Showing 255001 words to 258000 words out of 321579 words

Chapter 86 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

lokaci kice kinaso kwara ki fadamin tun yanzu in sani.."

"Unaisah karki.." ummi data dauko maganar bata karasaba, Dr shureim Ya toshe mata baki"pls, kibarsu suyi magana atsakanin su"! Cike da takaici tayi shiru

"Kada kiji komai Batool, tun da har kika nuna kina son gown dina, ni kuma na bar maki ita har abada, nama haramtawa kaina sanyata, koda zan rasa suturar da zan sanya ne aranar aurena.."

"Wallahi bazai yiwuwa ba, Batool bazata sanya rigarki ba, sai dai ita kada taje bikin, kima daina wannan maganar bame yiwuwa bane.." cikin fushi ummi ta fada ranta ya baci

"Shashasha Unaisah har tafiki hankali da wayou bayan ke yakamata kifita saboda kin girme ta da shekaru biyu amma saboda kawai ki kunyata mu a idon duniya shiyasa kika nace akan rigarta kikeso to wlh ba zaki sanyata ba..."

balbaleta da fada tayi ta inda ta shiga bata nan take fita ba.


Dr shureim yace"ummu batool, ki bar su suyi magana atsakanin su please.."

"Aunty Ummi, Uncle Shureim pls, ina neman alfarma agurinku, kada ku hanani kyautatama yar uwata, idan har ban bata rigar nan ba wani abu da ba'a fata ya faru zanyi danasani ne,.."

bata ?are maganar ba ummi ta katse ta"Unaisah, koda zata hadiyi zuciya ta mutune ba zata saka rigarki ba.."

bata kare maganarba dr shureim yaja hannunta suka fuce daga dakin.

Batool ta fashe da kuka tana fadin"unaisah banaso, bazan kar6a ba, ki tafi kawai ki bani guri, na tsani kaina, na bata ma iyayena rai, kowa haushina yake ji, bansan meke damuna ba, bansan meyasa nake jin haushin inga kin fini da wani abu ba.."

tallabo fuskarta Unaisah tayi ta soma lallashinta dakyar ta samu ta shawo kanta.

"Yanzu fada mun bayan rigar me kikeso? Karki wani damu da su ummu, ni nasan ta yadda zan shawo kansu... "

ajiyar zuciya ta sauke, idanunta sun kankance saboda kukan da ta sha.

"Inasan komai da zaki sanya ranar auranki, Jewelry dinki, da takalmanki, da irin make up din da za'ayi maki"

gaban Unaisah ne ya faWi arude ta Wan zare idanunta tana kallon Batool, cike da fargaban kada ta furta tana son mijinta a ?arshen zancen ta.

Cikin sauri ta katse ta"ki kwantar da hankalin ki, za'ayi maki komai irin nawa.." farin cikine ya cika zuciyar Batool.

"Nagode sis, yanzu na kara yarda ina da yar uwa maison farin cikina, wadda zata iya sadaukar da komai saboda ni.."

murmushin ya?e Unaisah tayi zuciyarta cike fal da zullumin kada nan gaba tace tana son mijinta, ba zata iya bar mata shi ba saboda shi kadaine madadin danish a duniyar nan, kuma bazata iya bari Batool ta zama kishiyar ta ba, saboda tana jin tsoron kishin batool tun ayanzu tana gasa da ita inaga idan su ka auri miji Waya"?

Sau uku Batool tana kiran sunanta bata amsa ba, ta lula duniyar tunani.

"Unaisah! " ta fada tare da bugun kafadarta, aWan firgice ta
?yaf?yafta idanunta tare da duban Batool.

"Me kike tunani ne"? washe baki tayi"bakomai sis dina, Ina fata babu sauran abunda kikeso ko"?

"Idan kin bani kayan auran naki, ke wanne zaki sanya"

"Karki damu, zan za6i cikin kayan da nake da su in sanya"

"Amma baki tunanin yaya Owais zaiyi magana idan yaga baki sanya kayan daya siya maki ba ni na sanya? Kuma mutane ma zasu tuhume ni.."

"Karki damu Batool, ai babu wanda yasan kalar rigar, mu ma awaya muka ganta baza asan tawa bace.." murmushi Batool tayi"amma bana so ki sanya wasu kayan da suka fi nawa kyau, nafison komai namu iri daya.."

daure fuska Unaisah tayi ganin ta fara wuce gona da iri.

"Batool, tun da na baki rigar, ni naji bazan sanya wata bridal gown dinba, idan bakiso in fi ki kyau Ki bani ankon ki in sanya kinga sai in saje da yan matan amarya, ke kuma ki zama amarya! Ina fata hakan ya yi maki" ta tambaya babu fara'a akan fuskarta

Shiru tayi da alamun rashin jin dadi akan fuskarta, sai tayi abu yazo yana damunta.

"Kiyi hakuri idan na bata maki rai"

Girgiza kai Unaisah tayi"baki bata min rai ba" yanzu ki tashi mu tafi gida, kinsan yau daren biki ne, yan matan amarya zasu haWu saboda su yi final rehearsal na rawar dinner da za'ayi bayan biki"

"Toh, zan yi wanka, Ki jira ni" amsawa tayi da toh, ta zauna shiru tana jiran ta..

Saukowa Batool tayi daga kan gadon ta nufi gaban dressing mirror nata, ta wutsiyar ido Unaisah ta hangota yayin da ta ke kokarin boye robobin kayan matan data satar mata a cikin drawer chest.

Ta Wauki roba daya wanda na wanka ne, tayi sauri ta shige toilet da shi.

Murmushi tayi tare da dan girgiza kanta.

Lamarin Batool na nema ya Waura mata hawan jini, yanzu ta daina tunanin hassada take da ita ko gasa, cos in har gasa ta ke yi da ita meyasa batason tafita da wani abu? Ita kawai burinta komai nasu ya zo Waya kada Waya yafi ?aya W'S'


~_____



Da marecen Ranar bridemaids su ka haWu gidan biki, abayan gidan suka yi Final dance rehearsal.

kowa dai ya ci burin zuwan ranar auren Unaisah, ni kaina jiran ta nakeyi, dani da readers dina, kai hatta alkalamina a ?agare ya ke daya rubuta.

har sai wuraren ?arfe goma tukunna kowaccen su ta nufi gidan su da ke a cikin Estate din.

kasa runtsawa tayi saboda zullumi da fargaban ranar daurin auran nata, gani take data runtse idanunta, safiya zatayi, ita kuma bataso hakan ya faru, da tana da halin da zata ?ara kwanakin da tayi sai dai ita kanta ta ?agu data ga ranar nan da ta dade tana jiran ta tunkan ta mallaki hankalin ta, tarasa meyasa take jin kamar batayiwa Danish Adalci ba idan ta auri wanin sa? Amma in ta tuna baya araye kuma dan uwansa zata aure sai taji sanyi aranta.

Yayin da take wannan tunanin tana a kwance kan gadonta tayi rubda ciki, babu haske a dakin saina laptop screen dinta data kunna tana kallon wani shortdrama mai taken Let me taste your husband, ta daura chin dinta saman pillow.

su biyu su ke yin kallo daga bisani Batool ta 6ingire da bacci, tana a gefenta ta rufe masu rabin jikinsu da duvet.

Abun da yafi damunta, yadda zata fahimtar da iyayenta game da rigar auranta da zata ba Batool, duk da tasan ba lallai su nuna bacin ransu ba tunda Batool ce amma dole suji ba dadi.

Mutun Waya da take ganin ya kamata ta sanarmawa shine Chief, tasan bazaiji dadi ba ya sayi abun da kudin shi don ta sanya ya ji dadi, fisabilillahi kuma sai yaga taje gidansa babu rigar? Me zata faWa masa idan ya tambayeta, sai dai batajinma zata iya fada mashi saboda tasan a karshe zaice zai siya mata wata ne, ita kuma bataso ?wara ta nemi wata mafitar.


Bacci ne ya fara cin karfinta ta fara gyangyadi tana ganin biji biji a idanun ta, a hankali ta fara yin hammar bacci tana lumshe idanunta.


Phone ringing dinta ne Ya katse mata kallon, agajiye ta rufe laptop din ta tureta gefe, ta janyo wayar tayi picking ta kara a kunne..


"Na kira ne don na tuna maki, daga yau ne, ina fata kin fara bankwana da kowa, cos daga yau kin gama kwana a ko'ina sai a gidana" duk da baccin dake nema yaci karfinta sai da taji dadin muryarsa.


"farin ciki kake yi don zaka rabani da iyayena"?

"Yeah, ina farin ciki zan daukaka darajarki, in aureki, mu raya sunnar manzon Allah SAW, mu kuma hayayyafa kamar yarda iyayenmu suka yi, ko bakison kiyi koyi da su ne"?..

Batasan sa'adda murmushi ya su6uce mata ba, tattausar lafazinsa, Yana kashe mata jiki


"Inaso, burina ne tun ina ?arama... " kasa kasa take magana gudun kada batool taji ta farka tasan halinta yanzu ta matsa number akan tana son itama ta yi aure rana Waya da ita.

"Fadamin me za ki shirya a agobe? Me kika tanadarmin? Me kuma zaki fara yi idan kika ganni amatsayin angonki? Hamma tayi cikin muryar mai kama data rada ta furta"ka jira goben tayi zaka ga shirin da nayi maka, zan tanadar maka kaina da soyayyata, idan na fara ganin ka amatsayin angona zanyi sujjada don nuna godiyata ga Allah daya mallaka min kyakkyawan bawan nan nasa..."

shiru taji baiyi magana ba.

"Yaya Owais? Kana jina ko kayi bacci?.. Har saida tafara gajiya, ga bacci daya kanainayeta har ta fidda rai da zai yi magana taji yace"bana tunanin zan iya cin abinci gobe, har sai naganki agidana, a tare zamu ci dinner saboda inaso ki bani abaki"


"Nima bazanci komai ba, zan jira har time da za'a kawo ni gidanka"

Tsawon mintuna babu wanda ya kara furta kalma sunyi shiru sun nutsu suna sauraron sautin numfashin junan su..

Kowannansu da abun dayake sa?awa aran shi.


A haka bacci yaci karfinta bata ?ara sanin inda kanta ya ke ba.


~_____

=إ?=ث?RANA BATA ?ARYA SAI DAI UWAR DIYA TAJI KUNYA! FRIDAY AFTERNOON, THE WEDDING DAY (RANAR DAURIN AURE) =?%?


A washe garin ranar Waurin aure, tun da asubahin farko, baki suke ta yin sammako suna zuwa gidan biki

Kafin rana ta haska, tuni Gidan Biki Ya cika makil da Al'ummar annabi, babu masaka tsinke, Yan Uwa da Abokan Arzi?i sun cika gida, Abun sai son barka..


Tun da asubahi Hajiya Layla da Hajiya Sarah tare da Ummi da Mami su ka fara Waura girke girken abincin bikin.


Auren Unaisah Ya zo da abun Waure kai, Har ranar biki babu wanda yasan menene sadakin ta, ko lefenta ba'a kawo gidan su ba, kuma ba'a san ina za'a kai ta ba, amma kowa yasan da katafaren sabon Duplex house din Owais da ke a cikin Estate.


Gaba Waya Unaisah ta rasa nutsuwarta da kwanciyar hankalin ta, jiya sun kwana adaki daya da Batool, Yau da safe ta farka babu Batool, ta kira layinta batayi picking ba, sai text message da ta ga ta turo mata.


_sis kiyi ha?uri da abun daya faru jiya, bazan iya sanya Bridal Gown din ki ba, saboda bada ni ta dace ba, kece amarya ke ya dace ki sanya, pls na rokeki don darajar manzon Allah SAW kada ki ki sanya rigarki, In har kina son farin cikina, kuma kada ki damu da rashin zuwana, bana jin dadin jikina ne, sai zuwa anjima zan shigo, ki kula min da kanki rabin raina_


Abun da takaranta a cikin sakon kenan, sai dai takasa yarda cewa Batool ta hakura da sanya gown dinta, tana kokwanton anya ita ce da kanta ta tura mata sakon? Kodai sanyata akayi dole ta rubuta mata? Saboda tasan mawuyacin abune Batool ta canza ra'ayi, kuma jiya taga halin da ta shiga akan son rigar, bata tunanin ta cikin sau?i zata iya hakura, saidai idan wani abunne ke faruwa.


Taso taje gidan nasu, sai dai ba halin ta fita, saboda shirye shiryen da ake yi mata na shiga Wakin Mijin ta.


A yanzu haka tana a tsaye cikin bedroom Win ta agaban Dressing Mirror, tana fuskantar madubin ta nutsu tana jin motsin hannuwan designer din da ke ta aikin gyaggyara mata Bridal Gown din da ke a jikin ta, designer din ce ta zo da ita daga Wedding store din su da ke a cikin garin, a wurin su Owais ya yi Order din ta, daga waje su ke shigo da kayan su, babbar macace bayerabiya.


tuni makeup artist ta kammala yi mata kwalliya, idanun ta suna a rufe gam, ta nutsu tana sha?ar fragrance Win jikin ta, Yayin da ta yi zurfi a cikin tunanin ta..

_Kada ki yi kuka Unaisah, kada ki bari wani yasan abunda ke damunki! Nasan da wuya, amma Ki daure ki jure, ki rufa mana asiri, dan Allah Unaisah, kada ki bamu kunya a idon duniya, ki bari ayi auran nan Lafiya, Allah yana sane dake, yasan halin da kike a ciki, idan kika mi?a lamuranki gare shi zai kawo maki mafita ta inda ba mu zata_

Maganganun mommynta take tunanowa a cikin zuciyarta, a lokacin data sameta da safe adaki tana kuka kan darduma.


A cikin Kunnan ta ta tsinkayi Muryar Designer din da ke ta ya ba kyawun ta.



"Wow, Oh My God! Unaisah, you look absolutely stunning, just like a real queen, This bridal gown fits your curves perfectly, and I can't wait to see your husband's reaction when he sees you in this amazing gown I'm sure he'll be blown away"


"Unaisah, now you can open your eyes, please I want you to see how this bridal gown transforms you."


Gently ta soma buWe idanunta kaitsaye ta fara hango kanta ta cikin madubin gabanta.

Speechless, da sauri ta karasa buWe idanunta ta zare su, bakin ta abuWe take kallon ikon Allah..

Wata hadaddiyar mermaid silhouette bridal gown ce, strapless dandatsetsiya



"Unaisah, this bridal gown is custom-made and a limited edition, designed by the renowned fashion designer, Your husband bought it especially for you, and it was expensive"

Waro idanu waje tayi ta kara bude bakin ta da mamakin jin abun da designer din tace.




Kyaf?yafta idanunta tayi kamar a mafarki take kallon kanta ta cikin madubi da tsantsar mamaki akan fuskarta.

A hankali Designer din ta soma kokarin daura mata wani diamond-ecrusted veil asaman hadadden hair style din ta.

Ga wani hadadden Bridal flower hair pin da akayi mata ado da shi asaman gashinta.


?afafunta suna asanye da wasu hadaddun High Heels, irin takalmin da in ka sanyasu kake jin tsoron taka ?asa saboda fargabar kar su 6aci, dakyar aka sanya mata takalman saboda bata saba sanya takalmi mai tsini irin wannan ba..

Akan idanunta ta Wauko hadaddiyar diamond necklace mai fasalin 5-carat diamond center stone, an kewayeta da adon smaller precious stones, daga cikin jewelry box din data buWe agaban mirror

ta fara sanya mata a wuyan ta.


Gaba Waya ta ruWe da ganin tsadaddun kayayyakin da take sanya mata a jikinta sai kace wata sarauniya"?

Gaba daya ji take kayan sunyi mata nauyi, adon yayi mata yawa, bata kai matsayin da zata sanya su ba, gaba daya kanta ya daure tamau da al'ajabi, So take ta tambayi designer din farashin su sai dai takasa saboda tana jin tsoron taji abun dayafi karfin kunnanta, tarasa gane diamonds din gaske ne ko na ?arau?arau ne? Taga dai sai kyalli stones din sukeyi, Badan badan kar ace matar dg batasan diamond ba ko ace tayi ?auyanci da ba abun da zai hana ta tambaye ta.


"Something Is missing!" designer dinne Ta furta.


AruWe Unaisah ke kallon ta ta cikin madubin gabanta, ta Wan yamutsa fuska, adabarbarce tace "ma'am ban gane me ki ke nufi ba?


Murmushi tayi"its something special daya kamata ace na gani a yatsanki, wanda shi kadaine zai kara tabbatar mana da cewa Ke din amarya ce.."


confusingly, ta Wago da yatsunta da suka zanu da lalle ta ?ura masu ido, nan take ta gane me ta ke nufi wato zobe da babu"

"Meyasa Angon naki bai sanya maki ba har ranar auranku, Bansan ko mantawa yayi ba amma ko dai bakuyi dating din juna ba before, auran haWi ne babu shiri?" (gulma ajali)

Wani irin haushin ta ne Ya kamata, dama tagaji da tsayuwa..

"Karki damu, bai rage maki kyawun yatsunki ba, kawai muhimmancinsa nake dubawa"

Shiru tayi cike da takaici batare data furta kalma ba.

"bari na kira angon naki muji" tana kokarin zaro waya daga aljihun rigarta Unaisah tay saurin ruko wuyan hannun ta..

"Pls, babu bukatar ki kirasa! yanzu haka suna a masallaci gurin daurin aure, bana so mu takura masa, Indai zobene ba mantawa yayi ba, ya riga daya fadamin zai saka min bayan daurin auren mu.... " ajiyar zuciya ta sauke..



A gidan Dr Shureim


Yana atsaye gaban Mirror Yana karasa shirya kan shi, tsadaddar shadda ce a jikin shi Launin Blue sky, A hankali Ya ke sanya agogo awuyan hannunsa sai sauri yakeyi ganin Lokacin sallar juma'a na dab da cika..

Mika hannu yayi da niyar ya dauki arab turban dinsa daya daura gaban mirror, Unexpected yaga ta zura hannu ta bayansa ta riga Wauka, juyowa ya yi tare da duban ta, sleeping gown ce sanye a jikin ta, ta tufke gashin kanta da ribbom.

"Sanyin idaniyata"

ta karashe maganar tare da manna masa sumbata kan kuncinsa, ta shafo sajen shi ya lumshe idanun shi tare da furta"Masha Allah"

Janye hannun ta yayi tare da kawar da shi ya lura nema take ta zautar da maluntakarsa.


"please, Ustatha, kada ki karya min alwalata, baki ga time ba, nafa kusa makara.." ya fada yana nuna mata agogon bango.

"I'm Sorry, mijin so, nima yanzu zan shirya in tafi gidan bikin, Benazir tana ta kira na, kasan mune manyan kawayen uwar amarya, Yar mu zatayi aure yau dole mu kure kur adakanmu"

Murmushi dr shureim yayi"Zan yi missing ummu Batool, inaso na zama mutun na farko da zai fara ganin shigar da zakiyi yau, but please ki rufemin ko'ina na jikin ki, bana so wani ya gane min sirri na.."

Yar dariya tayi"karka damu abban batool, zanyi yadda ka ke so" murmushi suka sakar wa juna.

"Ina Batool sarkin rigima? Ko acan ta kwana ne"?

"Eh, tana atare da yar uwarta"

Numfasawa yayi"pls nasan abun daya faru jiya ya 6ata maki rai, mu yi hakuri da ita, tun da bata taba mana haka ba.."

"Kada ka damu komai ya wuce, amma zanji kunya yau in har Unaisah taba batool bridal gown dinta, mutane zasuyi tsegumi, su kansu iyayen ta bazasu ji dadi ba, inaga mijinta da ya siya mata rigar? Ta fada da damuwa akan fuskarta..

Shima damuwarce karara akan fuskarsa"bamu da mafita, kuma bana son ganin Batool cikin damuwa, jiya naji zafin ganin yadda take kuka akan mun furta ba zamu iya siya mata kalar rigar Unaisah ba, amma da Unaisah tazo kinga ta sasanta komai, muyi hakuri da komai zai biyo baya, tun da ta riga da tace zata ba, karmu shiga tsakaninta da yar uwarta pls.."

ta6e baki Ummi tayi"tom, Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa" ya amsa da ameen.

"Muje na rakaka bakin mota"

"But ki tsaya abayana" dariya tayi dan ta gane mi yake nufi.

Ahaka suka tafi yana agaba tana abayan shi..

Bayan taga Tashin Motar dr shureim da sauri ta nufo upstairs tun tana tafiya akan matakalar ta soma jiyo sautin bugun kofar da Batool takeyi daga cikin dakin ta

Bam! Bam!! Bam!!!


Daga bisani tajiyo muryarta cikin kuka

"Ummina ki budemun Kofar pls, ki taimaka ki buWe min, na gane kuskure na, kuma na tuba bazan ?ara ba, dan Allah don sonki da manzon


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login