Showing 60001 words to 63000 words out of 359620 words

Chapter 21 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

3040

bata ɗago ta kallesu ba.

"Ke Jessie wuce ki gayawa uncle ina nan kiran me yake yi mini". Cewar Aseef, ya yi maganar yana yi wa yarinyar kallon banza.

Da sauri ta juyo jin zazzakar muryarsa, ganin shi yasa ta taho da sauri ta faɗa saman jikinsa tana faɗin "Michael i really missed you, long time ina ka shiga?". Ɗaure fuskar nan sosai ya yi, tamkar bai taɓa sanin menene dariya ba, sai ya dawo sak Lion. "Tashi mini a jikina da wuri, kuma sunana ba Michael ba!". Ya faɗa yana mai kara ɗaure fuska kamar hadari.

Da sauri ta ɗago idanu tana kallonsa jin yadda ya yi magana a kausashe, da yake Musharraf yasan halinsu sai bai wani damu ba, ya san abin da ya fi hakan ma zasu iya ai katawa, dan ta kwanta a jikin Aseef ba wani abin bane, ai ƙaramin alhakine hakan.

Babu tsoro ko kaɗan a face nata, matso da fuskarta sai tin nasa ta yi, sai murmushi take yi tana ƙoƙarin kai mishi kiss a laɓɓansa, cikin zafin nama ya hankaɗe da karfi, abunku da yar siririr ba nauyi, sai gata a kasa kamar wata kayan wanki, a fusace ya yi kanta da nufin ya daketa, da sauri Musharraf ya ruƙe shi yana mai bashi hakuri, ina ai kwace hannunsa da Musharraf ya riƙe ya yi, jinin William jacop ne ke gudu a jikinsa, dukkansu akwai zuciyar bala'in, sun gado ne daga iyayensu.

Bai saurari Musharraf ba ya fara ball da ita, dama haushinta yake ji, wai tun tana yarinya ta kafe sai shi ko kuma Lion zata aura, idan baku mance ba His excellency ya taɓa zuwa gida har ya ce da daddy ya ce wa Lion ya zo ya kalli Jessie idan ta yi mishi sai a haɗasu aure, har daddy ya ce shi yana tsoro sai dai shi His excellency ɗin ya yi mishi magana, shima yaki, to wannan ita ce Jessie da ake magana a kanta, tun tana yarinya ta kafe lallai sai su, ko Lion ko Aseef, dan Areef kam ma bata san kammaninsa ba, tun ainahi bai cika zuwa white house ba, bai ma santa ba, kai ubanta ma bai sani ba bare ita, Lion da Aseef ke zuwa white house, su ta sani yasa ta kafe sai su, mahaifin ta baban abokin shawarar His excellency ne, kuma ɗan uwansa na jini ne, Jessie ta kasance jika ce a wajensa.

Sai ihu take yi, Aseef kuma ta bashi haushi, yana tsaka da tunanin lahiransa zata zo tana ƙoƙarin saƙe ɓata mishi duniyar nasa ma baki ɗaya, idanunsa sun rufe ya zaro belt ɗin wandonsa ya hau jibganta kamar an aikosa. KU DAGA GANI KUNSAN BA IYA YUNKURIN YI MISHI DA TA YI BANE YASA YAKE YI MATA WANNAN ƊAN ISKAN DUKA, DA AKWAI WATA A KASA, DOLE AKWAI ABIN DA YA TAƁA HAƊASU YASA YAKE JIN HAUSHINTA HAR HAKA.

Jin kukanta yasa mutanen gidan suka fito, ganin abin da yake faruwa yasa Madam matar His excellency ta ɗauko waya ta kira His excellency dan yazo ya ceci Jessie. Ko da shi ma ya zo bai iya karɓar Jessie ɗin ba, dan Aseef ya rufe ido sosai ta ko'ina yake kai mata duka, duk wanda ya yi gigin tinkararsa shima zai samu rabon nashi bulalar.

Waya His excellency ya ɗauko dan ya kira Lion, shi kaɗai zai iya dakatar da Aseef, ko da ya kira Lion ɗin da farko ya ce to ya kashe ta mana shi ina ruwansa, yasan idan da bata je in da Aseef ɗin yake ba, ba zai kamata ya daka ba, sai dai His excellency ya yi ta lallaɓa shi sannan ya ce a bawa Musharraf wayar, cikin sauri suka miƙawa Musharraf, a nitse ya karɓa tare da karawa kunnensa.

Magana na minti ɗaya Lion ya yi wa Musharraf ɗin kafin ya ce su sanya mishi wayar a hand-free, ba musu suka sanya wayar. "My pleasure". Ya furta a nitse, cak Aseef ya tsaya tare da juyowa yana bin wayar da kallo, sai sauke uban haki yake yi tamkar wadda ya ci uban gudu ya ƙoshi.

"Ku koma gida". Shi ne abin da Lion ya sake faɗa daga nan ya katse kiran, jefar da belt ɗin hannun nasa a tsakiyar palon ya yi tare da tahowa ya rungumi Musharraf kamar shi aka daka, hannunsa Musharraf ya riƙe suka fita daga palon, binsu da kallo His excellency ya yi, dama ya kira shi ne a kan zancen Jessie ɗin, ya kira shi ne a kan yazo ya ganta su shirya kansu, ga shi ya zo ya mata shegen duka kamar an aiko shi, dama daga jin yadda ya ce mata ke jeki gayawa His excellency ina nan, daga nan ya kamata kusan haushinta yake ji, abin ku da farar fata musamman ma fatar mace ba kwari, duk jikinta ya yi ruɗu ruɗu na zanen belt ɗin, ta yi wani jawur da ita kamar ka taɓa jini ya fallatsa, tamkar ruɓaɓɓen jan tumatir, sai hakuri mutanen gida suke bata, His excellency yasa aka kwasheta zuwa asibiti dan a dubata.

Su kuwa suna fita kai tsaye wajen motarsu suka nufa, a mazaunin passenger ya buɗewa Aseef akan ya shiga, shi kuma ya shiga mazaunin driver dan ya jasu.

"Uncle Hossain ka dawo nan bari na tuƙamu ko?". Yana magana yana haki kamar wadda ya yi gudu. "No Aseef Saif ya ce ni na tuƙa motar, dan haka kawai ka bari na tuƙa mu zuwa gida ko?" "Uncle daman ka iya mota ne?". Gyaɗa mishi kai ya yi tare da kunna motar suka bar gidan, suna tafiya a hanya yana bashi labarin rayuwarsa na Nigeria, har takatar shigaban kasa da ya nema da sauransu, abin da ya faru da shi na rabuwarsa da su Abba da kuma abin da ya faru da shi na rabuwarsa da su Rimsha ne kawai bai gaya mishi ba.

Har suka isa gida suna hira, Aseef har ya mance da ya jibgi Jessie,. Suna shiga gida bayan sunyi parking a parking space, a tare suka karisa cikin palo har zuwa bedroom nasu, a nan ne kowannensu ya wuce toilet nasa dan ya yi wanka.

Kusan a tare suka fito daga wanka, dukkansu pajama suka sanya, da yake shi ma daddyn Rimshan ba wani ƙiba ne da shi ba, duk dai irin zubin turawan ne, sai pajama ta yi mishi kyau over.

Saman gado suka haye Aseef ya ɗauko littatafan addini dan su cigaba da karatu, ba musu Musharraf ya cigaba da koya mishi karatu yana kara gaya mishi girman Allah, shiru ya nitsu yana saurara.

WANNAN KENAN ABIN DA YAKE FARUWA A WASHINGTON DC, BARI KU LEƘA NIGERIA GIDAN LION MU GANI ME YAKE FARUWA.

GIDAN LION💋

Yau dai Rimsha a ɗakin Lion saman sofa ta kwana, Areef, Lion suna kan gado, da alama sun mance da ita gabaɗaya.

Ita kuma Akila ta yi hiranta da masoyin ɓoye har barci ya ɗauketa, bata damu dan Rimsha bata dawo ba, dan ita bakuwa ce bata san yanda tsarin gidan yake ba, ta yi zaton ma sai tsakiyar dare Rimshar ke dawowa, yau ta yi barci da wuri, bata kai karfe 9 ba, barci ya saceta wayar na gefenta, ba dan masoyin nata ya so ba ya rabu da ita ta yi barcin.

A bangaren Imran kuwa, bayan ya yi wanka ya shirya shirin barci ya kwanta tare da jawo wayarsa ya kira number daddyn Jelly dan ya yi hira da matar tasa, amma ina number a kashe, mamaki ne ya kama shi, a ransa ya yarda cewa ita ta kashe wayar, yasan tabbas wayar tana hannunta, kuma kaɗan daga aikinta, yanzu wani abin take shiryawa kenan.

Bai damu ba ya ajiye wayar a gefensa ya ce zuwa anjima zai sake kiranta. Bai kai karfe 10 ba barci ta yi awon gaba da shi ba tare da ya shirya ba.

Can cikin barci, har tsakiyar kansa ya tsinkayo ringing ɗin wayar tasa, ɗan motsawa ya yi tare da ɗan juyawa kaɗan, kira ta farko ta katse ta biyu ta sake shigowa, a hankali ya waro idanunsa yana kallon saman ɗakin, idanun nasa sun yi jawur dasu saboda barci bai ishe shi ba.

Miƙewa ya yi tare da salatin annabi kafin ya ɗaura da addu'ar tashi daga barci, a hankali ya zura hannu ya ɗauko wayar tasa, ya kawota daidai saitin fuskarsa.

Ganin number daddyn Jelly ne yasa ya ɗan washe idanunsa tare da kai kallonsa kan time dake jikin wayar, karfe shabiyu da rabi, ɗan zaro idanu waje ya yi, kafin ya yi picking call ɗin kiran ta katse.

A gaggauce ya bi kiran, bugu ɗaya ta ɗauka, manna wayar a kunnensa ya yi, ban da sautin kukanta babu wani abin da yake tashi daga ta cikin wayar. Hankali a tashe ya miƙe zaune tare da yaye bargon da ya lulluɓa, bawan Allah har haɗe kalmomi yake yi wajen tambayarta me yake faruwa, me aka yi mata? Kara rushe mishi da kuka mai sauti ta yi, har da shessheƙa.

Bai san lokacin da ya diro kasa daga saman gadon ba, cikin matsanancin tashin hankali mara misaltuwa yake kara tambayarta menene ya faru? Ina daddy yake?, Ina su Abbi? Wani abu ne ya same su?.

Cikin kuka ta ce "Yaya Imran ni kazo yanzun nan, idan ka ɗan jima kaɗan mutuwa zan yi". "Subhanallah to naji zanzo yanzu, amma menene yake faruwa? Ina daddy? Wani abu ya same su ne? Idan baki gaya mini ba ba zan iya tuƙi ba WLH, hankali ba zai taɓa kwanciya ba".

Kara sautin kukan nata ta yi tana faɗin "Kai dai kazo yanzu mana, idan ba haka wlh zan mutu, wayyo mummyna, nashiga ukuna na lalace".

A firgice ya fita daga ɗakin, ko kashe wayar bai yi ba, tunaninsa kuma bata bashi cewa ya kira Abbi ko zai san me yake faru ba, ta rigada ta kiɗima shi sosai, Bawan Allah. Har ya kai tsakiyar palon sama, sai ya juyo ya dawo dan ya ɗauki key ɗin motarsa.

A gaggauce ya fice daga ɗakin bayan ya ɗau key ɗin, kai tsaye bakin gate ya nufa, gateman yana zaune a bakin aikinsa, cikin fitar hayyaci ya bashi umarnin ya buɗe mishi gate, ganin yanayin da yake ciki yasa gateman ɗin ya yi wa Lion massage akan Prof zai fita kuma ga yanayin da yake ciki, da yake sam Lion bashi da nauyin barci har cikin tsakiyar kansa ya ji shigowar saƙon, sai dai bai duba ba, saboda idan baku manta ba, baya haɗa abu biyu lokaci guda, baya aikin kaza lokacin kaza, yanzu lokacin barci ne, dan haka babu wani abin da zai duba kuma.

Shi kuma Imran cikin motarsa ya wuce tare da kunnata, ganin Lion bai yi mashi reply bane yasa gateman ɗin ya buɗe wa Imran ɗin gate, saboda duk wanda yake tare da Lion yasan shirun shi ma magana ce, baya shiru babu dalili, haka zalika baya magana babu dalili, a nasu faɗen idan har baya son Imran ya fita zai yi musu reply da su hana shi fita, idan ya yi shiru kuma yana nufin su barshi ya fita kenan.

Kai tsaye gidan Abbi ya nufa, wani irin mahaukacin gudu yake shararawa a kan titin nan, har lokacin bai katse kiran ba, ita ma bata katse ba, tana jin duk abin da yake yi.

Cikin ƙanƙanin lokaci ya isa gidan, horn ya fara zubawa ba ɗaga kafa, ba ƙaramin tsorota mai gadin ya yi ba, da sauri ya taso har yana haɗawa da gudu ya zo ya buɗe mishi gate ɗin.

A gaggauce ya danna hancin motar cikin gidan, ya kasa karisawa parking space na gidan ma, a tsakiyar gidan ya paka motar tare da fitowa da gudu, Allah ma yasa ya iso lafiya, kuma da yake darene babu motocin sosai a kan hanyan, da rana ne sai Allah kaɗai yasan me zai faru a irin yadda ya fiton nan, ga uban gudu da ya rinƙa shararawa.

Kai tsaye cikin palo ya nufa, da mamakinsa sai ya ga kofar palon a buɗe, ba ɓata lokaci ya afka ciki kawai, sai haki yake yi bawan Allah.

Wani irin birki ya ja ya tsaya turus yana ganin ikon Allah, zaune take saman sofa tana shan ice cream, kayan barci ne doguwar riga zuwa gwiwarta a jikinta, a wannan daren take shan ice cream mai uban sanyin nan, ta tsantsara make up kamar ba ita ba, sai tashin kamshi take yi, ta yi kyau sosai da sosai.

Ganinsa yasa ta ajiye ice cream ɗin ta nufe shi da sauri tana faɗin "Haba yaya Imran rabon da na ganka tun yaushe?" Ta kai karshen maganar tare da faɗawa a saman kirjinsa tana turo baki. Tabbas ya yarda da maganar daddynta da yake cewa idan ka biyewa jelly, in bata kasheka ba, to zata haukata ka, yanzu wannan abin da ta yi mashi da yazo da karar kwana ai da shikenan sai dai a kwashi gawarsa, dubi yadda ya rinƙa sharara gudu a kan hanya, ba dan Allah ya tsare ya kawo shi lafiya ba ai da wani zancen ake yi yanzu ba nashi ba, zuciyarsa sai harbawa da sauri sauri take yi, da mai ƙaramin zuciya ne ma bugawa zuciyar tasa zata yi.

A kule ya ce "Me yake faruwa kika kirani kina kuka?" Ba ko ɗar ɗar ta ce "Kewa mana, kewarka nake yi, wlh har ciwo zuciyata take yi mini, ka daɗe fa baka zo gidan nan ba, me nayi maka da zaka hana ni ganin fuskarka da kai kanka? Sai dai kayi ta kirana a waya ko?".

Haushi tamkar ya sakar mata mari, amma ba komai zai yi mata abin da ya fi mari zafi, ya lura idan ba mai da ita cikakkiyar mace ya yi ba, ba zata taɓa yin hankali ba, zata yabawa aya zakinta yau wlh, ba tare da ya yi magana ba ya ɗauketa suka nufi waje, bata tambaye shi ina zai kai ta ba, sai ma kwanciya da ta yi a kirjinsa.

Kai tsaye cikin motarsa ya sanyata a gidan gaba, har lokacin bata tambaye shi ba, shi ma bai yi magana ba, da gudu ya figi motar suka bar gidan suka nufi gidan Lion, matsowa ta yi ta kwantar da kanta a saman kafaɗarsa tana lumshe dara daran idanunta tare da shaƙar kamshin jikinsa........

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️


E15-16



Kai tsaye cikin motarsa ya sanyata a gidan gaba, har lokacin bata tambaye shi ba, shi ma bai yi magana ba, da gudu ya figi motar suka bar gidan suka nufi gidan Lion, matsowa ta yi ta kwantar da kanta a saman kafaɗarsa tana lumshe dara daran idanunta tare da shaƙar kamshin jikinsa.

Su Abbi kuwa, suna can suna barci basu san me yake faruwa ba.

Wani irin daddaɗar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da kai hannunsa yana shafo kanta yana tuki da hannu ɗaya, rage guduwar motar ya yi dan kada a je a sami matsala.

"Yaya Imran Allah nayi kewarka fa sosai, ka kai sati baka zo gida ba, kullum sai ka rinƙa cemin zaka zo zaka zo, amma shiru, yau dan ban san in da kake bane da sai na je na same ka". Allah sarki da iya gaskiyarta take kaunarsa kamar yadda yake kaunarta, bayan daddynta shi ne mutun na biyu da yake cikin zuciyarta, shi ne ko da yaushe yake ce mata zaizo zaizo kuma baya zuwa ɗin, shiyasa yau ta yi mishi wannan tsiyar dan ta samu ganin shi.

"Haba jelly shi ne zaki yi mini irin wannan wasan? Idan da wani abin ya faru da ni fa? Kin san a wani hali na baro gida kuwa? Kin san halin da kika jefani kuwa? Kin san da ya na kariso gidan bappa kuwa? Gaskiya bai kamata ki yi mini haka ba, kuma ko da sunan wasa kada ki sake yi wa wani haka, ba iya ni kaɗai ba, kowa da kowa kada ki sake yi mishi irin wannan wasa, babu kyau, zaki iya sanya mutun ya mutu ko ya suma kin ji ko?". Ya yi maganar cikin sanyin murya, yasan yarinta ce ke damunta, kuma ya haɗu da kaunarsa da take yi, nan take ya ji zuciyarsa ta yi sanyi, saɓanin ɗazun da yake jin haushinta, yake kuma jin zuciyarsa na tafasa kamar zata faso jirjinsa ta ɓullo waje.

Rungumo shi sosai tayi tare da manna mishi kiss a kumatu tana faɗin "To yaya Imran ba zan sake ba, amma kai ma dan Allah kada ka sake kin zuwa na ganka, idan kayi mini hakan Allah zan yi kuka".

Horn ya yi a bakin gate ɗin gidan Lion yana shafa kanta, kasa kasa ya ce "Ba zan sake ba, yanzu ma aiki ne ya yi mini yawa yasa ban zo gareki ba, amma badan haka ba ai kema kin sa dole na zo wajen matata ko? Kin san fa ina masifar kaunarki, dole na kai kaina gareki farincikina". Murmushi ta fara yi mishi tana turo ɗan bakin nan nata kamar na daddynta, daidai lokacin gateman ya wangale mugu gate ɗin.

Cikin natsuwa ya kutsa hancin motar cikin gida, kai tsaye parking space ya nufa. Bayan ya kashe motar ne ya juyo suna fuskantar juna. "Wannan kwalliyarfa?" Ɗan turo baki tayi. "Yaya Imran dan kai mana nayi, Aunty ce ta koya mini, dama nasan idan na kiraka zaka zo ne shiyasa nayi maka kwalliya idan kazo ka gani". Ba ƙaramin daɗi ya ji ba, hakan yasa ya jawota jikinsa sosai tare da rungumeta da kyau.

"My jelly ina matukar kaunar ki, ina son ki matata, ba'a son raina nayi nisa dake ba, kullun cikin tunani da kuma kewarki nake, bana taɓa jin farinciki har sai na kalli hotonki, wai baki gani bana iya barci da daddare har sai na ji muryarki ne?" Shigewa jikinsa da kyau da kyau ta yi, a shagwaɓe ta ce "To yaya Imran ai nima kasan ina sonka ko?". Jinnina mata kai ya yi alamar e.

"To tashi mu shiga ciki muje ɗaki ki kwanta a jikin nawa sarkin son jiki". Dariya ta yi tana ɓoye fuska na rashin kunya.

Buɗe kofar motar ya yi tare da zuro kafafunsa waje, ita ma miƙewa ta yi daga jikin nasa ta buɗe nata kofar ta fito waje.

Hannunta ya kama suka wuce cikin gida, sai zuba mishi surutu da shagwaɓa take yi, tun baya biye mata har ya fara biye mata.

Suna shiga ɗaki ta sake shi ta haye


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login