Showing 303001 words to 306000 words out of 321579 words

Chapter 102 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

take magana tana ?yaf?yafta idanunta yasa ta gane ba gaskiya ta fada mata ba.

"Hmmm me ya kai ki gidan Unaisah? Ko kinfi sauran yan uwan nakine da kika kwashi kafa kika bita? Ko kuwa kinje ne donki gano furniture dinta kice kema irin su kikeso ayi maki"?

Girgiza kai tayi a tsorace take kallon daddynta don ya taimaka mata saboda tasan shi zai fi fahimtarta, babu alamun zaiyi magana saboda Ummi taki sauraron shi.

"Ba haka bane ummi, ni banje da niyar hakan ba, kawai ina son in kara ganinta ne"!

"Wallahi ban yarda dake ba, karya kika fadamin, kuma na rantse zan kira Unaisah ayanzu in har naji akasin abun da kika fada saina zane ki"

ta ?arashe maganar tare da sakin Wuyan rigarta, har ta daga ?afa zata juya don ta dauko waya ta kira Unaisah batool tayi saurin furta"am sorry Ummina, nayi maki karya, ba gaskiya na fada maki ba, amma ki fahince ni, bana so na fada maki inda naje.. "

juyowa tayi a sukwane ta dube ta"Batool yaushe kika fara yin karya? wai meke damun ki ne meyasa kika sauya halayenki"?


Sunnar da kanta kasa tayi, hawayen da suka cuccuko idanunta suka soma dira kan kuncin ta, taso ace zata iya fada mata gaskiya sai dai bata son mutuncin ya Owais ya zube a idanunsu, tana son ta kare mashi martabarshi koda iyayenta zasu ?i yarda da ita ne.


"Batool, zoki wuce kije daki ki kwanta dare yayi, Gobe zamuyi magana," shurem ne ya faWa, amsawa tayi da toh abba, cikin sanyin jiki ta ra6a ta gefen ummin data saki baki sototo tana kallon ta, har saida taga tabar falon.

tukunna ta kawar da idanunta tare da duban shureim"kada son Batool ya rufe maka ido ka kasa bata tarbiyar data dace, saboda na fahimci baka son kaga inayi mata faWa, tayaya ba zamu tuhumeta akan ina taje ba? Kana ji tayi min karya bayan ba halinta bane, kuma ta sauya kaya awaje, hakan bai dame ka bane"?

Ta faWa idanunta cike tab da kwalla ciki karyayyar murya tace

"ina jin tsoron batool ta fuskanci irin rayuwar dana fuskanta abaya.." ta ?are maganar tare da kifa kanta saman kafadarshi, tuni zuciyarshi ta karaya, tsantsar tausayinta ya kama shi"ummu Batool, mu zauna zanyi maki bayani" bata musa mashi ba, ta dago da kanta ta zauna kan Sofa, shima ya zauna daga gefenta.

"Abun daya sa ban damu ba, ban kuma tsawatar mata akan ina taje ba, Saboda Na san inda taje.."

aruWe ta dube shi cike da son jin karin bayani tace"bangane me kake nufi ba! Kasan inda taje shine baka fadamin ba kabarni ina ta 6a6atu"?

Tattausan murmushi ya sakar mata"saboda kin?i ki saurareni shiyasa nakasa yi maki bayani, amma Batool tana a tare da mijinta, shiya Wauke ta ya kaita gidan ta, Nima sai daga baya ya kirani awaya ya faWa min" rudanine tsantsa akan fuskarta"har yanzu bangane me kake nufi ba! Dan Allah kadaina yi min wasa da hankali! wani irin miji? Yaushe batool tayi aure har da gidan miji ni da nake uwarta bansani ba"!? gyaWa kansa ya Wanyi.

"A yau baba Imam ya Waura auran Batool bayan ya kammala daurin auren Unaisah.."

bai ?are maganar ba, ganin yadda ta zabura ta mi?a tana kallon shi.

"ki yi hakuri na boye maki ne saboda mijinta ya bukaci da aboye mata har zuwa ranar da zata tare a gidansa, abun da kike burine ya tabbata, Batool ta samu miji nagari nagartacce, mai tsoron Allah, mai tsantsar ilmin addini da sanin yakamata, wanda nayi imanin Allah ne Ya rufa mana asiri ya kaddara son ta a zuciyar shi..."

bai ?are maganar ba ta katse shi "dagaske kake ko wasa? Wanene kuma mijin nata"?


"Wanda take so, za6inta shine mijinta... "

Kamar taji abun tashin hankali Ta furta Inna lillahi tare da dafe kai da hannu daya tana fadin"shikenan, Batool ta gama dani, taja min abun kunya, wato saida ta fada mishi tana son shi, shine Ya hada da ita ya aura, hankalinta ya kwanta, ta auri miji Waya da Unaisah, don taci gaba da yin gasa da ita.."

kamar zata fashe da kuka ta ?arashe maganar cikin ba?in ciki.

Yar dariya dr shureim yayi"ba haka bane, Ki zauna zan yi maki bayanin da zaki gamsu" cike da damuwa ta zauna gefen shi, a tsanake ya soma fayyace mata komai tiryan tiryan.

Yayin da take sauraron shi, tsantsar al'ajabine Ya kamata, batasan sa'adda ta fashe da dariyar farin ciki ba kamar wadda akayiwa albishir da gidan Aljanna, hawayen farin ciki suka cuccuko idanunta, ta Waga hannayenta sama tana fadin"Alhamdulillah! Alhamdulillah! Allah na gode maka daka cika mana burin mu, batool ta samu miji nagari, ta auri za6in ranta, mutumin da take ta hauka akanshi ashe shima yana sonta.." dr shureim da ke kallon ta murmushine akan fuskarsa.


Saukowa tayi daga kan sofa, ta dur?usa kasa tare da yin sujudushshukur,
Sa'ilin da ta dago hawaye ne sha6a sha6a kan fuskarta cikin harshen larabci ta dinga yiwa Allah kirari tana gode masa da ni'imomin da yayi masu arayuwa.

Daga bisani ta mike tare da duban dr shureim"na kar6i uzirinka da ka ki fadamin ?ata zatayi aure amma ai da ka fadamin kodan in shiryata ko"?


"Karki damu, ya bamu two weeks kafin ranar Dinner dinsu, don muyi shirinmu kafin amaryarsa ta tare a gidanta"

ihun farin ciki Ummi ta fasa wanda yayi silar razanar da Batool daga bedroom dinta ta jiyo ta, jikinta na kerma ta fito ta nufi down tana fadin ummina meke faruwa? Meke damunki"!

Kusan atare suka juya suna kallonta, har ta musanya kayan jikinta dana bacci"ki koma daki ki kwanta, babu abunda ke faruwa, fira mukeyi mai dadi" ummi ce ta fada tana dariya, Batool ta rude da ganin fara'a akan fuskar mommynta sa6anin dazu data rufe ta da fada ko annuri babu akan ta.


Bata musa ba, tace"toh, ku kulamun da kanku, sai Allah yakaimu" har suna hada baki gurin furta"muma ki kula mana da kanki, Allah yakaimu lafiya,"

da murmushi akan fuskarta ta juya ta nufi bedroom dinta, taji dadin ganin su cikin farin ciki, da tana ta zullumin fadan da ummi zatayi mata don tasan ba ?yaleta za tayi ba, amma yanzu taji hankalinta ya kwanta sosai.


FaWawa tayi saman gado tare da janyo pillow ta rungume shi a kirjin ta tana jin kamar shine ta rungume, a hankali ta lumshe idanunta tana tariyo abun da suka tattauna da shi bayan ya kawota agida a cikin motar shi.


_"Nasan yanzu kin daina ganin girmana, may be kin daina sona tun da na neme ki ko"?_

_"Har abada bazan daina ganin girmanka ba, mutuncinka bazai ta6a zu6ewa a wurina ba, saboda nasan wanene kai kuma na yarda dakai.. "_

_"zaki iya rufa min asiri ba zaki fada ma kowa abun da na nema a gurin ki ba"_

_"Babu abunda zaisa in tona maka asiri, koda za'a azabtar danine don in faWa"_


Da tunanin abun daya faru a tsakanin su ta kwana.


~___________________________________=؋?=ؗ?


*DESTINYSHIELD=ؘ?*


bayan daya ?arasa labarta mata, cikin fushi ta buga kanta jikin ?ofa ta fashe da matsanancin kuka kamar ranta zai fita, wani irin ?unci da bakin ciki ne ya ziyar ci zuciyarta, badan batayi farin cikin dawowarsa araye ba sai don takaicin tsawon shekarun da take ta dakon soyayyar mamaci ashe yana araye shiyasa soyayyarsa ta?i mutuwa a cikin zuciyarta, Hankalinsa ba ?aramin tashi yayi ba duk yabi ya ruWe duk da yasan halin kayan sa dama sai da yaji shakkar bayyana mata kan shi.



Cikin sanyin murya yace "Nasan ban kyauta maki ba, amma ki sani daidai da second ban ta6a mantawa dake ba, zuciyata da sonki take bugawa, babu abun daya sauya na daga kaunar da nake maki! kina araina Unaisah, kuma komai da nayi nayi ne saboda ke ! in har ban nisanta kaina dake ba bazan ta6a samun abun da na samu a yanzu ba"


Ya ?arashe maganar yana kallon gefen fuskarta da ta 6aci da hawayen ta sha6a sha6a.

Wai Yana araye bata sani ba, bai ta6a nemanta ba, babu wanda ya faWa mata.

Fashewa ta kuma yi da wani kukan mai tsuma Zuciya, cikin fushi da tsantsar 6aci rai ta juya ta fuskance shi batare data dubi fuskarsa ba, ta cakumi gaban rigarshi da hannayenta, ta bubbuga kirjin shi, idanunta da ke tsiyayar da hawaye ta runtse su gam..


Cikin shesshekar kuka tace"I will never forgive you! You hurt me! You left me with the pain of your love, causing me heartache and anxiety that put me unconscious for four days! Why did you do this to me? What did I do to deserve that from you"? Dakyar ta karashe maganar tana jan numfashi.

Kafin ta Waura da cewa "Ka ce saboda ni ka yi komai, Idan da na mutu fa? Ko kai ka mutu a cikin wadannan shekarun da bamu a tare"? ta faWa tana cigaba da zubar da hawaye.


Ko uffan bai ce ba, Yayi shiru yana sauraron ta.


can ?asan makoshin ta furta

"Man so kayi ka kasheni wallahi"


Numfasawa yayi a hankali cikin sanyin murya ya furta

"i know everything that happened to you after I left, Akhi Owais yana faWa min komai game da ke, and I'm not happy about it, I made a mistake by leaving you, duk da banyi hakan don na cutar dake ba, and I never stopped loving you Unaisah" ya fada yana kokarin fahimtar da ita.


"amma inaso ki sani komai nayi kece sila Unaisah, You caused it all, you're the reason I distanced myself from you"


Cikin ruWu ta buWe jajayen idanunta a cikin na shi wani irin ?warjini yayi mata da saurin ta kawar da su gefe Waya



"Da farko na tafi kai farmaki na kuma sadaukar da kaina saboda ke, saboda inason in zama jarumi mara tsoron zuwa ya?i don kuma in wanke kaina daga zargin da kike min na goyan bayan matsafa, ki san cewa ni ba matsafi bane, bana goyon bayan zalunci, ban kuma ta6a taimaka ma azzalumi ko ni nayi zalunci...."


kalamansa sun Waga hankalin ta.



"I chose to distance myself from you, even if the pain of loving you would kill me, alkawarine na daukarwa kaina Unaisah, bazan ta6a dawowa gare ki ba, har saina musulunta na kuma samu Ilmi don inyi yaki da jahilcina, saboda inaso kiyi alfahari dani Unaisah, And, Alhamdulillah, I now have everything I wanted, I've accepted Islam, gained knowledge, and overcome my ignorance, I'm proud to say that I've become a better person for you, ina da komai Harma da asali bawai iya kyau gare ni ba... "



Gaba Waya ya kashe mata baki, wutarta ta Wauke Wuff, ko hada idanu da shi ta gaza yi saboda wata irin shakkar shi da ta ke ji, yanzu ta gane dalilin dayasa ya yi komai, babu ?arya a maganarsa, itace sila itace kuma taja ma kan ta, duk da bata furta kalaman da nufin ta goranta masa ba.



"There's no evils in me now, Allah has freed me from them, I have no magic, and I have peace of mind to live with you without hurting you, since I've become a complete person.

(A yanzu babu Evils a jikina, Allah ya rabani da su, bani da tsafi, ina da kwanciyar hankalin da zan rayu dake batare dana cutar da ke ba, tun da na zama cikakken mutun)

ya ?arashe maganar tare da sauke ajiyar zuciya.



Ya lura da yadda tabi ta ruWe ta kame kanta ta shiga taitayinta kamar wadda tayiwa sarki ?arya.


"Ban faWa maki da wata manufa ba, ban kuma yi hakan donna goranta maki ba, face sai don inason nasa ma mana mafita, nima inaso na zama mutum mai daraja da kima, mai kuma mutunci a idanunki dana kowa ma"


ya faWa yana bin fuskarta da kallo, Ta?i yarda su haWa idanunsu cikin da juna saboda nauyinsa da ta ke ji.


"a zaman da nayi da iyayena na dauki darussa sosai, idan har kanaso mutane su mutuntaka dole sai ka mutunta kanka, jahilci duhu ne arayuwar mu, ilmine kadai hasken daya ke kore su, haka rashin asali baida dadi ko kadan saboda sai da asalin nan mutun zai yi tunkaho, kuma rufin asirin bawane, duk da komai ya faru da ni ba laifina bane ja mun akayi amma yanzu komai ya wuce bani da sauran damuwa... " a tsanake ya kare maganar.


Bai faWa mata da wata manufa ba, amma duk sai taji ta muzanta agaban shi, gani take ma kamar ba Danish dinta bane saboda wannan yafi ?arfinta nesa ba kusa ba, babban gorone magogin karfe, ba haka tasan danish din ta ba, tayaya ma zata iya rayuwa da shi bayan ya sanya mata tsoron shi a zuciyarta.


Cikin disasshiyar murya ta furta"My Danish is dead, he's not alive You're not him and you'll never be him, because I don't feel that you're him! Your name is Omair, Wan Prime ministern Canada da sheikha mujeedat, grandson of Emir Khalid of Dubai, knowledgeable, rich, purely beautiful, with royal blood and a noble origin"


("Dannish dina ya mutu, ba ya raye, Kai ba shi ba ne! kuma ba za ka taba zama shi ba, saboda bana jin kai ne! Sunanka Omair dan Prime Ministern Canada, da Sheikha Mujeedat, jikan sarki Khalid na Dubai, masani, mai kudi, kyakkyawa zalla, mai jinin sarauta da asali mai daraja")


dakatawa ta Wanyi tana share ?wallarta da yatsun ta dake kerma, ta haWi yawu mai Waci dakyar ta iya saka marayun idanunta a cikin na shi"meyasa ka aureni? Bayan kafi karfina? Ni ba ajinka bace! Ban kai ka ilmi ba, ban kai ka waye wa da asali ba, ni ba yar kowa bace, mahaifina bawani bane, mahaifiyata ba yar kowa ba ce, ba mu dace da juna ba Omair, ina kallon kaina a matsayin ?as?antacciya agaban ka, ba zan iya zaman aure da kai ba..

ta faWa cikin shesshekar kuka tana girgiza kanta..

_"I love my Danish! I can only live with him because he loves me for who I am I also love him for who he is, we lived through difficulties and sadness, and we never changed for each other_"

(Inason Danish Wi na! Da shi kadai zan iya rayuwa, saboda yana sona a yadda nake nima ina son shi a yadda ya ke, mun rayu cikin wahalhalu da bakin ciki, kuma bamu ta6a canzama juna ba)" da?yar sautin muryarta ke fita.


"inason shi da jahilcin shi, Inason shi da rashin asalin shi, kuma Inason shi da talaucin shi, and I love him for being nobody's son, Ina kuma son shi da kasantuwar shi ba dan kowa ba, da burin zan aure shi in rayu da shi in kuma taimaka mashi ya nemi ilmi don ya inganta rayuwarsa"



da?yar ta ?arashe maganar saboda sha?ewar da muryarta tayi sakamakon kukan da ta ke yi.

Gaba Waya babu annuri akan fuskarsa, tamkar bai ta6a yin dariya ba, ba haka ya zata daga gare ta ba, ta 6ata masa rai ta kuma karya masa zuciya, kwata kwata baiga alamun tayi farin ciki da dawowarshi araye ba, batayi murnar sauyawar shi ba! Bayan saboda ita yayi komai? Anya Unaisah tana son shi har yanzu? Tana kuwa son cigaban shi"?


Sam ya kasa furta kalma, ta kashe mashi baki, sai yaji dama bai dawo ba gaba Waya!.


Jinjina kan shi ya Wanyi cikin fushi yace "Tell me, how can I make you understand? What's wrong with you? kin sauya min! that's not what I expected from you, You weren't happy about my return at all, ba ki taya ni farin cikin samu asalina da kuma cigaban dana samu ba arayuwana ba"!

wani irin faWuwar gaba da sarewar gwiwa taji a lokaci Waya!


"Ina kokwanton in har yanzu kina sona! may be kin samu wanda ya maye maki gurbinane! kamar bakison cigabana! bayan ke da kanki kika furta bani da komai da zakiyi alfahari da ni ban da kyan da Allah yayi mini, Unaisah you're the one who inspired me to achieve those goals! I followed your orders and did everything for you! Why can't you see"?


Da?yar ya ke yin maganar saboda bai saba yin surutu mai tsayi ba, wahala ya ke sha.


"kin sauya magana Unaisah! Bakisan cigabana Unaisa! If not, why aren't you happy for me as Omair? You know I can never go back to being the Danish you knew, I regret coming back to you, I won't force you to stay with me If you can't live with me as Omair, you can choose to break up with me"


yadda yayi maganar da tsawa yasa ta gigice, wani irin matsanancin ciwon kai ne ya sara mata nan ta ke jiri ya kwasheta agalabaice ta yi taga taga zata faWi batasan sa'adda ta dur?ushe ?asa ba, duk akan idanunsa ko gizau baiyi ba, balle tasa ran zai taimaka mata.

Bai aune ba yaji ta rungume kafafun sa da hannayenta, jikinta na kerma ta rasa me ke mata daWi duniyar nan! cikin sha?a??ar murya ta furta Ina son Danish Wina ya dawo gare ni, ka koma Danish dan Allah! shi kawai nakeson gani, Danish dina ba haka ya ke min ba, baya fushi dani, baya son 6acin raina, yana fahimtana, baya min magana da tsawa, bamu iya rayu nesa da juna, amma kai ba kamar shi ka ke ba, tayaya zan ji ka a matsayin shi? Bayan ka sauya gaba Waya.."


zuciyarsa ta karaya da jin kalamanta, jikinshi yayi sanyi la?was kamar babu laka, baisan meyasa yayi mata haka ba? Meke damun shi ne, duk da itama da laifinta ta kasa fahimtarshi duk kokarin dayake Dan ta fahimce shi Abu yaci tura.

Tsantsar tausayinta ne ya mamaye zuciyarshi har yaji kamar bai kyauta mata ba, bai san ya zaiyi da ita bane! Baisan me ta ke so ya yi mata wanda zaisa taji shi a matsayin Danish!


_Tayaya zasu samu fahimtar juna a daren farko na ranar auran su? Bayan sa6ani ya shiga tsakanin su? Bayin Allah har alkawarin ciyar da juna su ka yi=ؔ?_

kwatsam Yaga ta kife kan floor babu numfashi, Tashin hankali, gabansa Ya faWi rass! arazane Ya zube kan gwiwowinsa Ya tallabo kanta da tafukan sa.

kyawawan idanunsa a kan fuskarta data jike sharkaf da hawaye kamar ba A.c a dakin gumi duk ya wanke ta, cikin karyayyar murya ya furta

"Ya rouhi! My Angel! Habib albi! Wake up pls, Ni ban dawo don na 6ata maki rai ba,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login