Showing 345001 words to 348000 words out of 359620 words

Chapter 116 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2048

ɗin yana tsaye. Ɗan zaro idanu ya yi yana kallon shi. Shi kansa da kallon farko ya ɗauka Aseef ne, sai da ya kalle shi da kyau ya fahimci ba Aseef ɗin ba ne, amma ba karya sun yi kama na wuce misali. Kawar da kansa ya yi tare da miƙa mata hannu, da sauri ta taho ta faɗa jikinsa.

Na san za ku so jin me ya je ya yi a sama, to ku saurara, binsu ya yi ɗaki ɗaki ya yi musu ɗaurin goro tare da ɗaure musu baki kamar an aikosa, kamar wasu kaji haka ya yi musu, harta tsofaffin wato yayyun Naurat ɗin bai bari ba, cikin dabara da salon iya aiki ya yi musu hakan ba tare da ya sami wata matsala ta sun yi mishi ihu ko makamancinsa ba, yakin sunkuru ya yi musu. To shi ne abin da ya je ya yi a saman ya dawo, yasan idan suka tafi da Rimsha tsab zata yi ihu ta tona mishi asiri, shiyasa ya bar Brady a mota. Idan taga ya toshewa mutun baki kuka zata fara yi, shi ne yasa ya barta a kasa tare da Mark, ya san waye Mark, haka kawai Allah ya sanya mishi kaunar Mark ɗin a cikin zuciyarsa, baya yarda da kowa, amma Mark yana da kusanci da zuciyarsa sosai, yana jinsa sosai a ransa.

Massage ya yi wa sojojinsa a kan su shigo dan su fito mishi da kowa dake cikin ɗakunan da ya bi ya ɗauresu kamar kajin nan, ya san idan ba haka ya yi musu ba, to wlh ba za'a sami fahimta a tsakaninsu ba, za su iya kira mishi sojoji su tada yaki a tsakaninsu, shi dai baya barin ko ta kwana, idan aka kawo mishi wargi to fa zai yi ba dai'dai, kuma kakansa His excellency ya ce ya bi komai a hankali har ya shiga ya fito, babu wata hukuma da zata tare shi dan ya shirya musu makarkashiya, dama kuma kunsan kasar America gwana ce wajen shirya shiryen sheyen abubuwa, to shi ne yasa ma kuka ga ya shigo kasar lafiya lou, kuma shi ne yasa ya ɗauresu dan ya yi komai a tsanake.

Ɗaukarta cancak ya yi suka koma saman. Bai zame da ita ko'ina ba sai ɗaki na karshe a sama bakiɗaya. Da akwai key a jikin kofar, dan haka sai ya murɗa ya buɗe.

Bakinsa ɗauke da sallama suka shiga ciki. Jin sallama yau a gidan GENERAL TRUMP ne yasa a hanzarce ta ɗago kanta. Tana daga zaune saman bed ta kifa kai da gwiwowinta, da alama tana cikin tsananin damuwa.

Dattijuwa ce, amma da yake jikin Turawa baya saurin nuna tsufa, suna da jiki mai kyau, sai tsufanta bai wani bayyana ba, idan ka ganta zaka ce 35 years gareta, gata kuma da ƙaramin jiki mai shegen kyau. Kyakkyawar gaske ce, fara tas tamkar ka taɓa jini ya zuba, ga dark black curly hair har bayanta a kwance. Ashe ita Rimsha ta ɗauko a gashi.

Tsawon shekaru 33 tana kulle a cikin wannan ɗaki, ko waje bata leƙawa, babban yayansu wanda Lion ya fara ɗaurewa yanzu shi ne ya rufeta a cikin ɗakin, suna azabtar da ita a kan lallai sai ta dawo kafura ta fita daga addinin Musulunci, ita kuma ta ce sai dai su kasheta, amma wlh ba zata yi ridda ta zama krista ba, ta rigada ta musulta kenan, bata ga wanda ya isa ya mai da ita krista ba, shi ne suka rufeta, abin ci ne kawai yake sanyawa suke buɗeta. Duk kudin nan nasu dan bakin mugunta sau ɗaya suke bata abinci a rana, ruwa ma ɗan kaɗan suke bata, ta azabtu matika na tsawon waɗan nan shekaru, amma duk da haka bata ji kamar ma zata iya fita daga cikin addinin musulunci ba, sun hanata hijabi dan kada ta yi sallah, amma a hakan sai ta yafa wani abin ta yi, dai'dai da rana ɗaya lokacin sallah bai taɓa wuce ta ba.

Daga karshe dai suka hakura suka barta a cikin ɗakin rufe kawai suna bata abinci sau ɗaya. Naurat ta sha bakar wahala sosai a rayuwarta, tasha na Amarya a Nigeria, ta kuma sha na ƴan uwanta a nan, ita da ta taso ƴar gata sosai, saboda su uku ne kawai mata a cikin yaran GENERAL TRUMP goma sha uku, goman dukka zaratan maza ne, su uku ne mata, da ita da kannenta mata biyu wanda su basu zaune a Russia ma, tun asali a America suka yi karatu, so suna can da zama basu dawo nan ba har yanzu, ita kaɗai mace ta rayuwa da daddynta, ya yi mata gata fiye da tunanin mai tunani kafin ya mutu ƴan uwanta maza su cigaba da kula da ita, haɗurwarta da Dr Salman a shopping ya fara canza komai, shi ne kuma mafarin wahalarta har zuwa yanzu.

Karisowa cikin ɗakin ya yi tare da sauke Rimsha kasa. A gefen bed ɗin nata kusa da ita ya zauna, haka kawai Allah ya sanya mishi kaunar dattijuwan nan har cikin ransa, musamman idan ya tuna irin gwagwarmayar da ta sha a kan cewa ba zata bar addinin musulunci ba, sai ya ji ya kara kaunarta over. Cikin harshen turanci ya fara yi mata magana a nutse.

Ya gaya mata ɗaukarta ya zo yi su koma Nigeria. Kin yarda da shi ta yi, duba da shi ma Bature ne, kafewa ta yi a kan cewa ita bata san Nigeria ba kuma bata da wata alaƙa da Nigeria. Baiwar Allah muryarta ma da kyar yake fitowa saboda jimawa da ta yi bata magana da kowa.

Da hannu ya yi wa Rimsha alama a kan ta zo, da sauri ta kariso kusa da shi ta zauna. Dama kamar yasan Na'urat zata yi mishi gardama, shi ne yasa ya taho da Rimsha, idan baku manta ba da Jehan ya so zuwa ma, dan ita ce mai kama da daddynta, a wani ɓangare kuma yana son zuwa da Rimsha dan launin fatarta irin nasu family'n Dr Salman, yanda Na'urat ta sha wahalar nan baya jin kamar zai yi mata dole a rayuwarta, shi ne yasa yake binta a hankali.

Cikin sanyin murya ya sake gaya mata da gaske shi ba cutar da ita zai yi ba, tafiya da ita ya zo ya yi dan ya mayar da ita cikin ƴaƴanta, hakan ce ma tasa ya zo mata da jikanta ƴar Nawazudden ɗinta dan ta shaida, ya san cewa ko zata manta kowa, to ba zata manta Nawazudden ba, dan shi ne ɗa mafi soyuwa a gareta. Ai kuwa duk kin yarda da ta yi da shi, jin ya ambaci sunan daddyn Rimsha sai da ta ɗago sosai tana kare musu kallo, sai dai fa ita a yanayin yanda take kallon face ɗin Lion da ƴan uwanta na nan yake yi mata kama, amma ganin Rimsha yasa ta ji ta yarda da su, duk da cewa Rimsha bata wani kama da daddyn nata, sai dai kama ta jini, da mum take kama.

Kara yi mata bayani ya yi a nutse dallah dallah yanda zata fahimta, yanda kuma rikicin tsufa ba zai sanya ta kasa ganewa ba. A takaice dai ya yi babban sa'a ta yarda da shi dalilin Rimsha, dan haka sai ta amince zata bishi. Ya ji matuƙar daɗi sosai, shi da kansa ya taimaka mata ta miƙe tare da saukowa kasan bed ɗin. Sai murna Rimsha take yi yau ta ga kakanta mai tsananin kama da daddynta.

Riko hannunta Naurat ɗin ta yi tana ji tamkar hannun Nawazudden ta rike, tana bala'in kaunar daddyn Rimsha da daddyn Anaya, tafi sonsu sama da kowa a cikin ƴaƴan nata.

A hankali suka fito palo, nan ya iske kowa na gidan, gabaɗayansu sojojin sun fito da su sun zube su a palon. Sun yi mugun bashi haushi ne na izayar da suka rinƙa yiwa ƴar tahalikan nan na tsawon shekaru, ya so ne ma ya yanke wa kowannesu koda kunne ɗaiɗai ne, amma kuma yana sauri, dan haka sai ya kyale su kawai.

Har ya kai bakin kofar palon rike da hannun Naurat ɗin ita kuma tana rike da hannun Rimsha. A hankali ya juyo ya ce da Mark ya kwance Alex da shi zasu tafi.

Cikin girmamawa Mark ya ce yana neman alfarma Lion ya yi hakuri ya sanya a kwancesu, dan saboda uncles nasa ne, ƴan uwan daddynsa ne, dukka ya sansu ta cikin hoto, yana da hoton kowannansu, Alex ɗin ne kawai dama suke waya da shi, kuma Mark ɗin ne ya nemo number Alex ɗin dalilin wannan zuwa da za su yi.

Shiru Lion ɗin ya yi yana mamakin, Allah mai iko, yau dai ga Mark a cikin family'nsa, Mark ɗin ma jikan gidan ne kamar dai su Rimshan.

Jinjina mishi kai ya yi yana faɗin, ya barsu idan sun tafi za'a kwancesu, dan sun ɓata mishi rai fa. Haka ba dan ya so ba ya kyalesu, ya kwance iya Alex ɗin kawai sojojin suka sanya shi a gaba suka bar palon.

Wani karfin hali sai wajen Lion, ya shigo har cikin kasarsu, kuma cikin gidansu, ya kuma ɗauki ƴar uwarsu da suka rufe tsawon shekaru, kuma a gaban idanunsu, ya kuma sa kafa ya fita, ba yanda suka iya da shi, wato a duniya idan kai wani nema fa ka ji daɗi, idan kana da goyon bayan manya daga sama ba abin da ba zaka aikata ba, kuma ka zauna lafiya, Allah ya yi wa dukkanin musulman duniya bakiɗaya arziki mai albarka mai kuma amfani.

Koda bodyguards na gidan suka gansu, ko sannu basu ce musu ba, dan sun ga da ɗan gida suke tare, ga kuma Naurat, sai dai abin mamaki Alex ya kasa iya gayawa bodyguards ɗin abin da yake faruwa a cikin gida dan su hana su Lion fita, ya rasa ya akayi bakinsa ta yi mishi muguwar nauyi.

A takaice dai haka suka sake fita daga gidan cikin waƴan nan motocin da suka zo ɗin, suka koma cikin jirgin ruwansu.

Ba ɓata lokaci suka ɗauki hanyar komawa gida. Naurat a ɗakinsu ta zauna, dan ya kula da ita, yana jin tsantar kaunarta a ransa.

After some hours. Bayan sun kama hanyar ne, jirgin ruwan nasu ya tashi, a nan ne yasa Mark ya turo mishi Alex. Har cikin ɗakin nasu Alex ɗin ya zo, saman sofa ya ce mishi ya zauna, ita kuma Naurat tana zaune saman bed nasu, Rimsha ta tada kai da cinyarta tana mai jin tsantar farinciki. A saman bedside drawer shi kuma Lion ɗin ya zauna.

❤️PRINCESS TEEMA💋......✍️

A nutse ya fara magana cikin harshen turanci, a in da ya gayawa Brr Na'urat cewa Alex fa yaronta ne ba ɗan yayanta TRUMP ba, zaro idanu ta yi tana mai gaya mishi ai ita yaron da ta haifa ya mutu, girgiza mata kai ya yi yana faɗin. "A binciken da nayi bai mutu ba, karya suka yi miki da ya mutu dan ma kada watara ya zo kawo miki abinci ki gaya mishi kece mamansa kuma ya musulta, shi ne yasa suka ce miki ya mutu, amma Alex ɗan ki ne, shi ne wanda kika baro Nigeria ba tare da kin san kina da cikinsa ba, sai da kika dawo nan da watanni kika san da hakan, so ba Abdul Malik ba ne autanki, Alex ne!." Babbar magana, zancen Lion gaskiya ne, bayan Naurat ta haifi cikin da daddyn Rimsha ya barota da shi, wato cikin daddyn Jelly, yana da shekara ɗaya da rabi a duniya sun sake samun kyakkyawar alaƙa da Dr Salman, da alama a lokacin asirin da amarya ta yi mishi ne ya karye, sun kowa kamar da, suna soyayya tare da kula da yaransu, suna kuma neman daddyn Rimsha, a lokacin shi kuma daddyn Rimshan yana Niger tare da abokinsa. Bayan wata uku da samun jituwar tasu suka sake komawa gidan jiya, faɗa kullum kullum, a lokacin ne kuma amarya ta karo sabon walaƙanci a in da ta mayar da Naurat ɗin ƴar aikinta, ganin ba zata iya jurewa ba ne yasa ta kira yayanta TRUMP a waya wato wanda aka ce shi ne mahaifin Alex yanzu, shi ne suka zo suka ɗauketa ta baro daddyn Jelly a hannun su Abba yana yaro, bai gama cika 2 years ba lokacin, sam bata san da shigar cikin Alex ɗin ba a lokacin, dan lokacin cikin bai kai ko wata ɗaya ba.

Sai bayan ta koma Russia ne da ƴan watannin da ba su yi biyu ba, nan ta fahimci ciki ne da ita, a lokacin kuma tana shan azaba wajen ƴan uwanta, wanda hakan ya zama tana danasanin biyosu, dan fa mugaye ne kuma mafaɗata ne na karshe, basu da sauki ko kaɗan ga zafin ran bala'i, ta ce gara mata gidan Dr Salman sau dubu a kan abin da ƴan uwanta suke yi mata dan taki yin ridda. A takaice dai haka ta yi rayuwa cikin kunci har cikin Alex ya girma, lokacin da take nakuda ba wanda ya kulata a cikinsu sai matar kaninta ɗaya, ita ta taimaka mata har ta haihu, bayan ta aihu ne kuma suka zo suka ɗauki yaron, after some minutes suka dawo suka ce mata ai ya mutu saboda bata je asibiti ba, alhalin karya suke yi mata, basu so ne ta koyawa yaron addinin musulunci. Haka suka reni Alex cikin so da kauna a in da da ya taso suka ce mishi ai yayan Naurat ɗin shi ne babansa, shi kuma ya tafi a hakan, basu barin shi yana kai mata abinci, kowa zai kai mata abinci a gidan amma banda shi, dan sun san uwa da ɗa ba wasa ba, wani lokaci ma dan walaƙanci barinta suke yi ta kwana da yunwa sai su ce sun manta ne da ita yasa basu kai mata abinci ba, izaya kala kala suka rinƙa yi wa ƴar tahaliƙan nan, sai dai Allah ya saka mata kawai.

Daga ita har Alex ɗin sun rasa bakin magana, Allah sarki yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa ma Alex ɗin ya kasa gayawa bodyguards ɗin sacesu su Lion za su yi, uwa ba wasa ba, yau Allah ya ƙaddara ne zai gane ba Trump ba ne babansa. Sosai ya rinƙa kuka da hawayensa, sai tunanin irin izayar da suka rinƙa yi mata ya fara yi, ya ma kasa ɗaga idanu ya kalleta tsabar shiga tashin hankali da damuwa ga kuma murna a gefe. Kifa kansa kawai ya yi da jikin sofa yana kuka. Ita ma Na'urat ɗin kuka take yi sosai, ƴan uwanta sun cutar da ita sosai, yanzu ace ɗanta na cikinta ne ya taso a krista tsawon shekaru? Bai san komai ba dan gane da addinin babansa, wannan abin ya yi mugun yi mata zafi. Amma fa kuma abin mamaki shi ne, Alex ya fita daban a cikin ƴaƴan TRUMP ɗin, shi ne yasa ma wani lokaci yake jin kamar ba su ne iyayensa ba, na farko yana da kirki sosai shi, jinin Hausa Fulani Bauchi state kenan, wato Dr Salman, yana da son mutane da saukin kai, yana da fara'a tamkar Dr Salman, wani lokaci idan aka taɓo shi yana da zafin rai, sak da ainahin babansa, so abin yana bawa su ƴaƴan TRUMP ɗin ma mamaki, sai dai duk cikin ƴaƴan Brr ɗin babu wanda ya kai Alex ɗin fitowa sak Turawa babu mix, sak kakansu GENERAL TRUMP wato mahaifin Naurat kenan.

Shi dai Lion ya yi shiru yana kallon yanda suke ta shan kuka dukkansu, ita ma Rimsha ta yi hawaye sosai na jin wannan labari nasu mai taɓa zuciya, mutun mahaifiyarsa tana raye amma dan bakin zalinci an hana ta bashi nono? Aka rinƙa ɗirkawa bawan Allah madara, Allah sarki, wlh zalinci bai yi ba, duk abinsu dai yau ga shi ya haɗu da mahaifiyar tasa, kuma da izinin Allah sai ya musulunta, bakinciki ya kashesu.

Sun sha kuka kamar ba gobe, shi dai Lion bai iya ce da su komai ba, bai ma san me zai ce musu ba, haka ya zuba musu idanu suka yi kukan har ya ishe su. Sannan Alex ɗin ya mike ya dawo kusa Brr.

Mikewa Rimsha ta yi daga saman cinyar tata ta bashi waje. Yana zuwa ya rungumeta yana jin tamkar ya koma ya kashe uncles nan nasa bakiɗaya na irin izayar da suka yi mata, zuciyarsa sai tafasa yake yi tamkar zata fashe. Rungume shi Brr Naurat ɗin ta yi tana rarrashinsa har sai da ya yi shiru. Miƙewa Lion ya yi tare da riko hannun Rimsha suka bar musu ɗakin zuwa na kusa da su, dan su basu dama su tattauna. Shi ma Lion ɗin yana son ya yi sallar azahar dan lokaci ta yi.

Rimsha tamkar zata yi kuka haka ta biyo shi, sam bata son rabuwa da kakanta, amma ba yanda ta iya. Suna shiga cikin bedroom ɗin ya saki hannunta tare da nufar toilet. Zama ta yi a saman bakin bed ɗin tana jiran shi ya fito. Wanka ya yi tare da ɗauro alwala ya fito. Ganin face nata a ɗaure tamau ne yasa ya ce lafiya take wannan ɗaure fuska, turo baki ta yi tana faɗa mishi ita wajen kakanta take son zuwa, da hannu ya nuna mata hanyar tafiya. Da sauri ta miƙe ta fita, har ta kusa kifawa saboda sauri. Shi kam ko a jikinsa, dadduma kawai ya ɗauko tare da shumfuɗawa dan ya gabatar da sallah.

Tana zuwa ta sami sun gama shan kukan suna tattaunawa, hayewa saman bed ɗin ta yi tare da komawa ta kwanta saman cinyar Brr. Kallonta Alex ɗin ya yi yana tambayar Brr wace ce ita. A takaice ta bashi labarin su daddyn Rimshan wato ƴan uwansa. Sosai ya ji tsananin kaunarsu a ransa. Shafa kumatun Rimshar ya yi yana mai jin kaunarta ita ma, ƴar autar family'n Dr Salman kenan. Duk familyn Dr ita ce karama, ita ce autarsu, daga ita sai Zaira kanwar Anaya, sannan Jehan da Anaya wanda su shekarunsu ɗaya, ratar ƴan watanni ne kawai.

Shi kuwa Mark yana can yana hira da Anaya a waya, a in da yake gaya mata nan da kwana huɗu zasu dawo dan tafiyar tasu ta canza salo. Sai murna take yi ya ce zai zo gidansu. Shi Mark sam bai san cewa ba za'a bashi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login