Showing 3001 words to 6000 words out of 321579 words

Chapter 2 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

yaga Benazir ta kwallafa rai ne akan son zuwa can tayi karatu kuma ta nuna tana son suje tare da Aisha shi kuma yayi la'akari da shakuwar dake a tsakaninsu In aka rabasu ba zasu ji dadi ba shiyasa ma har ya nemi Benazir data kar6o ma shi Academic record din Aishah.

A ranar da su ka yi maganar, bayan Alhaji ubaid yayi mashi sallama ya tafi, ranshi a bace Ya kira Aisha ya fara mata fada akan takardun karatunta data kai ma Alhaji ubaid don ya sama mata admission, tace mashi wallahi ba ita ta bashi takardun ba, hasalima ita batasan da maganar ba, ko da jin hakan nan take ranshi ya bashi da sa hannun Aunty Laura, Har daki Yaje ya same ta da maganar, maimakon ta kar6i laifin ta saima ta dinga masifa tana fadin taje ta bada kuma wallahi bai isa Ya hana Aisha taje karatu kasar waje ba, shi ko dan zumuncin dake a tsakanin shi da Alhaji Ubaid bazaisa Ya amince be? Idan Ma yana jin tsoron wani abu ya same ta acan din Ba Allah ke tsare bawansa ba, bayan haka tun da Ba ita kadai zataje ba hada Benazir ya bar ta mana, shiekh imam yace mata ya gama magana bata isa tasa shi canza ra'ayin shi ba.


Ganin da gaske Shiekh Imam zaiyi mata bukulun kudin da take samu agurin Alhaji musa yasa ta kwashi kafa taje gidan kakarsu ta bangaren Uba da ta rage masu mai Suna Hajjo, ta tsara mata karya da gaskiya akan kullan da Sheikh imam ya ke yi ma yarsa, ta ce ita bakin cikinta gorin da ya ke yi mata akan Aisha sai kace ba diyar yayarta ba, In da kara aisha ai yar ta ce tana da ikon juyata son ranta, bayan haka ta fada mata Alhaji Ubaid Ya sama ma Aisha gurbin karatu a kasar germany ita da Benazir amma Ya hana bai dubi zumuncin dake a tsakanin su ba, Hajjo da ranta ya 6aci ta sa Aunty laura ta kira mata imam a waya tace yazo tana son ganin shi, koda yazo ta balbaleshi da fada kamar zata rufe shi da bugu kasancewar shi mai biyayya yadinga bata hakuri kamar zai durkusa mata kasa tace mashi in har yana son farin cikin ta yabar Aisha ta tafi karatu kasar germany, Shiekah imam yayi kokarin ankarar da ita illar dake akwai na tura Wa karatu kasar waje balle ita da take mace amma Hajjo ta rufe ido tace itafa ta gama magana, kawai yabi abunda tace mashi, ta ko'ina ta matsa mashi lamba ba dan yaso ba ya amince zai barta, don yasan halin Hajjo rikicin tsufa ne ke damunta.

bayan komawarsu gida baibi takan Aunty Laura ba Ya kira Aisha ya tambayeta da son ranta zataje kasar waje karatu? Aisha tace aa bata so saboda batason tayi nesa da shi, amma benazir ta nuna tana so suje suyi karatun atare acan tun da ba wasu shekaru ne masu yawa ba" a maganarta shiekh ya fahimci bada son ranta ba amma tana son ta bi aminiyarta ba yadda ya iya hakanan ya amince.

Bayan Alhaji Ubaid Ya kammala yi masu travel arrangement, ana i gobe zasu tafiya sheikh imam bai iya runtsawa ba, saboda zazza6in tafiyar da Aisha za ta yi, wannan ne karo na farko da zatayi nesa da shi, bawan Allah akan dardumarsa Ya raba dare yana yin nightprayers duk akanta, washe garin ranar aunty laura ta shirya ta tsaf, a motar sheikh imam suka tafi, acan airport suka hadu da Benazir tare da family dinta da su ka yi mata rakiya, Aisha tasha kuka na rabuwa da Baba imam, har nasiha yayi mata akan ta ji tsoron Allah, kada ta canza a yadda yasan ta, sannan ta kare mutuncin kanta, karatu yakaita daga shi bai amince tayi wani abu da zai sa6awa mahaliccinta ba.

Baba imam bai ?yale Aisha hakanan ba saida Ya hadasu da Benazir ya karayi masu nasiha mai tsuma zuciya sannan ya dam?a ma Benazir amanar Aisha yace ya yarda da ita bai ta6a barin Aisha ta kula wata kawa in ba ita ba don haka ya bata amanar yar shi, ta kula mashi da ita.

Benazir jikin ta ba karamin sanyi yayi ba, har kuka saida tayi saboda tausayin baba Imam, Alhaji ubaid ma yayi masu nasiha, bayan ya gama dr shureim Ya kirasu agaban shi Yayi masu addu'o'i tare da yar nasiha A lokacin Aisha ta dinga kallon shi, tayi fatan Ya furta yana sonta kafin su tafi amma sai baiyi ba saboda shi kallon kanwa ya ke yi mata, bawai don baya sonta ba sai don kasancewarsa miskili da zurfin ciki ko kallonta bai cika yi ba, bayan Aunty laura da hajiya layla sun sanya masu albarka tare da fatan alkhairi a karatun su, daga nan suka yi masu bankwana.


Silar hawan su jirgi Allah Ya ?addara haduwarsu Da Aneelerh Muhammad falgore itama a lokacin za ta je yin karatu kasar germany, ta zauna a seat daya da Benazir taga ta burgeta ta Wan fara janta da fira har Benazir ta dan saki jiki da ita, A lokacin Aneelerh batasan da zaman Aisha a cikin jirgin ba tana a seat din bayansu ta rufe fuskarta da mayafinta zuciyarta cike fal da tunanin mahaifinta data bari da kuma muradin ranta.

Bayan jirginsu yayi Landing a airport na birnin hagen, Alhaji Musa Ya turo wani escord Winsa Yazo daukarsu a hadaddiyar mota, sukayi sallama da Aneelerh suka shiga mota, a zaton su kaitsaye escord din zai wuce da su Jami'ar da zasuyi karatu acan, amma sai suka ga akasin hakan, a wani katafaren gida da Alhaji musa Ya kama masu haya a kusa da Jami'ar, Anan Escord din yakai su a matsayin gidan da zasu zauna, Aisha tayi mamakin haduwar katafaren Gidan, tayi azan a hostel zasu zauna amma sai taga akasin hakan, tsabar gatanci hada masu aiki Ya aje masu agidan, kamar ba karatu suka je yi ba Aisha ta Wanji shakkun ta zauna agidan saboda gudun kada ta shagala ta kasa ta6uka abunda ya kawota amma saboda Benazir yasa ta amince ta zauna, rana ta farko da suka fara shiga jami'ar, ba zato ba tsammani sukayi arba da Aneelerh ashe itama a nan zatayi karatu, Sunyi farin ciki da ganinta duk da ba'a department Waya suke da ita ba, rayuwarsu a jami'ar gwanin ban sha'awa shiga class kadai ke rabasu amma da zarar sunfito zasu hadu da Aneelerh a karshe ma da kawancensu yayi karfi da Aneelerh sai suka yi mata tayin ta baro hostel ta dawo gidansu da zama, Aneelerh bata musa ba ta amince masu toh ita kanta data ga inda suke rayuwa saida ta girgiza da mamaki saboda haduwar Gidan.

Uncle musa ba karamin gatanci yayi masu ba, shi ke daukar dawainiyar komai nasu, tun daga cinsu shansu suturarsu masu kyau da tsada har account ya sanya yaronsa ya bude masu na kasar germany, baya gajiya da tura masu dollars kamar baison zafin neman su ba, lamarin shi ya fara daurewa Aneelerh da Aisha kai ganin yadda ya ke ji dasu yana tarairayarsu, wani abun daure kai Duk weekend sai yazo kasar germany daga America, kuma agidansu Yake sauka anan zai kwana su yi breakfast lunch dinner duk tare da shi, har yawon buWe ido Yake zagayawa dasu a motar shi, da abun ya fara damun aisha ta dai gaza hakuri ta fada ma Benazir itafa zata koma hostel da zama saboda tana jin tsoron baba Imam Yaji labarin ba a jam'ar take zaune ba zai iya yi mata fada bayan haka bata son yadda Alhaji musa ke kashe masu kudi abun yayi yawa, sannan meyasa yake zarya duk week end sai yazo ya kwana agidansu? A ganinta hakan bai dace ba, a matsayinsu na musulmai kuma mata su dinga barin Namiji yana kwana a gidan su, Benazir ta nuna kin amincewarta da komawar Aisha Hostel, ta dinga lallashinta akan tayi hakuri ta zauna, na dan wani lokaci ne, kada ta damu da Alhaji musa halinsa ne shi mutum ne mai son yin alheri yana da wayewa don haka kada ta dauka da wata manufa ya ke zuwa kawo masu ziyara, sannan kuma kada ta damu sheikh Imam bazai ta6a sani ba.

dakyar Benazir ta shawo kanta har ta hakura da komawa hostel Win, kusan kullum ne saita kira babanta a waya hakan ba karamin kwantar masa da hankalinsa ya ke yi ba, kuma duk in ya kira sai yayi mata nasihar daya saba yi mata, haka aunty laura ma suna yawan yin waya da ita, wasu lokuttan da dama tana son ta kira Yaya shureim amma idan ta tuna bai ta6a nemanta ba sai ta fasa saboda bata son ta zubda ajinta


Sai dai taji labarinsa awurin Benazir idan tayi waya da shi wani lokacin Benazir tana bata wayar don ta gaisa da shi hakan ba karamin dadi yakeyi mata, haka itama Aneelerh silar Benazir ta san Yaya shureim har suka saba da shi, itama Aneelerh duk in zatayi waya da mami da Abie sai ta hadasu da aminnanta donsu gaisa ta haka suka ?arfafa zumuncin su.

har whatsapp group suka buWe na sada zumunci da family dinsu harta baba Imam saida Aisha ta sanya shi aciki, Aneelerh ta saka abie da mami, itama Benazir ta sanya Alhaji ubaid da hajiya layla tare da dr shureim Wani irin zumunci mai karfi ne ya shiga tsakanin family din su duk time da suka hadu online fira suke sha ba kadan ba, har hotunansu suke tuttura masu.

Duk idan suka samu hutun School Nigeria suke dawowa tun a airport family dinsu zasu harhadu domin tarbarsu har party Uncle musa Yake hada masu, idan hutu ya kare zasu koma germany har kuka sukeyi saboda basu son rabuwa da family din su.

Akwana a tashi ba wuya gurin Allah, Cikin sa'a suka kammala degree dinsu, duk da Benazir da Ummi sun riga Aneelerh kammalawa saboda ita nata course din almost 6 years ne medicine and surgery su kuma Business Administration ne shekaru uku ne, Amma saboda shakuwar da tayi da su yasa ta matsa lamba akan zata ajiye karatun saboda bata jin zata iya cigaba da zama a germany batare da su ba, tasan in suka gama tafiya zasuyi su barta, suma sun damu da hakan, a wani zuwa da Uncle musa yayi gidansu, Benazir ta same shi da maganar Aneeleerh, Sai cewa ya yi karsu damu, zai sa arage mata shekarun karatun ta ya koma daidai da nasu, sunyi matukar yin mamakin hakan, aikuwa sai gashi Ya yi mata hanyar da zasu kammala a shekara daya da ita, Amma duk da haka In ta dawo Nigeria sai ta kara karatu akan wanda tayi.

Uncle musa yayi masu halaccin da bazasu taba mantawa da shi ba, Kyautatawarshi agare su bata misaltuwa, da Ayshah tana kokwanton dukiyar shi ganin yadda yake masu barin kudi kamar baisan wahalar nemansu ba, Benazir ce tayi brainwashing dinta, ta fayyace mata cewa kudinsa na Halal ne, babban Dan kasuwane kamar dai mahaifinta Alhaji Ubaid.


ranar da zasu yi graduation celebration (bikin yaye dalibar) wanda shuwagabannin jami'ar ne suke daukar nauyin yin shi a cikin makarantar, gaba daya family din kowan nan su saida Ya hallara hatta sheikh Imam saida Yaje masu aiko Aisha tayi murnar ganin baba Imam, Ranar sunyi farin cikin da basu ta6a yin makamancinsa ba saboda Yadda yan uwa da abokan arziki suka dinga basu kyaututtuka da yi masu fatan Alkhairi arayuwa, aranar ne sukayi hotuna sosai, abunda yafi basu sha'awa Yadda Family dinsu suka hada kai kamar yan uwan juna, musamman Aisha tayi murna da ganin yadda ya yadda Shikeh Imam ya yarda da Abie din Aneelerh sun zama abokai, haka iyayen su mata sun hada kai sai zumunci suke sadawa a tsakanin su.

(Bayan dawowarsu Nigeria, da sati biyu kacal)



A yammacin wata rana Sheikh Imam Yana zaune akan Sofa dake a cikin katafaren Sitting room din gidansa, yana tsaka da karanta Jarida, daya daga Cikin security Officer na gidansa yayi masa sallama bayan ya amsa Ya isar da sakon Ana sallama da shi, bai motsa daga Inda yake ba ya tambaye sa wanene ke nemansa? Officer din yace Kanin makwabcin su ne Alhaji Musa, Shiru ya danyi jim aransa yana mai mamakin karfin Halin Alhaji musa da har ya iya takowa yazo gidansa neman shi, daga bisani yace ma Officer din ya shigo da shi.


sallamar Alhaji musa ce ta katse zancen zucin nashi, dakyar ya sakar mashi fuska suka gaisa har ya taya shi murnar kammala karatun su Aisha, bayan sun yi shiru na dan lokaci kowa da abunda yake sakawa aranshi, daga bisani Alhaji musa yai gyaran murya ya ce"dama nazo ne don in nemi alfarma agurinka" bai jira jin ta bakin sheikh imam ba ya cigaba da cewa"Ina son ka bani auren Aisha, saboda ta kwanta min araina"

wani kallo shiekh Imam ya watsa masa mai kama da harara.

Tashin farko Yace"sai yau na tabbatar da baka da Hankali Musa, kai baka ji kunyar tunkarata ido da ido ka fadamin wannan maganar ba? an gaya maka ni mahaukacine da zan dauki ?ata mai daraja in hada ta da fasi?in mutun, irin ka"?

Maganar imam Ta sosa zuciyar Alhaji musa amma dayake shike nema agurinsa sai ya shanye bacin ransa, yace"bai kamata ka gaya min maganganun nan ba, wanda yace yana son naka ai masoyinka ne, saboda nasan mutuncinta shiyasa na tako nazo da kaina don in nemi aurenta agurin ka..."

murmushin takaici Sheikh Imam yayi"Haba Musa, ko kayi zaton namanta wanene kai"? Ya fada tare da mi?ewa daga kan kujerar da yake ya juya ya nufi bookshelves din dakin mai Wauke da kundin dokoki dana tarihi, da sauransu.

A cikin kundaddakin Ya curo Criminal record Na Alhaji Musa, Ya wurga masa akan kirjinsa, Kafin Ya dafe table din gabansa da tafukansa Ya soma magana Yana kallon Cikin idanunsa..

"Mara Kunya fitsararre, Sau nawa Muna yanke maka hukunci a kotu akan mugayen laifukan ka, amma da zarar kaje prison sai dai muji labarin ka fita, saboda kasan me ka taka kana da manyan mutanen da suke daure maka gindi, sune suke sama maka mafaka a kasar waje, shiyasa kake sheke ayarka" ya faWa yana kallon Cikin idanun shi.

"Tayaya har kake tunanin Ni Imam malik zan iya baka auren yata aisha bayan nasan Halinka ciki da bai? Musa kaine Dealer mai fataucin miyagun kwayoyi a kasar nan, kai ne Cin zarafin mata masu rauni gurin tilasta masu don suyi karuwanci a kasashen waje, baka gajiya da keta haddin mata, last shari'ar da nayi akanka, yara masu talla kayi ma fyade sannan ka binne su da ransu don kada asirinka Ya tonu, cikin rashin sa'a aka samu wani bawan Allah dayaga lokacin da kake aikatan hakan harya kaika kara police station bayan sun gama bincike akanka suka mika ka kotu abun takaici bayan mun yanke maka hukuncin daya dace dakai mun tura ka prison sai dai muka ji labarin babu kai a kurkuku harma Ka gudu ka koma America da zama, saboda bakin zalincin ku, kai da ubayen gidan ka kuna amfani da haramtacciyar dukiyar da ku ka tara gurin toshe bakin shaidu da bawa jami'ae cin hanci...." Ya karashen maganar yana huci tamkar zai doke sa.


Alhaji Musa ya sunkuyar da kansa kasa, ya dunkule yatsunsa, ransa ya baci matuka da jin maganganun da Sheikh Imam ke gaya masa saboda kawai ya nemi auren yarsa.

"ka yi ha?uri ka nemi wata, amma sam ba ka cancanci ka mallaki aisha ba, nafi sha'awar ta auri mutun mai tsantsar ilmin addini musulunci, mai jin tsoron Allah, mai kuma kyawawan halaye da dabi'u wanda zai ruke min ita amana, Wallahi idan har na aura ma Aisha kai banyi mata adalci ba, Allah ma bazai barni ba saboda ita din amana ce agare ni"!

yanayin fuskar Alhaji musane Ya canza ganin wahalar shi na niyar ta tashi abanza.


Cikin kankai dakai yace"kada kayi min haka, wallahi inason Aisha itace mace ta farko da nayi burin in mallaka don mu raya sunnah, idan har don saboda halayena ne, nayi maka alkawarin zan shiryu in har zaka bani aur??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????en ta"

cike da takaici Sheikh imam Yace"Oh har saina baka aurenta zaka shiryu! Ba zaka shiru don Tsoron mahaliccinka ba"?

"Naji zan shiru saboda Allah, Kawai ni ka amince min in aure ta, komi ka ke so zan baka ina da tarin dukiya wanda zai ishemu muyi rayuwar mu" Da gadara yakeyi masa magana,

Dariya sheikh imam yayi"Musa kenan, Kai abun duniya ya dama, ni dukiya bata agaba na, ban damu da kyalekyalen duniyar nan ba, wanda wata rana zaka mutu kabarsu ne, daga kai sai halinka za'a binne ka, sannan ka duba kaga gidan da nake rayuwa cikin rufin asirin Allah, babu abunda na nema na rasa don haka kadaina yi min bagu da dukiyar daka tara ta hanyar Haram.."! hankalinsa ba karamin tashi yayi ba, abunka ga mutumin da bai ta6a neman abu ya rasa ba, babban takaicin shi yadda ya aje girman kansa da komai yazo don ya nemi auren ta amma Sheikh imam Ya watsa mashi kasa a ido.

"Amma ai ka bari ita yar taka ta furta bata sona ko"? Ya fada tare da Wage masa gira...

Shiekh Imam Yace"Wallahi koda Aisha tana sonka ba zata aure ka ba! Balle ma nasan Jinina bazai ta6a kaunar fasiki irin ka ba, in sha Allah kaida Aisha sai dai hange daga nesa amma aure har abada, nayi fatan ma ace shureim ne yazo min da maganar auren ta, wallahi jiki na 6ari zan aura mata shi, saboda Ya cika duk wasu sharuddan da zan Iya mallaka masa Aisha..."

cikin rauni na murya Uncle musa yace"da me shureim yafi ni? wasu sharuddane ya cika wanda ni ban cika su ba"

Sheikh Imam Yace"ko ban fada maka ba, kai ka sani, shureim hafizi ne mai dumbin tarin ilmin addini, mutum mai tsoron Allah, mai koyi da sunnar manzon Allah SAW, ba kamar kai ba, daka sa duniya agaba...." wani irin zafin kishine Ya rufe idon Uncle musa, Yaji zafin maganar Shiekh Imam Ko sallama bai yi mashi ba Ya mike azafafe Ya fuce daga sitting room din.

Bayan Uncle musa Ya koma gidan yayansa damuwa ta hana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login