Showing 1 words to 3000 words out of 359620 words

Chapter 1 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1949

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️


BOOK 3 kuma shine na karshe.

*Ya Ubangiji ina rokonka da kasa kamar yadda na kammala book 1 da 2 lafiya, ya Allah ka bani aron lokaci da dama na kammala book 3 ɗin ma lafiya, Alhadulillah Alhadulillah Alhadulillah, a ko da yaushe ina kara godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ni'imar da ya yi mani, ina alfari da baiwar da ya yi mani, sannan ina matukar farinciki da hakan, ya Ubangijin kuskuren da yake a cikin wannan ɗan littafin, ya Allah ka ya fe mani shi, Allah ka bamu ikon ilmantarwa, wa'azantarwa, faɗakarwa, har ma da nishaɗantarwa*.

*Ina miƙo sakon jinjina ga jajirtattun iyaye na waƴan da suka tsaya kai da fata wajen ganin sun bamu ilimi mai albarka mai kuma amfani, sun inganta rayuwar mu, ina matuƙar alfahari da iyayena, haka zalika ƴan uwana, masoyana kai harma da makiyana, domin kuwa makiyi da munafiki, mahassadi, sune ke kara cicciɓaka izuwa sama*.

*To ƴan Group na ƴan amana kuma ban manta da ku ba, saƙon jinjinarku na daban ne, masu yi mani comments kullun ba su gajiya, suna kara mani karfin gwiwa, Alhadulillah, Alhadulillah, ba zan taɓa mantawa da ku ba a rayuwata, ƴan paid group kuma ina godiya, masu danna likes ina godiya, marasa dannawa ma ina godiya, Allah Ubangiji ya bar zumunci mai ɗorewa*.

GARGAƊI!! DA BABBAR MURYA!! BAN YARDA BA, KUMA BAN AMINCE BA WATA, WANI, SU KARANTA MANI LITTAFI SU MAI DA SHI AUDIO!! SANNAN DUK WANDA TA KARANTA MANI LITTAFI BA TARE DA TA BIYANI HAKKINA BA, TO ALLAH YA ISA, KUMA SAI ALLAH YA SAKA MANI, IDAN KINA BUƘATAR KARANTA LITTAFI NE GA NUMBERTA 0816 139 0581KI BIYA KI KARANTA HALAK ƊINKI!!.


💋STORY and WRITTEN by FATEEMA ZAHRA MUSA.....✍️💋


E1💋


A zafafe ya ɗago kansa yana mai juyo da idanunsa akan wayar tasa da ta faɗi kasa, tsabar tsorata da fargaba tare da faɗuwar gaba yasa numfashinta ya ɗauke diff, ta yanke jiki ta sulale kasa sumammiya.

Tana sulalewa kasa kuma ya yi daidai da dawo da kallonsa kanta da ya yi da nufin ya ɗauketa da wani gigitatcen mari, ganin ta sume yasa ya ciza laɓɓansa rai a ɓace ya miƙe ya fice daga cikin ɗakin, domin ba yadda za'ayi ya daki gawa, e gawa mana, wadda yake sume ai kusan gawa ne, idan ya ce zai daka ma, me zai daka a wajen? Amma ba haka ya so ba, ya sone ya bata lafiyayyen mari da zata sanyata ganin wuta na ci bal, bal, bal, a cikin idonta, domin yau shi ne karo na biyu tana buge mashi wayarsa yana faɗuwa kasa, cox ya kamata a wannan gaɓar ya hukuntata da kyau dan ta kiyayi gaba.

Yana fita ya nufi fridge dake a cikin Palon saman domin bai kunna fridge na ɗakinsa ba tun jiya, saboda baya jin daɗi baya shan ruwan sanyi sosai.

Ruwa ya ɗauko mai bala'in sanyi gora ɗaya sannan ya juya ya koma bedroom ɗin nasa, yana taku irin na cikakkun jaruman maza, masu lafiya tare da jini a jika.

Yana shiga kuma shi ma Areef yana shigowa, a kanta ya tsaya tare da ɓalle bakin robar ruwan, yana daga tsayen ya zazzage mata gaba ɗaya ruwan sanyin nan a kanta, wani irin firgita ta yi tare da tashi a razane tana kurma ihu.

Rai a matukar ɓace ya sanya kafa zai yi ball da ita kamar kwallo, tattare iya karfinsa dukka Areef ya yi ya shagabansa tare da riƙe kafar tasa, ko kaɗan babu tausayi a fuskar Lion ɗin, dan buge mashi waya da ta yi a karo na biyu yafi kona mashi rai sama da komai.

Hannu yasa ya hankaɗe Areef ɗin in da ya yi baya baya zai faɗi a saman table glass dake a tsakiyar wajen.

Cikin zafin nama ya sanya hannu ya riƙo wuyar rigar Areef ɗin, dan kada ya faɗa saman table ɗin, ya san idan har ya faɗa a saman table ɗin to tabbas fashewa zata yi, idan kuma ta fashe ba ƙaramin ciwo zata ji wa Areef ɗin ba, hakan yasa ya yi maza ya riƙo shi, duk fa wannan abin da suke yi Rimsha na a tsakaninsu, har lokacin bata ma dawo cikin hayyacinta ba, sai sambatu take yi tamkar wadda ƙwaƙwalwarta ta taɓu.

Riƙo rigar Areef ɗin nan da ya yi ba karamin famawa Areef ɗin ciwon dake a kirjinsa ya yi ba, domin kuwa yadda ya damko wuyar rigar ya haɗa da bandeji wadda aka sanya mashi a inda aka cire mashi bullet ɗin da Lion ɗin ya harbe shi, da yake a kafaɗa ne ta gefen wuyarsa, idan ba ku manta ba, to bandejin tana da ɗan girmar da ta zo mashi har a wajen wuyarsa, hakan yasa da Lion ya damki wuyar rigar ya haɗa da bandejin ya ja wo shi, hakan kuma ya yi sanadiyar ɓarewar bandejin ma gaba ɗaya, ba abin da suka gani sai jini da ya fara zuba yana bin cikinsa har yana zuba a kasa.

Shi kuma Areef wani wahalallen ihu ya saki tare da sake jikinsa gaba ɗaya yana ƙoƙarin faɗuwa kasa, a zafafe cikin zafin nama Lion ya jawo shi jikinsa gaba ɗaya dan kada ya faɗi.

Ɗan duƙawa ya yi tare da saɓar Areef ɗin a kafaɗarsa ya take ƴan yatsun Rimsha dake a tsakaninsu ya bi ta kai ya wuce ya nufi waje.

Ihu azaba ta saki tare kuma da dawowa cikin hayyacinta, dan ba takun wasa ya yi mata ba, idan kuma baku mance ba hannun nata akwai ciwo na chemical da ya sanya mata jiya, ta sha bakar azaba kuwa, domin wannan take ta da ya yin har jini wannan tsage tsagen da hannun nata ya yi wajen ya yi, sai wani irin wahalallen kuka take yi kasa kasa, ga shi kuma tana jin yunwar safe daman.

Ta ɗauki almost 10 mins a haka kafin daga bisani ta yunkura da kyar da makyarkyata ta miƙe, godiya ta fara yi ga Allah da ya tsareta, ya sanya Lion bai hukunta ta ba, sannan kuma ta fara ƙoƙarin tattara mashi ɗaki da sauri sauri kada ya zo ya taddata bata gyara ba.

Shi kuwa yana fita ɗakin Areef ɗin ya wuce da shi, a in da ya je ya fara ba shi agajin gaggawa, kwata kwata ya mance da wata Rimsha, burinsa kawai ya yi dressing na wannan waje da ya fama ta da kansa, sai famar cizar lallausan laɓɓansa yake yi, gaba ɗaya idanunsan nan sun riƙeɗe sun yi ja alamar bai ji daɗin fama wannan ciwon da ya yi ba, domin kuwa idan ba ku mance ba, ba shi da wani burin da ya wuce ɗan uwan nasa ya sami lafiya, kullun fatarsa da addu'arsa kenan, hakan ya sa ya ji babu daɗi sosai.

Ita kuwa tsab ta gyare komai tare da tattare komai ta fitar waje, sannan ta dawo ta ɗaga mashi wayarsa ta ɗaura saman sofa, sai kuma me? Tsayuwa ta yi tana tunanin ya za'ayi ta zubar mashi da abin ci, me kenan zai ci yanzu? Ya ilahi ya lillahi, ga shi bata isa ta je ta ce Mark ya yi wani girki ba, wannan mai fuskar shanun wadda take mutuwar tsoron nasa, ai bata ga fuskar cewa ya yi wani girki ba ma, to kenan yanzu ya zata yi? Kuma dai ta ji Areef ya ce ba su cin abinci a waje, ba su iya cin abincin restaurant ko makamancin shi ba, sai na gida, yanzu sai yaya kenan?.

Duk jikinta ya yi wani la'asar kamar an zare mata laka, haka ta juya ta fice daga ɗakin ta nufi nata ɗakin, fuskarta gaba ɗaya ya yi jaga jaga da busasshen hawaye, gaba ɗaya dara daran sleeping eyes nata nan sun kumbura sosai saboda uban kuka da ta ci, kuma idanun nata sun ƙanƙance sosai da sosai saboda kukan.

Tana shiga ɗakinta ta haye saman gado tana mai cigaba da furta hasbunallahu wanimal wakil, domin Allah ya kawo mata ɗauki, wannan addu'a ce wadda tana da sauƙin faɗe, kuma gata da babbar aiki, Annabi Muhammad (SAW) da bakinsa ya ce duk girman musifa da bawa ya shiga, matukar ya lizimci faɗin hasbunallahu wanimal wakil ko kuma ya hayyu ya kayyum to fa tabbas Allah zai ya ye mashi wannan musifa da yake a ciki, yawan yin istigifari wato astagfirullah waatubu ilai, yana da tasiri sosai wajen bunƙasa niimomi Ubangiji a tattare da bawa, kada ka je ka ce wani ko wata su maka addu'ar samun arziki ko kuma ka je wajen wani boka neman maganin arziki, ga maganin arziki nan wadda ko kana kwance ka yi shi zaka samu kofofi na ni'imar Allah ba adadi su buɗe maka, kaci halak ɗin ka, idan shago kake da shi a kasu wa to maza ka lizimci yin istigifari, In Sha Allah zaka ga buɗi, a lokacin da aka yi kwana uku a gidan annabi ba'ayi abinci ba, wata ruwa ta ce kwana uku, wata kuma ta ce wata ɗaya, to bari dai muyi amfani dana imamu Malik, kwana uku ba'ayi abinci ba a gidan Annabi, wannan zikiri annabi ya lizimci yi Allah ya buɗa mashi cikin ƙanƙanin lokaci, so Allah ya jarabci annabi ta hanyoyi da dama ba dan komai ba sai dan mu samu magungunar cutukar da suke damun mu a yau, idan mutun ya natsu ya fahimci tarihin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da kyau, zai gane cewa tabbas wa su abubuwa da suka faru da annabi, Allah ya yi hakan ne domin Allah ya fitar mana da mafita da maslaha, kamar dai yadda Allah ya fitar mana da mafita akan sihiri da tsafi ta hanyar bawa sheɗanu dama suka yi galaba akan Annabi, suka yi mashi asiri ta kama shi, a nan ne Allah ya saukar mana da maganin da Mala'iku suka karantawa annabi ya warke, idan zaka karanta shi, to tabbas ba dai ɗan adam ba sai dai Allah wlh, da zarar ka riƙesu to ka fi karfin wani matsafi ko boka, Aljani, dabbobi masu cutarwa, da sai sauransu, fatan mu dai shi ne Allah ya ba mu ikon yi Amin.

Wannan addu'a kuma da zaka karanta domin samun kariya daga matsafa, tsafi, sharri da komai da komai ba wani mai wahala bane face (Suratul Ikhlaash) kulhuwallahu ahad kafa uku, Suratul Naas kafa uku, sai Suratul Falaq kafa uku, sannan ku rufe da Ayatul kursiyu kafa ɗaya, kowani bayan Sallar farillah idan kayi, in ma azahar ne ko la'asar, mangariba or isha'i au asuba'i fatan mun gane?.

MACE MAI CIKI, WANNAN MAGANI NE DAGA MANZON ALLAH SALLAHU ALAIHI WASALLAMA WADDA NANA MARYAM MAHAIFIYAR ANNABI ISA ALLAH YA CE TA YI AMFANI DA SHI DAN SAMUN HAIHUWA CIKIN SAUƘI, IDAN KINA DA CIKI, CIKIN NAKI YA KAI WATA BAKWAI, TO KI LIZINCI CIN DABINO A KULLUN, IDAN DA SON SAMU ME KI CI GUDA BAKWAI KO WANI SAFIYA KAFIN KI CI KOMAI, DA IZININ ALLAH ZAKI HAIHU BA TARE DA WATA WAHALA BA, BA ZAKI SHA WAHALA BA, ALLAH KUMA ZAI BAWA KE DA ABIN DA ZAKI HAIFA LAFIYA DA IZINSA, ANNABI YA BAWA MATA DA DAMA WANNAN MAGANI, DAN HAKA A CIKIN ILIMIN DA ALLAH YA BANI NIMA NA BAKU ƊAYA DAGA CIKI, IDAN KIN JI DAƊI KI YI MANI ADDU'A DA FATAN ALKHARI TARE DA FATAN NASARA A RAYUWATA DA IYAYENA, INA GODIYA. IN SHA ALLAH MAGUNGUNAR MUSULUNCI IRIN HAKA ZAN RINƘA SAƘO MAKU SHI IYA ILIMIN DA ALLAH YA BANI, DAN KUMA KU KARU, IDAN KINA DA WATA TAMBAYA KI YI MANI ITA KAI TSAYE, KADA KI JE KINA TAMBAYAR WATA, NI NA RUBUTA MAGANIN, NI ZAKI TAMBAYA, ALLAH YA BA MU DACE WA. 09262620621 Shine numberta Ma'assalam.✍️

Story

RIMSHA

Wani irin barci ne mai shegen daɗi ya kwasheta, sakamakon samun natsuwa da ta yi saboda addu'ar da ta rinƙa yi tare da ambatar sunayen Allah. Baiwar Allah a cikin barcinma sai sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya take yi, yau ta ga karfin addu'a iya ganin idonta, domin kuwa ba dan addu'a da ta rinƙa yi ba, to wlh da sai dai a ɗauki gawarta yadda yau ta yi mashi laifi sosai ɗin nan.

A ɓangaren su Jelly kuwa, wato gidan Abbi, zaune suke a palon kasa ita da Hanan, yayin da ita kuma Aunty take faman shirya abinci a saman table, Ayla kuwa tana wajen mijinta domin jiya ta ci bakar wuya a hannunsa, wadda ya ja mata zazzaɓi mai zafi, hakan yasa bai bari ta fito ba, ya zaunar da ita yana jinyar kayarsa.

Sai kallo suke yi, ɗan kwana biyun da jelly ta yi har ta koyawa Hanan kallo, jelly shugaba ce a iya kallon Film, ta kware sosai da sosai, duk wasu Indian music ta iya su sanka sanka, ga shegen son rawa kamar wata jikar Michael Jackson, kuma ta iya rawar sosai, sannan kuma bata da ƙiba ne yasa bata jin hauyin jikin tata take takawa son ranta, tana bawa jikinta a jikinsa shi ma.

A haka Hjy Batula ta shigo palon ta same su, ta yi wanka ta ci wani haɗaɗɗe kuma tsadadden lace black color, ɗinkin bubu gown, da yake dai gaba ɗaya familyn su daddy kyawawane tamkar wasu turawa or larabawa, haka suke, kuma gidansu two colors ne, akwai farare tas kamar turawa, sannan akwai chocolate color, Abba dai farine tas haka ita ka Hjy Umaiya, amma kuma Imran chocolate color ne irin Rimsha, to haka a gidan Abbi ma, Aafia da Irfan chocolate colors ne, saɓanin Umaisha da take fara tas Kamar ka taɓa ta jini ya fito, kun ga ita ma JEHAN fara ce tas kamar daddynsu, while shi kuma daddyn jelly bai yi tas ɗin ba dai, amma kuma ba chocolate color bane, shi irin farin Nigeria ne, su kuma farin waje ne da su gaskiya, da alama a cikin kakanninsu akwai Bature ko kuma balarabe, ɗaya dai daga ciki, domin kuwa wannan hasken nasu ba na nan bane, na can ne.

Sosai Hjy Batula ta fito reras abinta, saman sofar kusa da su ta zo ta zauna tana faɗin "Ke Jalila ina ɗan kwalinki?".

Turo bakin nan ta yi kamar biro zata yi magana kenan Ommu ta sauƙo kasa tana surfa uwar masifa akan su rage Volume na Tv ko kuma ta kashe Tv gaba ɗaya.

Hanan dai da yake ta san halin ta, sai ta ɗauki remote ta rege Volume ɗin, ko sannu jelly bata ce mata ba, suka cigaba da yin kallonsu, yayin da ita kuma Ommu ta juya ta koma sama dan ta cigaba da abin da take yi, yau ta yi nasarar samun number Umaisha ta hannun Hjy Turai da ta karɓa mata daga wajen Aafia, murna a wajenta ba'a magana, tuni ta kyankyasawa Umaisha abin da take buƙata, da yake uwa da ƴa, kuma babba kam ko yaya babba ne, sai bata sha wahala wajen shawo kan Umaisha ɗin ba, karya ta zuba mata akan cewa ai bata da lafiya ne, tana da ciwo a zuciyarta, aiki za'ayi mata a kasar India, Abbi kuma ya ce ba zai biya kuɗin ba, tun da mijinta yana da kuɗi, idan ba damuwa ko sata ne ta sato mata wajen shi, tun da ba zai rasa ajiye kuɗi a gida ba, ko da bai cika 10 million ɗin lokaci guda ba, ta sato da kaɗan da kaɗan, kada ta yarda ta bari ya gane, da farko Umaisha ta ce a'a zata tambaye shi dan tasan ba zai hana ta ba, yana da kyauta sosai, kuma wa su ma a waje ya yi masu bare ita da take mahaifiyarta, ba zai taɓa hana ta ba, sai dai ma ya ce ta shirya su tafi asibitin a tare, da yake ba wani asibitin da zata je karya ce kawai, sai ta sawa Umaisha ɗin kukan munafurci tana faɗin "Ta ya za'ayi ki bari surukina ya san sirri na? Yanzu so kike ki tonawa Abbinki asirin na yaki biya mani kuɗi a kaini asibiti? Wannan ai abin kunya ne, me yasa ke kam wayuya ce? Ai ba'a gayawa miji sirrin gidan iyaye, domin watara sai ya yi maki gori".

Kafe wa Umaisha ta yi akan lallai yaya Akil ba zai yi mata gori ba, saboda ai Abbin babbansa ne, nan fa Ommu ta rinƙa yi mata bayani akan ko uwa ɗaya uba ɗaya kuke da mutun ma, wata rana sai ya yi maka gori, dan haka ta daina wani zancen ba zai yi mata gori ba.

To da yake kunsan yadda ƙwaƙwalwar ta Umaisha take, Baiwar Allah ko nonon uwa bata samu damar wani sha ba, ga wahala da ta sha na tasowa a hannun maza da suka reneta, wato Irfan da Abbi, kun san dai renon Namiji da mace daban daban, hakan yasa Ommu ta yi wasa da tunaninta, tare da gwada mata ainahin bariki har sai da ta yarda ta amince zata sato mata kuɗin Akil ɗin idan za su zo gida. BABBAR MAGANA. Kuna ganin Umaisha zata ɗauki kuɗin Akil ba tare da ya sani bane? Kuɗi kuma ba kaɗan ba, lallai ba shakka Ommu tana son kai Umaisha ta baro ta. Mu dai je zuwa.

Ommu kuwa abin da ya sanya bata son Akil ɗin ya sani, saboda a baya ta yi zama da Hjy Umaiya ai, ta san Ammie akwai shegen bala'in basira sosai da sosai, ga zafin rai da faɗa, sai dai sai an taɓa ta take faɗar tata, to tana da tabbacin da wuya idan su Akil ba su ga ji wannan basira ta Ammie ba, ta san tsab zai ce ta shirya su tafi asibitin ko kuma ya gane karya take yi, shiyasa ta fito da hanyar sanya Umaisha ɗin sato mata kuɗin kawai, a nata tunanin da wawtarta ta hakane kawai zata sami biyar bukatarta.

Lallai da akwai kura kenan, tab ɗi jam.

Bayan Aunty ta gama shirya masu abincin ne ta zo ta zauna kusa da Jelly tana faɗin "Jellynmu ba karamin kyau kunshin nan ya yi maki ba". Murmushi ta yi tana faɗin "Aunty da gaske na yi kyau?" "E mana my baby jelly sosai ma kuwa".

Jelly zata yi magana kawai a ka sako wakar Sharukhan Kuci kuci hotaye, haba malam ai tuni ta miƙe tare da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login