Showing 249001 words to 252000 words out of 359620 words
suka girma, hasashe ta yi hakan yasa ta yi musu haka, ga shi kuma hasashenta ya zama gaskiya, sam sunki bata dama su saurareta, bata wani damu ba, dan tasan duk lokacin da Lion ya natsu, ya kuma mallaki hankalin kansa sosai, ya lura da abubuwan da ta bar musu, to dole shi da kansa zai zo in da take dan neman wasu amsoshi wanda ita ce kawai zata bashi wannan amsoshin, a nata hasashen kenan, kuma hakan ce take shirin faruwa, dan kuwa idan baku manta ba, a dube duben da Lion yake yi kwanaki har yaso yasa a kawo mishi ita dan ya yi mata wasu tambayoyi, case ɗin daddyn Rimsha data kunno kai tasa ya watsar da zancen mummyn nasa, yanzu kuma ya gama da case ɗin daddy, abin da ya rage ɗauko Na'urat ce wanda kuma ya san in da take, sai mummy wanda ita ma yasan in da take, so a takaice ya gama da case ɗin daddy Shiyasa yau ya fito da kayan mummyn nasa yana bincika dan gaskiya yana son sanin gaskiyar abin da yake faruwa a tsakaninta da daddy, yana da bukatar amsoshi da dama daga wajenta, ciki kuma har da fassarar abin da ta rubuta a takardan nan dan shi bai san wani yare bane wannan, shiyasa ma taki rubuta mishi da yaren da zai gane dan dolensa ya je neman faffasar yaren a wajenta, tarko ta kafa musu sosai ta yadda in dai sun mallaki hankalin kansu to dole zasu nemeta a koma ina ne su kai kansu gareta.
Ganin ba zata iya karanta abin da yake rubuce a jikin sarkar ba ne yasa ta ajiye hoton tana santin kyau irin na Josephine, dan fa ba karya kyakkyawace ajin farko.
Takardan sakon wasikar da ta rubuta musu ta fara budewa dan ta kalli me a ciki, wow ta furta ganin wani irin good handwriting, abin mamaki kuma handwriting ɗin sak irin nata, yana ɗaya daga cikin dalilan da ya sanya da suka je Abuja Lion ya ɗauki takardanta na makaranta guda ɗaya ba tare da saninta ba, saboda wlh handwriting nata da wannan handwriting da aka rubuta sakon nan babu banbanci, da yake ita tasan yadda daddynta yake rubutu, sai ta kalli ma handwriting ɗin tafi kama ta tasa sosai, dama gadon rubutun daga wajensa ta yi.
Ƙoƙarin fara karanta sakon ta yi sai ta fahimci bada turanci bane, haka ta rinƙa kwaɓawa tana karantawa, ba abin da ta gane ko ɗaya, dan dama yare idan ba naka ba ai ko haɗa kalma ka karanta ba iyawa zaka yi ba. A karshen rubutun ne da ta karanta sai taga an rubuta da turanci wajen da aka sanya i really love you my pleasures, and i will going to miss you more than your expectations.
Shiru ta yi tana tunanin irin wannan rubutu haka kamar yaren aljanu, ta kasa karanta komai, sai wasu kalmomi take haɗawa kamar tana tsinewa kanta ne da yaren, irin wannan abu haka anya ba yaren aljanu bane kuwa?.
Ta yi nisa cikin tunanin da take yi sai jin motsinsa ta yi a palon sama alamar yana shigowa cikin bedroom ɗin, a guje ta miƙe ta nufi toilet ta ɓuya a bayan wasu kyawawan fararen towals dake gere a wajen kusa da show glass na su mayukan wanke kansa.
Kasa kasa ya yi sallama tare da wucewa dressing room nasa, kayan jikinsa ya cire kafin ya ɗauko wani towel mai azababben kyau fari tas ya ɗaura a kugunsa ya fito ya nufi toilet ɗin da ya yi wanka ya yi shirin barci.
Yana shigowa ta runtse idanunta kirjinta na dukan uku uku, yau tashiga uku ta lalace a cewarta. Wajen brush nasa ya nufa, haɗa mayukan goge bakinsa ya yi tare da fara yi cikin natsuwa, bayan ya kammala sai ya nufi wajen tampatsetsen baf ɗin wankansa dan ya haɗa ruwa, ruwan zafi ya fara zubawa zuwa daidai rabin baf ɗin kafin ya cikata da ruwan sanyi, sannan ya ɗebo sabulansa kala kala ya zuba a cikin ruwan, kunsan dama su Turawa yadda suke wanka, mafiya yawan lokuta sun fi zuba zabulan wankansu a cikin baf ɗin sai ruwan ta yi kunfa over suke shiga, sai su goge jikinsu da kyau kafin su fito idan sun kammala su shiga shower dan ɗauraye jiki, suna son tsunduma cikin ruwan kumfar sosai, suna kuma ɗan jimawa a cikin ruwan idan suka shiga, shiyasa basu cika amfani da sabulai irin namu ba, sun fi yin amfani da sabulai na ruwa.
Bayan ya zuba duk wasu soaps nasa da sauran kayan wankansa, tsab ya kammala komai, duk abin da yake yi tana kallon shi, tsabar dukan uku uku da kirjinta yake yi yasa gabaɗaya gaɓoɓin jikinta sun yi sanyi, sun kasa ɗaukarta, dap take da ta zube kasa dan wlh ba zata iya ba, a hakan ma dan ya bata baya ne yake harkokinsa, ba ta gabansa take kallon ba, da ta gaba ne ina ga sai suma.
Yana ƙoƙarin kwance towel ɗin dake kugunsa dan ya shiga ya yi wanka ne, ta ji ina bazata iya jurewa ba, dan haka sai ta fito daga bayan towels ɗin da gudu gaske ta nufi waje, taku biyu ya yi ya damkota ta shafaffen cikin nan nata, dama tun shigowarsa ɗakin yasan ta shigo mishi, duk kuma abin da ta yi ta taɓa mishi ya gani kuma yasan an taɓa, sai dai bai yi tunanin a toilet ɗin ta ɓuya bane, ya yi tunanin dressing room ta shiga da ta ji motsin nasa, lokacin da ya shigo toilet ɗin ya ji kamshin perfume nata, so ya yi tunanin nan ma shigowa kawai ta yi ta mishi taɓe taɓe kamar a cikin ɗakin, bai kawo ɓuya ta yi a ciki ba, sai da ya je zai ɗauki brush ne ya ganta, amma ya yi kamar bai ganta ba ya yi brush nasa zai fara wanka ko a jikinsa.
"What brought you in to my room?. Me ya kawoki cikin bedroom na?" Ya yi maganar a nutse cikin wannan cool sexy voice ɗin nasa. A hankali ta juyo suna fuskantar juna har lokacin hannunsa a saman flat tummynta ya riketa sosai ta wajen, gabaɗaya ilahirin jikinta kerma yake yi, harta laɓɓanta ɓari suke yi dan bala'in tsoro.
Ya ilahi ya lillahi, wani irin mahaukacin razana ta yi na ganin surar jikinsa a zahiri ba riga, musamman faffaɗar kirjinsa, ga wannan baƙin gashi dake kwance a iya tsakiyar ɓul ɓul ɗin breast nasa, gashi bashi da yawa, ɗan daidai tsakiyar breast ɗin nasa ne, ga breast ɗin ba sai na sake gaya muku ba, suna nan ɓul ɓul saboda training da yake yi, damatsansa kamar zasu fashe, a cike suke tab, ga wasu siraran jijiyoyi ɓaro ɓaro a saman damatsan nasa alamar cikar jarumin namiji kenan.
Datse idanunwanta gam ta yi kirjinta na dukan tara tara, jikinta na kara tsananta kerma da yake yi, iya razana ta yi ba karya, soft skin nasa ma kawai abin kallo ne yadda yake wani sheki tamkar fatar jariri, kamar bai taɓa fita waje ba, ga jikin nasa da tsantsar daddaɗar kamshin perfume nasa da already ya rigada ya kama fatarsa gam, ko bai saka ba yana zuba kamshin.
Duka dukanta bata wuce dai'dai tsakiyar ɓul ɓul ɗin breast nasa a tsawo ba, kanta ya tsaya a dai'dai breast ɗin nasa, dan ba karya Lion yana da tsawo sosai irin daddynsa, biyunsa kuma Areef, Aseef ma yafi Imran tsawo sai dai bai kaisu ba, so tanannan ƴar dai'dai a gabansa, musamman idan ya mannata da faffaɗar kirjinsa da ya ji training ya koshi, sai ta lafe luf a gefe guda.
"Open your eyes". Ya faɗa murya can kasan maƙoshinsa, ya yi maganar kuma yana cire hijabin jikin nata dan sai haɗa uban zufa take yi, ta tsorata over ƴar kaniya, yana cirewa nan take zanen sunansa dake saman tudun breast nata ya bayyana, da yake ta yadda ya damko cikin nata yasa wuyar rigar kayan barcin jikin nata ya yi kasa, tudun breast ɗin nata sun bayyana sosai, zubawa sunan idanu ya yi yana kallon yadda zanen ya zauna ɗas tamkar da shi aka haifeta.
A tsananin shagwaɓe ta ce "Yaya Saif na tuba wlh, ba zan iya buɗe idanuna ba, ba zan iya kallonka a haka ba, na yarda idan ka fito wanka ka shirya, to koma wani irin hukunci ne a lokacin ka yi mini zan karɓa, amma yanzu Allah ba zan iya buɗe idanuna ba, kuma na maka alkawarin ba zan sake taɓa maka komai naka ba, ba ma zan sake shigowa ɗakinka ba idan ba abinci zan kawo ba, wlh tsautsayi ne yasa yanzu ma na taɓa abubuwan da na taɓa, wayyo daddyna nashiga uku yau kam, yaya Areef kazo ka ceceni". Ta kai karshen maganar hawaye na zuba daga idanunta, danasanin abin da ta yi ta farayi, me ma ya aiketa ta taɓa mishi abubuwa? Ga shi har da kayan mummynsa tsab ta buɗe komai.
Yadda ta zuba shagwaɓa over wajen yi mishi magana tasa ya ji gabaɗaya jikinsa ya mutu, ba zai iya yi mata wani hukunci ba, da ya yi niyar hukunta ta sosai, dan babu wanda ya taɓa taɓa mishi abin da ta taɓa yau, ko su Aseef basu san da shi ba, amma sigar da ta yi mishi magana da shi yasa ya ji ya hakura.......... E LALLAI SOYAYYA NA ƊAWAINIYA DA ZUCIYAR LION BA TARE DA YA SANI BA TA BAKIN AREEF, IDAN BA SOYAYYA BA ME ZAISA TA YI MISHI LAIFI YA CE YA YAFE MATA? MUTUMIN DA A BAYA KO BATA YI MISHI LAIFI BA MA IDAN TA BIYO TA HANYAR DA AKAYI MISHI LAIFI SAI TA KARƁI HUKUNCI, BA SHAKKA LION KA FAƊA TARKON KARAMAR YARINYA.
A hankali shasshekar kukanta ya fara ratsa zuciyarsa, ɗan ɗago idanun nasa ya yi daga saman zanen sunan nasa zuwa kyakkywar fuskarta, ganin yadda hawaye wani na abin wani suke zarya a face ɗin nata ne yasa ya ji sam babu daɗi a cikin zuciyarsa, ga shi ta datse idanu gam tamkar zata fasasu, hakan bai yi mishi daɗi ba, baya son ganin hawayen, bai san lokacin daya ɗago hannunsa ya ɗaura saman lallausan kumatun nata ba, a maimakon ya goge mata hawaye, a'a shi salon rarrashinsa daban ne, yasan ko ya goge hawayen ma wasu ne zasu zubo, so kukan ya kamata ya dakatar ba goge hawaye ba, kara jawota jikinsa ya yi da ɗayar hannunsa dake saman cikinta, ta shiga firgici sam bata ma san da hannunsa a saman cikin nata ba.
A hankali ya sanya latsarsa guda ɗaya a........
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️
E63-64💋
A hankali ya sanya latsarsa guda ɗaya a saman lips nata dake ta faman kerma kamar mai rawan sanyi, ɗan murza lips ɗin nata ya fara yi tare da zame hannunsa dake saman cikinta ya mayar saman mazaunanta ta baya dan ya ji daɗin rikota da kyau. Saukar hannunsa a saman mazaunan nata ne yasa ta waro idanunta ba shiri, kai tsaye sai cikin dara daran blue eyes nasa idanun nata suka sauka, dan kuwa ya tsareta da idanu yana kallonta, wani irin azababben sonta ne yake kara ratsa shi ba tare da ya shirya ba, wani irin daddaɗar yanayi yake jin kansa a ciki mara misaltuwa.
Har lokacin idanunta suna zubar da kwallah zuwa saman face nata bata dai'na ba, zame hannunsa ya yi daga saman lips ɗin nata a hankali ya gangaro da shi zuwa saman lallausan wuyarta, blinking idanunta sau biyu ta yi dan ta tabbatar wa da kanta ba mafarki take yi ba, tunani ta fara yi wai ko dai akwai wani abin da ya shiga kansa ne? Anya yaya Saif ɗin da ta sani ne kuwa? Anya Malika bata yi mishi wani abin ba kuwa?.
Tana can tana tunani sai jin saukar lallausan hannunsa ta yi a saman tudun tula tulan ya sanya yatsa ɗaya babbar cikin yana shafa sunan nasa dai'dai in da ta rubuta GAR, kasa ɗaukar hakan ta yi, bata san lokacin da numfashinta ya tsaya cak ba saboda razana da shiga yanayin da bata taɓa tsintar kanta a ciki ba. Tana ƙoƙarin zubewa kasa ya rikota da kyau da hannunsa dake saman mazaunanta, dawo da kallonsa saman face nata ya yi yana kallon yadda ta sha kuka, ta sume mishi a jiki sarkin tsoro.
Ranƙwafo da kansa sosai ya yi daidai saitin face nata, shiru ya ɗan yi kamar mai tunanin wani abin, can kuma sai ya ɗan ɗaga kai tare da sanya hannu ya goge mata hawayen kafin ya ɗauketa cak a saman kafaɗarsa ya fito da ita zuwa cikin ɗakin. A saman bed nasa ya ahinfiɗeta kafin ya koma cikin toilet ɗin dan ya yi wanka.
After 45 mins, ya fito shirye cikin tsadaddun kaya barcinsa farar tas, sai shaki soft skin nasa yake yi sosai, yana ta zuba kamshi. Saman bed ɗin ya nufa kamar zai zuba mata ruwa, kome ya tuna sai kuma ya fasa ya nufi waje dan ya duba ƴan uwansa da kuma daddy.
After some minutes ya dawo, sai da ya bisu ɗaya bayan ɗaya ya duba su sannan ya dawo, har Aseef sai da ya yi musu knocking suka buɗe ya duba lafiyar Aseef ɗin kafin ya dawo bedroom ɗin nasa.
Saman bed ɗin ya haye bayan ya ɗauko ruwa roba ɗaya daga cikin fridge, ya buɗe robar ruwan yana ƙoƙarin tarbowa a hannunsa dan ya zuba mata ta tashi ta koma bedroom nata, bai kai ga yin hakan ba daddynsa ya shigo bedroom ɗin dan yana son ya yi magana da ɗan nasa, ganin daddyn yasa ya tsaya bai zuba mata ruwanba yana bin daddyn da kallo.
"Son me yarinyar nan kuma take yi a saman bed naka?". Shiru ya yi bai tanka mishi ba. "Son ka tasheta ta fita magana nazo in yi da kai, kuma kasan cewa nace bana son yarinyar nan since before nazo nan ko? To dan haka bana sonta! Bana son ganinta a kusa da kai! Dan haka yanzu ba sai anjuma ba ka tasheta ta fita a ɗakin nan, kuma kada ta sake zuwa dan bana sonta kusa da kai". Yanayin yanda daddyn yake magana sai ya ga kamar daddyn yana wani nuna mishi isa da izza ne, shi kuma kun sani ba sai na sake faɗa ba, baka isa ka nuna isa a gabansa ba, kuma shi daddyn shi ya basu wannan tarbiya, dan haka iyaye ku ji tsoron Allah ku bawa ƴaƴanku tarbiya da zata sanya su yi abin alkhari, ku sani duk abin da kuka koya musu wlh sai sun yi muku shi a kwana a tashi, to dan haka ku koya musu alkhari dan kuma kuga alkhari, kada ki yarda ko irin gulmar da yara suke kawowa irin idan sun je gidan mutane duk abin da ya faru suzo suna gaya miki, kada ki yarda, tun wuri ki taka musu birki, da sun fara ki hanasu ki ce waye ya tambayeku? Idan ba haka ba, wlh haka zasu tashi da wannan kananun maganganu da gulma da munafurci, a kwana a tashi kema sai sun yi miki, Allah dai ya dafa mana ya bamu ikon aikata alkhari a duniyarmu dan muga lahira mai kyau.
Jin yanda daddyn ya yi mishi magana cikin nuna isa ne yasa ya fasa zuba mata ruwan ma bakiɗaya, tare da yin kwanciyarsa bayan ya ajiye ruwan a saman bedside drawer, ya jawo bargo zuwa dai'dai cikinsa, ganin bargon ya rufe har kanta ne yasa ya mike ya gyara mata kwanciya a in da ya ɗaura kanta a saman pillow dake manne da jikin headboard na gadon, sannan ya ja musu bargo dan shi bashi ma da lokacin yin wata magana da daddaren nan bare ya biyewa daddy su yi.
Ganin hakan yasa daddy ya ɓata rai sosai ya fara faɗa babu kama hannun yaro, shiru ya yi bai tanka ba tamkar babu shi a ɗakin.
Sai da yaji surutun daddy fa yana neman sanya shi ciwon kai, a fusace ya miƙeq zaune, cikin nuna isa da izza ya fara magana "Daddy do you know what? She is my wife yanzu da nake maka magana matata ce, a da bani da niyar kulata, amma tun da ka ce baka son ganinta a kusa da ni, as from today ta dawo bedroom ɗin nan da zama kenan, ko waje ba zata fita ba idan ta dawo school, kuma zan kula da ita saboda baka sonta, wai ka manta cewa ni abin da ba'a so ne ni kuma nake so? To idan ka manta na tuna maka, tun da baka sonta dole zan kulata, zaka iya tafiya yanzu barci nake ji, ita kuma matata ce babu wanda ya isa ya canza hakan!".
Tashin hankali, a tsananin razane daddyn ya miƙe, cikin fushi shi ma ya fara magana "Romeo ni fa na haifeka ba kai ka haifeni ba, to ina mai baka umarni da ka fitar da yarinyar nan daga cikin bedroom naka, in fact daga gidan nan baki ɗaya, na ce bana sonta ko?". Shiru ya yi bai sake yin magana ba, sai ma kwanciyarsa da ya yi tare da jawota jikinsa tun da daddyn ya ce baya son ta zo kusa da shi, to barima ya rungumeta suyi barci tare sai ya ga karshen tsiya, shin daddyn zai mutu ne ko yaya? Mutun sam baya son zaman lafiya?.
Bakin ciki tamkar daddyn ya haɗiyi zuciya ya mutu, Allah dai yasa yanzu ya sami sauki sosai, da yanzu ciwonsa ya tashi saboda tsananin azabar ɓacin rai, ko kallon in da yake Lion ɗin bai sake yi ba, hannu ma ya ɗaura a saman bayanta yana shafawa a hankali tare da lumshe idanuwansa kamar mai barci.
Daddy bashi da zaɓi dole ya juya ya fita daga ɗakin, domin kuwa babu yanda ya iya da Lion, dole dai ya hakura ne. Daddyn yana fita ya rabata da jikinsa tare da juya mata baya ya yi kwanciyarsa, batun bedroom nasa kuma ta dawo kenan kamar yadda ya faɗa, dan baya magana ya canza, bare ma kuma da ya zamana daddyn yana gidan, ai ko dan ya cika maganar tasa dole ta zauna a bedroom ɗin.
Yana juyawa ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi, dama ita kam already tana sume baiwar Allah.
A ɓangaren