Showing 153001 words to 156000 words out of 321579 words

Chapter 52 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

daka, ta dinga tari tana nishi


Da ?yar ta iya furta, "Ni kuwa nasan wanene kai, mugun uban da ya sadaukar da ?arsa saboda neman abun duniyan da bazai amfanesa ba a ranar gobe alqiyama, kuma mugun mijin da ya raba ?a da mahaifiyarta tuntana jinjira batare da sanin ta ba, ka raine ta batare daka bata tarbiya ba, da kai da fasi?ar uwarta ta bogi kuka hadu gurin lalata rayuwarta, duk hakan baiyi maka ba, ka hanata sanin komai game da addininka ka barta a matsayin arniya saboda kada Allah Ya tuhumeka a ranar gobe ?iyama, shiyasa duk ?a'?anka daka sadaukar babu musulmi a cikin su, saboda jakkanci da da?i?anci, da kuma shafewar basira irin naka..."


bata ?arasa maganar ba, ya kwasa mata wani marin da ya ja har hancinta ya fara bleeding..



Idanunta suka cicciko da kwalla, ta ji zafin marin nan, radadin sa ya ratsa ta, kuma bata fasa maganar ba,


"Ai koda hakkin rai Waya aka barka wlh makomarka ba zata yi kyau ba, saboda Allah baya barin hakkin wani akan wani, kuma baya yafe hakkin dake a tsakanin bawa da bawa, balle kaida ka daWe kana zaluntar rayukan da basu ji ba basu gani ba, rai nawa ka kashe? Rai nawa ka zalunta? Rai nawa ka lalata uhym? Ko an gaya maka Allah baya gani ne?" Ta faWa tana ciccije la66anta tsabar masifa duk ta faffasa su, gaba daya ta kashe mashi baki, ko kaWan bai girgiza ba bai kuma dakatar da ita ba ya bari ne ya ga iya gudun ruwanta, don shi har yanzu baya mata kallon mai hankali saboda ?arfin halinta..


Tana jan numfashi cikin fushi ta Waura da cewa, "Bayan haka kaine mugun da ya raba mahaifiyata da danginta, kuma kaine shaidanin da ya shiga tsakanin Aunty Ummi da mahaifinta, sannan kuma kaine makirin mutumin da ya hada Aunty Ummi da Uncle Shureim, ka kuma raba su da ?ar su, bayan haka, kaine fasikin da ya mayar da aunty Umminmu karuwa ka rabata da kowa nata ka mayar da ita America, saboda wani dalili naka mara amfani.."



ta6e la66ansa ya yi batare da ya furta kalma ba..


"Jahilin addini jahilin rayuwa, wallahi ka ji haushin rayuwarka, ka daina farin ciki don ka daWe kana zalunci wlh kanka ka zalunta, ka gur6ata duniyarka da lahirar ka da kanka, shi zalunci ?ai?ayi ne dake komawa kan mai shi?a, kuma guba ne dake cin wanda yayi da wanda aka yi mawa, sannan ?arshen zalunci nadama ne, kuma duhu ne aranar gobe ?iyama! Wata riba ka ci yanzu? ni Ban ta6a ganin rai mara buri asararre tambaWaWWe irinka ba.."


Ransa ya yi mugun 6aci da jin maganganun da ta gaggaya masa, a rayuwarsa ya tsani mutumin da baya jin shakkar shi, abun da ya fi bashi takaici ?ar ?aramar yarinyar dake gaya masa magana..

Yana fitar da numfashin bacin rai mai huci ya ce, "Ni ba asararre bane, ni ne mai buri, ban ta6a yin asara ba, komai na nema saina same shi, tun da nata so rayuwata ni mai nasara ne, mai faukaka kuma shahararre mai arzi?i, har matsayin shubagan ?asa na taka, me yafi wannan?"

Ya faWa yana Wage mata gira.

"Kuma na ci riba, tun da na dade ina she?e ayata batare da asirina ya tonu ba, ina da karfin ikon da babu wanda ya isa ya ja da ni, ko mutuwa tsorona take ji.."

Ya fada cike da alfahiri,


Girgiza kai ta yi, "Wanda ya 6ace ya 6ace, lokacin mutuwar ka ne bai yi ba, ka daina alfahari saboda har yanzu baka yi nasara ba, Allah baya mantuwa, kuma shi mai ji ne kuma mai gani.



Manzon ALLAH (??) Ya ce:  Ha?i?a ALLAH Yana yiwa azzalumi jinkiri har zuwa ranar da idan ya kama shi bazai kuSuce masa ba.



"Na fi ki ilimin addini ki daina kokarin yi min wa'azi.."


"Banga alama ba, kuma koda kana da ilmin toh baka aiki da shi sannan baka fahimce shi ba, ka dai yi asara, kuma ka ji kunya. Unaizah ta mutu tana ambaton kalmatusshahada, abun da kake ma ba?in cikin ta samu, kuma ta gane wanene mugun ubanta, mun fayyace mata komai kafin mutuwarta, idan ma kana tunanin ?arya na ke yi maka, da akwai wasiyyar da ta bar min in baka kai da kwartuwar karuwarka, sannan tasa na yi mata al?awarin Waukar fansa akanka, kana ganin kanka mai wayou da dabara bakasan komai kake yi Allah yana a sane da kai ba, baya mantuwa, dama ce ta Wan lokaci, Unaizah ita ce silar tonuwar asirinka, nasan ka girgiza da jin hakan lokacin da aka faWa maka, ?aramin kuskure ya yi silar tonuwar asirin ka..."

da tsantsar ruWani akan fuskarsa ya furta, "Unaizah ta musulunta? Kuma kun faWa mata komai! Ta yaya hakan zai yiwu? ba gaskiya kike fadamin ba, karya ki ke yi..." Ya fada cikin 6acin rai..


Murmushin takaici ta yi. "Ka yarda ko kada ka yarda matsalarka ce, sannan twin Winka ya musulunta, nasan ka gane wa nake nufi, duk da bansan ko su kaWai ne twins din da kake da su ba, tun da na ga kai din bunsurune baka da aikin yi sai zazzaga ya'ya kamar kashin awaki, kai ta sadaukar da su.."

Maganganunta sun ?ona masa rai, cikin ruWu ya furta, "Wanene twin din da kike magana akai?

?yal?yacewa ta yi da dariya ganin yadda ya 6ata fuska.

"Ina magana akan Sajeed, ko da ya ke bari na yi maka ta yadda zaka gane, Gabriel nake nufi."

"Tayaya akai kika san Wana ne?" Ya tambaya a ?agare da son ji.

A takaice ta fayyaca masa komai..


Runtse idanunsa ya yi cikin bakin ciki ya ke tariyo lokacin da ya sadaukar da su, ?a'ida idan ya sadaukar da yaro zai ?one komai nasa da yake amfani da shi, amma a lokacin da ya sadaukar da twins dinsa, sai bai ?one wayar Gabriel ba, sabuwa ce bai jima da siya masa ita ba, sai ya yi restore din wayar, sham ya manta bai cire sim card Winta ba, ya dawo da ita gidansa na Abuja, ya ba Hajiya Sarah ya ce taba Zeenatu ta dinga karatu da ita kafin ya mayar da ita school, bai ta6a zaton ?ananun kuskuren da ya yi zasu iya zamar masa matsala ba, lamarin ya Waga hankalinsa, ta yadda kwakwalwarsa ta toshe a lokacin da ya kawo wayar batare da ya tuna da sim card ba! Abun da ya fi daure masa kai meyasa bai tuna ba? Meyasa kuma bai yi tunanin siya mata wata wayar ba sai ya kai mata ta Gabriel ( Ga dukkan alamu Musa baisan ?arfin Ikon Allah ba, idan Allah ya so ya tona maka asiri, wallahi da kanka zaka aikata ?aramin kuskuren da zai yi silar tonuwar asirinka, dubararka ko wayonka baza su ta6a amfanar da kai ba, dole ne ka aikata ta hanyar da ya so)


Yayi zurfi a tunaninsa muryar Unaisah ta katse shi,


"Dukiyar da ka ke ta?ama da ita ay bada guminka ka same ta ba, haka itama Waukakar taka bata Allah bace, daga gani kai din irin fa?iran talakawan nan ne marasa galihu marasa godiyar Allah masu kwaWayin abun duniya, wadanda zuciyarsu ta mutu, ai ba a tun?aho da dukiyar da aka tara ta haramtacciyar hanya. Tausayi ka ke bani saboda na fahimci har yanzu baka san musibar da kake a ciki ba, kaifa yanzu taka ta ?are, asirinka ya riga da ya gama tonuwa, yanzu ne zaka gane komai daka tara baida amfani, zaka rasa darajar ka! mutuncinka da ?imarka zasu lalace, al'ummar duniya zasu fara yi maka kallon ?as?antaccen Wan ta'adda, ?an jam'iyarka da yan uwanka da abokananka kowa zai juya maka baya, zaka zama abun gudu, zaka rasa su na har abada, lalacewa ta same ta, daga inda duniya tasan me ka aikata zaka tashi daga Alhaji Musa richest former president ka koma gur6ataccen Wan ta'adda, mutane zasu fara aibata ka, za a dinga zagin ka da tsine maka albarka kuma ko bayan ranka ba za a daina sukar ka ba, waWanda ma basu san da tarihinka ba, idan sun zo duniya zasu ji, amma ba a matsayin mutun mai daraja ba, a matsayin fasi?i, azzalumin Wan ta'adda. Kuma ina taya ka murna bayan tozarcin da zaka fuskanta, da kuma azabtarwar hukuma, zaka fara ganin sakayyar mutanan da ka zalunta, ka aikata sin jariya, zunubi mai wanzuwa, idan mutun ya mutu halinsa ne ke cetonsa, Musa da wani hali zaka ceci kanka? tun wurin zare ranka zaka fara shan azaba, ka yi tunanin makomar wanda ya sani ya take sanin, ai kai kana a can cikin ?warin azaba, ?asa da kafiri, a halin yanzu ko titi baka isa ka ?etare ba matsoraci, rundunar sojoji tana jiranka, ga al'ummar gari, kana dira kafarka zasu fara jifarka... ." Ta ?arashe maganar tana sakin dariya kamar zautatta.

Ransa yayi mugun 6aci, daga yanayin fuskarsa zaga gane ya ji zafin kalamanta kuma ya girgiza, tsabar yadda zuciyarsa ke tafarfasa har wani gurnani gurnani ya ke yi..

Sha?e wuyanta ya kuma yi, kamar zai tsinka shi, numfashinta ya dinga kokawar daukewa tana ta nishi, yadda zufa ke tsattsafo mashi kan goshin shi itama haka gumi ke tsattsafo mata, tana ta kokarin kwatar kanta sai dai ta kasa saboda a WaWWaure ta ke da sar?a.


"Dole in yi maki azaba mai radadi, tun da nake wani Wan adam bai ta6a gaya min bakaken maganganu ba sai a kan ki, duk da ba na yi maki kallon mai hankali hakan bazai hana in hukunta ki ba, daga yau ba zaki ?ara sha?ar numfashi ba, kashe ki zan yi mahaukaciya, laifi Waya da nake danasani a rayuwata shine barin ki da na yi a raye, duk abun da kika faWa akaina ba zai ta6a faruwa ba, ina da sihirin da zan kare kaina da shi..." Yana fada yana fitar da numfashi mai huci, baiwar Allah ta gaza taimakon kanta, idanunta kamar zasu zazzago ?asa sunyi luhu luhu.


"Ni fa Uncle din Uwarki ne, kamar kaka nake a gurinki, ko dan haka yakamata ki girmamani don ubanki, ba zan kashe ki cikin sau?i ba, ina so na saka tsorona a cikin zuciyarki, ta yadda ko haWa idanu da ni ba zaki iya ba, ko kin manta da ?ar uwarki dana Waukko ku a tare? Baki tunanin a ina take? Tana a raye ko ta mutu? Ya tambaya cike da izgilanci yake Wage mata gira, sakin wuyanta ya yi ta fashe da kuka kamar ranta zai fita.


Da?yar ta iya furta, "Allah yana a tare da ita a duk inda take."


"Ki daina ambaton sunan Allah, kina wahalar da kanki ne, Allah bazai ta6a taimakonki ba, ko kin taba ganin inda ka nemi taimakon Allah ya amsa maka nan ta ke?"


"Tunaninka irin na marasa hankali ne, masu gajan hakuri, addu'a ita ce ta kare mutanan da ka so ka wulakanta rayuwarsu, Addu'a ita ce ta yi silar barin mu gidan kurkukun ?addara batare da saninku ba, baku iya yi mana komai ba har muka kawo wannan lokacin a raye.."


"Ki daina tutiya, ba addu'arku ba ce ta cece ku, Danish ne ya zama garkuwar ku, badan yana a tare da ku ba, ko gidan kurkukun nan baku isa ku ?etare ba.."


sunan Danish da ya ambata ba ?aramin karya mata zuciya ya yi ba.


"Idan muka nemi taimakon Allah, ba kaitsaye ya ke taimakon mu ba, ba ganinsa muke da ido ba, sai dai ya yi mana hanyar da taimakonsa zai isa gare mu, Danish ya taimake mune saboda Allah ya kaddara shi ne zai zama garkuwar mu..."



Shu'umar dariyarsa ya saki...


"Meyasa na ga kamar jikinki ya yi sanyi? Saboda na ambaci sunan shi?" Harara ta watsa mashi batare da ta furta kalma ba.


"Ko har yanzu kina son shi? Ya faWa yana Wage mata gira.


Ta6e bakinsa ya yi, "Ni ban ga abun da ya gani a jikinki da ya ja hankalinsa ba har ya fada tarkon son ki, ko da ya ke ba yin kansa bane, Danish bai ta6a sonki ba, nasan ba a ta6a faWa maki hakan ba, amma Danish bashi ne ya ke sonki ba, Evils din jikin shi ne suke son ki...."


Wani irin faduwar gaba ta ji, maganarsa ta razanar da ita, saboda tunawa da maganar Salsabeel da ya ta6a cewa wasu abubuwan da Danish ya ke yi bayin kansa bane, kenan maganar Musa zata iya zama gaskiya.


Shu'umin murmushi ya yi ganin ya fara ba?anta mata rai.


"Tayaya ki ke tunanin zankaWeWan saurayi kamar shi zai so kucaka irin ki? Shi ba ajinki bane, Danish ya fi karfinki nesa ba kusa ba, ba abun da zai yi da ke, abun da baki sani ba, Danish Wan homo ne shi, baisan daWin mace ba sai na namiji, he's my guy, na daWe ina kwanciya da shi, tun kafin ya mallaki hankalinsa, yana da dad..."


Bai ?are maganar ba ta kwatsa mashi tsawa, tsigar jikinta na tashi ta furta, "Bana son ji, ka daina faWa min, ?arya ka ke yi mini, Danish dina ba Wan homo bane, meyasa ka ke min magana akan shi? Bayan Danish ya mutu, ka barsa ya kwanta a ?abarinsa lafiya..."


wata yar iskar dariya ya tuntsire da ita yana kallon ba?in cikin dake a cikin idanunta

"Na ga kishi tsantsa a cikin idanunki, har yanzu bakisan wanene Danish ba, bakisan reality dinsa ba, he's really a bad guy, da kinsan adadin fursinonin da muka sa ya kwanta da su da baki 6ata ma kanki lokaci ba, kuma ba don baya haihuwa ba, da yanzu an samu ?a'yansa a cikin fursinoni. "


Fashewa ta yi da kukan ba?in ciki duk da tana kokwanto akan abun da ya fada, amma kalamansa sun rikita tunaninta, jikinta har kerma yake yi, "Ni ban damu da komai Danish zai aikata ba, idan ma kana faWamin ne don ka ba?anta raina to ka sani ba zaka ta6a yin nasara ba, har yanzu ina son Danish fiye da yadda nake son raina, kuma na yi masa uziri saboda nasan komai da ya aikata ba yin kansa bane, tursasa masa ku ka yi, don haka ka daina 6ata shi a gurina, kuma ka daina yi min magana akan shi, saboda a yanzu shi ba rayayye bane..." Bata ?are maganar ba ya katse ta, "Waya fada maki Danish ya mutu um? Kin ga gawarsa ne?" A ruWe ta ke kallon cikin idanun sa.


Makirin murmushi ya saki. "Danish yana a raye, kuma yana a tare da ni, bayan da ya faWa rijiya, batare da sanin kowa ba, na taimaka masa ya fito sannan na kashe Jeremiah..."


tsantsar ruWani ne akan fuskarta, ta kasa yarda da maganar shi, "?arya ka ke yi, Danish ya mutu, baya a raye, saboda in har yana a raye bazai iya rayuwa batare da ni a kusa da shi ba..."

dariya ya saki tare da buga tafin hannunsa ga ?asa, nan take wani madubi ya bayyana a saman iska..

"Ki kalla ki gani wanene wannan?"

Kura idanu ta yi akan madubin, su biyu ta gani a kwance saman gado, sun rungume junansu sunata aikata alfasha, kwata kwata babu sutura a jikin su...."


runtse idanunta ta yi gam ta cicccije la66anta, saboda kishi har saida ta fasa lower lip Winta jini ya shiga daddigowa, nan take wani zazza6i mai zafi ya lullu6e jikinta.


Cike da nishaWi ya ke kallon ta.


Cikin karyayyar murya ta ce,"Ba Danish Wina bane, Danish ba zai iya aikata fasi?ancin nan ba, kawai ka yi amfani da tsafin ka ne don ka ba?anta raina, kamar yadda ka yi editing hotunan Aunty Ummi don ka cutar da mahaifinta..."


haushi ya ji ganin ta ?i yarda da gaske ne, sumar kanta ya dam?a kamar zai tsige gashin ta.

"Dole ki yarda da abun da idanunki suka gane maki, Danish yana a raye, kuma yana a tare da ni ."



"Ban damu ba ko kaWan, saboda nasan cewa Danish ya mutu.."


"Bansan meyasa ka matsa saina yarda da ?arairayin ka ba, dan Allah ka tafi ka bani guri, ka rabu da ni, idan kuma kashe ni zaka yi ka kasheni kawai zai fi min kwanciyar hankali saboda na gaji da ganin ka, na tsani ganin mummunar fuskarka wallahi..." Girgiza kanshi ya yi cike da takaici yake rarraba idanunsa akan fuskarta..

"Nasan bakisan dalilin da yasa na dauko ku ba ko?" Banza ta yi da shi.


"Saboda in dawo da ran kurkukun ?addara, saboda in samu ?arfin sihirin da babu wanda zai iya ja da ni, zan gagari kowa, zan zama mai power, zan juya kowa, zan kuma sake gina kurkukun kaddara, bazan iya yin hakan ba dole saina cire zuciyar ?ar uwarki Batool na ba dodon tsafin mu ya haWiyeta, sannan kuma in kashe ki, idan na yi hakan zan samu karfin iko fiye da na Elder."


Abun da ya Waga hankalinta jin zai cire zuciyar Batool yaba dodon tsafi don ya cika mugun nufinsa, kwata kwata bata damu da ta mutu ba amma bata jin zata iya bari Batool ta salwanta, no matter what..

A ruWe ta furta, "Ni bazan iya maye gurbinta ba? Ka cire zuciyata, ka bar batool a raye, kada ka kashe ta, ko da baka da imani amma yakamata ka tausayawa Aunty Ummi, wani irin bauta ne bata yi maka ba? Ka rasa dame zaka saka mata saida hakan? Dan Allah ka da ka kashe mata babynta, gaba daya rayuwarta a cikin jarabawa take, tun tana jaririya kasa daddynta ya binne ta da ranta, sannan ka bi ta bayan fage kasa aka Wauko maka ita, sannan ka sadaukar da ita, meyasa wai ba zaka rabu da ita ba ne? Ka hana ta rayu da iyayenta, gaba daya ta ko'ina ka tauye mata hakkin rayuwarta, wai wata irin shaiWaniyar zuciya gare ka??" Ta faWa cikin kuka.


Cikin halin ko in kula ya ce, "Ba shawararki nake nema ba, babu wanda ya isa ya dakatar da ni, dole in cika burina ko ta halin ?a?a, yanzu haka suna can zasu cire mini zuciyarta, ko zaki iya taimakonta ne?"

Tana kuka tace bazan iya ba amma Allah zai taimaketa, kuma in sha Allah ba zaka ta6a cika burinka ba, ina ji araina zasu farmake ku a yau din nan, ka jira ka gani, ?arshenka ne ya zo, tun da har ka yi kuskuren daukko mu, In sha Allahu daga yau ka gama yawo.

Bushewa yayi da dariya,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login