Showing 231001 words to 234000 words out of 359620 words

Chapter 78 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2014

Allah ya fita a hayyacinsa, yau ma a karo na biyu ya faɗa tarkon mace.

(A gaskiya Justice for Lion😭 Malika bamu yafe ba, kina son lalata bawan Allah😭 anyi breaking heart nawa a garden ɗin nan💔😭😌)

Babban yatsansa ya ɗaura saman lips nata yana ɗan shafawa a hankali tare da lumshe dara daran blue nasa, dan shi kaɗai yasan me yake ji, while har lokacin hannunsa ɗayar tana saman lallausan kumatunta. Ta kasa jurewa hakan yasa ta buɗe idanunta dan ta ga wai shi ne ko an canza shi ne? Ko dai yana neman in da zai yanke mata ne yau kuma a jikin nata.

(Wayyo cikina, Rimsha da Lion duniya🤣 wai yana neman in da zai yanke omg, wlh salonku daban yake da kowa💃)

Ganin idanuwansa a lumshe ne yasa ta tsare shi da idanu tana mamakin abin da yake yi a face ɗin nata, tunani ta fara yi to ko dai Malik ce ta shaga jikinsa? Bata san ita ma Malika tana can tana zuba soyayya a duniyarsu ba, yau kwana wajen uku ma Malika bata sauko duniyar mutane ba, kawai dai yanayi ne da kuma tarkon da Malikan ta kafa mishi da farko ya kuma faɗa, su ne kawai suka sanya yake yi mata hakan.

A hankali ya zura latsar tasa cikin bakin nata tare da fitar da chewing gum da yake ciki ya jefar a kasa sannan ya cigaba da ɗan murza laɓɓan nata, da alama fa wlh baya cikin hayyacinsa, hannunsa dake saman kumatunta ya zame a hankali tare da mayar da shi saman.............

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️





💋Dedicated to myself...✍️🔥❤️



E59-60💋



A hankali ya zura latsar tasa cikin bakin nata tare da fitar da chewing gum da yake ciki ya jefar a kasa, sannan ya cigaba da ɗan murza laɓɓan nata, da alama fa wlh baya cikin hayyacinsa, hannunsa dake saman kumatunta ya zame a hankali tare da mayar da shi saman kanta, a hankali ya zame hijabinta daga kanta zuwa wuyarta, lallausan dark black curly hairnta ya fara shafawa har lokacin idanuwansa a lumshe.

Ita dai ta zuba mishi ido tana kallon ikon Allah yau, ta kasa koda motsawa, gangaro da hannunsa ya yi zuwa saman dogon wuyarta da yake yawan shakewa, a hankali ya fara shafa wuyar tata yana wani irin numfashi, abin da bai taɓa yi ba a rayuwarsa bai ma taɓa tunanin zai taɓa kwatantawa ba, daidai in da ya shaketa ɗazun ya tsayar da hannunsa shiru kamar mai tunanin wani abin, sai kuma ya zame hannun nasa gabaɗaya daga jikinta ya mayar cikin dark black curly hairnsa ya fara watsawa, miƙewa ta yi daga jikinsa a hankali, bai hanata ba dan da alama ya shiga duniyar tunani, bai ma ji mikewan nata ba.

Wajen wayarta ta nufa, a hankali ta ɗauko, screen ɗin ya yi raga raga ya tarwatse, ta ji babu daɗi, amma bata ce komai ba, kwanikan abincin ta zo ta kwashe ta nufi cikin gida hijabin yana wuyarta bata mayar kanta ba, shi kuma a hankali ya fara sauke numfashi mai ɗauke da wasu abubuwa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa.

Shi kuma Brady ya kama kansa ya tafi yawo, dan dama baya wani zama waje guda, yanzu ma daga wajen Aseef ya fito.

Ko da ta je shiga cikin gida kofar palon a rufa, ajiye kayan abincin a wajen ta yi tare da dawowa garden ɗin, ɗan gefensa ta tsaya tana kallonsa, a hankali yake sauke numfashi irin na mai barci, da alama ya yi barci, lallaɓawa ta yi ta ɗauki wayarsa dan ta kira daddynta ko kuma Areef ya zo ya buɗe mata kofa.

Wayar da akwai password a jikinta, kokarin gwada buɗewa ta yi tana ɗan satar kallon shi, sunan Aseef ta fara sakawa, nan take wayar ta fara kara dan wrong password aka saka mata, wani irin razana ta yi jin yadda wayar take kara tamkar jiniyar motar ƴan'sanda, a hanzarce ta ɗago dara daran sleeping eyes nata ta saukesu a kansa, ko motsawa bai yi ba, amma dai ya farka daga barcin dan bashi da nauyin barci.

Jikinta na kerma ta mayar mishi da wayar ta ajiye tare da komawa saman sofar dake kusa da shi ta zauna tana tunanin ko dai ta je ta buga kofar ne wani ya zo ya buɗe mata? Sai dai ko ta buga ma ba zasu ji ba.

A can cikin gida kuwa, bayan tafiyar su Abba, bedroom ɗin su Jehan Areef ya wuce dan ya je ya tsokane ta kamar yadda ya saba yi bayan ya kai Aseef bedroom ɗin Lion ya duba lafiyarsa tare da bashi abinci kenan.

Da sallama ɗauke a bakinsa ya faɗa cikin ɗakin, tana kwance ta yi shiru tana tunanin duniya, ta manta da wayar Adiva dana Abubakar jaja da ta ɗauko, wayoyin suna ɗakin da daddynta ya sauka, suna bayan gado ta ajiye su, sai dai duk sun mutu babu charji.

Saman bedside drawer ya zo ya zauna yana faɗin "Tashi muje na baki abincin a baki dan nasan yunwa kike ji". Tamkar babu ita a ɗaki, sam bata kula shi ba, hannu ya kai ya ja dogon hancinta yana faɗin "Wai ke baki dariya ne? Ni na gaji da kallon face naki tamkar na Lion ɗin nan, na je ɗakin Lion naga Tiger face, kema nazo wajen ki naga Tiger face, ina kuke son na saka raina naji daɗi to? To ni nagaji gaskiya!". Still ko sannu bata ce mishi ba.

Zai sake yin magana sai ga daddynta ya shigo rike da hannun Akila, kara faɗaɗa murmushin kan face nasa ya yi kafin ya ce "Uncle ka ce baby ta tashi muje na bata abinci ko kuma na ɗauke na je na yi mata ɗure kamar baby". Ƙayatatcen murmushi daddyn ya saki yana faɗin "Ai dole ma ta tashi amma yanzu bari ta rarrashi ƴar uwarta tukunnan, ina Rimsha?".

Kallon Jehan ɗin suka yi suna jiran amsar ina Rimsha, turo baki tayi kafin ta ce "Daddy Rimsha ta tafi kaiwa wani wai yaya Saif abinci, wai daddy waye shi? Kuma ita Rimsha dama ƴar aiki ce?". Ta kai karshen maganar tare da mikewa zaune tana cigaba da cewa "Wai yarinyar nan ina cewa kada ta je tana ce mini bata shirya mutuwa ba, ban gane bata shirya mutuwa bane? Kisa akeyi a gidan ne ko yaya? Shi ne nake jiran ta dawo ta yi mini bayani".

Kallon Areef daddyn ya yi yana faɗin "Sai ka gaya mata waye Saif". Wayarsa ya ciro tare da fito da hoton Lion ɗin ya nuna mata, kallon hoton ta yi ba tare da ta karɓi wayar ba, wani irin mummunar faɗuwar gaba ta ji ganin fusataccen fuskarsa, nan take ta sha jinin jikinta, dan kuwa wlh ganin face ɗin Lion a ɗaure dole ya raza mutun, ga uban kwarjini da Allah ya yi wa TRIPLETS kamar me, shi ma Areef ɗin dannewa kawai take yi tana yi mishi abin da taga dama dan taga yana dariya ta kuma san bazai yi mata komai ba, amma mugun tsoronsa take ji, sai ɗan banzan farinjini garesu TRIPLETS ɗin nan kamar su suka bawa kansu, ko'ina zasu shiga sai an so su, amma kusantarsu kuma ba kowa yake iyawa ba sai wanda suka so, suka ja shi a jiki.

Shiru ta yi bata sake yin magana ba, dan kuwa bata san me zata ce ba, a bata ga laifin Rimsha ba, dole ta ce bata shirya mutuwa ba, wannan mai fuska kamar Tiger face ɗin, a haɗe kamar hadari, yadda damisa bai san murmushi ba shi ma haka bai san menene ko da yake ba bare murmushi har a kai ga dariya, duk bai sansu ba kuma bai taɓa yi ba, bai ma iya ba, bashi da wani sassauci a rayuwarsa, dama dole za'a iya samun haka daga gare shi, dan kuwa matsayin GENERAL OF THE ARMY ba wasa ba, duk wasu sojoji da kuka sani a duniyar nan, duk girman mukamansu kama daga kan BRIGADIER GENERAL, GENERAL, LIEUTENANT GENERAL, MAJOR GENERAL, da sauransu, duk a karkashinsa suke, daga kan mukaminsa babu wani mukami ta sama, shi ne kololuwa, star biyar ke gare shi, shi ne on top, so dama dole a ganshi haka, dan ya tsallake abubuwa da dama kafin ya taka wannan matsayi, ba irin horar da mutane da bayyi ba, kisa ba kalar wanda bai yi ba, babu wani masifa da tashin hankali da bai gani ba, horo kuwa ba'a magana irin horon da ya samu, duk wata wahala ya ganta, dama dole a samu rashin tausayi a tattare da shi, dan tun yana gani yana jin tausayi har zuciyar ta bushi babu komai a cikinta face zallar aiwatar da aiki babu ɗar ko wasa, dole idan aka gansa a razana, dole ya razana maza, dan shi ma ya razana kafin ya taka matsayin, damma dai babu abin da musulci ya bari, musulci rahma ce babba da babu irinta, ta sanya mishi imani, ta sanya ya sauya, lokacin da yake krista, ya ilahi ya lillihi, a lokacin Lion zai iya ɗaure mutun yana yankar wasu sassa na jikinsa har ya kashe shi da haka idan ya yi mishi laifi, babu imani ko ɗigo ko miskala zarratin a ransa, idan babu imani kuma ai babu tausayi, lokacin kam bawani bawa mai imani da zai so jin irin rashin imaninsa da zafin zuciyarsa, baya ɗagawa kowa kafa, haka zalika baya ganin kowa kamar mutun bayan TRIPLETS, tun fil azar bashi da tsaro, ga aiki kamar agogo idan ya yi ra'ayin yi, idan kuma bai yi ra'ayi ba, to fa ba'a haifi wanda ya isa ya ce ya yi ba, ambatar sunansa a waje ba ƙaramin razanar da mutane yake, dayawan sojoji da criminals da ace Lion ya yanke musu hukuncin da za'ayi musu idan suka yi laifi, gara su harbe kansu da kansu da bindiga su mutu yafi musu sauki, dan rashin imaninsa ba'a magana, daddynsa sam bai ishe shi kallo ba, su uncle T sun sha bakar wahala a hannunsa, dan idan suka yi mishi kuskure sai ya bankaresu kamar wasu kajin da za'a gasa, ya yi musu mummunar ɗauri, ya barsu tun safe har gobe da safe ko motsi basu yi, wani lokaci idan ya sanya aka kwancesu ko mikewa basu iya yi, suna zaune ma suna faɗuwa dan azaban wahala ga yunwa da kishi, sai ya shanyasu a rana kamar wasu kayan wanki, a hakan ma dan su na gida ne, duk wata horo na mugunta babu kalar wanda bai iya ba, idan baku manta ba akwai lokacin da daddy ya kirashi a waya da ya ɗauka, ranar daddyn ya yi murna over har yake cewa ba zai manta da wannan rana ba yau Romeo ya ɗauki kiransa, to a lokacin ya musulta ne, ya san hakkin iyaye a kan ƴaƴansu, shiyasa yake ƙoƙarin saukewa, bayan daddynsa su uncle Herry gabaɗaya tsoron tinkararsa da karamar magana ma suke yi, ganin face nasa razanasu yake yi a lokaci, baya magana ya canza koda kuwa mutane goma zasu mutu sanadiyar wannan hukunci da ya yanke, to fa sai dai komai ya faru ya rigada ya yi ta kenan, babu mai iya kusantar shima bare ya tankwara shi, sai dai bayan TRIPLETS nasa yana son kakansa His excellency, amma duk da haka bata hana idan suka sami saɓanin ra'ayi ya yanke abin da yake so, kakan nasu kuma Allah ya jarrabesa da bala'in son Lion ɗin kamar ba gobe, kunsan Turawa idan suna son abu ba'a magana, hakan tasa yake biye mishi, idan nace zan tsaya gaya muku wanene Lion lokacin da yake krista yake amsa sunan Romeo or GAR wlh zamu kwana mu wuni bamu yi ko kwata ba, dan fa ya yi rashin imani tsantsar ta, ga bala'in zuciya na wuce misali, ga azababben kishi tun suna school, baya taɓa bari wani na wucesa a kan abu saboda kishi, shiyasa yake zuwa na farko a komai, dan idan wani ya wuce shi ko da marking ɗaya ne, to ranar baya iya barci saboda azababben kishi da zuciya, sai yaga ya wuce kowa a class ɗin yake samun kwanciyar hankali, haka a wajen aiki kafin ya zama babban baya yarda a wucesa, ga kafiyar bala'i kamar ba gobe, taurin rai da kuma taurin kai kamar me, kai fi ɗaya ne tak!! Ga bala'in tsanar musulmai da bakaken fata, amma lokaci guda kaunar addinin ta yi mishi mummunar shiga sanadiyar Imran, wannan shi ne dalilin musultar, kira'ar AlQur'ani mai girma ce ta ja ra'ayinsa, jin yadda Imran yake rerata ta yi mugun tafiya da shi lokaci guda, da Allah ya kaddara yana da rabon samun rahma sai ya fara karatunta kafin ya musulunta, ya kuma yi bincike sosai a kan addinin tare da karanta littattafan musulci, sai da ya tabbatar da addinin ita ce ta gaskiya kafin ya karɓi kalmar shahada, so silent da shi baya magana kuma baya son hayaniya!!.

Da Lion bai musulunta ba lallai akwai aiki ba kaɗan ba, dan kafurar zuciya ke gare shi na bala'i, bugu da kari ga irin tarbiyar da suka samu, ga abin da suka taso a kai na sune sama da kowa a cewar daddynsu, ba wanda ya isa ya ɗaga musu murya, amma yanzu Alhamdulila komai ya yi sauki sosai, am very very proud to be a Muslim wlh, musulci duniya ne, daga kansa kuma babu ma na kusa da shi, shi kaɗai ne, addini mai sauki daɗi ga sakamako mai kyau idan kayi aiki wato aljanna, jama'a aljanna fa babu mai iya kwatanta muku ni'imominta, jama'a ayi aikin Alkhari a shigeta fisabillilahi, dan wlh duniya ba komai bane, aljanna wayyo Allah, Allah ka bamu ita da ni da duk masu karanta littafina dama musulman duniya bakiɗaya, kai idan Allah ya yi ka tsinci kanka a cikin musulci to harka mutu kada ka dai'na gode mishi, yanzu idan ba dan musulci ba ya kuke tunanin rayuwar Lion zai kasance?.

(Komai na Lion ya canza kamar ba shi ba, ga shi Malika ta kara sauya mana shi😭 ta mayar da shi ɗan soyayya😭 justice for Lion, gaskiya babu karya Rimsha da iyayenta sun ciri tuta a cikin rayuwar Lion duba da irin rayuwarsa a baya na tsanar musulmai da bakaken fata, sunci albarkacin TRIPLETS nasa ne sosai,)

STORY💋

Mayar da wayarsa aljihu Areef ya yi tare da miƙewa ya nufi waje, yana fita ya shiga bedroom ɗin daddyn ya haye saman bed nasa ya kwanta, shi kuma daddy zaunar da Akilar ya yi a kusa da Jehan ɗin yana faɗin "To Jehan ga ƴar uwarki, ki kula da ita kafin Rimsha ta dawo". Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya fita zuwa bedroom nasa.

Kwance ya isko Areef yana ɗan latsa wayarsa, yana ganinsa ya miƙe zaune, gefen bed ɗin ya zo ya zauna yana kallon Areef ɗin kamar mai son cewa wani abin, kwanto da kansa ya yi a saman cinyar daddyn yana faɗin

"Uncle I really missed you wlh". Shafa gashin kansa daddyn ya fara yana faɗin "Gaskiya dai nima na yi tsananin kewarka my Tiger, ya aiki? Kayi nasara ko?". Jinjina mishi kai ya yi kafin ya ce "I don't know the reason why nake kaunarka uncle, ko Lion na kasa gaya mishi aikin da nake yi a lokacin, amma kai ban ɓoye maka komai ba, kai idan na tuna abin yana bani mamaki fa, gaskiya i really like you my uncle". "I really like you too my Tiger, yanzu dai gaya mini kayi nasara ne? Amma fa ka sakani a cikin damuwa a lokacin, bare ma da na ga halin da Aseef ya shiga na rashinka, har nace gaskiya zan gaya musu gaskiyar in da kake kawai suje su ɗauko ka, sai kuma na tuna nayi maka alkawarin ba zan gayawa kowa ba, amma na sha wuyar danne wannan sirrin naka, dan na kasa jurar ganin tashin hankali da Aseef ya shiga gaskiya".

Murmushi ya yi kafin ya shiga bashi labarin yadda komai ya faru tun shigarsa Kasar Spain har izuwa shigarsa South Africa, da kuma isowarsa Nigeria, da kama shi da aka yi a Naija, yadda Lion ya karɓo shi da komai da komai, daga karshe ya gaya mishi ya yi nasara sai dai Lion ya cire shi a cikin hukumar C I A, yanzu haka idan ya sami sauki aikin soja zai fara, Lion ya ce baya son C I A sam.

Ba ƙaramin jinjina mishi daddyn ya yi ba tare da zuba mishi addua'o'i da fatan samun nasara, gaskiya daddyn Rimsha ya bawa Areef gudumawa ba kaɗan ba a nasarorin da ya samu, kwana sallah yake yi yana rokan Allah da ya kare Areef ɗin a duk in da yake, ya bashi nasara, ba dan addu'ar da yake kwan yi mishi ba, ai da sun jima da kashe shi a Nigeria, duk azumin da daddy yake a Washington DC Areef ɗin yake yi wa dan ya roka mishi Allah ya tsare shi ya dawo da shi lafiya, da yake ya gaya mishi har in da zai je da kuma aikin da zai je ya yi, shiyasa Allah ya jarrabi TRIPLETS ɗin da kaunar daddyn har ta Lion, dan ya yi musu aikin Alkhari kuma a ɓoye ba tare da sun sani ba, babu aikin da Ubangiji ya fi karɓa da wuri yake baka sakamakon da wuri irin ka kyautatawa bawa ba tare da sanin kowa ba, ka taimakawa bawa ba tare da sanin kowa ba sai Allah kawai, ko shi bawan kada ka gaya mishi kai kayi mishi kaza, to idan Allah ya tashi biyanka zai biyaka ne ta in da kai ma baka yi tsammani ba, shiyasa ga shi yanzu Allah ya jarrabi Lion da abubuwa da dama dan taimakawa daddyn ba tare da sun sani ba, bugu da kari ga soyayyar Rimsha wanda shi kansa Lion ɗin bai san yana yin soyayyar ba, bai san ta ya akayi ta shigesa ba, shi dai kawai yasan baya son wani ya raɓeta ne kawai, amma bai taɓa yarda cewa soyayya bane, dan bai ma san soyayyar ba bare ya ce ita ɗin ce, kawai tana burgesa.

"Uncle do you know something?" Girgiza kai ya yi yana mai cigaba da shafa gashin nasa. "Gaskiya ba zan ɓoye maka ba I fall in love with


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login