Showing 261001 words to 264000 words out of 321579 words

Chapter 88 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

tace"ni kuma abun da nake tunani game da dinner din da za'ayi after one week da yin auren, watakil yana son kafin ranar ta samu ciki.... "
waro idanu waje su ka yi jin abunda Ummi tace ita kanta da tayi maganar sai taji abun bankwarakwai, gaba daya suka bushe da dariya cikin nishaWi..


Knocking din ?ofa ne ya katse firar ta su.

"Wanene"?

"Mommy ni ce..." ajiyar zuciya ta sauke"shigo ciki" buWe ?ofar tayi ta shiga, waro idanu waje su kayi tare da bude baki suna kallon ta, wata irin kunya taji ta kamata, tayi saurin sunnar da kanta ?asa.

"Wow, babe Unaisah irin wannan kyau haka? Kamar wadda zataje gasar miss world? aisha ce ta faWa tare da rungumar ta, tana dan shafa bayanta"masha Allah Unaisah finally kin zama matar dg, Allah ya sanya Albarka a auranku..."

amsa mata tayi da ameen Benazir ta nufo ta, da murmushi kan fuskarta, tana ganin mamanta ta yi saurin karasawa gareta ta rungumeta tightly a kirjinta, batare da sun iya furta kalma ba, kowa yana jin rashin dadin rabuwar da zasuyi da juna.

"Unaisah.." Anila ce ta kirata a hankali ta raba jikinta daga na mommynta taje ta rungume Anila.

Bayan data dago Ummi ta ru?o hannunta ta zaunar da ita daga gefen gadon mommynta, suka zauna gefe da gefen ta, Benazir tana daga tsaye tana kallonta da rinannun idanun ta.

Ummi ce ta fara yi mata nasiha game da zamantakewar Aure, mai matu?ar ratsa zuciya, ta bata shawarwarin da zasu amfane ta, ba Unaisah ba hatta Benazir da Aneelerh sunji dadin nasihar da Ummi tayi mata sosai, bayan da tagama Aneelerh ta Waura da yi mata huWuba, gaba Waya suka sa taji ?arfin gwiwa atare da ita.

Bayan da Aneelerh ta gama, Benazir tace"Unisah, ni ba abun da zance, saboda duk wani abu da zan faWa, mommies dinki sun faWa, illa iyaka ince ki Wauki shawarar su, in sha Allah ba zaki ta6a yin danasani ba ..." idanun ta ne su ka cuko da kwalla.

"Please kada ki zubar da hawayenki Unaisah, Zaki 6ata kwalliyar..."

Ummi ce ta fada jinjina kanta ta dan yi tana kokarin shanye hawayen ta.

In a broken voice tace"gaba daya Kun kashe min bakina, na rasa tayaya zan iyayi maku godiya, kun gatantani, kun nuna min ?auna, kun yi min abun da bazan iya biyanku da shi ba, kullum cikin bani shawarwari kukeyi, kun gyarani, kun ilmantar dani, Allah ne kadai zai iya biyanku, Ina alfahari da ku.."

tun da ta fara yin magana suke kallonta da murmushi kan fuskar su.

Wayar Ummi ce tayi ruri ta mike ta nufi kofar dakin tayi picking, Unaisah tabi bayanta, sai da tabari ta kammala wayar sannan tace"Aunty Ummi, Yar uwata bata zo bikina ba, meyasa ko bata da lafiya ne"? juyowa tayi ta dubi Unaisah

"ba zata samu zuwa ba, cikin ta ke ciwo, amma karki damu tasha magani, lokacin dana baro gidan bacci ta ke yi, ko ba yau ba Batool zatazo gidan ki tun da nan kusa ne"

girgiza kai Unaisah tayi kamar zata saka kuka tace"Aunty Ummi, kiyi ha?uri amma raina na bani wani abu ne ya faru! Ko sakon da ta turo min raina na bani ba ita ta rubuta shi ba, Ba dan ban yarda da maganar ki ba, dan Allah ki fada min meke damunta? Meyasa ta canza ra'ayinta na kar6ar rigata"?

"Me kuma ya hanata zuwa bikina? Bayan itace babbar ?awar Amarya, nafi bukatar ganinta akan kowa"

yanayin yadda tayi maganar da damuwa ne yasa ummi taji jikinta ya yi sanyi la?was.

In a cool voice tace"haka ne Unaisah, kin faWi gaskiya, amma ba abun da kike tunani bane, bazan iya fada maki ba, amma zuwan Batool gidan bikinnan ba alkhairi bane! Kwara zamanta a gida, zaifi mana kwanciyar hankali, ni narasa gane meke damunta kamar mai iskokai..."

ta fada cikin kunci da 6acin rai.

"Batool ta bani kunya Unaisah, ta karya min zuciyana..."

gaban Unaisah ne ya faWi ganin hawayen dake sauka kan kuncin Ummi.

Cikin rudu tace"Aunty Ummi! Meyasa kikace haka? Saboda abun daya faru jiya? Ko wani abun tayi maki"?

numfashi taja tare da dan jinjina kanta tace"ba wannan ba Unaisah, ai ?wara abun da tayi jiya, yau takarasa haukacewa, kawai abun da nakeso dake, pls ki manta da batun zuwan Batool, ba zan ta6a bari tazo ba, kuma kema ban yarda kije inda take ba, ki bata lokaci har sai ta canza tunanin ta..."

kalaman Ummi sun Waga hankalinta, kamar tayi kuka take ji, magiya tadinga yi mata akan ta taimaka ta yafe ma Batool laifin da tayi mata, tabarta tazo in ba haka ba bazataji dadi ba.

Amma ummi ta rufe ido tace wallahi Batool ba za tazo ba, tama cire rai da ganin ta har sai an kammala bikin ta, kuma karta kuskura taje inda take ko tace zata faWa ma wani in ba haka ba zata sa6a mata, Unaisah ba yadda ta iya dole tabi umarnin Aunty Ummi.

Babu wanda yasan meye faru a tsakanin su, gashi kowa ya damu da rashin ganin Batool, musamman bridemaids, duk wanda ya tambayi ummi ko Unaisah game da Batool sai dai su ce bata da lafiya.



~_____________________________________


Around ?arfe biyar na yammacin ranar, motocin su Taj suka karaso cikin gidan domin daukar Amarya, bayan ya kira Benazir ya fada mata su fito da Unaisah suna jiran su.


A main Falo, Benazir tare da aminnanta suka shugo da Unaisah...

A saman Carpet ta zauna, Hajiya layla da Hajiya adama ne suka fara yi mata nasiha bayan sun gama daga bisani suka sanya mata albarka tare da yi mata fatan Alkhairi dakyar take amsawa kamar zata sanya kuka, Mamie da Ummi ma su ka yi mata huWu ba kan zamantakewar aure a karshe suka sanya mata albarka tare da fatan Alkhairi..
Daga bisani Hajiya sarah tayi mata nasiha itama.

Kowa dake agidan saida ya yi mata addu'o'i da nasiha tare da fatan Alkhairi, kamar zata fashe da kuka saboda sun karya mata zuciya ji take kamar in ta tafi ba zata sake ganin su ba.

Sallamar ?an Uwanta Maza ne ta katse hanzarin su, atare suka kai duban su gare su..

Su biyar ne suka shigo, sun Wauki wankan Shadda getzna blue sky, hannayen su sanye da tsadaddun agoguna, ga wasu hadaddun takalma a kafafunsu, hair cut din su yafi komai jan hankali, Sajeed da Haris ne agaba, Naufal da javeed suna abiye da bayan su tare da Mubeen a gefen su.

Bridesmaids na ganin su suka fara murna tare da nufar su kamar za su yi hugging din su, suna ta sakin wani ?ayataccen murmushin gefen fuska.



"Daddy Taj ne Ya turo mu don mu fito masa da Unaisah muna jira" Sajeed ne ya faWa



"Tashi mu tafi Unaisah..." Hajiya adama ce ta faWa, sai da suka taimaka mata gurin mikewa saboda raunin da ta yi, rungumeta Benazir tayi sosai, ta dinga zuba mata addu'o'i tare da sanya mata albarka, tace ta kwantar da hankalinta, a duk lokacin da take bukatar ganinta ta kirata awaya, cikin shesshekar murya ta amsa mata da toh, kowa dake agurin sun basu tausayi sosai, tsakanin uwa da ya sai Allah..

Yan Uwanta maza suka shiga gaba, Bridemaids suka take mata baya, yayin da sauran yan rakiya suke abiye da bayan su.

Daga cikin waWanda zasu rakata, bayan braidsmaids, sai hajiya adama da hajiya layla, da kuma Aneelerh, da Ummi da sauran su.

Har suka fuce daga falon Benazir bata daina bin bayansu da kallo ba, kamar tabi su take ji, badan hajiya layla ta kwa6eta ba ai da ba abun da zai hana taje raka diyarta, a karshe zama tayi dirshan kan kujera ta zabga tagumi idanunta cike tab da ?walla, Mami da Ummi ne suka kewayeta suna lallashin ta.

A Parking space suka hango iyaye maza, gaba dayansu ankon shadda getzner su ka yi suna atsaitsaye suna jiran fitowar su, tun daga kan Taj dake a ru?e da hannun Baby junaid, ya shige cikin manya, shima ankon ne ajikin shi, Ya manna bakin glass sai shan kamshi ya ke yi kamar shine angon, Dr shureim yana atare da su, Uncle Abdallah, ga mijin dr yusra wato yaya Salsabeel namu ya sauya ya zama babban mutun, amaryar fa yar gata ce, gaba Wayan su ne su ka zo tafiya da Unaisah gidan Iyayen mijinta.


Fuskokin kowan nan su Wauke da fara'a, ta cikin mayafinta take hangen su, kaitsaye ta nufi daddynta, tana karasowa yayi hugging din ta yana shafa bayan ta, ji ta yi kamar ta fashe da kuka.

A kunne yayi mata raWa"Unaisah, nima inajin abun da ki ke ji, please kada ki sanya damuwa aranki, ki kwantar da hankalin ki, kinsan wa kika aura, ni nayi imanin ba zaki taba danasanin auran za6ina da ki ka yi ba, yau ranar farin ciki ce a gare ki dani kaina, burin da kika daWe da shi Allah ya cika maki shi Unaisah kin tuna? Ko in tuna maki"?

Ya faWa yana leken fuskarta, dariya ta saki har fararen hakoranta su ka bayyanta.

?agowa tayi da kanta daga kan kirjin daddynta, Uncle Abdallah Ya ru?o hannunta tare da yin hugging dinta, yayi mata addu'o'i tare da fatan Alkhairi, kafin ta matsa gurin Uncle shureim shima ya sanya mata albarka tare da fatan Alkhairi, ta dinga amsawa da ameen hadi dayi masu godiya, Salsabeel ma ya yi mata addu'o tare da fatan Alkhairi.

Zu?unnawa tayi gaban baby junaid daya haWe rai kamar bai ta6a yin dariya ba.

Shafa kumatunsa tayi"my little bro, fadamin waya 6ata maka rai"? Yana cika yana batsewa yace"hmm fushi ni ke da ke, bani ki ka ce zaki aura ba! Shine kikayi auran ki" gaba daya suka sanya dariya, tunawa ta yi da Uncle Uzair da daddynta a lokacin baya, sunyi burin su haWa ya'yan su Aure, Allah bai nufa ba.

Saitin kunnanshi takai bakin ta cikin raWa tace"na gane laifi na my little bro, ka yi ha?uri, amma nayi maka al?awarin in sha Allah zan haifa maka kyakkyawar baby kaga kaima sai kayi auran.."

6a66akewa yayi da dariyar farin ciki.

"Ki haifa min kyakkyawa mai irin idanunki, da komai naki" dariya tayi cike da nishaWi.

"Pls kada ka fada ma kowa, daga ni sai kai, alkawari" ta fada tare da mi?a masa yatsanta, Ya sargafo shi da yatsan shi, suka sakarwa juna murmushi.

Kowa ya nutsu yana kallonsu sun burgesu sosai.

Peck ta manna masa a forehead dinsa.

Kafin ta mi?e tsaye, Suna haramar shiga cikin motocin.

Unexpected suka tsinkayi muryar Batool a cikin kunnuwan su.

"Sister ku jira ni... " gaban Ummi ne ya faWi rass! aranta ta ayyana kamar muryar Batool? Anya itace? Tayaya akai ta buWe ?ofa bayan na kulle ta, Ya salam in kuwa itace An yanka ta tashi..

kusan atare suka dubi inda take..


cikin sauri ta ke yin tafiya dakyar take taka kafarta saboda tsinin high heels din kafarta, tayi bala'en yin kyau a cikin ankon ta, ta saka Red Aso ke headband akanta, Sumar kanta da tasha gyara ta lullu6e bayanta, sai ka rantse da Allah itama amaryar ce saboda yadda ta yi kyau.

hankalin Ummi fa ya tashi a sukwane ta daura hannu daya akanta.

sam ta?i yarda ta haWa idanunta da Ummi saboda gudun karta hanata sukuni, tunkan ta karaso Unaisah ta nufe ta suka rungume juna, sauran ?awayen suka nufe su gaba Waya su ka kewaye Batool suna ta santin kyan da ankon yayi mata.

Jiki asanyaye Ummi ta dubi dr. shureim harara ya watsa mata tare da yin ?wafa, nan ta ke ranta ya bata shine ya buWe ma Batool ?ofa, haWe rai tayi tana dan murguWa masa bakin ta a fakaice.


Ru?o hannun ta Unaisah tayi suka nufo su, with respect ta gaishe da iyayen nasu, suka amsa mata da fara'ar su.


daga bisani, daddyn Unaisah ya buWe mata backseat ta shiga ta zauna, Aneelerh da hajiya layla suka sanyata tsakiyarsu.

Taj Ya shige mazaunin driver,

tuni ummi ta ru?o hanun Batool suka shige motar dr Shureim, hajiya adama a motar abdallah ta zauna tare da baby junaid.

bayan kowan nan su Ya shiga a jere motocin su ka soma tafiya slowly saman titin estate din wanda zai sadasu da gidan su Ango.


Acikin motar Taj Aneeleerh da Hajiya layla sai ?ara yi ma Unaisah Nasiha su ke yi duk don ta sake ta daina jin fargaba.


A hankali dr shureim keyin driving yana satar kallon Ummi da ke zaune a gefen sa ta cikin madubi, kwata kwata bata lura ba, ta dage sai aikawa Batool harara ta ke yi ta mirror, duk tabi tasha jinin jikin ta da ganin irin kallon da mommyn nata keyi mata, tuni idanun ta sun cuko da ?walla.


"Why Aisha? meya haWa ki da Batool dayaja har kika kulleta adaki? Laifin me ta yi maki please? Ko dan saboda abun daya faru jiya ?


Har saida ta Wan ji gabanta ya faWi, cike da ?arfin hali tace"bata faWa maka abun kunyar da ta gaya min ba ne... "?


Walwalar fuskarsa ce ta Wauke, cike da damuwa yace"koma me tayi maki bai kai laifin da zaki kulle ta aWaki ba, ita ka Wai agida, idan wani abu ya faru fa? Baki ga yadda na taras da ita ba, kwance kan floor, hancin ta yanata bleeding, kwata kwata bata a hayyacin ta, badan Allah yasa naje gurin dakin nata ba har na jiyo shesshekarta da ban san me zai biyo baya ba"


Hankalin ta ba ?aramin tashi yayi ba jin abun da ya ce, duk tabi ta rude ta juyar dakai ta dubi Batool data sadda kanta kasa.

"Am sorry babe, banyi don na bata maki rai ba, kodan na ?untata maki, sai dan ina gudun abun da zai biyo baya, kinsan ina sonki, bana son duk wani abun da zai bata maki rai, nasan in har kikazo gidan biki za'a iya samun matsala shiyasa naso ki zauna gidan, zaifi mana kwanciyar hankali, bansan haka abun ya faru ba... "

Cikin sanyin murya tace"bakomai Ummina, ya wuce, ni yakamata in baki hakuri, ban kyauta ba, nayi rashin hankali amma bana so ki damu akaina, In sha Allah bazan kara maimaita kuskuren da nayi ba,.."

ajiyar Zuciya Ummi ta sauke, taji dadin maganar Batool.


"Bakiji yadda naji dadi ba, haba yanzu nasan batool dina ce.."_

murmushin karfin hali Batool ta yi wanda bai kai zuci ba,


~____________________________________

Idan muka koma bangaren Gidan su Ango, gaba Waya Dangin su sun hallara a main falo suna jiran ?arasowar Amarya da dangin ta, wasu daga cikin matan family din suna a tsaye gaban entry Hall suna jiran zuwan su don su tarbe su.


Lokacin da Motocin suka ?araso slowly su ka yi parking a gefen Entry hall a jere, cikin sauri Securities din dake sintiri agurin su ka yi hanzarin matsowa tare da bude cardoors din su.

Gaba dayansu suka fito, Unaisah tana a tsakiyar Aunty Aneelerh da Hajiya layla, ta rufe fuskarta da veil.


Yan Matan Family din dake jiran karasowarsu suna ganinsu suka nufesu suna rangwaWa buWa Ayyiriyiriiii, gaba Wayan su sun Wauki wankan swiss cord Lace riga da skirt, sun saka asoke akan su dana kafada, sun wanku abunka ga dirarrun mata.

Suka kewaye su suna rangwaWa buWa.

A haka suka nufi ciki da Unaisah gabanta nata faWuwa rass rass ta rasa me ke mata daWi..

Suna shiga cikin katafare falon wani daddaWan ?amshin turare ya cika hancinan su, ga sautin kiWan wa?ar larabawa da ke tashi..


Ta cikin net din gyalen take satar kallon al'umar dake a cikin falon..

Gaba Waya Iyayen ango da kawunnansa da iyalan su sun hallara a babban falon, kowan nan su yana a zaune kan Sofas karkuso kuga yadda manyan matan suka ca6a adon zinari a wuyansu da hannayen su, wasu diamond necklaces suka sanya, sunyi shiga ta alfarma, sunyi matu?ar yin kyau, Yayin da Uban Ango da Uncles dinsa suke a sanye da dandatsetsiyar shadda blue sky, wuyan hannayen su asanye ya ke da expensive watches.

cike da aji da ?asaita su ke sakin murmushin dattako suna kallon dangin Amarya da ke shigowa falo tare da amaryar su..

Hajiya saratu tana a zaune kan sofa tsakankanin Uwar Ango da sheikha mujeedat, tayi ?iba dumurmur da ita kai kace bata taba shiga damuwa ba arayuwarta, a yanzun ma da ta ke a zaune plate ne ruke a hannunta mai Wauke da chicken wings soyayyu hankalinta kwance ta ke cin abun ta, hali na nan

Can na hango Hajjaty da mommy Turai zaune kan Sofa suna ta fira, yanzu fa sun zama dangi, babu mai goranta musu, shigowar dangin amarya ne Ya katse hanzarin su, kusan atare suka mi?e gaba dayan su don nuna girmamawa, hakan ba ?aramin faranta ran dangin amarya ya yi ba, cikin fara'a da mutunta juna suka soma gaggaisawa, mazan suka soma yin musabaha, matan kuma sunayin gaisuwar larabawa a tsakaninsu, sunyi masu kyakkyawar tarba, daga bisani kowan nan su Ya samu guri Ya zauna, Dangin amarya suna fuskantar dangin Ango, Unaisah da bridesmates da yan uwan ta maza suna zaune kan lallausan rug..


Unexpected idanunta suka hango mata Prime minister ta cikin gyalenta, yana a zaune kan sofa, daga gefen shi mai girma Sharafuddeen suna fira, wani irin faWuwar gaba taji, wallahi sai taga kamar Danish ne, saboda sumar kan da Hateem ya tara ta kara fiddo da kamanninsa da Danish, nan take tafara tariyo kyakkyawar fuskarsa, ta dinga jin zuciyarta na bugawa da matsanancin ?arfi, hawaye su ka ciccika idanun ta, ?uncin ya mamaye zuciyarta har wani zazza6i take ji a jikin ta, a hankali ta dauke idanun ta daga kan Daddy minister ta mayar da su kan Sheikha Mujeedat, mahaifiyar Man dinta, bazata ta6a manta al,ajabin da tayi ba aranar da taji cewa Danish dan Hateem ne, dama ta daWe tana ji aranta danish dan wani hamshakin mai kuWi ne ko basarake ashe hasashenta ba karya bane, wallah taso Danish Ya rayu da iyayen sa, duk da tasan koda yana araye bama lallai ya kulata ba, saboda yafi karfinta nesa ba kusa ba, ba ma ajinta bane indai ta matsayin family za'abi, aranta ji take inama man dinta yana araye koda bazai kulata ba, zataso tagansa cikin rayuwar farin ciki.


Batasan sa'adda hawaye suka fara zarya kan kuncin ta ba..
Kunnuwanta ne suka soma jiyo mata tattaunawar su.


"Madallah, Munji dadin karramawar da ku ka yi mana, wannan ya kara tabbatar mana da cewa yarmu ta shigo gidan mutane masu daraja, da ?ima kuma gidan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login