Showing 9001 words to 12000 words out of 359620 words
kasa take da ƙiba ba ta sama ba.
Tana sanye da wandon jeans palazo blue color, da kuma riga high neck t-shirt black color, ta yi kyau sosai, kanta na sanye da ɗan karamin hijabi please call me launin blue color, kalar wandonta kenan, jikin hijabin dukka akwai stones manya manyan masu kyalli sosai, hakan ya karawa hijabin da ita kanta kyau.
Yana sauke idanunsa akanta wani irin azababben sha'awarta ne ya kama shi, kashe mata ido ɗaya ya yi tare da yi mata alama akan ta zo, da sauri ta tafi ta faɗa jikinsa tana sauƙe ajiyar zuciya.
Shima wani irin nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin nan ya zame mata Hijabin jikinta, ya ɗaura hijabin a saman mirror yana wani irin sauke numfashi a hankali hankali.
Laluɓeta ya fara yi yana ƙoƙarin capko breast ɗinta, cikin dabara ya ɗauketa sai saman gado, ya manta da cewa shirin fita ya yi, tuni ya cire kayan nasa ya hau sabuwar aiki na wucewa sama jannati..........
Takaitacciyar Nasiha garemu mata, da farko zan fara da TSAFTA!! TSAFTA!! TSAFTA!! a addinance tsabta tana daga cikon addini, a zamanance ita ce garkuwan lafiya, duk macen da bata da tsabfa tabbas kusan da ita da dabba duk ɗaya ce, bambancin kawai tunani, bai kamata kina mace ki saki jiki duk datti ba, Hajiyata mace ƴar kwalliya ce, mace da gyara aka santa, mace ƴar gayu ce, ina kara gaya maku, ke ko nawa ne Hajiya ki kashewa jikinki, in dai a fagen gyara ne, sai kaga wata mace ta zauna fatar jiki duk ya bushe kamar wani bayan kada, haba mana ƴar uwa, me namiji zai taɓa ya ji daɗi haka? Jiki kamar bayan bushasshiyar kifi, kai ina kada ki yarda ki zama guzuma, kayan gyaran nan fa ba wani tsada ne da su ba, kuma ma yafi kyau ki zauna ki haɗa kayan gyaranki da kanki a gida, kama daga sabulun wanka, man shawa masu kyau da inganci, turaruka, dilka da sauransu, kada ki rinƙa sayan na haɗawa a waje, domin kuwa suna mixing nashi da chemicals, wadda idan kika saya kika yi amfani da shi, idan suka yi expire suna kashe matar mace, suna lalata mata jiki, wani daga nan fatarta zata daina karɓar kayan gyara, to yana da kyau duk wasu kayan gyara ki haɗawa kanki da kanki, zan baku kaɗan daga cikin sirrin kayan gyara na addini musulci domin lokaci ya tafi, page na ya kai dai dai munzalin da nake Dakatawa.
Abu na farko ki sami ganyen ɗanyar lalle ta Hausa, sannan ki sami dilka, nescafe, kwai (egg) da kuma madara ta ruwa, sai lemon tsami kaɗan, sannan sai zuma and ruwan tumatir kaɗan.
Wannan ganyen lallen zaki fara daketa sai ta yi laushi ta fitar da ruwa, sannan ki kwashe ki ajiyeta a gefe, kada fa ki daka a turmi mai yaji Hajiyata, to idan kika daga a cikin mai yaji matsalarki ce, ke zaki je kina ihu Princess Teema tana kwance a gado bata san me yake faruwa ba.
Bayan kin kwasheta kin ajiye, sai ki ɗauki kwai ki fasata a wata roba daban, dukka kwan zaki haɗa har da na cikin, wasu suna cire na cikin, amma ki zuba har da shi yafi kyau, idan iya yi ɗaya ne, kwai ɗaya ya isheki. Ki kaɗen kwannan sosai, sannan ki zuba wannan dakakkiyar ganyen lallen, ki sake kaɗesu sosai, ki yi tabbatar ganyen lallen nan ya yi laushi luƙui sosai ta yadda zai haɗe da kwai ɗin.
Idan kin kaɗesu sai ki zuba madara ta ruwa, idan ma ta gari ce ta samu, sai a jiƙata, sai ta narke, sannan a zubata a ciki, ruwa kaɗan za'a sanyawa madarar, sai ki sake kaɗewa kafin ki zuba zuma da ruwan tumatir kaɗan, sannan sai a zuba nescafe, na sanyawa a tea, shi wannan nescafe ɗin kala kala ne, akwai mai kyau, akwai mara kyau, to a nemi mai kyau dan a sami biyan buƙata, a haɗesu sosai ta yadda za su game jikinsu, daga karshe sai a matsa ruwan lemon kaɗan dan a kashe karnin kwan, sannan kuma yana kashe kananan dark sport na fata, tana kuma taimakawa fata sosai wajen ganin kananan kuraje sun dai'na fita.
Idan aka gamesu suka haɗe sosai, sannan za'a iya zuba kuka kaɗan, is and optional, bayan anyi haka, sai a shafe jiki gaba ɗaya, a barshi ya yi minti talatin, ya bushe, idan ya bushe, sai ki murje jikin naki, Hajiyata tun daga kan murjewa zakiga yadda jikinki ke murjuwa, yana fitar da wasu dattin da ke kanki sai kin yi mamakin ta ina wannan datti ya bayyana.
Idan kin murje, sai ki je ki yi wanka, wayyo Allah, zakiga yadda fatarki zata koma, wani irin fresh zaki yi, ki fito luwai luwai, kina glowing Hajiyata..
Lokaci ya tafi, sai mun haɗu a wani page ɗin, In Sha Allah duk sauran wasu kayan gyara suna nan tafe, daga gyaran fatar jiki, har kan gyaran can ciki, ma'ana kayan karin ni'ima na mata da sauransu, amma fa ba alkawari na yi maku ba, idan na sami time zan rinƙa jefo maku a cikin page's ne....... Ma'assalam...✍️ PRINCESS TEEMA💋
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️
E3-4
Laluɓeta ya fara yi yana ƙoƙarin capko breast ɗinta, cikin dabara ya ɗauketa sai saman gado, ya manta da cewa shirin fita ya yi, tuni ya cire kayan nasa ya hau sabuwar aiki na wucewa sama jannati.
Can kasan maƙoshinsa ya ce "Babyn daddy ya naga kamar daddy ya yi ajiya ne?" Cikin nuna ko in kula domin bata ma san ma'anar maganar tasa ba, ta ce "Daddy ajiyar me kuma? A ina kuma kayi ajiyar?".
Miƙewa ya yi daga rumfar da ya yi mata ya zuba mata ido sosai, yana kare mata kallo, tabbas ta kara kyau sosai, amma kuma ba abin da yake tunanin ɗin bane, kawai dai kyau ne na tsantsan kula da take samu daga gare shi.
Ganin ba abin da yake tunani bane yasa ya shafa shafaffen cikinta nata tare da haɗe fuskokinsu, kasa kasa ya ce "Jelly ita kaɗai Allah ya bani, ina bala'in son yara, wlh idan na kalli yara a hannun wasu, ji nake tamkar in je in kwacesu, ya Allah ka bani baby a wannan haɗuwar tamu da zamu yi yanzu". Ya kai karshen maganar yana yana mai hauro da hannunsa zuwa saman kirjinta.
(Tofa shi kuma Romeo ba abin da ya tsana kamar yara, ga wasu kuma a nan suna nema ido a rufe, Allah ya shirya Romeo da rashin son yara)
"Daddy nima ina son yara wlh, musamman ma kanana suna da kyau kamar me". A hankali hankali ya fara shafo breast ɗin nata yana faɗin "Musamman ma idan a kace yaran sun yi kama dake ba, wlh ba ƙaramin kyau za su yi ba".
Zata yi magana ya capko bakin nata tare da zura mata harshensa cikin tata ya fara kissing nata.
Shiru ta natsu tana biye mashi, yanzu idan da sabo, ta gama sabawa da jarabarsa, tun abin yana damunta har ya dai'na, ta rungumi kaddararta na hakura da jararrabar mijin nata, sai dai kuma shi ba kamar sauran irin mazanmu na yau da kullun bane, mafi yawancin maza suna ɗauka jima'i shi ne kawai aure, shi ba haka yake ɗauka ba, tabbas yana da jarabar tsiya, amma kuma yana ƙoƙarin ya zama cikakken miji, yana ƙoƙarin ya yi koyi da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, domin Annabi har wanke wanke yana taya su Nana A'isha, Nana A'isha da bakinta ta ce har ƴar tsere suna yi da Manzon Allah (S.A.W) a gida, ya kama maza su sani ba iya biyan buƙatarsu a wajen mace, da ciyar da ita da shayar da ita ne kawai ya zamana hakki a kansu ba, ya kamata su nemi sanin tarihin fiyayyen halitta domin su samu gobe mai kyau, ga dai misali akan daddyn Jelly, yana balain kaunarta, yana kula da ita, yana faranta mata, ya mai da ta tamkar wata sarauniya, to yanzu ku gaya mani me ya ragu da shi da yake yi mata hakan? Wlh babu abin da ya ragu da shi, sai ma karuwa da ya yi na samin ɗumbin lada wajen Ubangiji, ya yi koyi da Manzon Rahma, ba ko wani namiji ne zai iya yin hakan ba, amma yana da kyau ku rinƙa kwatantawa koma yayane, domin a rage wasu matsalolin na cikin rayuwar aure, kuma, mata na juyo gare mu, yana da kyau mu gyara halinmu, misali akan Aunty, Ayla, da kuma Umaisha, irin halinsu yasa dole mazajensu ke kyautata masu, hakuri, juriya, riƙo da addini, kyautata mashi, kome ya ce matukar bai saɓawa Allah ba cene mashi to, kuma kiyi mashi a lokacin, kada ki yi gardama ko ki yi musu da shi, ki daure ki jure ki yi biyayya, ko da baki samu jin daɗi yadda kk so a nan duniya ba, ki sani a lahira zaki more, zaki huta, zaki ji daɗi fiye ma da yadda ki ke so ɗin, kada ki yarda ki yi biyu babu, babu duniya kuma babu lahira, kada ki yi koyi da irin halinsu Ommu, ki tabbatar kin yi koyi da halin ɗaya daga cikin waƴan nan Aunty, Ayla, ku kwatatan ku yi tunanin me yasa mazansu ke kyautata masu? Meyasa suke kaunarsu? Saboda sun nunawa mazan nasu cewa sune sarakunansu, sune sama da su, ko wani namiji yana son girmamawa, dan haka mu gyara, Allah Ubangiji yasa mu dace.
STORY💋
Sosai ya more kayarsa ko in ce suka mori juna, domin kuwa yanzu ita ma ta kware sosai, ya koya mata, ta zama irinsa.
Sun jima kwance manne da juna yana zuba mata kalamai tare da shagwaɓa kamar wani yaro, ya zama tamkar ƙaramin yaro a gaban matar tasa, ba ya wani damuwa da zancen zata raina shi, dan yasan ba haka take ba, shiyasa yake zuba mata shagwaɓarsa son ransa, kuma da yawan maza ba wai basa son yin hakan da matansu bane, kamar yadda na faɗa a baya, gani suke yi kamar idan suka yi hanan da matan nasu, matan za su rainasu, wannan dalili yasa suke tsare gida abinsu, wani ma da ya fara hakan sai ta fara ce mashi ragon namiji, to ƙalu bale garemu mata, ko yau a ka haifi namiji to fa sama yake da ke, ko da kuwa kin kai shakara hamsin, Ubangiji ne ya fifitasu akan mu, mune a kasarsu, ba lallai sai miji bama, ko wani irin namiji sama yake da mace, to ina ga kuma ance mijinki? Wadda shi ne Annabi ya ce, da bawa yana yi wa bawa sujjada, to da tabbas zai yi wa mace umarni ta rinƙa yi wa mijinta domin girmamawa, tabbas Allah ya girmama miji sosai akan mata, ko me miji zai yi maki bai kamata magana ta raini ta shiga tsakaninku ba, tun da Ubangiji da kansa ya bashi wannan girma da kuma power, yana da kyau mu kula da hakan dan kada mu zo duniya a banza kuma mu koma a banza, Annabi ya ce mata sunfi yawa a wutar jahannama, wannan magana kuma kunsan tabbas haka ne, innalillahi wa inna ilaihir rajiun......😭 Ba kuma komai ne yasa mata suka fi yawa a wutar jahannama ba fa ce kin bin umarnin mazajensu, zagin mazajen da kuma rainasu, hakan yasa suka fi yawa a wuta, to dan Allah mai karatun littafi na, kada ki bari ki zama ɗaya daga cikin irin waɗan nan mata, nasihata a gareku shi ne, ku yi hakuri ku daure ku danne, da ki cuci mijinki, wlh gwara shi ya cuceki, kuma ki yi wa Allah ki yafe mashi tare da yi mashi addu'a shiriya, tabbas Allah baya barci, yana ganin komai da yake faru, sai ki ga sanadiyar yafe mashi da kika yi, Allah ya baki gidan aljanna ko da kuwa baki yi aikin shigarta ba, to dan haka ina mai mana nasiha akan hakan, sannan kome zaki yi ki tabbatar domin Allah zaki yi, dan ki samu wannan rabo ta ni'imar Allah, idan ki ka yi domin wani, to ki sani wanin bashi da wuta kuma bashi da aljanna, to is better for you ki yi domin mai wuta da aljanna, dan ki shiga cikin aljannar, Allah Ubangijin ya sa mu dace, ya kuma bamu ikon gyara kura kuran mu, ina kara jaddada mana, muji tsoron Allah, a duk in da muke, mu san Allah yana ganin mu, kuma mutuwa bata da tabbas, tana iya zuwa a ko da yaushe, tana iya ɗaukarki kina tsaka da cin abinci ko aikata wani abin, ace mutuwa ta ɗauki mutun yana aikata saɓon Allah, ina zai tsaya da wannan bala'in,. Akan abin da kika mutu za'a tasheki, kada ki manta a ranar gobe kirayama tabbas ba ke zaki yi magana ba bare ki yi karya, hannun da kika aikata sharri ko alkhairi, shi ne zai yi magana da izinin wadda ya halince shi da mu baki ɗaya, shi zai faɗi abin da kika aikata da shi, haka zalika sauran sassa na gaɓoɓin jikinki, to dan haka mu kiyaye, fatana shi ne mu gudu tare, mu kuma tsira a tare, Allah kuma ya sa hakan Amin, ba zan so ace mai karanta littafi na ta kauce hanya ba, zanji zafin hakan fiye da tunanin mai tunani. YA ALLAH KASA DUK MASU KARANTA BOOKS NA, SU KASANCE NA KIRKI DAN KA HAƊA MU A ALJANNA, IDAN MA AKWAI WANI HALI MARA KYAU DA SUKE YI A ƁOYE, YA ALLAH KA YAFE MASU, KASA SU GYARA DOMIN MU KASANCE A TARE A ALJANNA, INA SON MASU KARATUN LITTATAFAINA💘💋❤️.
STORY💋
Sai da ya ga ta fara yi mashi barci a jiki sannan ya ce ta tashi su je su yi wanka, make mashi kafaɗa ta yi, cikin shagwaɓa da magagin barci ta ce "Ni barci nake ji daddy".
Shafa kanta ya yi yana faɗin "Babyn daddy, ki hakura na yi maki wanka sannan ki yi barcin ko? Bana son ki yi barci da najasa a jiki, Annabi ya tsawatar akan hakan, ya hanemu da hakan, domin hakan babbar barazace ga lafiyar ɗan adam, idan bawa yana cikin najasa fa to komai yana iya faruwa da shi baby, ciki kuma harda asiri, tsafi, aljanu, shaiɗanu, da dai sauransu, dan haka ki daure daddy ya yi maki wanka, in yaso sai ki zo kiyi ta barcinki har sai time da kike so, ni kuma zan yi zaman jiranki har sai kin tashi daga barcin sannan mu fita unguwar ko?".
Duk jikinta ya mutu da jin nasiharsa, hakan yasa ta miƙe, jikinta duk a mace saboda barci, haka ta diro kasa daga saman gadon, sannan suka nufi toilet.
After some minutes, ya fito riƙe da hannunta suka nufi gaban mirror, dukkansu suna ɗaure da towel, da alama dai a tare suka yi wankar.
Lotion ya shafa mata kafin nan ya sanya mata kananan kayanta tare da fesheta da perfume nasa masu daɗin Kamshi, sannan ya ruƙo hannunta suka wuce saman gado yana faɗin. "To jeki kwanta bari na shirya na zo mu kwanta sai zuwa anjima mu fita ko?".
Gyaɗa mashi kai kawai ta yi kafin ta wuce ta haye saman gadon, shi kuma, ya wuce ya nufi gaban mirror dan ya shirya.
Kafin ya gama shiri ya dawo, har ta yi barci abinta. Kusa da ita ya zo ya kwanta yana fuskartar sama, kamar mai yin wani tunani.
Can kuma kasa kasa ya furta "Ina son sanin su waye iyayenki? Ina son sanin a ina suke? Meyasami babanki? Meyasa mamanki ta rayu dake cikin kunci da wahala duk da cewa ta ce mahaifinki yana da kuɗi? Ina buƙatar waƴan nan amsoshi wadda kuma nasan mamanki ce kawai zata iya bani su!".
Shiru ya sake yi yana mai jin tsantsar kaunarta yana kara ratsa shi, tabbas yana bala'in kaunarta, amma kuma yana tsoron samun haihuwa da ita ba tare da ya san tushenta ba, in fact a matikar tsorace yake a duk lokacin da ya haɗa jiki da ita, jarabace kawai irin tasa yasa yake kusan tar ta ɗin, domin kuwa yana ji a jikinsa tabbas tana da alaƙa da su mummyn jelly, damuwarsa ɗaya kada ya kasance wadda ta haramta ne a gare shi ne, yasan mumyn jelly bata da ƙanwa, to yaya abin yake kenan?.
Da wannan tunane tunane barci ya kwashe shi, sai wani sauƙe ajiyar zuciya yake yi cikin barci, ita kuwa, Baiwar Allah, cikin kwanciyar hankali take zuba barcinta, numfashinta na fita a hankali.
GIDAN ABBO.
Tun da suka isa gida, Aafia ta kasa sakin jiki da su, sai wani ƴan kame kame take yi, ba yadda Ummi bata yi ba, amma ina, A'AFIA taki yarda ta saki jikinta, da suka ga haka, sai suka kyaleta, ɗakin Jelly Ummi ta kaita kafin ta dawo ta fara sallamar ƴan biki, shi kuma Nawid ɗakinsa ya wuce abinsa, ya je ya yi wanka ya kwanta yana tunani irin auren da aka yi mashi, gabaɗaya ya mance da zancen Abbo, ita ma Ummi bata kara tambayar ina Abbo ɗin ba, bata kara neman numbersa ba, abin kamar ba lafiya ba, duk sun mance Abbo kam.
Gabaɗaya jama'ar da suka zo bikin Ummi ta sallamesu akan anriga da an ɗaura aure an wuce wajen, taki nunawa bakin waje Aafia, ƴan uwanta kawai ta nunawa ita tare da yi masu bayanin abin da ya faru na canjin Amaryar da aka yi, ba karamin daɗi suka ji ba, sun kuma yi alkawarin zasu yi gangami suje su gaishe da Abbi, sannan su yi mashi godiya, sosai Ummi ta ji daɗi, amma kuma har yanzu tana tunanin Jelly, kewarta na nan a cike a cikin ranta, Allah ya jarabceta da son jelly ba kaɗan ba.
Har karfe 10 na dare Abbo bai dawo ba, babu shi babu labarinsa, haka zalika su kuma, ba wanda ya sake zancen shi, da alama ya rufe masu baki ne, ya kuma mantar da Nawid abin da ya faru a daren shekaran jiya.
Ummi da kanta ta shirya Aafia tsaf, ta yi mata kwalliya tare da bata kayan da ta sayawa jelly wadda zata sanya a ranar shiganta ɗakin miji, da yake Aafia ɗin bata da wani ƙiba, sai kayan suka zauna mata a jikinta sosai, danƙareriyar lace ce, milk color, kwalliyar jikin lace ɗin nan an yi sune da manya manyan zanen fulawa blue color, sannan an zuba mashi wasu