Showing 6001 words to 9000 words out of 321579 words

Chapter 3 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

shi sukuni, Yana ji aransa in har bai mallaki aishaba har ransa zai iya rasawa, bakomai yake hadama ba face surar jikin ta..

Dayaga bashi da wata manufa sai ya yanke shawarar tunkarar Aisha don ya nemi soyayyarta, yasan in har ta amince mashi Shiekh imam bai isa Ya raba su ba, Har court zai iya kai shi ?ara.

Da taimakon Aunty laura ta shirya mashi ranar da zaizo gidan donsu gana da aisha aranar shiekh Ya tafi gurin aikinsa. .

Agarden suka zauna, tana asanye cikin dogon hijab dinta cikin girmamawa ta gaishe da Alhaji musa ta kara yi mashi godiya bisa ga kokarin da yayi akan karatunsu, yaji dadin tarbar da tayi masa har yaji aransa ba zata ta6a ?in amsa bukatarsa ba.

Cikin nutsuwa Uncle musa ya fayyace mata irin kaunar da yakeyi mata, tashin farko Aisha tace"kayi hakuri da amsar da zan baka, wallahi bawai bana sonka bane, kawai ban ta6a yi maka so daya shafi aure ba, Ina jinka kamar Uncle dina saboda zumuncin dake atsakanina da Benazir, amma ni inada wanda nakeso..." bata kare maganar ba Yai saurin dakatar da ita ta hanyar Waga nata hannu har saida tadan sha jinin jikin ta.

"Karya kike kice bakisona, babu macen dana ta6a nuna inaso tayi rejecting dina, don haka kema akwai soyayyata acikin zuciyarki, idan ma kina jin kunyata ne to ki daina, ni ba Uncle dinki bane, ashirye nake da in aure ki, Aisha kiyi tunani akaina kafin ki yanke shawara, zan jira naji daga gare ki"

yana fadan hakan yayi tafiyarsa, gaba daya tashiga halin damuwa kuma ta kasa sanarma kowa, hatta Benazir da Aneelerh basu san da maganar ba, kusan sau biyar Alhaji musa yana tuntubarta a waya don yaji in ta canza ra'ayi amma ta nace akan ita bazata iya auren shi ba, tana da wanda takeso, daya matsa mata akan ta fada masa wanene takeso sai tace mashi yaya shureim ne, a lokacin ji yayi kamar ya binne ta da ranta saboda bakin kishine da shi, ya ji zafin furta sunan shureim da tayi, zuciyarshi ta raya mashi cewar ba ra'ayinta bane Shiekh imam ne ya cusa mata nasa ra'ayin dama ya nuna yafi sha'awar ta auri shureim daga nan ne ya kuduri aniyar saiya shiga tsakanin su.

Har gida yaje ya samu shureim Ya tambayesa meke a tsakaninsa da Aisha, dr shureim yace babu komai face mutunci, shi ya dauke ta kamar kanwarsa.

Uncle musa yace bai yarda ba, in har yana son ta ya fada mashi zaiyi mashi hanyar auren ta, daya matsa mashi da tambaya kawai sai yace mishi eh yana sonta amma bai ta6a sanar da ita ba.

Hankalin Uncle musa ba karamin tashi yayi ba, saboda ya fahimci dukan su suna son juna, kuma In har Shureim Ya furta yana son Aisha tofa babu makawa sai Sheikh imam Ya bashi ita.

hakan yasa shi yanke shawarar komawa gurin imam malik don ya kara rokonsa akan ya bashi ita, kusan sau biyar yana zuwa gurin imam amma ya rufe ido akan bazai ta6a aura masa aisha ba, ta ko'ina babu sauki, har aunty laura yaba cin hanci na makudan kudi donta karkato da hankalin sheikh imam akansa amma duk abanza, itama aishar ba irin magiyar da baiyi mata ba akan ta amince da soyayyar shi akarshe sai tayi blocking duk wata hanya da zata haWa ta da shi, hatta gidansu Benazir ta daina zuwa sai dai Benazir tazo gidansu ta same ta, ranshi ba karamin baci yayi ba, shi a ganin shi bata yi mashi halacci ba, kodan saboda dawainiyar da yayi dasu yaci ace ta saka mashi amma saita butulce dama shi baya abu dan Allah sai idan yasan zai samu riba.

bayan wasu kwanaki Uncle musa ya Wauke ?afa da zuwa Gidan yayansa kwata kwata suka daina jin duriyarshi, da Benazir ta sanar da Aisha baya kasar Ba karamin dadi taji ba, kuma ta saki jiki ta cigaba da zuwa gidan, wani lokaci atare suke zuwa gidansu Aneelerh wani sa'in kuma Anila ce ke zuwa gidajen su ta kawo masu ziyara, har takaiga iyayen su na ziyartar junan su.

Daga baya da soyayyar Aisha ta fara addabar Dr shureim har takaiga dakyar yake runtsawa saboda tunaninta, baya da burin daya wuce ya aureta, aranar daya shirya tunkararta don Ya fada mata irin kaunar da yake yi mata, A lokacin Aysha da Aneelerh sunzo Gidan su suna a dakin Benazir Suna fira, A bakin kofar dakin ya tsaya yana tunanin taya zai tunkareta da maganar? Zata kar6i tayin soyayyar shi ko kuwa? yana jin fargaban Aisha taki amincewa da shi shiyasama tuntuni yaki sanar da ita saboda fargaban amsar da zata ba shi.

Har ya zaro waya daga Aljihu da niyar Ya kirata don ta fito su ke6e, kwatsam kunnuwansu suka jiyo mashi firar da su ke yi..

"Yanzu tun da mun kammala karatu me ya rage mana"? Benazir ce tayi tambayar.

Aneelerh tace"Aiki da kuma Aure, amma Abie yace bazai bari in fara aiki a private hospital din daya buWe min ba har sai na tsayar da miji"

Benazir tace"Why not Ki ba Uzair damar ya turo da magabatansa? Tun da naga Jininku Ya haWu da shi"

Murmushi Anila tayi"Wai da Ke nake Jira, Idan Kinba Taj damar Ya tura da nasa magatan Gidan ku nima sai in ba Uzair Damar Ya tura gidan mu..." wani kallo mai kama da harara Benazir tayi mata..

"Pls mana ki amince masa nasan fa Kin mutu akan kaunarsa amma sai ki ta wani Ja mashi Aji"

"hmmm nifa ba aji nake ja masa ba, Ina tunanin ta yadda zan tunkari mommy da wannan maganar, daddy baida matsala nasan zai amince min, amma mommy bansan ya zata dauki abunba kinsan Mommy bata son dan jarida sannan shi ba dan wani Hamshakin mai kudi bane..."


Tun da suka fara magana Aisha bata tsoma baki ba, tayi shiru kamar hankalin ta baya akansu, har saida Benazir ta Wan dafa kafadarta tukunna ta mai da hankali akansu.

"Meke damunkine? Tun dazu kin yi shiru ba ki ce komai ba, ko baki ji abunda muke magana akai bane"

Murmushi tayi"Naji mana, mamakine ya kamani, Naji kuna maganar Taj da Uzair su wanene su din? Yanzu duk kawancen mu daku ashe har akwai wani sirri naku da bansani ba"?

Dariya su ka yi, Anila tace"Ay mana afwa Ustatha, ba haka bane, wlh mu ma bamu dade da sanin su ba, kin tuna ranar da muka fada maki zamuje shopping mall? One week da dawowarmu"?

"Hakane na tuna, Ay ranar na fadamaku Uzirin daya hana ni fita"

Benazir tace"toh A ranar muka hadu da su, kyawawan Samari kuma sun kwanta mana arai"

Taya su murna tayi Allah ya sa su zama Alkhairi agare ku

Suka amsa mata da ameen.

Anila tace"pls muna so muji ra'ayinki, Donni bana so mu riga ki yin aure, nafi so yadda muke aminnan juna, Muyi aure atare ya'yan mu su taso a tare"

Benazir tace"Aisha fa bata da matsala, Kinsan Allah yayi ta da farin jinin samari iri iri, attajiran masu kudi, Manyan Malamai sai ta zaba ta darje, Ko yau ta fidda miji baba Imam aurar da ita zaiyi Allah"

ta fada tana dariya, Murmushin takaici malama Aisha tayi Cikin raunanniyar murya tace"Bazan boye maku ba, dani daku mun riga da mun zama daya, Munsan sirrin Juna, Wallahi bana alfahari da farin jinin da nake da shi, saboda mafi akasarin mazan da suke sona ba dan Allah bane sai don Surar Jikina, Wlh Benazir da wuya namiji yazo gurina da sunan soyayya batare daya neme ni ba, Ina jin bakin ciki da taikacin hakan, ni nasan zaiyi wuya asamu wanda zai soni dan Allah..." dakyar ta kare maganar saboda kukan daya ciyota, Kalamanta sun karya masu zuciya.

Cikin shesshekar kuka tace"Inason Aure fiye da tunaninku, inaso in raya sunnar manzon Allah SAW amma taya zan samu wanda zai soni dan Allah"? Gaba daya tausayinta ne ya kamasu.

Lallashinta suka somayi tare da kwantar mata da Hankali, su ka ce In sha Allah zasu tayata da addu'a Allah ya bata miji nagari wanda zaiso ta tsakani da Allah.

Dr shureim dake a labe yana sauraronsu tun dayaji maganganun Aisha sai jikinsa yayi sanyi zuciyar shi ta karaya, Har Yaji shakkar furta Yana sonta saboda gudun kada tayi tunanin shima surar jikinta ya ke so.

Bayan wani Lokaci, Alhaji Ubaid Ya tsunduma a harkar siyasa kuma cikin sa'a ya shiga da kafar Dama, Arzi?in shi ya habbaka sosai, Rawar kai a wurin Hajiya layla har ba'a fada, dama ta jima tana cusa mashi ra'ayin ta akan ya shiga siyasa saboda taga yadda Alhaji musa ke fantama da dukiya abunda take ma kwadayi kenan, dama arayuwarta ta tsani taga Alhaji musa yafi Alhaji Ubaid Arzi?i tana jin haushin hakan sosai.

Dr shureim ya so ya kalubalanci siyasar da mahaifinsa ya shiga, Amma Hajiya layla ta take mashi burki ta hana shi magana adole yaja baki yayi shiru.

Alhaji musane yayi mashi hanyar da ya shiga Jam'iyarsu, a Karon farkon da Jam'iyar JDP ta tsayar da shi a matsayin Dan takararsu Na Gomna sunyi murnar da bazata Misaltu ba.


Saboda Farin Cikin hakan yasa Hajiya Layla ta shirya masu gagarumin Party don taya Alhaji Ubaid murnar takarar da aka tsayar da shi da kumayi mashi fatan Alkhairi.


Kafin Shigarshi siyasa saida ya fara tuntubar Shiekh Imam don ya bashi shawara, Sheikh yace shi bazai hana shi yin siyasa ba amma da zai bashi shawara yacigaba da kasuwancinshi sai yafi zama alkhairi a gare shi, saboda yawancin yan siyasa sai sun kauce hanya suke samun mulki, Nasiha sosai yayi mashi har yace ya dauki shawarar shi amma daga baya sheikh imam sai dai yaji labari agurin mutane cewa Alhaji Ubaid Ya tsunduma a harkar siyasa yayi mamaki sosai saboda bai ta6a bashi shawara bai dauka ba sai a wannan karan, abun daya kara Waure mashi kai, Wauke kafa da Alhaji Ubaid yai kwata kwata ya daina shigowa donsu gaisa sai in sun hadu a masallaci, daya fahimci kaukaucewar da yakeyi masa sai ya kyale shi don ya gano baya son ya hana shi yin siyasa shiyasa ya janye jiki da shi.

Lokacin da Celebration din Ya matso, Hajiya Layla ta gayyaci yan uwa da abokan arziki don su tayasu Murna, daga cikin wadanda ta gayyata hada Aunty Laura, Benazir kuma ta gayyaci Anila da malama Aisha, koda Aisha ta nemi izni agurin baba Imam yace bai amince taje party ba saboda yahudancine babu shi a addinance, bata ta6a musa masa ba sai akan maganar Party din nan, ta dinga rokonshi akan yabarta taje saboda ta yi ma Benazir alkawarin za ta je, In har ba ta je ba Benazir ba za ta ji dadi ba, Shiekh imam Yace tayi hakuri kawai, don bazai ta6a bari taje ba, wunin ranar kwata kwata babu walwala akan fuskarta, Har Aunty laura ta roka akan ta nema mata alfarma agurinsa aunty laura tace ita bazata sanya masu baki ba, saboda an nuna mata iyakarta don haka suje can su karata ita da uban nata, abunda yasa tace haka saboda taji haushin bukulun da shiekh imam yayi mata akan kudin da Alhaji musa yayi mata alkawarin zai bata intaja hankalin imam da Aisha suka amince da auranshi amma gaba daya suka watsa mata ?asa a ido abun ya kona ranta.

Ana i gobe za'ayi partyn, Tafiya ta kama sheikh Imam malik, manyan abokansa wadanda suka kasance shahararrun malaman addinin Islam yan kasar sudan dayake acan yayi karatu lokacin daya zauna gurin Kawunsa, abokanne suka gayyace shi wani taron karrama malamai da za'a gabatar a kasar sudan, kafin tafiyarshi saida ya kira Aisha ya kara gargadinta akan bai lamunta taje partyn nan ba, tace mashi toh in sha Allah bazata je ba, bayan tafiyarsa Aunty laura tace ma Aisha ay yanzu tunda mai gadin nata bayanan, sai ta shirya ta tafi tace ta fasa zuwa saboda batason ta sa6ama mahaifinta, bata matsa mata ba amma da Alhaji musa Ya kira ta waya yace mata yana son Aisha ta halarci Partyn in har tasa tazo zai bata Dala dubu goma sha biyar, Jiki na 6ari Aunty laura taje har dakin Aisha ta tunzurata akan ta shirya su tafi, baiwar Allah duk yadda taso ta hana zuciyarta bijirema mahaifinta saida takasa saboda tana son zuwa itama.

Wuraren ?arfe biyar na marece dai dai, suka shigo gidan Alhaji Ubaid, Aunty Laura ta dauki wankan shadda, Ta coge daurin dan kwalin ture kaga tsira, Ita dai Aisha Abayane a jikin ta doguwa har kasa, sai nikab din da ta sanya.

Anan suka iske manyan bakin su Hajiya layla, babu masaka tsinke, Yan uwa da abokan arziki duk sun hallara a katafaren garden din gidan da aka kawata shi da kayan ado da kujerun da baki zasu zauna an tanadi duk wani abu da baki zasu bukata don jin dadin su, Ga mawaka da Maroka sun Cika gidan sai kaWe kaWe sukeyi da yan raye raye.

Tunda suka shigo gidan gaban Aisha keta faduwa rass rass, kwata kwata hankalinta ba akwance yake ba, duk sai taji ba dadi saboda ta sabawa mahaifinta.

Lokacin da ta lula duniyar tunani Yayin da Aunty laura ta shige Cikin mutane tabarta.

Sam bata ji takun mutun ba, sai dai taji an rungumeta, har firgita saida tayi amma da taga Benazir ce sai ta sauke ajiyar zuciya, cike da farin Ciki suke kallon juna, Banezir ta Wauki wankan tsadadden leshi ko arzikin dan kwali babu akanta..


"Amma wallahi naji dadin zuwanki Aminiyar, har na fara fidda rai, ashe zakizo, ya ki ke ya baba imam? Cikin sanyin murya tace"baba bayanan ya tafi sudan, atare da aunty laura mukazo" ruko hannun ta Benazir tayi "mu shiga ciki, ki gaishe da Uncle Musa, tun Shekaran Jiya ya dawo Nigeria, tare da matar daya aura baturiya, amma baizo da ita nan ba, acan gidansa na Abuja yabarta, bai sanar da kowa game da auransa ba sai dai muka ji abakinsa jiya daya zo"

tun da Benazir ta fara surutu Hankalinta ba akwance yake ba, wani irin faduwar gaba taji jin ta ambaci sunan Uncle musa fuskarta babu walwala tace"kina nufin Uncle musa yana acikin gidan nan"?

Jinjina mata kai tay"eh," tace toh tabari da anjima in an gama partyn sai suje su gaida shi, Benazir ta amsa da toh, damuwace karara Akan fuskarta, Benazir bata lura da halin da take a ciki ba.


bayan sun shiga falo ta iska kawayen Benazir Hada Anila kowaccen su ta dauki wanka na mutunci Aneelerh na ganinta cikin sauri taje ta rungumota, Sauran kawayan Benazir sai murna suke yi Aisha bintu imam tazo, har rige rigen daukar hotuna sukeyi da ita, baiwar Allah tadinga kakkauce masu saboda gudun kada baba Imam yaga hotanta agurin partyn daya hana ta zuwa, Aneelerh ce ta lura da yanayinta hakan yasa taja ta gefe daya ta tambayeta meke damunta? Bata boye mata komai ba ta sanar da ita, ta kara da cewa ita kawai hankalinta bai kwanta ba, tana ji aranta kamar wani abu zai faru, cikin sigar lallashi Aneelerh ta soma kwantar mata da hankalinta har saida taga ta saki jiki...

tun da aka fara gabatar da shagalin hankalin Aisha ba kwance Yake ba, ga kawayen Benazir sai cashewa suke yi suna tikar rawa ga abinci kala kala ko kadan batay sha'awar ci ba.

Tana zaune kan kujera Wayarta ta fara ringing, tayi picking tare da karawa kan kunnanta
Muryar shureim Taji yana fadin ta same shi a upstairs yana son yin magana da ita"

Bata kawo komai aranta ba, ta yi azan zai bayyana mata soyayyar shi ne Hakan yasa ta mike batare da sanin kowaba Ta nufi upstairs, abakin kofar dakin dataga takalmansa tayi knocking ana bude kofar dakin aka janyota ta fado ciki, a firgice ta dago don taga wanene rass taji gabanta Ya fadi ganin Alhaji musa atsaye fuskarsa babu annuri daga shi sai short a jikin shi, wani irin faduwar gaba taji, da tsantsar mamaki ta furta"uncle kaine"? Daga mata gira yayi"nine Aisha.."arude tace"amma yaya shureim ne Ya kira ni, yana ina"

"Ni ne nayi muryarsa, saboda nasan idan kikaji ni ke kiranki ba zuwa zaki yi ba" matsawa yayi dab da ita tayi saurin ja da baya cikin sanyin murya yace"aisha, inaso ki dubeni daga kasa har sama ki fadamin me Allah ya rageni da shi"? Kawar da kanta gefe tayi muryarta na rawa tace"bakomai"

"In har hakane meyasa baki sona?..

"Saboda bakai nake so ba,"runtse idanun shi yayi saboda jin zafin maganar shi

"Aisha idan kikai min hakan baki min adalci ba, kin hana zuciyata sukuni saboda ke na kashe makudan kudi donki samu rayuwa mai kyau, Harta karatun da kukayi a germany nine na dauki nauyin shi ba Alhaji Ubaid ba, kawai nayi amfani da shi ne saboda nasan Halin mahaifinki da tsautsauran ra'ayi ba lallai in yaji nine nayi hakan Ya amince kije ba, kuma nayi hakanne saboda in dinga samun ganinki akai akai, saboda Imam bazai bari ina zuwa zance gurin ki ba, amma da kuna karatu a germany ba karamin morewa nayi ba saboda ina ganinki a duk lokacin dana so"


Hankali atashe tace"Dama duk dawainiyar da kayi mana a germany ba dan Allah kayi ba? saboda son da kake min ne" jinjina mata kai yayi...

"Wallahi da ace nasan kaine ka dauki nauyin karatunmu a kasar germany, da ba abunda zaisa inje"

tana fada ta juya zata fuce yayi saurin ru?o qugunta da tafin hannun shi ya janyota da karfi ta faWo kan kirjin shi, ya soma matsa mazaunanta yana sakin nishi, For the first da ta fara hada jikinta da namijin daba muharramin ta ba, rai a6ace ta banbare jikinta daga nashi ta daddage ta wanka mashi zazzafan mari ji kake fasss!.

dafe kuncinsa yayi da tafinsa, idanunsa suka kada jawur cike da bacin rai yace"ni kika mara"? Tana haki tace kadan ka gani, Nan gaba idan ka kara gigin ta6a jikina wallahi saina yi maka abunda har abada ba zaka manta ba, dama ba don Allah kakeso na ba, sai don wata mummunar manufa taka" tana fada ta buWe kofa ta fuce...

Tun da yake wani dan adam bai ta6a daga hannu ya maresa ba sai akan Aisha, yaji zafin marin nan adaddafe Ya fada kan gadon shi yana juyi, ransa ya baci matu?a jikin shi har gumi yake zubdawa.

abangaren malama Aisha bayan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login