Showing 243001 words to 246000 words out of 321579 words

Chapter 82 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

tayaya ma zan iya fada masu? Abun da kunya kuma ba zasu dauki maganata serious ba, zasu ce bani da hankali ne"

Jinjina kai Batool tayi"kin faWi gaskiya Ukhty, to ko in fadama daddyna" wani kallo mai kama da harara Unaisah tayi mata, Batool ta kwashe da dariya..

"In haka ne nima inje in faWawa daddyna mana ..' dariya su ka yi..

"Kinsan wani abu, pls mu cigaba da addu'a, babu abunda ya gagari ubangijinmu, in sha Allah zai yaye maki damuwarki, ni yanzu burina ki maida hankali akan shirye shiryen dake tunkaro mu, daga yau hutu ya kare mana, babu zama har sai mun mika ki dakin mijinki..."

yamutsa fuska tayi"dama ni ai ba hutu gare ni ba, gaba dayana a takure nake, tun da aka sanya bikin nan bani da hutu, wlh har nagaji da zuwa beauty spa din nan, kamar wata yar sarki zatayi aure, gaba daya an sauya min jikina da gyara"

dariya Batool tayi"sis tsakaninki da Allah baki ji dadin yadda kika koma ba? Fatarki tayi smooth babu ?warzane ko tabo kamar ka taba jini ya digo, ga gashinki ya ciza launin shi yayi laushi sai kamshin ya ke yi, ?in ?ara kyau sosai, masha Allah kamar hurul aini..." ta6e baki Unaisah tayi aranta taji dadin yabon kyanta da Batool ta yi.

"Kema kin sauya sis, gyaran jikin nan ya kar6eki wlh, kamar kece amaryar ma" murmushi batool tayi"Albarkacinki nake ci Unaisah, shiyasa nima nake samu ana zuwa dani spa din, naso ace tare zamuyi aure arana daya, amma Allah bai nu??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????fa ba, daddy yace saina kammala karatu ko zai barni in kula masu zuwa neman aurena"



"Nima nayi fatan haka batool, amma karki damu, kema in sha Allah zakiyi aure nan bada jimawa ba"


"Na cika ki da surutu mrs owais, ki kwanta ki huta, Yau henne night ne, har nakosa time yayi wlh..."


Ta faWa tare da lullu6e mata jikin ta da bargo

"Nan da wasu yan kwanaki a gadon mijin ki zaki dinga kwanciya" harara Unaisah tayi mata tana murmushi..

Tana jiyo motsin fitar Batool daga dakin sama sama kafin bacci mai daWi ya yi awon gaba da ita..


Wuraren ?arfe 4 da rabi, Yan matan Amarya suka fara taruwa cikin gidan, idan kuka ji na ambaci yan matan amarya kunsan wa nake nufi, Abokananta na amana wato ex-prisoners.


Ringing din wayarta ne ya farkar da ita, slowly ta buWe idanunta da suka kada jawur, tayi shiru tana kallon ceilling.

Har kiran ya katse batayi picking ba, wani kiran ne ya kara shigowa da sauri ta Wauko wayar daga kan drawer ta yi picking tare da karawa a kunnanta.


"Na kira ki ne, don na tuna maki saura kwanaki kaWan ki zama matata"


murmushi tayi"I can't wait to own you my man"

Sautin kayataccen murmushinsa tajiyo mai haWe da fitar numfashin sa.


"I saw your graduation pictures on social media, and people were commenting on them, I felt indescribable jealousy why did you share your photos? why babe? Ba nace banda pics ba.."

yamutsa fuska tayi kamar tana a gaban shi"Am sorry, kasan ba yadda za'ai in hana photographers Waukar hoto na banma san sunyi ba, kuma wallahi bani nayi sharing din su ba, friends dina ne, amma zan kiyaye nan gaba"


"Okay, karki damu, na fahimce ki"

Yana kokarin katse kiran tayi saurin furta"am na manta ban fada maka ba, Yau Henna night ne, wani kalar lalle kake so inyi"?


"Unaisah, check your WhatsApp I'll send you a message, take care"

"Okay ka kulamin da kanka" daga haka su kayi sallama.


Saukowa tayi daga kan gadon ta nufi toilet ta shige don tayi wanka.


Bayan mintuna, ta fito Jikinta sanye da bathrobe fara,
Closet ta nufa don ta shirya kanta, jim kadan ta fito jikinta sanye da kimono Robe.

Wayarta ta dauko ta shiga whatsapp chat dinsu don taga idan ya tura mata sakon


Murmushine ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta sa'ilin da idanunta suka sauka akan screen din wayar tana karanta message din shi.


_I prefer maroon henna, zaifi dacewa da soft skin din hannun ki, When the henna is done, send me pictures so I can see"


Batasan ya akai ta ke jin dadi a duk lokacin data ga sakon shi ta whatsapp.

Reply ta yi masa "Okay Sir"

~______________________________~



Unexpected ta tsinkayi muryoyin su daga waje


"Our bride-to-be! Sis! Mrs Owais! Unaisah! Where are you? It's time for the henna! Masu lallen sun zo, we're waiting for you"


Kafin ta yi wani yunkuri suka turo kofar Wakin nata, Ko sallama babu, zare eyes dinta tayi da mamakin ganinsu ta shiga furta sunayen su"Hibba! Hawwa! Rubina! Hannah! Saukar Yaushe? Shine baku kira kun fadamin za ku zo ba"? Ta faWa tare da nufar su ta soma yin hugging din su.

"Muna sane muka ki sanar dake saboda mu baki mamaki" hanna ce ta fada tana dariya.

Hawwa tace"tun bayan sallar La'asar, muka iso, a gidan daddyn mu mu ka sauka.."


"Amma dai kun shammace ni wlh, naji dadin ganin ku mutan kaduna da lagos, da har na fidda rai da zuwanku"!


HaWa baki su ka yi gurin furta

"mun yi missing na ki, muna tayaki murnar kammala karatu, ay mana afwa bamu halarta ba, mun zo a makare, fatan mun same ki lafiya"?


"Nima nayi missing naku, wlh karkuji komai zuwan da ku ka yi ya fanshe laifin ku.. "


ta fada tana kallon su, kowaccensu hutu ya zauna mata, sun ?ara girma sun zama cikakkun yan mata, suturun jikinsu masu tsada.


"Ya gajiyar tafiya? Ya kuma kuka baro mutanan gidan" har suna hada baki gurin furta"suna nan lafiyalou, sunce mu gaishe masu da amaryar su"

"Wow Sis kinga yadda kika canza? Kinyi haske kin kara kyau, fatar ki sai ?yalli take..."


rubina ce ta fada tana taba skin dinta" buge hannunta Unaisah tayi tana dariya.


Hibba Tace"wallahi nima abun da zance kenan, kin zama babbar mace, tubarkalla anya Unaisah baki shan maganin ?ara hips da breast" zare mata idanu Unaisah tayi, gaba daya suka tuntsire da dariya..

Kamar daga sama suka tsinkayi muryar Batool daga bayan su..

"?an sa ido, Tubarkalla, komai na sis dina natural ne daga Allah, dama zuwa kukayi don ku sanya mata ido ko" ta fada da zolaya yayin da take karasa shigowa cikin dakin.

Dariya suka sanya gaba dayansu..


"Ba zuwa nayi don muyi fira ba, nazo ne don in fada maku ku fito mu sauka down lokacin ?unshi yayi"


ta ?arashe maganar tare da ruko hannun Unaisah a cikin nata su ka yi gaba sauran suka bi bayan su.

Tunkan su ?arasa saukowa down, suka hango sauran bridemaids din da ke shigowa.

Parveen ce agaba ta dauki wankan abaya, idanunta sanye da shade baki, Yadda kasan hajiya saratu na tafiya, Cikin dattako take taku WaiWai tana hura hanci, ta ruke hand bag a hannunta na hagu, Wayan hannun ta ru?e Cupcake din da take ci.

Sai shan ?amshi ta ke yi kamar iska nayi mata wari, tana ji da kanta Wiyar minister.

"Wa nake gani kamar foodie? Dagaske ke ce"? Hawwa ce ta faWa.

Muryar ta da taji ne yasa ta kai dubanta garesu tana ganin su ta washe baki tare da Waga masu hannu ta nufe su, bakomai ne ya basu dariya ba face ganin gefe da gefen bakinta da yayi dama dama da cake din da take ci.

Tana karasawa gurinsu suka soma rungumarta.

"Ni babu wanda zai rungume ni? Ko baku ganni bane"?


A tare suka dago tare da duban ?ofar shigowa falo, waro idanu waje su ka yi ganin Jemimah a tsaye ta ru?e qugunta, sanye take da lace ta coge daurin kallabi, Yarinya fa ta girma a yanzu takai kusan shekara goma sha biyar.

Su biyu ne su ka zo, tana a tare da yayarta Azeeza da ke tsaye a bayanta, itama ta ?ara girma duk da har yanzu babu tsawo sai dai tana da dirin jiki, ayanzu ta wuce shekara ashirin da Wauriya.


"Jemimah? Wa ya gayyace ki? Ba mun ce bamu san ganin Yara ba? Ko akwai tsaranki anan ne.."?

da zolaya Parveen tayi maganar tare da nuna mata hanyar fita"Get Out"!


harara Jemimah ta watsa mata"ki bari idan bikin ki yazo sai ki hanani zuwa, kuma ai Sis Unaisah ne ta gayyace ni, ba ke ba"


"Gaskiya jemimah ki nemi tsararrakin ki, tayaya zaki zo cikin mu, akwai tsaranki ne"?

?yal?yacewa su ka yi da dariya..
Zura hannu tayi cikin purse dinta suka kura ido suna jira suga dame ta zo masu.

Pistol ta zaro, ta saita su da ita.

Gaba daya suka razana tare da du?ewa ?asa suna rokonta karta harbesu, kwashewa tayi da dariya.

Bushewa da dariya Azeeza tayi tare da girgiza kai tace


"bafa bindigar gaske bace, ta wasan yaran ce.."


ajiyar zuciya suka sauke tare da mikewa tsaye gaba daya sunyi zaton bindigar gaske ce, saboda sunsan zata iya dauko ta daddyn ta..

"Duk wanda ya kara gigin kora ni, sai na fasa kan shi da bindigar nan" ta fada tana nuna kawunan su da bindigar, daga ka ganta kaga sangartacciya dabi'un ta irin na yara, tuntsirewa su ka yi da dariya..

Batool tace"Like father Like daughter, Jemimah wannan bindigar ta wacece kika dauko ko ta daddy mubarak ce"?

Azeeza tace"shiya siya mata hada kakin sojoji, saboda ta faWa mashi idan ta gama karatu soja zata zama irin shi, don ta dinga zuwa ya?i"

?yal?yalewa su ka yi da dariya cikin nishaWi.

Kafin suka fara huggin dinsu irin gaisuwar da suka saba yiwa junansu duk idan suka hadu..

"Assalamu alaikum, me ake tattaunawa ne ba a jira na karaso ba... " gaba daya suka jiyo tare da kallon su, kusan a tare suka shigo, Deeja ce tayi maganar, shigowarta kenan jikinta sanye da atampa, ta kashe daurin dankwalin ture kaga tsira, ga wani hadadden shade da tasaka ma idanun ta.


A kafaWa ta yafa veil din ta hannunta ruke da wayarta..
Cike da farin ciki suka hada baki gurin furta"DEEJA!"


"Na'am ?an amanana! Am sorry amaryar mu, banzo da wuri ba, yau natashi ba lafiya amma da sau?i yanzu Alhamdulillah".


ta faWa tana nufar su, daya bayan daya ta yi hugging din su tare da manna masu peck a foreheads in su, duk su ka yi mata ya jiki? ta amsa da sau?i.

Badajimawa ba, Sajeeda da Zeenatu suka shigo tare da Sarah da yasmin da sauran kawayensu wadanda gaba dayansu Ex-prisoners ne gaba dayansu sun daukin wanka na mutunci, sun kai su Ashirin bayan sun gama gaggaisawa da junan su nan fa wata sabuwar firar ta 6arke a tsakanin su, haniyar firar da su ke yi ta cika Gidan gaba Wa ya, bakajin komai sai sautin surutun su da dariyar su.


?arfe biyar daidai masu ?unshi su ka ?araso gidan.


A main Falo suka baje kolin su, sai da suka fara ?awata seating area din falon da kayan decoration din su, daga daidai inda zasuyi zaman ?unshin suka shimfiWa Red Rug (jan kilishi) daga kewayen shi floor sofa set ne daga saman kilishin wasu WunWuma WunWuman floor cushions ne a jere, kamar shimfiWar sarki, daga tsakiyar rug din farantai ne Wauke da kayayyakin ?unshi.


Kafin su fara Aunty Danejo ta kawo masu soft drinks da snacks a cikin tray, sunji dadi har su ka yi mata godiya.


Music Win da su ka kunna a speakers ya karaWe ko'ina na gidan, hakan ba karamin armashi ya karawa daren na su ba.

Daga tsakiya Amarya ta zauna kan cushion.

Bridemaids suka zazzauna gefe da gafen ta, Batool tana a hannun damanta kamar yadda suka saba kasancewa, yayin da Hennah artists din su ka zauna akan floor Sofas, batare da bata lokaci ba suka fara harhada kayayyakin lallen kafin daga bisani suka fara yiwa yan matan amarya ?unshi.

Gaba Waya Jira suke wadda zatayiwa Amarya ?unshi ta ?araso saboda ta ce ?unshin ta kaWai ta ke so.

Bridemaids cikin nishadi da annashuwa suke, ana masu kunshi suna bin wakar da aka kunna ma su...

Wadanda ba'a farawa kunshin ba, suka mi?e tare da jan layi suka fara taka rawar tambola..

Jemimah da Parveen sun za?e sai tikar rawa su ke yi har haWa qugunsu su ke yi.


"Da girman kujerar ki Yar ministern Lafiya, Takawarki lafiya toron giwa, Hajiya Parveen, rai ba buri saina abinci, an gaishe ki ?aramar su babbarsu Naja'at bi ni ka lalace"

har sun fara washe baki jin kirarin da Unaisah keyi masu amma da sukaji sharrin da tayi masu sai suka haWe rai suna zumbura baki.

Gaba Waya suka sanya dariya hada ma su yi masu ?unshin sai da su ka dara..


*HAJJATY

Gaba daya ta shiga damuwa ganin Lokaci na nema Ya kure mata, sai sauri ta ke yi ta kammala Girkin da ta ke yi, tasan in har ba zuwa tayi ba, Unaisah ba zata bari wani yayi mata kunshi ba, duba da yadda ta kwalla fa rai akan son tayi mata kunshi tun da ta ta6a ganin zanen kunshinta a hannunta ta rude da kyawun shi.

wannan ne karo na farko da zata farayi mata kunshi bataso taji ba dadi, shiyasa take ta sauri ta gama girkin ko ta samu ta shirya ta tafi.

Tana atsaye gaban Gass Cooker ta bude soup pot tana jujjuya miya da spoon din hannun ta.

Kwatsam taji an fusge spoon din hannun ta, aikuwa a razane ta saki murfin tukunyar, tayi saurin juyawa don ganin wanene


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da idanunta suka shiga cikin na shi..

Cikin rawar murya ta furta"um..yay.. Yaya mubarak, am sorry, bansan ko kayi min sallama ban ji ba"

Murmushi yayi yana jin dadin rudewar da takeyi idan ta gan shi, ba karamin kyau takeyi mashi ba idan tana magana a tsorace.

"No karki damu banyi sallama ba, ni yakamata na baki hakuri na tsorata ki" murmushi ta Wanyi sam hankalin ta ba akwance ya ke ba

Mika mata spoon din yayi tasa hannu ta kar6a.

Wani kallon so da ?auna suke jefawa junan su, duk tabi tasha jinin jikin ta, zallumine ya cike ta, tana jin tsoron Turai ta gansu a tare cikin kitchen, tasan zataji kishi.

"Kin bar babynki da yunwa, Baki bashi abinci ba" ya faWa yana shafa cikin shi..


Cikin rawar murya tace"am.. Sorry yayana, na kusa kammala girkin, ka koma dining ka jira ni yanzun nan zan kawo maka.. " ta fadi hakanne don ta samu ta lalla6a shi ya fita..

Allah mai jujjuya al'amurra, bata taba zaton zata so wani Wa namiji bayan Praveen ba, ada ji take babu wanda zai iya maye mata gurbin dan uwanta Praveen amma a yanzu da babu shi, Sir Mubarak Ya sace zuciyarta da soyayyar shi, kulawar shi, komai ma..

"Kora ta ki ke yi ko"? Girgiza mashi kai tayi a'a wallahi..

Murmushi yayi "nasan me kike jima tsoro, to meye na damuwa a ciki? Ta riga da tasan ina sonki, da amincewarta ko kin manta cewa itace ta fara bani shawarar in nemi soyayyarki saboda tana son ku rayu a karkashin inuwa Waya.. "

Kamar zata sanya kuka tace"na sani ni ba wannan bane damuwana, kasan dai babu kyau mace da namiji su ke6e ko"?

Har ya buWe baki zai yi magana Unexpected muryar Naufal ta katse su.


"Daddy! dama kana a kitchen?



Da sauri Sir Mubarak ya ja da baya tare da shan mur yace


"Tambai, kai zan tambaya yaushe ka dawo gidan"?


?umshe dariya Hajjaty ta yi tare da juyawa ta cigaba da duba girkin ta.

yamutsa fuska yayi aransa ya furta"hmm a sannu zan gano menene a tsakanin ka da mommyna, kai ta daure min fuska kana shan mur"

"Tun Wazu na dawo.."

ya fada tare da nufar mommynsa data basu baya.

"Mommy, Unaisah ta kira ni awaya tace tana ta kiran ki bakya picking, ke suke jira kije ki mata ?un shi"

Cike da jin kunyar shi ta furta"na manta wayar a daki, pls, Idan sun sake kira ka fada masu aikine ya rukeni, amma dana gama zan taho.."

amsawa yayi da toh, ya juya zai fita ya Wan juyo ya saci kallon Sir mubarak karaf idanunsu suka shiga cikin na juna.

?age mashi gira yayi"Wan sa ido kwanan nan zan sake aske maka sumar kanka"


?asa ?asa da murya yayi maganar don kada taji su.


Cike da jin kunyar shi Naufal yayi saurin fucewa daga kitchen din cike da fargaban kada ya aske mashi sumar kanshi daya tara kamar mace.


Girgiza kai sir mubarak yayi..
Yana son Yaron sosai kamar yadda ya ke son Jazz ba ka ta6a gane ba ?a'?ansa ba ne.


fuskarsa da murmushi ya dubu Hajjaty.

"Ki aje girkin ki tafi zanyiwa yar uwarki magana tazo ta karasa, kin sa masu rai, Jira bashi da dadi"

Girgiza kai tayi"no, pls, kada kayi mata magana, zanyi kokari in gama"

"tun da baki so in kira ta, to ni ki bari in karasa maki girkin"

zare idanu tayi da mamakin maganarsa tace "ya mubarak, da kanka.." girgiza kai tayi"ban yarda ba, bazan bari kayi girki ba, bayan kana da masu girka maka"

Sallamar Turai ce ta katse firar su, AruWe hajjaty taja baki tayi shiru,

gaba daya idanun su akan ta.

Fuskarta Wauke da murmushi tace"love birds, zan iya sanin me kuke zantawa ne"?

Murmushi su ka yi
Sir mubarak yace"kin hana in ajiye masu aiki a gidana, gayanan yar uwarki aiki yayi mata yawa, ga gidan biki sunata jiranta zatayiwa amarya ?un shi..."

6ata fuska Turai tayi"banji dadi ba, meyasa baki faWa min ba? Kin bar bayin Allah sunata jiranki"

"Banaso na takura maki ne, kuma nama kusa karasawa.."

bata ?are maganar ba, Turai ta katse ta"bana son jin wani abu, pls, kije ki shirya ki tafi in ba so kike raina ya 6aci ba" har cikin ranta taji dadi"nagode sosai"
Ta fada tare da kama hanya ta fuce.

Kallon Sir mubarak tayi"pls, yakamata kana dan jurewa, ka san inda zaka dinga tunkarar hajjaty, yaron nan har yanzu wani kallo ya ke maka..." dariya su kayi.

"In sha Allah zan gyara uwargidana, ina fata ban 6ata baki rai ba.."

Harararsa tayi"kishi nake ji, idan naganka da hajjaty..." ta fada da zolaya.

"Amma kasan wani abu, silar zuwanta cikin rayuwar mu abubuwa da dama sun sauya, Hajjaty tana da kirki bata gajiya da kyautatawa ya'yana, kamar ita ta haife su tana son su, bata gajiya dayi masu kunshi da kitso da kwalliya, saida nace ta bari bana so tana wahala amma ta nuna rashin jin dadin ta.."

tun da tafara yin magana murmushi ne akan fuskar sir mubarak, yana jin dadin yadda Turai ke yabon ta.

"Babe, bana jin zan iya kishi da hajjaty, duk da nasan dole inji ba daWi amma Kuma idan na tuna, Nina


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login