatu kowace addu'a ta zo bakinta furta ta kawai ta ke yi..

Runtse idanunta ta yi ruWu yama hana ta iya tantance me Khala take nufi, buWe idanunta keda wuya Unexpected ta hango Pravin da ya arta a guje ya nufi sashen yan aikin gidan, aikuwa jikinta na 6ari tabi bayan shi...

Khala bata dakata ba, ta ci gaba da cewa, "Sir Benjamin baturen amuruka, abokin mahaifinku wanda suka yi tashen yawon duniyarsu atare da obie da amininsa, shine jan le6e na gidan kurkukun ?addara, mugun fasi?i ne....."

"Bayan shi sai ba?in shaidanin da ta?adarancin sa yafi na fir'auna, zan iya cewa tun da Allah ya halicce ni ban ta6a ganin mugun bawa irinsa ba, bazan iya misalta mugayen zunubban da yake aikatawa ba, shine mai bada shawara kuma head na kula da bangaren bada horon giants Win kurkukun ?addara, baida imani ko mis?ala zarratin, asalin shi bawan Obie ne daga baya da likafa ta ci gaba sai ya bashi mu?amin Elder...shish.. Shish.....

Kasa ?arasawa ta yi saboda abun da ya sar?e ma?oshinta, dama ba koshin lafiya ne da ita ba, jiri ne ya kwasheta a galabaice ta yanke jiki zata faWi, cikin sauri Sharafudden ya sungumeta ya kwantar da ita akan doguwar kujera, sai kokarin ?arasa maganar take yi amma ta kasa...

Wai shin Ina Chief Owais? bawan Allah Komai dake faruwa akan idanunsa kuma kunnuwansa na sauraro, kwata kwata baya acikin hayyacin shi, zufar dake tsastsafowa ta saman fatarsa ta ji?e jikin shi sharkaf, kwata kwata ya gaza yarda da abunda Khala ta faWa, Gani yake kamar mafarki yake yi ba gaske bane, duk da ya gama raunana zuciyarshi ta karaya da ganin yadda baba Obie ya yi shiru bai tanka ba! Hakan na nufin da gaske ne ba kazafi aka yi masa ba tun da ya kasa kare kan shi, inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! La'haula wala quwata illa billah, da wannan ranar ?wara mutuwarsa, addu'o'i yake ta nanatawa acikin zuciyar shi..

Jiki a mace Sir mubarak ya zauna kan Sofa, zafi ne ya taso mashi har ta kai ga ya tu6e rigar shi ya jefar da ita ?asa, ya Waura gwiwar hannunsa akan hand sofa ya zagba uban tagumi, kamar wanda ya rasa gata a duniya.

"Deen! kana jin abun da nake ji kuwa? Deen Ka tsun?ule ni dan Allah inaso na tabbatar in ba mafarki nake yi ba..."

Cikin raunanniyar murya His excellency Abdul Razak ya faWa yana kallon His excellency Deen da ya haWa uban gumi a jikin shi, girgiza kai ya yi cikin karyayyar murya ya ce, "Ba mafarki bane, kada mu yaudari kanmu! Da gaske ne komai ke faruwa, baba da muke sa ran zai kare kansa daga ?azafin da tsohuwar nan ta yi masa ya kasa, gashi nan yana ji ya yi shiru..." Ya faWa yana nuna Obie..

Muryar Sharafuddeen ce ta katse shi da cewa, "Abun da momma ta faWa akansa ba ?arya bane, ya aikata ne shiyasa ya kasa kare kansa....."

"In kuwa hakan ya tabbata gaskiya ne, Baba ka kashe mana rayuwa, ka gama da mu, mun mutu, mun bani mun shiga Uku! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un......"

Senate Lateef da ya Wauko maganar bai kaita karshe ba Ya yanke jiki ya faWi a sume, a firgice Deen da Abdul Razak suka rufa akan shi suna ambaton sunan shi haWi da bubbuga jikin shi don ya tashi..

"Ruwa, tana bu?atar ruwa..."

Hateem ne ya yi maganar, cikin sauri Sharafuddeen ya je ya dauko bottle water me sanyi yana gab da zai ?araso Ya lura da Owais dake a tsaye baya motsi da alama suman tsaye ya yi, wuce shi yayi ya nufi Hateem ya mi?a masa robar ruwan Ya kar6a yatsun hannunsa na kerma ya kanga ma tsohuwa Khala a baki, kusan rabin ruwan ta shanye sam ta kasa magana idanunta ma sun rufe gam bata iya buWe su.

Kar6ar robar Sharafuden ya yi daga hannun Hateem cike da rashin kuzari ya nufi su Deen Ya mika masu bayan sun yayyafa ma Senate Lateef ya farfado yana sambatu kamar mai tabin hankali har yana fadin Allah yasa mafarkine abunda ya ji.


Kar6ar robar ruwan ya yi daga hannun Deen ya je gaban Owais ya daddage ya watsa mashi ruwan a saman fuskar shi, lokaci Waya yaja dogon numfashi ya furzar da shi da wani irin zafi.

Kamar mahaukaci haka ya dam?i gaban rigar Sharafudeen hawaye na zarya akan kuncinsa da wata irin karyayyar murya ya ce,"Ka faWa min kaima kana Waya daga cikinsu?"

Ya fahimci ba ya acikin hayyacinshi, tsigar jikinshi duk ta tashi hai?am zuciya ta riga da ta tsinke.

Tsananin tausayin shine ya kama shi, Cikin sanyin murya ya ce, "Bana Waya daga cikin su Owais..."

"Meyasa ka kasa kare kanka lokacin dana tambayeka?"

Girgiza kanshi ya yi, "Saboda na daukarwa baba al?awarin bazan faWa ma kowa ba..." Katse shi ya yi, "Wani al?awari ne ka daukar masa?"

"Shine ya kira ni a waya ya faWamin zaku je kai farmaki gurin matsafa masu haWarin gaske, ya gargade ni akan kada in kuskura in barka ka je, nace mashi ai yafi kusa da kai kafi jin ma maganarshi, me zai hana ya yi maka magana, sai ya ce min ba ya son bacin ranka ne yasan idan ya hana ka zuwa baza ka ji daWi ba, shiyasa ya kasa amma yasan ni idan na yi maka magana bazaka ji komai ba, kawai in baka umarnin kada ka je, nace mashi baba ban ta6a hana Owais ya je kai farmaki ba, hasalima ni nake ?arfafa masa gwiwa akan aikinsa idan na hana sa wannan karan dole zai ji ba daWi ne, sai ya fara min faWa yana fadin har shi zai bani umarni in ?i bi! Yana magana ina magana, da ni da owais din duka ba a ?ar?ashin ikon shi muke ba? Na dinga bashi ha?uri har saida na amince zan yi maka magana tukunna ya ha?ura, Sannan ya ce zai turo da Wan sa?o da maganin bacci in saka maka a cikin Coffee, saboda in kasa kafiya ka turje akan ba zaka bi umarnina ba, sai in baka kasha coffee din, kuma baya son kasan shi ya sakani, nayi masa alkawarin bazan bari ka sani ba, kaji dalilin da yasa lokacin da na kira ka a resting home dina ka ?i bani hadin kai ni kuma na baka coffeen dana zuba maganin baccin ka sha...."

Gaba Waya maganganun Sharafudden a cikin kunnuwansu sun ji komai, hankulansu sun ?ara tashi, cikin rawar murya Owais ya ce, "Kana nufin baba shine ya hanani kai farmaki, kuma shine ya sa ka bani maganin bacci, amma a daren ranar ina ka je saboda an faWa min ba a gan ka ba?" Ya fada a ?agare da son jin amsar shi..

"Owais ni ban je ko'ina ba, ina a villa, adakin mommynka na kwana zaka iya tambayarta ka ji, bayan haka sanin kowannanku ne Villa tana da tsaro, ba yadda za'a yi shugaban ?asa ya yi fitar sirri in the midst of the night batare da wani daga cikin security ya bi shi ba, Allah shine shaida ta..." Ya fada fuskarsa a yamutse.

"Hakan na nufin Baba shine ya ?ulla maka makirci saboda ya Waura maka laifin sa? Ko don ya shiga tsakanina da kai?"

Jinjina kai Sharafudden ya yi,"Babu tantama Owais, baba shine Master planner Win da ke shirya ma?ar?ashiya atsakaninmu, bansan meyasa ya yi hakan ba..."

Cikin shesshekar kuka ya ?arashe maganar, wata irin juwa ce ta Wibi Chief ya yi taga taga zai kife ?asa cikin zafin nama Sharafudeen ya janyoshi ya rungume abunsa akan kirjinshi, atare suka fashe da matsanancin kuka tamkar ransu zai fita.

Ha?i?a baba Obie ya muzanta, kunyar duniya ta kama shi, ya shiga matsananciyar damuwa, bai ta6a zaton wannan ranar zata zo ba, Wani irin azababben ?unci da bakin ciki da takaici ne suka turnuke zuciyar shi, jin kanshi yake kamar ba mutun ba saboda tas???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?hin hankali.

A zabure ya mi?e kamar mahaukaci ya juya jikinsa na 6ari zai bar wurin sai dai kafin ya kai ga tafiya Owais ya hango shi, a zuciye ya 6an6are jikinsa daga na daddynsa ya nufi baba Obie cikin zafin nama ya dam?i damtsen hannunsa ya juyo da shi suka fuskanci juna gaba da gaba, kunya ta hana baba Obie ya haWa ido da Owais saidai ya sadda kanshi ?asa.

Cikin raunanniyar murya ya ce, "Baba kai kaWai ne zaka share min shakku na, Ina so na ji daga bakin ka, da gaske kaine Elder na gidan kurkukun ?addara? Kuma kaine mutumin da ya fitar da ni daga fagen ya?i ya jefa ni a daki uhum??"

Ya faWa cike da fargaban amsar da zai bashi, wlh ya yi fatan ace zai iya kare kansa sai dai ya kasa saboda asirinsa ya riga da ya tonu.

Gaba Waya idanunsu na a kan fuskarshi amsar shi kawai suke jira su ji, batare da ya Wago da idanunshi ya dube shi ba ya jinjina mashi kai alamar Eh, a lokaci ji ya yi kamar ya ha?a ?asa ya binne kansa saboda ba?in cikin da ya ziyarci zuciyarshi, raWaWin da suka ji yafi na ?unar wuta zafi..Ya Ilahi!

Zuciya ce ta Wibi Owais baisan sa'adda ya ci kwalar rigarshi ba, da hannu biyu ya dam?e shi sosai jikinshi na 6ari.

Hakan ba ?aramin karya zuciyar Obie ya yi ba, duk irin jarumtakar namiji hakan bai hana sun fashe da kuka ba kamar ?ananun yara, gaba Waya sautin koke kokensu ya cika falon, wasu suka dafe kawunansu da tafukan hannayensu saboda azabar radadin da zuciyarsu ke yi musu, wlh sun yi danasanin zuwansu duniya a lokacin, sun ji Waci a ransu, ranar ta zame masu mafi muni a rayuwarsu. Gaba daya suka kewaye shi suna tambayar shi don me zai yi musu haka? Meyasa ya ci amanarsu ya ha'ince su? Wannan wani irin neman duniya ne? Me yasa ya aikata musu hakan? Wlh Hankalinsu ya tashi matu?a, duk sun fita hayyacin su, kuka kawai suke yi kamar ransu zai fita..

Hakan ba ?aramin karya zuciyar Obie ya yi ba, bai ta6a danasanin irin rayuwar da ya daukarwa kansa ba irin yau, saboda Allah ya jarabce shi da masifar son ya'yan shi, Koda ya ke sadaukar da jikokin shi bai ta6a sadaukar da ya'yan shi ba.

da?yar ya iya haWiye ba?in cikin shi, da wata irin karyayyar murya ya furta, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN!!! Na shiga Uku! wlh na daWe ina fargaban zuwan wannan ranar, dama nasan duk mun daran daWewa asirina zai tonu ne sai dai ban ta6a zaton zai tonu ta wannan hanyar ba! Ranar da nake jin zullumi da fargaban zuwanta, ranar da nake jiye ma kaina tsoron zuwanta, ya zan yi da rayuwana? ya zan yi da rayuwarku? Nasan na cutar da rayuwarku cuta mafi muni, na zalunce ku, na kuma zalunci kaina, Amma koma dai menene bakin al?alami ya riga da ya bushe, na riga dana tabka babban kuskure, ban kuma san da wasu kalmomi zan ro?e ku gafara ba, banma cancanci in nemi yafiya agurinku ba, wlh na muzanta, na tozarta, na ji kunyar haWa idanuna da ku, kaicona!...."

Bai ?arasa maganar ba ya fashe da kuka, hawaye suka wanke fuskar shi, mutumin da sun manta when last suka ga hawaye ya zuba daga cikin idanunsa saboda jarumtakarsa ashe tsantsagwaran matsafine, Yana kuka suna kuka an rasa me lallashin wani, da?yar yake kallon fuskokinsu cike da jin nauyin abun kunyar da ya aikata musu.

"Nasan na biyewa son zuciya, amma wallahi ba laifina bane, Nima gado na yi, tun kakanninmu da iyayenmu na taso acikin matsafa, shine hanyar samunmu, na yaudare ku da musulunci amma ni ba musulmi bane, arne ne ni kamar yadda ta faWa muku, tun da na taso rayuwata bansan mai kyau da mara kyau ba haka iyayena suka tarbiyantar da ni, duk abubuwan da suka faru son zuciya ne da son Waukaka, buri na in tara dukiya, in Waukaka in zama shahararre a duniya, ?a'?ana ma su Waukaka a idon duniya, wannan dalilinne yasa gaba Waya kuka Waukaka kowannanku na nema masa duniya kuma ya same ta..." Bai ?are maganar ba HATEEM ya katse shi ta hanyar cakumar shi cikin tsananin tashin hankali ya furta, "Baba! Baba!! baba!!!...." Idanuwansu cikin na juna a marairaice yake kallon shi..

"Meyasa ka za6i ka ciyar da mu haram? Baba duk irin ?aunar da muke yi maka, kullum burinmu mu kare maka mutuncinka sai gashi kai ka zubar mana da namu mutuncin, Waukakar daka sama mana ta tashi a banza wlh! Saboda da zarar mutane sun ji abunda kake aikatawa wlh mun zama abun gudu, za'a juya mana baya ne a tsangwamemu zamu zama abun ?yama, makiya zasu samu damar cuzguna mana, Baba ka bar mana mummunan tabon da mutane zasu dinga cin zarafin mu da shi! Haba baba! Wlh ka bamu mamaki baba, wai mahaifinmu ne yake aikata munanan zunubban nan?" Ya faWa yana haWiyar yawu mai tsananin Waci cikin mutuwar jiki ya sake shi..

Sharafudeen ya Waura da cewa, "Baba yanzu ina amfanin irin wannan? Wace riba ka samu baba? Ina hankalinka yake? Tayaya ka bari shaidan da zuciya suka rinjaye ka? Kamanta da wata rana zaka mutu ka koma ga Allah, baba Idan ka nema mana duniya lahirarmu fa? Ya kake so mu yi baba? Muna alfahari da kai, kaine abun tun?ahon mu, kaine silar Waukakarmu ashe mun yaudari kanmu baba, A yau mutuncinka ya zube acikin idanunmu baka da sauran daraja baba, wlh da wannan bakin cikin daka ?unsa mana da kashe mu ka yi kamar yadda ka saba kashe ya'yan mutane...!"

Kuka ne ya ci ?arfinsa har ya kasa karasa maganar..

Baba Obie sai kuka yake yi babu ?a??autawa..

Senate Lateef ya ce, "Baba wace shafewar basira ce ta same ka? Ni abun da ya dauremin kai yadda har ka iya kashe mutun ka sha jinin shi, ka kuma lalata rayuwar yaran da basu ji ba basu gani ba, baba wa ya koya maka zaluncin nan? Har yanzu na gaza yarda kaine kake aikata hakan Baba, Tsawon shekara nawa kana aikata fasadi a doron ?asa! Wallah baba da ace ka yi hakuri tun fil azal ka yi rayuwarka cikin talaucinka da sai ya fiye mana kwanciyar hankali, shi arziki da daukaka na Allah ne, sai wanda ya so yake bawa, watakil ma kana Waya daga cikin wadanda Allah ya tsaga da rabonsu kaine baka sani ba, ka biyewa son zuciyar ka baba, gayanan ka jefa rayuwarmu a halaka, bayan haka jin dadin duniya ?alilan ne baba, gaba dayanmu mutuwa zamu yi, komai muka mallaka anan gidan duniya zamu barshi, lahiri itace dawwamammiya, wlh da wannan masifar daka jefa mu a ciki wlh gara ace mun taso rayuwarmu a matsayin musakai marasa gata a duniya da dai irin wannan rayuwar, baba yanzu da ka Waukakamu ya zaka yi da mu? sai da ka bari duniyar tasan da zamanmu ana yi mana kallon mutane masu daraja da ?ima, masu martaba a idon duniya, yanzu idan suka ji miyagun laifukan da kake aikatawa me kake tunanin zai biyo baya?" Ya jefa mashi tambayar yana kuka yana girgiza kai.

kafafunsa ne suka gaza Waukarsa ya zube kan gwiwowinsa, idanunsa sun rune jawur, kumatunsa sun yi jajir, duk ya faffasa labbansa da ha?oransa, gemunsa ya ji?e sharkaf da ruwan hawayensa, Ko'ina na jikinsa zufa ce take tsattsafo masa kamar babu A.c a falon.

Wlh ya sada?as bai ta6a zaton zai ji kunyar zunubban da yake aikatawa ba sai yau da Khala ta fallasa asirin sa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login