Showing 216001 words to 219000 words out of 321579 words

Chapter 73 - Kurkukun Kaddarata Takun Karshe Complete Hausa Novel

zai yafe ma kowa zunubinsa banda irin mu, fir'auna ma daya nemi ya musulunta kasa karasa furta shahada yayi ruwa ya haWe da shi, dafa hankalin mu mun sani muka take sani Owais.."


"Baba Ka fahimta, kai ba musulmi bane, atlease in ka musulunta da imani a zuciyarka ko yayane zaka iya samun sassauci.."


magiya owais yadinga yi masa yana driving a hankali saboda baison suyi saurin karasawa Headquarter din su, sarai baba Obie Ya lura da yadda ya ke yin driving din ya kuma fahimci dalilin dayasa ya ke yin hakan.


"Owais, zanyi tunani akan maganar ka.."


"Baba baka da lokaci daya wuce wannan! Dama ce agareka, daga jibi zamu shiga kotu za'a yanke maku hukunci, ba lallai mu sake haduwa ba, musuluntar da zakayi ita zata bamu kwarin gwiwar yi maka addu'a ko bayan ba ranka.."

maganar Owais ta kayar masa da gaba.

Duk yadda yaso ya shawo kanshi abun ya gagara, ya fahimci yana son ya musulunta sai dai yana jin fargaban koya musulunta Allah bazai kar6i tubansa ba, kawai ya cire rai ne da komai.


Har suka ?araso Headquarter din baba Obie bai kar6i tayin Owais ba.


da shi da amininsa agents suka tasa su agaba Owais Yana a ruke da hannun kakansa Ya kasa sakinsa yana ta nanata masa kalmatusshahada don ya kar6a amma ya?i ya furta abakin sa.

Gaba Waya Isod agents din dake a head quarter din da sojojin tun shigowar su, suka cire hulunansu tare da sadda kansu ?asa, alama ce ta nuna girmamawa ga kakan dg.


A inda cells dinsu suke suka nufa da su, suna jiyo kururuwar sauran Elders din da su ka kulle a ciki, sai dai basu Iya ganin su, saboda kofar cells dinsu ta dabance, na waje bazai iya ganin na ciki ba, haka shima na ciki bazai iya ganin na waje ba, amma jami'an dake kula da bangaren cctv suna kallon komai da su ke yi a cikin cells din.


Bayan da suka saka kowan nan su, A cikin cell, suka kulle su.


DG bai iya barin headquarter din ba, saboda bayason Ya tafi yabar kakansa.


Bawan Allah Har dare Yana a nan, a karshe ma Cikin cell din Ya shiga, Ya zauna tare da shi, ya dinga kwantar masa da hankalinsa.


Har ya samu ya Wan nutsu Ya dakata da yin kuka, sannan Ya soma tambayarsa yayin da suke a zaune kan kujera suna fuskantar Juna daga tsakiyarsu table ne mai Wan tsayi.



"Owais, Idan akwai abun da kake son sani game dani ko kurkukun kaddara ka tambayeni na baka dama, nasan daga yau ba lallai Mu sake samun damar da zamu gana da juna ba... "


cikin sanyin murya yace"ka fara fada min idan akwai inda ke yi maka ciwo a jikin ka, zansa docs dinmu su duba ka"


Yace a'a baya bukata, saboda a halin yanzu babu likitan da zai iya shawo kan abun da ke damunsa.."


gwiwarsa ta sare da jin maganar sa.


"Tayaya zamu iya gano dangin fursinonin kurkukun ?addara da suka rage? Nasan mawuyacin abune mu iya ganowa da kan mu, bamusan ma ta ina zamu fara ba"

"Owais, baku da matsala da wannan, akwai bayanin da zan yi maka wanda zai amfane ku, sadaukarwar kurkukun ?addara kala biyu ce! Sadaukarwar jini da sadaukarwar mallaka, duka dai dole sai na jini ake sadaukarwa, amma akwai banbanci, ita sadaukarwar mallaka wanda zai yi ta, ba zai taba zama member na kurkukun kaddara ba, zamu yi yarjejeniya da shi ne, zai bamu abunda muke so, shima zamu bashi abun da ya ke so, da ga zarar ya sadaukar mun bashi abun daya keso to shikenan, mun raba jaha da shi, babu mu babu shi, ba member Win mu ba ne, Elders su kaWai ne members na kurkukun ?addara, da sauran ma'aikatan ciki, tun lokacin da salon tsafin mu ya sauya muka gano cewa in muka sadaukar da jinin mu munfi samun karfin sihiri da iko, daga nan salon tsafin ya sauya wanda ada, ba sadaukarwar jini mu ke yi ba, mutun zai kawo ko ba jininsa ba mu kar6a mu biya masa bu?atarsa daga bayane komai ya sauya.."

ya Wan dakata yana mayar da numfashi kafin ya dasa da cewa

"Littafin rijister na fursinoni wannan litattin da al?alamin sirihi na rubuta shi, tun shekarar dana gurfanar da gidan kurkukun ?addara, ni ne mutun na farko dana fara sadaukar da jikokina na farko da yan ukuna suka haifa (Yana nufin Senate lafeef, Abdul razak, da sir mubarak) bayan na aurar da su tun suna da shekara ashirin da biyar a duniya, a lokacin basu shirya yin aureba amma saboda manufata akan abin da nake hari, ni na matsa masu har saida suka amince akayi aurensu da matayensu, kusan atare matayen su suka fara haihuwa, jariran suna zuwa ba araye ba, har sau biyar a shekara biyar, tukunna na barsu suka samu ya'ya bibbiyu daga nan naci gaba da sadaukar da jariran su, ko sun nemi su hana matayensu haihuwa ganin sunata wahalar daukar ciki yara suna zuwa ba'araye ba, ni nake canza masu ra'ayi, in nuna ina son inga jikokina da yawa saboda bani da dangi suyi ha?uri zan cigaba da nema masu maganin matsalar su, in sha Allah idan suka cigaba da jarabawa za su haifi masu rai, da haka na dinga samu suna haifamin ya'ya ina sadaukarwa"



Shi wannan Littafin rijistar na fursinoni yana Wauke da sunan wanda yayi sadaukarwa da bayanansa, da kuma sunan waWanda ya sadaukar, amma banda mutanan farko da suka fara sadaukarwa saboda lokacin ba cigaba, amma fursinonin da aka sadaukar daga baya duk na rubuta wadanda suka sadaukar da su, kuma babu wanda yasan inayin recording din nan sai Aurora, itace mutun ta farko data fara sani, tasan sirrina fiye da kowa, kuma da iznina tasani saboda kundin Yana da makulli a jikin shi, mai karfin shirine kadai zai iya buWe shi, owais in har ku ka duba littafin zaku samu saukin gano duk wanda ya sadaukar da jininsa, bayan haka nima za ku ga adadin jikokina dana sadaukar da sunayen su har ma da sunayen mahaifan su, da kuma sauran Elders kowa akwai bayanansa a ciki fiye ma da haka za ku samu a cikin littafin sai dai bansan ko za'a iya samun littafin ba tun da nasan yanzu babu Kurkukun ?addara"



Bayan daya ?arashe maganar su ka yi shiru kowa da abun da ya ke sakawa aranshi, ta wani bangaren Owais yaji dadin bayanin daya basa game da littafin saboda zai taimaka masu sosai.


"Baba a tsawon shekarun da ka ke sadaukar da jikokin ka, baka taba jin nadama ko rashin jin dadin irin azabtar da su da ka ke yi ba? Ko dan su ba kai ne ka haife su ba? Bakasan ciwon su ba"?

Murmushin takaici yayi"Owais, ba lallai ka fahimceni ba, Wallahi mugune ni, zuciyata ta ?e?ashe, ba Wigon imani ko tausayi araina, tun lokacin da aminina ya bani shawara akan in kar6i gadon iyayena da suka barmin saboda muna a hali na talauci da matsin rayuwa, gashi ana farautar rayuwar mu, bayan haka muna da burin muyi arzi?i mu daukaka a fadin duniya, a lokacin dana mayar da sihirin jikina daga nan ne, Zuciyata ta rikiWa ta koma irin ta shaidanu, sai nayi mugunta ko na zalunci wani nake jin dadi.."


owais da ke sauraron shi, jikin shi yayi sanyi lakwas.


"Ina son Ya'yana fiye da kaina, fiye da kuma komai na duniyar nan, amma Jikokina da nake sadaukarwa ban taba danasani ba, Sai akan Yaro Waya wanda banyi niyar sadaukar da shi ba, na kuma yi danasanin sadaukar da shi, saboda bada son raina ba, tsantsar son da nakeyi masa ne Yaja mashi! Kowa yasan cewa kaine jikan da na fi so, a zahirin rayuwa, amma a baWini, son da nake masa yafi na sauran jikokina harya zarce son da nake ma ya'yan cikina, tunkafin a haifesa nake jiran zuwan shi duniya saboda Allah ya jarabceni da son shi, kuma tunkafin a haifesa nasan cewa shi ne magajin kurkukun kaddara, Nasan za ka yi mamaki, amma ni kowani Wa da ya'yana zasu haifa sai nayi duba akan shi don insan menene acikin matayen su, a canada aka haifesa, a asibitin Family din aurora, lokacin da mahaifiyarsa ta haife shi, for the first time da nayi tozali da shi sai da na razana, ganin ya ma wuce yadda nake tsammanin shi..."


"Wanene"? Ya tambaya yana duban shi.


"Hmmm, ko ban fada ba, nasan ka san wa nake magana akan shi, auraro ta fada maka ko ba haka ba" jinjina mashi kai ya yi.


"Amma naji kace shi kaWaine zai iya gadonka sihirinka meyasa? Kuma me hakan ke nufi"


"Owais, ilmin mu ne na matsa fa, abun bin jini ya ke yi, tun da ga kaka da kakanni, bakowa ne zai iya hawa karagar mulkin Elder ba, dole sai wanda kaddarar ta fadamawa ba.."



"Ina neman ?arin bayani akan Sauran yaran, ?addarar Kurkuku da Bugun Zuciyar Kurkuku? Tayaya akai kuka za6e su a cikin fursinoni, kuka basu mukaman nan, Kuma kuka dau?a?a darajar su fiye da sauran prisoners din, sannan kuma saida Zuciyar Batool za'a iya dawo da ran kurkukun kaddara abun ya Waure mun kai na"!


Murmushi Elder yayi"tun kafin a haifesu muke jiran su suma.."


Wan zaro ido Owais yayi.


"Nasan za ka yi mamaki, mu matsafan kurkukun kaddara munsan da akwai yara da za'a haifa wadanda zasu zo da wata baiwa wadda zai yi wuya asamu mai irin ta a duniya, amma bamusan ta ina zasu 6ullo ba, abu Waya da muka iya ganowa a duban mu, shine za'a haife su a Waya daga cikin family din Elders"


"Kuma cikin ikon Allah hasashen mu Ya zamana gaskiya, ni aka samu Waya a family dina, musa Kuma aka samu biyu daga family dinsa.. "

asannu Baba Obie ya fayyace masa komai.


Yaji dadin bayanin nan sosai.


"Zaka iya tuna wani Wan Jarida da kuka kashe a lokacin baya, shekara bakwai da suka gabata"?

"Meye sunan shi?

"Uzair Abdallah buzu, Wan uwan Zaheer Tajuddeen wanda ayanzu ina tare da shi kuma nasan kasan shi..."


A ta?aice Chief Owais ya maimaita masa labarin don ya tuna masa.


?yal?yacewa baba Obie yayi da dariya kamar fa ya fara zaucewa


"Owais ?wa?walwata bata mantuwa, tun da ka fadi sunan shi na tuna shi, nasan mahaifin Unaisah, da Wan uwansa Uzair, Yan jarida mazauna garin Jos, ya'yan wa da kani, Taj yana zaune a gidan Uncle dinsa abdallah mahaifin Uzair..."

da mamaki ya ke kallonsa jin yadda ya iya ruke komai.


"Inaso nasan ainihin abun daya faru? Tayaya kuka gane Uzair Yana yi maku le?en asiri har kuka kona shi a cikin motar shi?


Numfasawa yayi kafin a tsanake Ya soma labarta masa..

"Doka ce duk wanda yayi mana le?en asiri ko yasan sirrinmu sai mun kashe, idan bazan manta ba, Mun kama Uzair Yana yi mana le?en asiri agidan gonar mu dake a joss, a lokacin Muna tsaka da tattaunawa game da kurkukun ?addara, karfe wani abu na dare, Yaje da camera Yana daukar mu batare da sanin mu ba, kuma a lokacin bamu boye fuskokin mu ba, Yagan mu kuma yaji komai da muke aikatawa, kwatsam Musa ya hango hasken camera din shi.

ya fada mana akwai wanda keyi mana leken asiri, kuma ya dauki video din mu.

Dayaji mun gane akwai mutun sai yayi saurin shigewa motar shi, Ya bata wuta, muka bishi a cikin motocin mu tare da bodyguards din mu.


Da muka ga zai iya tsere mana, sai nayi amfani da sihirina gurin sarrafa motarshi, burki ya ?wace mashi, motar ta bugi bishiya ta tsaya cak ta kashe kanta, yana ta ?o?arin Ya tada motar ta?i ta shi.


Cikin sauri Ya buWe motar ya fito da niyar ya gudu sai dai kash tuni mun kewaye Motar shi, yabi ya rude, hankalinsa Ya tashi Ya dinga rokonmu akan mu kyalesa Ya tafi zai fita a harkar mu, bazai tona mana asiri ba, a lokacin munyi mamakin ta yadda haryasan sirrin mu, muka tambaye shi meyasa yake mana le?en asiri? Kuma tayaya akai yasan inda muke har yazo? Bayan haka dame dame ya sani agame da mu?


Cikin rawar murya yace ya kai ziyara gidan gonar babansa da marece har dare yayi masa acan, yana akan hanyar dawowarsa ne yaga motocin mu suna shiga cikin dajin dake a kusa da gidan gonar, al'ajabi ya kamasa yayi ta tunanin su wanene a cikin motocin? Me zamuyi da tsakar dare a cikin daji a irin wannan lokacin, shine sai yabi mu don ya gane ma idonsa, yayi ta bin mu har yaga lokacin da muka shiga gidan gonar mu, Yabi bayan mu har yaga abun da muke aikatawa a sirrin ce, a lokacin daya bamu labarin bai bayyana mana cewa bashi kadai ne yasan sirrin mu ba, sai ya boye mana.


Na mi?a masa hannu nace ya bani Wayarsa, bai musa mun ba, jikinsa na 6ari Ya bani, dana duba sai naga babu abun da ya dauka, na tambayesa ina videon daya dauka namu, yace min bai yi saving ba, nace masa kada ya yi mana karya, in har yanason ya tsira da ranshi, Ya faWa mana gaskiya, Amma ya kafe akan bakansa, mun fahimci yana da kafiya da taurin kai, musa daya zuciya yace"mu kashe shi kawai" dan iya yace"a'a kada mu kashe shi, saboda idan muka kashe shi, ba zamu iya sanin sirrinmu daya sani ba, zai iya yiwuwa bashi ka Wai ya sani ba, wata?il ya tura ma wani.

Daya ki faWa mana gaskiya, Musa ya dauko galon din fetur abayan motar mu, ya fara masa barazanar zai kona sa in har bai sanar damu ba.

Bawan Allan nan, ya razana jikinsa ya kama kerma.

Unexpected muka ga ya yanke jiki ya faWi.

Da muka dudduba shi sai muka gane firgicine yayi silar da zuciyarshi ta buga ya mutu, bamu ji dadi ba, mun so Ya fara fada mana kafin mu kashe shi da kan mu, musa da yafi mu zuciya ransa ya baci, Ya Wau?i gawar Uzair ya zaunar da shi a mazaunin driver, Ya rufe motar, kafin Ya soma zazzaga mata fetur, kwatsam sai ga kira ya shigo wayar Uzair dake a hannuna, dana duba screen din wayar sai naga sunan dan uwana, aminina ya bayyana, Musa ya kar6e wayar daga hannuna ya Waga kiran da yaji muryar wani yana kira sunan shi, shine yace mishi idan yana son sanin meke faruwa ya maida kiran video call.

Bayan da suka maida video call, daya tabbatar dan uwan nasa na kallon komai ta screen din wayar, sai Ya karasa zazzagawa motar fetur, Ya cinna mata wuta.

Daga bisani bayan ya katse kiran, muka binciki wayar Uzair din anan ne muka ga firar da su ka yi ta whatsapp chat din su, akan leken asirin da su ka yi mana lokacin da muka handame wani malamin ahlis sunna da ya'yansa, Taj ya nuna kin amincewarsa akan bin diddigin mu, amma Uzair Ya matsa number akan saiya gano su wanene mu don ya fallasa asirin mu.

Da muka ga haka, sai muka yanke shawarar zuwa gidan Taj, Don mu kashe shi, tunda mun fahimci shima yasan sirrin mu.

Bamu tsaya bata lokaci ba, muka garzaya unguwar da taj Yake, adaidai Lokacin da motocin mu suka shiga layin muka hango motarsa yayin da ya ke kokarin guduwa, aguje muka bi bayansa..."


girgiza kai chief owais yayi, idanunsa suka cuccuko da kwalla.

"Kaji yadda komai ya faru, mu bamu san Taj yana araye ba, ai da tuni mun kashe shi, mun dai san Yarsa tana araye, bayan da muka cinna masa wuta, bamusan tare da yar sa ya ke ba, sai daga baya muka gano cewa tare da yarsa Ya gudu, hankalin mu ya tashi, muka fara nemanta, cikin sa'a muka gano tana araye, hannun Fulanin daji, muka cigaba da bibiyar rayuwarta, har zuwa lokacin da muka Wauke ta.."

ya ?arashe labarin tare da sadda kan shi ?asa cikin nadama da takaici.

Shiru su ka yi na wani lokaci, babu mai magana a cikin su.

Owais ya zaro wayarsa Ya kira cook Winsu Ya umarci a kawo mashi lunch a cell din kakansa.

Jim kaWan Jenior agent Ya shigo da madaidaicin tray mai dauke da kayan abinci ya ajiye a tsakankanin su.


"Nasan kana jin yunwa"


girgiza kai yayi"a halin yanzu owais, babu abun da nake jin daWinsa, ko naci Waci zanji"

"Ka daure ka ci, dan Allah"


"In har zaka bani abaki kamar yadda ka sabamin lokacin da kana yaro zanci ." bai musa mashi ba, da ya ke yaji dadin hadin kan daya basu, komai ya tambaya yana amsa mashi, hakan Yasa shima Ya Wan faranta masa.

Abaki ya soma bashi yana ci suna fira.

"Malaman Jazuli, tayaya akai kuka kama sa yana maku leken asiri? Naji ka ambaci sunan shi, nasan komai game da labarinsa, sheikh imam ne Ya fadamin.."

a takaice ya fayyace masa komai.

Murmushi baba Obie yayi"Allah sarki sheikh imam malik, ashe dama da biyu ya shiga jikina ban ta6a ganewa ba, Allah ya taimakesa da tuni shima mun kashe shi.." ya faWa yana dan girgiza kansa.

"Malam Jazuli, tun ranar da yaje suka hadu da dan iya agidan gonar mu, akan maganar sadaukarwar da zaiyi, kallo daya dan iya yayi masa ya gane basaja yayi don ya shiga jikin mu, amma sai bai nuna masa ya gane komai ba, har sukayi sallama Ya tafi, arana ta biyu dayazo yi mana leken asiri cikin rashin sa'a dan iya yajiyo kanshin mutun bare a gurin da muke, anan ya gane akwai mai bibiyar mu yana mana leken asiri, amma bamu iya kama shi ba, Harya tsere mana, sai dai abun da baisani ba, mu matsafa ne, idan muka so da sihiri zamu iya ganin komai daya faru abaya ta madubin tsafin mu, ta haka muka gane wanene shi.

Da farko bamu yi niyar kashe shi ba, Na kirasa awaya na gargaWesa akan karya kuskura Ya fitar da sirrin mu, Ya manta da abun daya gani, ya fita sabgarmu, In ba haka ba, zamu dauki mataki akansa.." da budar bakinsa sai cewa yayi"ta Allah ba tamu ba, bai fara don ya tsaya ba, mu bamu isa mu sa yaji tsoron mu ba, Da Allah ya dogara, mu zaija ma kunne muji tsoron Allah mu daina ta'addancin da mu ke yi, Idan ba haka ba zai tona mana asiri.."

A lokacin nayi ?o?arin shawo kansa Yaki saurarena saima Ya kashe


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login