Showing 120001 words to 123000 words out of 321579 words

Chapter 41 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

Kin bata mun raina, meyasa zaki bar abu yana cinki a zuciya baki sanar dani ba? Kin ?ullace ni aranki, ba halinki bane Batool, kamar yadda kike burin ki fi kowa kusanci da ni nima haka nake buri Batool, inasonki fiye da sauran yan uwan mu, saboda halaccin da kikayi min arayuwa bazan ta6a mantawa ba, dan Allah ki buWe mun kofa, inason yin magana dake, zan fada maki abun da kikeson ji sannan ki daina kuka bana jin dadi."

ta faWa cikin shesshekar Kuka, Kamar marasa galihu sun dage sai kuka su ke yi.

"Ba zaki fito ba? Kuma ki daina kuka acikin toilet babu kyau"

"Ki ?yaleni, bazan fito ba, saboda kona fito babu amfanin da zanyi maki" bubbuga kofar Tayi kamar zata balle ta tace"ki daina wannan maganar Batool bana son ji"!

"Naje nayi ay gaskiya na fada.." ji take kamar ba Batool dinta ba, ta burkice mata lokaci Waya..

"Ki yi mun ko wani irin hukunci zakiyi min in har hakan zaisa ki huce, Ko ki fada min me zanyi in gyara kuskure na"? Ta fada tare da jogana kunnanta jikin kofar..

Sai da ta mula ta sha iska tukunna tace"kin makaro Unaisah, sai da na fada sannan zaki gyara? Hmmm, kawai ki rabu da ni, ko ganinki bana son yi"

"Bazan iya rabuwa dake ba, bana jin dadin maganarki, Batool jinki nake kamar twin sister dina.."

"DaWin bakin ki bazaisa in hakura ba" murmushi Unaisah tayi still da hawaye akan fuskarta"ba daWin baki nake maki ba, wallahi dagaske nake maki my heartbeat, Ki fito in nuna maki irin kaunar da nake maki"

banza tayi da ita, tunani ta shiga yi meya kamata tayi don ta shawo kanta? da sauri ta nufi wadrobe Shelves inda ta ajiye sauran kayan da suka siyo a shopping mall, Batool ta dade tana kwakwar ta bata wayar nan taki bata a lokacin saboda ta raba gaddama tsakaninta da sajeed da shima ya kwallafa rai akan wayar, sai yau da take son faranta mata.

Phone box din ta ruke a hannunta ta dawo bakin toilet door din"Ukhty na, come and see something special"

banza tayi da ita, magiya ta dinga yi mata amma tayi shiru, still batayi fushi ba, saboda ta fahimci halin da yar uwar tata take a ciki, tasan Batool tana da hakuri baiwar Allah.

a lokacin Batool tana a zukunne gaban kofar toilet din ta ciki ta jingina bayanta, kunnuwanta suka jiyo mata sautin wakar da Unaisah ta ke raira mata daga cikin dakin.

_?awata kina jina? In har kika barni sai na sha wuya_

_Sai na zam tamkar tsokar da babu jijiya_

_In ba dake ba sai dai rijiya_

_Rijiyar ma mai dauke da ?ugiya_

_Wacce zata caki rai na, ban kara kwana_

_Mai zai sa in kwana? Ban gano masoyiya ba_

_Kece aljannata duniya ta_

_Masoyiya ta, aminiya ta_


yayin da take sauraron wakar batasan sa'adda murmushi ya su6uce mata ba, wani sanyi taji ya ratsa zuciyarta, kamar ana wanke mata damuwarta.


"Please idan kinji dadin wakar da nayi maki, Ki fito mu fuskanci juna, Inason na ganki, wallahi har nayi missing Winki Batool dina, pls ki fito zan baki kyauta ta musamman, da zata faranta ranki"

shiru tayi bata tanka mata ba, kamar zata saka ihu, Bubbuga kafafunta tayi"wai me kikeso nayi maki ne wanda zaisa ki yafe min"

_"Ki Wauke ni kamar yadda na Wauke ki, shi kaWai ne zai sa ni farin ciki"_

ta fada a cikin ran ta

"Ina ta maki magiya ki fito amma kin ?iya, ai ko Allah muna masa laifi ya yafe mana balle mu yan adam, Kada Allah yasa ki yafe kinji ko, Ki ta zama a cikin toilet, madaddalar shaiWanu.."

still bata tanka mata ba, yamitsa fuska tayi tare da hararar kofar toilet din, dabara ce ta fado mata, da gudu ta fuce daga dakin tana fadin"oyoyo Aunty Ummi, welcome back home, we really missed you, Muna ta jira ki dawo har munyi fushi.."

A zabure Batool ta mike jikinta na 6ari ta bude toilet door din, ta watso a guje ta nufi kofar tana lekowa taga wayam babu kowa nan take ta gane set up din Unaisah ne don ta fito, nan da nan walwalar fuskarta ta Wauke duff, kamar bata taba dariya ba, tana niyar ta fucewa daga dakin harta daga kafa Unexpected taji an dam?i wuyan kafarta, atsorace ta zare idanun ta tare da kallon ta, ajiyar zuciya ta dauke ganin Unaisah..

"Am sorry Aunty Batool, Kaina bisa wuyana, na tuba bazan ?ara ba, bansan ki da fushi ba, pls, ki tausayawa yar kanwarki Unaisah, Zan gyara kuskurena, nasan bana jin magana amma ki min uziri hada yarinta ke damuna.."

ta karasa maganar tare da kama kunnuwanta.


Batool dake kallon ta, kiris ya rage ta fashe da dariya, saboda ta bata nishadi musamman da ta kama kunnuwanta kamar zomanya, ta wani marairaice mata fuska.

"Bai kamata ki biyemin ba, kiyi fushi dani, kefa babba ce ni kuma ?anwarki, idan nayi badai dai ba, nasiha yakamata kiyi min sai in gyara bawai kiyi fushi dani ba.."

idanunta cike tab da kwalla tayi maganar, ita kanta batool din wasu hawayen ne suka cika idanunta, ta rasa gane meyasa take jin Unaisah fiye da sauran yan uwanta da ta fara sani kafin ita.


Bazata iya jure fushi da ita ba, A hankali ta cire hannu ta mi?a mata, Jikin ta har kerma yakeyi gurin Zura hannunta a cikin na Batool, ta janyo ta, ta mike tsaye suka yi hugging din juna.


Lallashin juna sukayi tare da ba juna hakurin sabanin da suka samu.


"Zan fada maki abun ki ke son ji, daga yanzu babu boye boye atsakanina da ke, sirrina naki ne.."


ta faWa yayin da suke raba jikinsu daga juna, cheeks dinsu sunyi ja saboda kukan da suka sha.


Ruko hannun Batool tayi suka zauna kan tattausan rug din dakinsu suna fuskantar juna, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin kunyar Batool, tayi mata ?warjini ko dan yau tayi gaba da gaba da ita.


Lumshe idanunta tayi a hankali

In a cool voice tace"a duk lokacin da kika ganni ina kuka, to na tuna da shi ne, wallahi shine silar halin da nake shiga! nayi iyakar ?o?arina dan ganin na daina tunaninsa sai dai nakasa, Ya mutu amma babu abun daya sauya na daga son da nake masa"!


Nan ta ke Batool ta gane wa take nufi.

"akwai wasu kalmomi daya furta min kafin su tafi kai farmaki sun tsaya min araina! da su nake kwana da su nake ta shi araina, nayi nayi in cire gur6ataccen tunaninsa da nake yi amma nakasa, zuciyata takasa mantawa da cewa shi fa yanzu mamaci ne ba rayayye ba, meyasa take tsananta min akan shi.."


wasu zafafan hawaye ne suka wanke fuskarta..


Ruko hannayenta Batool tayi a cikin nata, wani irin tausayin ta ne ya mamaye zuciyarta, tayi zaton Unaisah ta daina son shi tun da baya araye ashe har yanzu da son shi sosai a cikin zuciyarta.


shiru tayi tana tariyo kalaman daya faWa mata a cikin brain dinta, a ranar da zasu tafi kai farmaki lokacin daya yi mata raWa a cikin kunnanta..


_Unaisaah, my desire for you burns fiercely,Taking your virginity has become my utmost dream, For what feels like an eternity, I've been tormented by my longing for you, I've concealed it for your sake, but my craving for you only intensifies_

_I'm patient, Unaisah, not wanting to rush or harm you, I yearn to make love to you with your trust, your consent, I don't mean to pressure you, I simply can't wait to be with you_

_When I return, grant me my heart's desire, Unaisah. Fulfill my wish, And let's create a memory that will last a lifetime_


kifa kanta tayi saman kafaWar Batool, cikin karyayyar murya ta furta"a lokacin daya furta mun kalaman nan, duk da bakomai na fahimta ba, amma naji wani bakon abu da ban ta6a jin shi ba a tare da ni..."

ta fada tana jan numfashi, gaba daya tausayinta ya kama Batool


_"Daga baya, na zauna nayita yin nazari akan kalamansa, na yi bincike ta hanyar wayana akan abun da ban fahimta ba, har saida na gano komai dayake nufi, i was shocked, Danish da baisan komai ba, tayaya ya samu ilmi kan abun da ni bansani ba, ko Aunty ummi bakomai take fayyace mana ba, saboda tana jin kunyar mu.


shafa bayanta Batool tayi da tafin ta"mutuwa tayi min yankan kauna, naso ace na cika mashi burin shi akaina, sai dai Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, ina daurewa ne idan kewarshi ta addabe ni, bana bari kowa ya sani, saboda abu biyu, bana so na fama ciwon Zuciyata saboda inason na rayu ko dan na ga ?arshen Elders, sannan bana so in Waga hankalin ku, gaba daya na hana kaina kallon hotunansa da vidoes din da nayi masa wasu ma batare da sanin shi ba, saboda yanayin da nake shiga idan ina kallon su, da ace idan na bishi zamu rayu a kabari daya ne da ba abun da zai hana in roki Allah ya dauki raina nima, amma bana fatan hakan saboda a duk lokacin da na farka yin nafilfili nayi masa addu'a inajin wani dadi a cikin zuciyata"_


Lallashinta Batool ta cigaba da yi gwanin ban tausayi, a yanzu ta fahimci wasu abubuwan tanayi ne saboda ta kawar da damuwar rashin Danish.



"Yanzu da na faWa maki sirrina sai naji kamar an yaye min damuwana, musamman da kika kwantar min da hankali, pls amana ne atsakanin mu, daga ni sai ke, kema idan akwai abunda ke damunki ki fada min.."


murmushi suka sakar ma Juna.


"Kada ki damu, zan fada maki nima, amma ayanzu bani da wani sirri daya wuce in taimaka maki gurin ganin mun shawo kan matsalar da ke damun ki" ta fada tana shafa sumar kan ta.


sun jima suna tattaunawa, fira tayi dadi, har saida cook yayi knocking Ya sanar da su su fito su ci lunch din su tukunna suka tsagaita.

Phone box din ta dauko ta mika ma Batool, Wani uban tsallan farin ciki ta daka, hada yin sujudusshukr saboda dadin da taji, hakan ba karamin nishadi ya ba Unaisah ba, ganin ta sanyata farin ciki.

"Ki yi hakuri tuntuni Yakamata in baki ita, sai dai banyi hakan ba saboda Sajeed ya nuna yanaso yanzu da baya nan gayanan na baki, kiyi ma daddy magana ya siya maki sim"

tana faman washe baki tace thank you sis, you're special, kin faranta min rai

atare suka buWe kwalin wayar, sabuwa gal da ita ?irar Samsung galaxy,

"Nasan yau dakyar zaki Iya runtsawa" tana dariya tace "kamar kin sani"

"Kije ki sanya kaya, zan jira ki"

Ta fada tare da ruke mata wayar, da sauri ta nufi closet dinsu, shaf shaf ta zura gown a jikinta, ta dawo.

"muje muyi lunch daga nan sai mu kira yan uwan mu mu gaisa da su ko"


"Yeah" da farin ciki suka fito daga dakin.

A dining room suka taras da Cooks dake jera masu kayan lunch din su, bayan sun zauna kan kujera suna fuskantar Juna, a tsanake suka soma cin abincin su.

"Har yanzu shiru, aunty Ummi bata dawo ba, gidan duk ba dadi, babu Aunty Ummi, Chief tun safe bai dawo ba, daddy ma ya fita anguwa, sai mu kadai, nayi kewar su" Batool ce ta fada yayin da take tura Steak kebab abakinta tana taunawa.

"Idan muka kammala Cin abincin zan sake jaraba kiran su, Inji yaushe zasu dawo gida"

Unaisah ce ta faWa tana tsoma hannunta cikin plate din gabanta dake a shake da farfesun ganda mai zafi da tafshi, daukowa tayi tare da turawa abaki tana taunar gandar.

"Kwanakin baya kin yi min alkwarin zaki bani labarin aunty Ummi, har yanzu ban manta ba, Inaso naji..."


dakatawa tayi da sharbar farfesun ta danyi shiru tana yanke shawara da zuciyarta, Chief ya hana ta fada amma kafin ya gargaWeta akan kada ta faWa ta riga tayi wa Batool al?awarin zata bata labari, kuma tasan in har bata fada mata ba, zataji ba dadi.

Dagowa tayi suka hada ido cikin na juna, ta kura mata idanun ta..

"Ki bari mu gama cin abincin mana"

Girgiza kai tayi"haka kullin kike kawo uzirin da zaisa ki manta, kawai ki fada min a yanzu.."

Saboda gudun 6acin ranta yasa tace "Okay, zan fada maki amma pls, amana, daga ni sai ke my sis" murmushi Batool ta saki taji dadin maganarta..

"In sha Allah.." a tsanake Unaisah ta fara labarta mata tiryan tiryan kamar yadda ta saurara a audio din da Chief ya kunna mata.

tunkan takai karashen labarin Idanun Batool suka cicciko tab da ?walla cikin sanyin murya tace"sai yanzu na gane meyasa aunty ummi kuka rannan, nayi zaton ni Batool din take fadin ta rasa na mutu ashe bani bace, sunan babynta ce data rasu, na tausayawa aunty Ummi da uncle Shureim, labarinsu ya taba zuciya ta, ashe sheikh Imam ne mahaifinta amma meyasa ya yanke mata hukunci cikin fushi?

Ta faWa fuskarta babu walwala..



"ko dai ni da bani da ilmi bazan iya aikata abun daya aikata ba, abun daya faru tsakanin Aunty Ummi da Uncle shureim sharrin shaiWanne, bayin kansu bane, duk da ba agabana komai ya faru ba, amma ni ina kyautata masu zato, kuma duk wata kaddara da ta faru da bawa, da akwai wata hikma ta ubangiji wanda mu ba zamu iya gani ba, kamar yadda bamu taba sanin ta arayuwar mu ba sai gashi silar taimakon mu da sojojin America su ka yi mun hadu da ita, kuma mune silar da ta dawo Nigeria harta sake haduwa da mahaifinta, da aminnanta, da kuma ya shureim.."


muryarta na rawa ta karashe maganar, Unaisah tace"kinyi magana mai ma'ana, pls ki share hawayenki, nasan labarin akwai taba zuciya, amma ni ban fada maki donna sanyaki a damuwa ba, tsakanin mu da su aunty Ummi da babynta Addu'a ne da ita kadai zamu iya taimaka masu..." ta fada tana kur6ur juice da ta zuba a cup.


"Chief yayi alkawarin zai sasanta tsakaninta da kawayenta, da kuma Mahaifinta, in sha Allah.."

ta karashe maganar tare da zaro tissue cikin box ta mika mata, yatsun hannayenta na kerma ta kar6a tana share hawayen ta, Unaisah dake satar kallonta, batai mamakin ganin yadda jikinta ke kerma ba saboda tasan irin kaunar da take ma aunty ummi, dole labarinta ya karya zuciyarta, shiyasa ba komai ta sanar da ita ba, ta boye mata batun Uncle musa da kuma binne jinjirar da Uncle shureim ya yi.

"Inama ace babyn aunty Ummi tana araye, da yanzu muna a tare da ita, Ni dai na kamu da son ta, Inason aunty ummi da ya shareim harma da mommynki da Aunty Anila"


dariyar farin ciki Unaisah tayi"kuma kinsan wani abu, dana ji labarin nan sai na ji araina kamar ke ce babyn Uncle shureim saboda bala'en kama da ki ke yi da shi, don dai ta rasu ita bata araye.."



murmushi Batool tasaki aranta tana tariyo farkon haduwarta da Uncle shureim har yau takasa manta lokacin daya cire mata errings dinta daya sargafe veil dinta.



Ganin ta shagala da tunani yasa ta katse ta"mu karasa cin abincin kada ya huce" sai da suka ci suka koshi tukunna suka koma falo a saman sofas suka zauna.

Sai jaraba kiran layin Ummi ta ke yi baya shiga, Har kiran daddyn ta ?arayi shima baya picking, ta damu sosai, a karshe ta kira layin Danejo kamar dama jiran kiranta su ke yi, suna Wagawa muryoyinsu suka cika kunnuwansu dayake handsfree ta saka kiran

"Angel, Kun manta damu, almost one month and weeks An kulle mu a part din daddy taj, Pls mun gaji, wallahi, Muna so mu dawo inda kuke..

"Unaisah wai har yanzu su Chief basu dawo daga kai farmakin bane? Muna jira shiru ba labari, Ko mun kira bakya daga kiran mu, Hankalinmu ba akwance ya ke ba ku fada mana in wani abu ya faru pls"

Angel, Ina danish dinmu? Ina yaya Salsabeel da Chief? Ina daddy taj, babu mai leko mu, kowa ya manta damu.

"Ni abinci ma yanzu ya daina min daWi, ki6ar har tayi min yawa, baku ga yadda na koma ba, pls Unaisah ku fada ma Chief abude mu, kullen Ya isa haka, mun takura sosai, Muna so mu sakata mu wahala.." muryar Parveen ce

tuntsirewa su ka yi da dariya ita da Batool kamar zasu shake .

"Pls ku kira mu video call mana" maida kiran Unaisah tayi video call, sai gasu reras su goma shabiyar, waro idanu sukayi ganin yadda hutu ya zauna masu, sunyi kiba kamar rainon turai, fatarsu tayi jajir yadda kasan ya'yan larabawa hatta masu duhun fatar cikinsu sun yi fresh fatarsu tayi kyau.


fashe masu da kuka Azeeza da jemimah su ka yi, ji suke kamar su yi tsalle su shige ta cikin screen din wayar.



Haris sai tambayar Danish Ya ke yi, yana ina? Ya yake? Sun dawo daga kai farmaki ko har yanzu basu kaiga zuwa ba, Kasa amsa mashi su ka yi, shiyasa suke fargaban su kirasu saboda tsoron su tambayesu ina Danish gashi kuma duk sun damu da shi sai tambayar shi sukeyi.


"Pls Sis, Ku fada mana gaskiya, ina ji araina kamar wani abu ya faru, sunje kai farmakin ko basu je bane"? Sajeed ne ya tambaya, fuskarsa amarairaice

dakyar Unaisah tayi karfin halin furta"har sun dawo" waro idanu waje suka yi cikin mamaki da rudu, atare suka hada baki gurin firta"suna ina? Sunyi nasara? Meya faru da suka je? Sun kashe su um? Sun taimaki sauran prisoners din um?

Kamar yan jarida suka tsare su da tambayoyi.

Numfasawa tayi cikin karyayyar murya tace"sunyi nasarar taimakon fursinoni, yanzu haka suna a asibiti karkashin kulawar likitoci.." tunkan ta kare maganar Suka fara shewar Farin ciki..

"Yar uwata fa? Hada ita cikin su?

Cike da zumudi Sajeed ya tambaya.

Bata san amsar da zata bashi ba, Batool ce tay saurin cewa"hada ita, wata mai bala'en kama da kai, ai munje asibitin mun gansu, tana nan cikin koshin lafiya, sai tambayar dan uwanta Gabriel ta ke yi"


bai ?arasa sauraran Batool ba ya shiga furta Alhamdulillah, Alhamdulillah... "

"Mu damuwar mu, ina bugun zuciyar mu?

Murmushin ya?e Unaisah ta saki"ku kwantar da hankulan ku, Danish, Yana nan Cikin koshin lafiya, ya Wan samu rauni ne shi da ya Omar da salsabeel, shiyasa aka kwantar da su asibiti amma jikin nasu da sauki, har tambayar ku ya ke yi kuna ina muka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login